Sashe 48
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mu'allim ya dinga kallon ta ya rasa abin da zai ce mata, yaushe ma zai sake ganin Baffa balle ya nema mata izini a wajansa, shi ɗin wa ma? a hankali ya juya ya nufi part ɗin Mamy yana jin gajiya na saukar masa a jikinsa saboda driving da ya yi daga airport zuwa gida, ba kowa Baffa yake son ya dinga driving jikinsa ba, baya son damuwa, rawar kai a komai, yana buƙatar mutum me nutsuwa da kamala da kuma taka tsantsan, baya son stress ko hayaniyar da ta saka mutum ya yi driving kamar bashi da nutsuwar sanin me yake, hakan yana saukar masa da ciwon kai me tsanani, ciwon kan da baya buƙatar shi ko kaɗan, wata baiwa ce ko kuma haɗuwar jinin da ya yi yawa tsakaninsa da yaransa, muddin ya kwanta ciwo sai Nadiyaah da Diyanah Sayyadi Baffa sun kwanta, shi ya sa yake kulawa da jikinsa da duk abin da zai shafi lafiyarsa ɗin baya wasa dashi. A ƙarƙashin wannan dalilin ya ware mutane biyu da ya yi na'am da nutsuwarsu, duk da a hakan ma cike yake da yi musu gargaɗi da wa'azin babu kyau wasa da kowanne irin rai da Ubangiji ya wanzar a duniya. Al'ameen Hafizz Hafizz Baffa wato Mu'alim, sai kuma wani babban yaron shi a ɓangaren aikin Hisba me suna Ansar Khamal Khashim. A wannan dawowar ma tun kafin su taso Ansar ya kira Mu'alim ya sanar masa, yana airport ɗin jirgin nasu ya sauka, bashi da tabbacin ko sun yi nasara akan Da'awar da suka je yi bashi kuma da ƙwarin gwiwar tambayar Baffa sai Ansar.
Ansar ɗin kuma tun a airport suka rabu dashi. Sanda ya shiga part ɗin Mamy bayan ya yi sallama sai daya jira izinin shiga daga bakin Hidaya bisa umarnin Mamyn da kanta. A nutse ya sako kan shi cikin parlourn nata da yake ta ƙamshi, bakinsa ɗauke da sallama. Hidaya ce kawai zaune hannunta da riƙe da Mi'ata Hadith tana karantawa. Ya nemi waje ya zauna. Cikin sauri Hidaya tace
"Ahky Mu'alim yaushe zaka kai ni shan Ice cream ɗin, ka yi mini alƙawari fa, shi alƙawari kaya ne cika shi wajibi ne"
Ya dubi ƙanwarsa, wacce take yanayi da late Hafizz Hafizz Baffa, cikin kulawa ya ce "Zan kai ki Hidaya in sha Allah, but not now"
"Than, when?"
Sai ya yi ƙasa da muryarsa domin gani yake a hakan Baffa yana takura da maganar da suke yi. "Baffa is back, da zarar ya ji labarin ina ɗaukan ki zuwa wajan shan Ice cream mun kaɗe a gidan nan, kinga ke little sis ce autar gidan nan, kuma amanar Hafizz Hafizz Baffa, kenan Baffa ba zai taɓa yi miki faɗa ba" Hidaya ta yi shiru tana kallon Mu'allim cikin rashin fahimta ta ce "Baffa baya faɗa ai Akhy"
"And who told you that? Bakya nan ya kwakkwaɗawa Liman mari, wata ƙara da ihu da ya yi wa Liman sai da kowa ya firgita a gidan, don Allah Hida mu ajjiye shan Ice cream a gefe zan siyi na kawo miki, ni aure zan lallaɓa Baffa ya nema mini please?"
Ta washe fararan haƙoranta masu kyau ta ce "Idan baka kawo mini ba, I'll go and tell Baffa everything kana zuwa wajan Ice cream"
Mu'allim ya dafe goshinsa yana murzawa ya ce "Ya rabb, ke ba'a sirri dake ne Hidaya?"
