← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 64

Sashe 44

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin hangame baki Shatu ta yi ta ƙanƙame idanu kafin ta ce "Don ki ji aure za'a yi mata, a kwarkwaɗa aka kamata da Iro yana mata maɗe shine Baffan Hawwa ya ce aure zai yi mata, daman ko a dandali idan Hawwa na rawa Iro ne yake mata manne, to duk wanda yake manne a dandali alama ce ta yana son ka, shine take ta kuka wai tsoro take ji ni kuma na ce bata da wayo dama ni ce za'a yi wa auren kullum na dinga girki da share gida na gyara bukkarmu idan gari ya waye na gaida mijin sai na dawo gidanmu, da sassafe na koma gidan mijin, kuma ya dinga kawo mini tsaraba na dinga cin abinci ina ƙoshi sosai" Batty ta yi shiru tana tunani da nazarin maganar Shatu kafin ta nisa tace

"Idan akai auren a gidanku kake kwana?" Shatu ta É—an jujjuya taga ba kowa cikin raÉ—a ta ce "Daga safe zuwa yammaci kana gidan mijin idan almuru ya yi sai ka tafi gidan Baffanku saboda babu kyau zama waje guda da namijin shaiÉ—an ke shiga tsakani Inji Innarmu sai kiga an yi miki maÉ—e a yi miki iskar balo ki mutu" Batty ta haÉ—e fuska

Ta ce "Ce Allah?"

"Na rantse masoyiyar"

"To na yarda mutuniyar"

Shatu ta miƙe tsaye tana kakkaɓe jikinta "Muje wajan Innata ta ba ki abinci ki yi kari" ta kama hannun Batty suka nufi gidansu.

*
Tsoron daya gama rikitowa duniyar Iftihal ya gama razanar da ƴar nutsuwar da ta yi mata saura, da kekketa zuciyar data riga ta gama macewa da rauninkan da ƙaddara ta wanzar mata dashi ta haɗaɗɗan rubutun daya samu waje,a inda ba'a rubuta ƙarya na abin da Ubangiji ya wanzar a rayuwar bawa a allon Lauhil Mahfouz. Wannan tsoran ya ɗauke ganinta na wani lokaci kamar yadda wannan tsoran ya saka fitsari sakin kan shi daga cikin mararta, ta jiƙe sharkaf. A firgice ta ce "Na shiga uku....," sai ta kasa ƙarasa maganar saboda wani abu daya tukare mata maƙoshi ko numfashi ta gagara ja da saukewa, hatta iskar dake cikin daƙin a gurɓace take shaƙa, da ɗan ƙarfin da ya yi saura a jikinta ta lallaɓa tana jan jiki zuwa inda Alhaji Baita yake tsaye ya riƙe ƙugunsa tare da zuba mata ƴan iskan idanunsa masu ɗauke da manufofi da yawa. Tana ƙarasawa inda yake ta haɗe hannayenta biyu alamar neman alfarma, alamar dake nuna ƙasƙanci da karayar zuci ta ce. "Idan na ce ka ji tsoron Allah na san na makara, sai dai an ce fazzakir fa'innal zikira tamfa'ul mu'uminun" Ya kalle ta ya ce "Ka tunatar domin tunatar wa tana amfanar Musulmai" ya ƙare da shafa tsakiyar jikinsa daya kwanta ya zame masa kaya. Ji ta yi ɗan raguwar hope da confidence ɗin da suke rage mata sun yi nasu waje ta kuma neme su ta rasa su. A tsakanin mutuwa da rayuwa bata san a wanne ɓangare ta fi ƙarfi ba a yanzu, tana buƙatar ta rayu saboda Mahaɗinta da kuma Innti sai taurarinta Yaa Jaheed da Yaa Jadid da Babban yaya. Tana buƙatar rayuwa ko zata zama silar shiryuwar Daada, ita kam tana son mahaifinta sosai, so mara algus mara kuma wa'adi, idan ta rayu, za ta yi rayuwa ne da wannan soyayyar ko da bai sauya halinsa ba, idan kuma ta mutu zata mutu ne da begen babu shi a tsaginta a yanzu haka kuma har zuciyarta ta yafe masa dukkan wata musgunawa da ya yi wa rayuwarta. Ta kalli Baita ta ce

"Me kake buƙata a wajena?"

