← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 64

Sashe 53

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaa Sam na ƙoƙarin cilla igiya a cikin rijiyar sai ga Babban yaya ya fito, goye da Iftihal yana fitowa ya saka hannunsa wajan kunce rigar jikinsa wacce ya yaga ya yi amfani da ita wajan goya Iftihal, da hannu ya yi alamar a bashi tabarma, Jaheed ne ya ɗakko ya shimfiɗa, shi kuma ya kwantar da Iftihal akai, kallo ɗaya ya yi wa Iftihal ya ɗauke kai ya miƙe ya ce yana zuwa kar wanda ya taɓa ta, cikin ɗakinsu ya shiga, Ana kasa biyayya ta yi wa maganar Abbaa ta yi saurin nufar Iftihal ta zauna tare da janyota jikinta ta rungumeta sosai tana sauke wata wahalliyar ajjiyar zuciya. Sanda Yaya ya shiga ɗakinsu ya mance da Jadid ya zube akan ƙafafuwansa, gabaɗaya jijiyoyin dake kwance a goshinsa suka firfito, ya zaro harshensa ya haɗe da haƙoran sama dana ƙasa ya datse su da ƙarfin gaske har sai da ya ji ɗanɗanon jini a bakinsa, gabaɗaya jikinsa rawa da ɓari yake yi, baki yake son ya buɗe ya saki kuka sai ya yi saurin ɗora hannunsa a bakin yana girgiza kai dukkan wata jijiya da Ubangiji yake halitta a jikin mutum sai data jikin Yaya ta bayyana, idanunsa ya zama kamar ba nasa ba, ya yi wani irin ja kamar gaushin wuta, ya kasa zubar da hawaye. Jadid ya ji sautin tashin hankalin da Babban yaya ya shiga, amma ba zai iya motsa ko hannunsa ba shima ɗin.

Ana ta sake rungume Iftihal tana sauke ajjiyar zuciya, tana jin wani abu mai kama da relief yana sauka a jikinta sannu a hankali. A hankali ta shiga faÉ—in "MahaÉ—ita"

"Sannu MahaÉ—ita, in sha Allah kin bar gidan mutumin nan, idan ya zama dole zani ni"

"Kema babu inda za ki, babu wanda ya isa ya sake saka mini Æ´a a caca ko waye shi"

Cewar Innti tana riƙe hannun Iftihal gam a cikin nata

Yaa Sam ya yi wa Iftihal ƙuri da idanu zuciyarsa na bugawa.

"Sahibarmu tashi MahaÉ—ita mu koma É—aki"

Daada dake gefe ya ce "Ba dai ɗaki ba, wannan yarinyar sai ta bar gidan nan yanzu" wani irin ƙasƙantaccen kallo Innti ta yi wa Daada, bata ma da lokacin yi masa raddi. Ta juya kan Iftihal ta ce

"Indo,Aysha"

Sai taga bata motsa ba.

Yaa Jaheed ya ce "Ki danna mata ƙirjinta ko ta sha ruwa a cikin rijiyar ina tunanin haka"

Kamar yadda ya ce ɗin, ta saka hannu biyu ta danna ƙirjin Iftihal ta yi har sau uku amma babu ruwan daya zuba daga cikin bakinta ko hancinta. Ƙirjin Innti ya buga ta zubawa fuskar Iftihal idanu, sai taga ta yi mata kyawun da bata taɓa gani ba, fuskarta wasai alamar babu wani tashin hankalin da yake cin zuciyarta, alamar babu wani ciwo ko raɗaɗin da yake damun gangar jikinta. Wani haske fuskar yarinyar ke yi, me ɗauke da annuri. Ta kira sunan Allah a zuciyarta.

"Iftihal É—ita, Ayshatuna, Indota...

"Sannu Iftin Innti, sannu da jiki" ta ce tana sake riƙota sosai

Ana ta ce "Ta farka ne? Ya ba ta yi motsi ba?"