"Ka rasa dawa zaka yi sirri sai da Hidaya Hafiz Hafiz Baffa? Baka san halinsu É—aya da Nadiyaah Sayyadi Baffa ba? Ai Baffa yana jin komai dake faruwa a gidan nan ta wajan Hidaya da Nadiyaah da Diynaah tas ma kuwa"
"Sannu da fitowa Mamy" Mu'allim yace yana bata girma wajan miƙewa, ta nemi waje ta zauna idanunta akan Mu'allim, tana sanye da baƙar Jallabiya me kyau ta yi rolling kanta da mayafi a nutse ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, hannunta riƙe da counter da azkar. "Al'ameen Hafizz Hafizz Baffa" Mu'allim ya ɗaga kai ya kalli Mamy bayan ya amsa cike da kulawa da rashin sakin fuska ta ce "Zaryar me kake wajan nema na haka?" Ya yi ƙasa da kan shi na wani lokaci.
Kan shi a ƙasa ya ce
"Akan yarinyar nan ne"
"Yarinya?" Ta maimaita a fili ta É—ora da "Wacce yarinya? Wani abu ne ya faru?"
"Mamy akan Iftihal yarinyar da aka kawowa su Nadiyaah da Diynaah aiki, da gaske ina son yarinyar nan sosai a cikin zuciyata tun kallon farko da na yi mata na yaba da hankali da nutsuwar da take dashi. Sunanta Iftihal na gaskiya Aysha, a unguwar Kankarofi suke, na sake komawa na yi bincike akan ta sosai" Ta ɗan gyara zama kafin ta ce "Ina fata binciken da ka yi ya yi daidai da tsarin matan da Baffa ya ɗora ku akai wanda suka dace da zama surukan Baffas family. Ba ƴar ƙananun mutane bace"
"E, gaskiya su talakawa ne sosai Mamy"
"Shine me? KuÉ—i da talauci mutum ke yin su ko Ubangiji? Mutumci da tarbiyyar gidansu nake magana akai"
Ya yi jim, domin binciken da ya yi ba mai daɗi bane akan gidansu, binciken da shima sai da ya hana shi bacci, da ace yarinyar bata tsaya masa ba, tabbas zai iya haƙura da Iftihal amma me? Ko idanu ya rufe ita yake kallo, idanunta, fuskarta, komai nata sune suke masa gizau a cikin idanunsa. Da wannan muryar tata me sanyi da kamala.
Mamy ta ce "Uhm? Ina jinka?"
Ya girgiza kai, "Mamy ban saba ƙarya ba kin sanni akan gaskiyata ko za ta yi ajalina. Da ina da iko da fara yi miki ƙarya to zan fara a yau ne, a dalilin Iftihal. Mutanen unguwar sun ce mahafinta yana shan giya, yana yin caca, kawai dai ba mutumin ƙwarai bane, mahaifiyarta tana da ilimi sosai ta taɓa koyarwa a makarantar gwamnati kafin sabuwar gwamnati tazo ta sauya ma'aikata. Ta basu tarbiyya sosai, komai na rayuwarsu ita ce. Suna da ƙanin uba sunansa Bala amma ɗan daudu ne.....," tun kafin ya ƙarasa ta ɗaga masa hannunta tana miƙewa tsaye cikin rawar ɗari da kakkarwar jiki ta ce
"Auzubillahi! Ka bincika komai kaga komai, amma baka gamsu ba sai ka faÉ—a mini? Tun a can unguwar tasu ya kamata ka ajjiye soyayyarta. Irin wannan jinin da tsatson zaka kawo mana cikin zuri'ar Baffas? Al'ameen ka haukace ne me yake going ta cikin kanka daka kasa controlling zuciyarka"
Sai ta yi baya kaɗan tana salati. Ba tare data juya ta kalle shi ba ta ce "Karka kuskura Baffa ya ji wannan maganar hukuncin da zai maka na san ba zaka iya ɗauka ba. Zai nemi wata can cikin matan da suka amshi musulunci ya ɗaura maka aure da ita ne for sure" jikin Al'ameen ya dinga rawa ya zamo daga kan kujerar ya ɗora ƙafafuwansa a ƙasa, idanunsa sukai jajur duk da acn dake cikin parlorn zufa ce ke wanke masa fuska.