Ya ɗan gwame numfashi da ƙoƙarin sarrafa nutsuwar dake shirin kwance masa yace "ke nake buƙata, ki saki jiki kuma ki tsayar da zuciyarki waje guda. Ki kuma zama jaruma"

Ta ɗan dube shi. "Yes, ni mabuƙaci ne a ƙalla zan iya buƙatarki sau biyar haka a rana"

A kiɗime ta ce "Ba zan iya ba, ban ma san mene buƙatar ba, ba zan jure ba, ba kuma zan iya sakin jikin nawa ba ban ma san me kake nufi da kalamanka ba. Duk abin da za ka yi Bisimillah na san Ubangiji yana kallo yana kuma ji ya kuma fini sanin abubuwan da suke yawo a zuciyarka. Duk abin da ya same ni ƙaddarata ce, Innti ta ce bawa baya taɓa shige ƙaddararsa, faman ƙaddarallahu haƙƙa ƙadirihi. Ba wani abu da zai samu bawa face abin da Ubangiji ya hukunta masa" tana faɗin hakan ta yi ƙasa da kanta ilahirin jikinta rawa da ɓari yake yi kamar an jona mata hutar lantarki. Idan abin da Iftihal take ji a yanzu shine daidai bai shige zaucewa da ta yi kamar tunaninta ya yi ƙaura a jikinta, ta amince da ƙudurin Baita, amma zuciyarta ta gaza ɗaukan tashin hankalin da yake neman kunno kai cikin rayuwarta... "Tashi ki cire kayanki"

"Ba zan iya ba" ya buÉ—e ido sosai. Sai kuma ya ce "Ni ina da hannaye har biyu"

Ganin da gaske kayan yake shirin cire mata ya saka ta riƙe hannunsa a ƙyamace ta shiga girgiza masa kai, "kalle ni" rashin sanin rashin kallon nasa shine fa'ida a gare ta aka yi rashin sa'a ta ɗago ta kalli cikin tsakiyar idanunsa, a hankali komai ya shiga warware wa a kanta jikinta ya saki, komai nata ya tafi ya barta babu abin da ya yi mata saura sai tunaninta da raɗaɗin zuciyarta, Allah take kira da Innti da kuma Anarta, abokiyar haihuwarta wacce suka gama tsara kalar rayuwar da za su yi tare daga kan girma, karatu, cigaban da za su kawowa rayuwarsu.

"Ban san me kake shirin yi mini ba" ta ce da ƙyar Idanunta na tsiyayar da hawaye daga gefen fuskarta, ta ƙarasa buɗe idanun da ya yi mata nauyi a fuskarta, ta dubi yadda ya yi mata tsaye a saman kanta, baƙi ne shi sosai, yana da buɗaɗɗan jiki da kuma ƙaton tumbin da yake fara shaida zuwan shi waje, sai jajayen idanunsa da suke manyan gaske wanda yake rambaɗa musu farin ƙwallin da bata san na menene ba. Dole ta shaida kamannin mutumin daya zama silar rusa duniyarta. Ya gyara tsaiwa yana washe mata bakinsa da faɗin "Ki kwantar da hankalinki, abin da zan miki shine abin da kowacce mace ake mata idan ta girma idan an yi mata aure, budurcinki zan ƙarba saboda kin kwanta mini, dalilin daya saka na saka miliyan ashirin saboda makwaɗaicin ubanki ya faɗa cikin cacar na kuma yi sa'ar gaske ya sakaki ni kuma na yi nasara, daman nasara a jinin Alhji Baita take Ƴan'mata. Sai kuma buri na biyu yi, wanda idan na aikata zan samu biliyoyin kuɗi, wani sirri ne da ko matana basu taɓa sani ba, sai abu kaɗan dana shaidawa matata kuma uwargidana wato Jummai, macace azzalumar gaske, mun haɗu da ita a yawan da nake yi na gari-gari har muka yi aure, tana shan taba, sigari, tana kawalcin mata da niyyar samar musu aikin yi sai a buƙe da safarar su zuwa ƙasar waje, ko kuma ta siyar dasu kamar yadda ake siyar da bayi a zamanin baya, ina yi mata aiki na rufe bakin iyayen yara dama su kan su yaran, duk abin da aka ce musu ba za su taɓa bijirewa ba, iyayen kuma ba za su taɓa neman yaransu ba har abada, idan kin ga sun yi magana to na lahira ne ya dawo"