Sai ta É—aga hannun Iftihal tana É—agawa ya koma inda yake sharaf. "Ta karye a hannu" ta sake faÉ—in

"Hannunta ya karye" da sabon tashin hankali ta faɗi hakan jikinta na rawa ta fara ƙoƙarin fita daga hayyacinta. A gigice take girgiza Iftihal tana kiran sunanta. Yaa Sam ya jima da fahimtar abin da yake faruwa, zuciyarsa ta fara rawa na tsananin tausayin Ana ya juya wajan saka hannu yana share hawayen da suka cika masa idanu. Jaheed ko ƙafa ma ya kasa ɗagawa yaja ya cake yana kallon Iftihal kamar zai kira ta amsa masa. Innti ce ta kira Ana tare da faɗin "A'a, bacci take yi kar ki tashe ta kuma ki batta"

"Bacci take yi?" Ana ta maimaita sai ta lumshe idanunta da faÉ—in "To nima zan yi bacci a kusa da ita, Innti nima bacci zan"

Babban yaya ne ya fito ya shiga takawa a hankali, fuskarsa babu walwala kamar ya ce ya shiga uku, wayar daya mance da ita a cikin alijuhunsa ita ce take ta haske, alamar shigowar kira Allah Ya sa a silent take, kuma irin wayar nan ce da ruwa baya kassara su. Bai bi ta kan wayar ba, ya janyo wani zani dake saman igiya, yana zuwa ya durƙusa dai-dai in da Iftihal take kwance a cinyar Ana, ya miƙa hannu zai ɗauke ta. Ana ta girgiza kai ta ce "Ka barta a jikina Abbaa"

Bai kalli ko fuskar Ana ba, balle idanunta ya sake miƙa hannu zai ɗauki Iftihal da ƙarfi

Ta ce "Abbaa.....

"Ina jin kamar zuciyata ce kake janye wa, bar ta a jikina don Allah Abbaa bar mini ita"

Sannu a hankali ya janye hannunsa ya zubawa waje guda idanu, da sauri kuma ya miƙa hannunsa ya zare Iftihal daga wani irin riƙo da Ana ɗin ta yi mata, ganin tana shirin bin Iftihal ya saka Yaa Sam ya yi saurin riƙe ta suka shiga kokawa zata ƙwace. Yaya ya kwantar da Iftihal saman tabarma, ya shiga yin addu'a a hannunsa ya tofa a tafin hannunsa ya shafi idanun Iftihal zuwa fuskarta, ya yi ƙasa da kan shi ya sumbaci goshinta, ya riƙe hannunta sosai kamar kar ya cika alamar ban kwana, ya jima cikin wannan yanayin, ya sake sumbatar goshinta daidai nan hawayen daya cika idanunsa ya sakko a saman fuskarta, a hankali ya ja zanin ya lulluɓe ta gabaɗaya.

"To me ya sa kake rufe ta haka Yaya?" Jaheed ya ce yana girgiza kai domin shima bai fahimci abin da yake faruwa ba.

Ana ta ce "Ya ce bacci take yi, Innti ma ta ce bacci take yi, nima zan kwanta ka rufe ni Abbaa" ta sake yunƙurin ƙwacewa daga hannun Yaa Sam. Miƙewa Innti ta yi ta matsa kusa da Babban yaya ta ce

"Meke faruwa?"

"Allah Ya yi mata rahama....,

Sai Babban yaya ya kasa ƙarasawa ya miƙe gently yana ɗan ja baya ya nufi inda Yaa Sam yake a hankali ta wata laushin murya me cike da kasala, kwarjini da haiba ya ce

"Allah Ya ji ƙan Ayshatul-Iftihal"

Dam! Ƙirjin Innti ya buga da ƙarfi ta ce

"Ta rasu ne Muraad? Na rasa Iftihal?"

Ya jinjina mata kai a hankali.