"Mamy don Allah.....,"
"Kar ka roƙe ni Mu'allim, tashi ka fita" Ya ce "Ki yi haƙuri. Amma Mamy tarbiyya daman ta iyaye mata ce, yau da mahaifiyarta ke aikata abin da mahafin nata ke yi wallahi ba zan sake ɗaga maganar ba" wani uban kallo ta yi masa, a karan kanta zata iya barin Mu'allim ya auri yarinyar itama ta yi mata, amma hakan ya saɓa dokar ahhalin Baffa. Zai ja musu ƙasƙanci ne a idanun jama'a. Wannan maganar ma ba zata bari Hajiya Umaimah ta ji ba. Ta juya ta kalli Hidaya ta ce "Da kika je kitchen kinga baƙuwar me aikin nan tazo yau ɗin nan?"
"A'a Mamy, bata zo ba"
"Good, ta bar aikin daga yau ɗin" ta nemi waje ta zauna fuska babu walwala "Ko auren za ka yi ma ai ka haƙura a fara na Baffa, tunda na ji Malami ya ce yau za'a saka rana"
Hidaya sai kallon Mamy take yi sai ta ce "Mamy zani wajan Anty Diynaah ta yi mini ƙarin karatu" ta jinjina kai ta fice. Al'ameen da ƙyar ya iya jan jikinsa ya fice zuwa nasu part ɗin, ɓangarensa da yake kusa dana Liman ya shiga babban ɓangare ne me kyau yana shiga ya zube a ƙasa yana riƙe kai.
***
Ruwan daya sauka akan fuskarta shine ya sakata sauke ajjiyar zuciya me ƙarfi, ta ɗan juya kanta kaɗan da ya yi mata nauyi, sannu a hankali ta miƙa hannunta ta ɗora saman ƙirjinta daidai saitin zuciyarta da take bugawa da ƙarfin gaske. Laɓɓanta a bushe ga wani irin ciwo da kan yake mata bata iya ko buɗe ido balle taga mutanen da suke kanta. Ta ware bakinta da take jin ya bushe mata sosai tace
"Yau dai da gaske bani da lafiya mahaɗita, ban san me yake mini ciwo ba, amma ko ma mene Alhamd gaki a kusa dani, na san ciwon da kan shi zai ji kunyar kamani akan idanunki" ta yi shiru sai ta miƙa hannunta.
"Ki ɗora ni a cinyarki mahaɗita, ki rungume ni a jikinki ina jikin kamar Innti ce ina son ki danne mini ƙirjina ki hana zuciyata fitowa"
Jummai ta yi wa Iftihal ƙuri da idanunta, yarinyar ta yi fari fat saɓanin jiya, ga jini sai zuba yake yi a jikinta tunda Baita ya yi mata aika aika. Jummai ta juya kaɗan taga Baita shimfiɗe a saman gadonsa ya ɗora hannunsa a saman cikinsa sai bacci yake yi yana sakin munshari. Hannu ta saka ta maka masa dukan daya saka shi buɗe ido da miƙewa tsaye, ganin Jummai sai ya yi siririn tsaki ya ce "Uwar Kasko ya kai ne?"
"Ya akai kake tambayata? Sakko ka kalli ɓarnar da ka yi wa yarinyar nan Baita"
Alhaji Baita ya kalli Jummai sai ya juya ya kalli inda Iftihal take kwance, ya ƙurawa ƙirjinta idanu ganin da ƙyar take iya jan numfashi da saukewa. "Jummai ke sanda na amshi budurcinki ya kike a lokacin? There's nothing serious, pain ne kawai a bata magani" Jummai ta girgiza kai ya ce "Wannan pain ɗin bana iya budurci bane, hadda na zuciya. Ka faɗa mini ka yi aiki a kanta ne?" Sai ya jinjina kai na wani lokaci.
"E, na yi mana. Kalli can kiga Jummai" Juyawa ta yi sai taga sabbin daloli bandir bandir, kamar kuma bayan su akwai saura.