Ya ɗan murmusa yana durƙusawa daidai kan Iftihal da take kwance kamar gawa saboda sakin da jikinta ya yi babu abin da yake motsi a jikinta sai Idanunta da laɓɓanta, kallon shi kawai take yi da fuskar dake nuna tashin hankalin daya gama mamaye rayuwarta da zuciyar dake ƙuntacce a tsakiyar ƙirjinta. Fat! Fat! Haka zuciyarta ke bugawa, bugun da take jin kamar zata yaye fata bakwai dake lulluɓe da ita ta fito zuwa sarari. Ya miƙa hannu kaɗan ya shafi fuskarta ya ce "Sorry fa. Kina ganina kamar bagidajen ƙauye ko irin mutumin ƙawayen da yake da kuɗi amma babu ilimi?"

"...... haka kike tunani ko? You have to think gaskiya ni da kaina tsoran kaina nake yi"

Ta lumshe idanunta ta buɗe a kan shi. "Yeah; when it comes to money gaskiya bani da imani ne ko kaɗan akan hakan. Na yi niyyar na zauna dake ki dinga bani nishaɗi kina ɗebe mini kewa da hutawa a jikinki, haka nan kike birgeni fa Ƴan'mata. Ranar dana fara ganinki aka shaida mini ko biyu ne nazo na buga ƙasa, kuma ƙasa ta shaida mini naso sauya ƙudirina zuwa kan uhm"

Sai ya É—an murza goshinta alamar tunani, a hankali ta dinga girgiza kai jikinta ya shiga rawa, idan wani abu ya samu mahaÉ—inta ba zata iya yafewa kanta ba, duk da cewa basu san wacece babba ba a cikinsu, amma tuni ita ta É—auki girma, Ana da kanta take cewa

"Haƙurinki dabanne mahaɗita, kece yayata zan iya kallon ki a matsayin Innti a lokacin da babu Innti a kusa dani, ke yayata ce ta"

Ƙoƙarin tashi take ta kasa idanunta na zubar da ruwan hawaye ta ce "Karka taɓa mini Anata, ita ɗin rayuwata ce kar ka...," Ya yi saurin ɗora yatsarsa ɗaya a saman laɓɓanta ya ce "Shhhh, duk yadda nake son abu idan na duba naga taurarina dana mutum bai zo ɗaya ma ina haƙura dashi. Ki kwantar da hankalinki babu ruwana da ita"

Ajjiyar zuciya ta sauke a wahale alamar relief. Ya ɗora da; "Bayan matata Jummai na auri Karime, a kanta kuma na buƙaci zama abin da nake a yanzu, me kuɗi kuma bagidaje kuma hatsabibi sirrin manyan ƴan ƙasar nan. Fulani, ita ce sunan aljanar data aure ni a jerin Jinnul Ashqie na mata, ita ta bani umarnin sai na fara kwanciya da ƴata da take shekara shida a haihuwa, ƴar gidan Karime ce, sunanta Anisa, kaf cikin yarana tafi kowacce kyau ita ce fara kamar ka wanke hannu ka taɓa, tun tana yarinya bata da rigima tana da haƙuri gata da farinjini, na taƙaita miki kaf yarana ba wacce nake so sama da Anisa. Sai dai kin san wani abu?"
Chapter 44 · 0% Book details