Cak Ana ta tsaya daga kokawar ƙwace kanta da take yi, ta ƙurawa gawar Iftihal idanu, bata ko blinking eyes ɗinta, ta san mutuwa tabbas, ta san yadda mutane suke faɗar raɗaɗin mutuwa, kuma ta san idan an mutu ba'a taɓa dawowa, mutuwa ɗaya ce, tafarkinta yana da yawan gaske, ita dai wannan mutuwar me raba uwa da ɗanta tun yana ciki, wannan mutuwar me ɗauke uwa ta bar jariri a cikin jini, wannan mutuwar mai ɗauke miji ta bar mata da ƴaƴa, wannan mutuwar me ɗauke uwa ta bar yaranta cikin maraici da kewa ta mahaifiya, ita ce me raba soyayya da iyakance jin dadi lokaci guda, ita ce me saka mikin da baya taɓa gogewa sai ya yin da naka lokacin ya yi, ita dai-dai wannan mutuwar me raba masoya, me raba mutum da arziƙinsa na duniya. Irin wannan mutuwar Mahaɗinta ta yi? To a cikin rijiyar ta rasu a cikin ruwa data kasa shaƙar numfashi? Ko kuma wani abu ne ya daki kanta a lokacin da Daada ya cilla ta rijiyar? Ita wanne irin bacci ne me nauyi ya ɗauke ta wanda bata taɓa yin irinsa ba har ya cilla mata rayuwarta a cikin rijiya? Ina Abbaa yake a lokacin, Innti me take a lokacin?

Ta yi wata iriyar shaƙuwa ta zubawa ƙawar Iftihal, ita sam bata yadda gawa bace ba.

That's meana Daada ya kashe mata mahaɗinta kenan? Ya raba su? Ita tana duniya ita kuma zata tafi lahira? Me ya sa Iftihal za ta yi mata haka? Duk soyayyar da take yi mata? Da ƙaunar da take nuna mata? Ta ɗauka ita da kanta mutuwa za ta yi mata halacci da alkunya wajan ɗauke idanunta daga kan danginta more especially Mahaɗinta? Ta ina zata fara rayuwa without her? Without Iftihal, itama mutuwa za ta yi.

Da ƙyar ta juya kanta ta zubawa Daada idanu, gabaɗaya ƙwayar idanunta ta jirkice ta shiga bin da Daada da kallon da ita kanta bata san dalili ba. Sai ta yi murmushi ta ce

"Yaa Sam"

"Uhm" kawai ya iya cewa.

Tana ta murmushi ta ce "Ka cikani ganinta kawai zan yi na tabbatar ta rasu É—in ka ji?"

Yaa Sam yaƙi sakinta, Abbaa ne ya miƙo mata hannunsa, ganin hakan ya saka Yaa Sam sakinta kamar wacce ƙwai ya fashewa a haka take takawa, tsoron ganin abin da zuciyarta ta kasa ɗauka shine ya hanata yin sauri. Tana zuwa ta durƙusa a gaban gawar Iftihal ta miƙa hannunta wajan yaye fuskarta, ta zuba mata idanunta na wani lokaci. Ta juya ta kalli Babban yaya ta ce "I told Iftihal ai, sai Daada ya zama ajalinta, sai ya rabata da duniya, sai takaicin Daada da mugun halinsa ya kai ta zuwa lahira. Now..," sai ta yi murmushi tana shafo fuskar Iftihal da hannunta. "Abbaa..." Ta kira sunan Babban yaya ya matsa ya ɗora hannunsa a kafaɗarta ta ce "Mijin Innti ya kashe mini wacce muka fito ciki ɗaya da ita, muka zauna a mahaifa ɗaya ita, muka fito duniya a rana ɗaya, Mijin Innti ya rabani da ƴar'uwata, ƙawata, aminiyyata, abokiyar faɗa da wasana. Abbaa ya zan yi?"

Ta sake shafo fuskar Iftihal ta ce "Ina so na mutu nima Abbaa ina son na bi mahaÉ—ita, ina son na je inda Anum da Jarumi suke, ina son na je inda Iftihal zata tafi yanzu Abbaa"

Innti ji ta yi surutan Ana suna dukan tsakiyar kanta, kamar ana mata shocking a cikin ƙwaƙwalwarta haka take ji, kanta ya yi mata nauyi ta saka hannu ta dafe ƙirjinta.

As a mother, ya kamata ta ji baƙinciki, ta kuma zubar da hawaye na rashin Iftihal, madadin hakan wani abu me nauyi da girma da ciwo ta ji ya tsaya mata a ƙirjinta ya danne mata zuciya. Ana ta girgiza kai

"Abbaa kar ka binne mini MahaÉ—ita, ni ina son ganinta haka nan, zan zauna da ita"
Chapter 53 · 0% Book details