Sashe 31
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fita ta yi ɗauke da addu'ar fita daga gida a bakinta tana buɗe gate ɗin gidan ta fice sai taga mota daga can nesa kai tsaye ta yi gaba bata tsaya ba. Me motar ya sake kunnawa ya yi horn yasha gabanta, tsayawa ta yi tana ƙoƙarin yin masifa wanda ya buɗe motar ya saka gabanta faɗuwa ta yi saurin yin ƙasa da kanta jikinta duka ɓari yake yi. Ta cikin glasses ɗin idanunsa ya zuba mata ido yana daga kishingiɗen da yake a kujerar motar tasa....
*H I Y A A M*
Page 9: The Secret
Bright pens
Yota/001
I can repeat it again, this book dedicated to Nazeefah Sabo Nashe.
AUTAR MANYA: Thank you so much na gode da ƙoƙarinki Allah Ya saka da alheri Ubangiji Ya bar zumunci.
Ta cikin motar ya É—an sake ware idanunsa kaÉ—an ya kalli yadda take tsaye a waje tana rarraba idanu. Kamar zai yi mata shiru sai ya É—an duba agogon dake hannunsa sai yaga lokaci yaja yana kuma da abin da zai yi. A nutse yana kame fuskarsa ya dube ta ya ce "Are you getting into the car, or will you keep standing outside, looking around like someone who has something to hide?"
Yadda take kallon nasa sai yaga kamar bata fahimci me yake cewa ba, ya danna mata horn da ƙarfi sai ta yi saurin sakin ajjiyar zuciya saboda ɗan firgitar da ta yi duk ta kasa samun sukuni da nutsuwar zuciya. Ta ɓata fuska ta ce "Me kace ne?" Ya yi mata ƙuri da ido sai kuma ya ce "cewa na yi za ki shigo motar ne ko za ki tsaya a waje kina rarraba ido kamar mara gaskiya?" Sai ta tura bakinta gaba kaɗan itama ɗin ta makara ƙwarai da gaske, amma a yau ɗin sai ta ji bata samu ƙwarin gwiwar shiga motar ba, ta kuma rasa dalili, ba zata yadda saboda auren da yake kanta bane bata jin hakan. Kai bama shi ɗin bane, aure ai ba zai iya shata mata layi da abin da ta zaɓa kuma take so ba. Sai ta taka sannu a hankali ta buɗe murfin motar ta shiga kanta a ƙasa, bayan ta shiga da sallama ta zauna taja murfin ta rufe. A kunne motar take sai ya fara driving da hannu guda ɗaya hannun kuma yana shafa gemun fuskarsa yana sakin murmushi lokaci zuwa lokaci yake juyawa yana kallon ta. Sai ta ɓata fuska tace
"Allah ban shirya mutuwa yanzu ba, ka kalli gabanka ka yi driving a nutse please"
A kasalance ya ce "Nima hakan take baby"
"Shine kake ta kallo na?"
Ya ɗan ɗaga shoulders alamar rashin damuwa da furucinta ya ce "Wataƙila da bana kallon naki shine zai yasar damu a titi, but trust me baby, ki yarda dani baby kallon fuskarki ke bani energy a jikina kin ji ko?"
Ta yi masa shiru saboda faÉ—uwar gaban da take ji ta yi kaÉ—an ta kwanta a jikin kujerar. Shiru ne ya ratsa cikin motar lokacin da ya É—auki titin da zai kai shi Bright Fm É—in tasu.
"Ahlam.....
"...Tell me something please!"
"Kamar me kenan a something É—in?"
Ya sake shafo sajensa ya ce
"Me kike ji yau?"
Ya ɗora da "Ina nufin wanne irin farinciki kike ciki yau ɗin nan, domin na san a jerin shekarun da kika ruska a rayuwarki yau ɗin zata iya zama ta musamman a gare ki kamar dai nima haka nake ji yau ɗin" ya nuna tsakiyar ƙirjinsa alamar nuna kan shi. Ta yi shiru alamar nazari da tunani, tunani ta fara saboda kamar wani aiki ya sata wanda ba ta yi niyya ba ko kuma bata san dashi ba, ta fara processing da ƙwaƙwalwarta wajan haƙaito anahin abin da zai iya zama na musamman a yau ɗin a kuma rayuwarta. "Aure?" Sai ta yi saurin girgiza kai a ranta ta ce "No, impossible" Wannan aure ba zai zama na musamman a wajanta ba, wannan auren dai ba zai zama abin da zata rubuta shi a history na rayuwarta ba, auren da Engineer da Anty Jiddah ne kawai suka san dashi, suka san waye mijin ma? Sune suke ɗoki da zumuɗin yau ta zama matar aure, matar wanin da bata waye shi mene halinsa da ɗabi'unsa. Ita fa ko sunan shi ma bata buƙatar ji ɗin, tana son ta ƙarfin dole ta fuskanci matsalarta kuma ta yi maganinta. Ƙaddarar cimma burinta bata san ina zata tsaya ba, bata kuma san ina zata kaita ba. A fusge taja numfashi bayan ta lumshe idanunta tace. "Bani da wata rana ta musamman"
"Bana jin akwai wani abu special....
"Really.... Da gaske kike?"
Ta dude shi kawai ba tare da tace komai ba.
Ya murmusa "Ni ina da, ina jin akwai ta" Ya sake jan gemunsa "Ina jin ƙamshin zama ango, ina kusantar rayuwar aure da amarci"
Dam! Gabanta ya faɗi ta yi saurin cewa "Anees!" Yadda ta kira sunansa da ƙarfi ya saka shi juyawa ya kalle ta suka haɗa ido sai ta yi saurin ɗauke fuska ganin ya kashe mata ido ɗaya. "Yes baby, soon zan tare da matata in sha Allah. Aure zan yi ko na ce...,"
"Stop.....
Ta yi saurin dakatar dashi tana taro ƙirjinta da take jin kamar zuciyarta ce zata yanko ƙirjin ta fito, bata fatan ace abin da take hasashe ya zama gaskiya. Sarai ta san mahaukacin son da Anees yake yi mata amma babu haka a lissafinta ya shi ya sa ma bata bashi fuska ba, kar ta wahalar da zuciyar ɗan mutane a banza. "Ahlam"
Ya kira sunanta a tausashe ya ɗora da faɗin "wannan satin za'ayi Annual Media Excellence 2025. Shagalin karrama ma'aikatan kafafen yaɗa labarai na shekara ta 2025. Kina expecting karramawa ne a wannan shekarar ne kikai da za'a iya baki wani award, wanne kalar award kika hasashe za ki samu a taron?" Jikin Ahlam har rawa yake yi ita gabaɗaya ta mance da taron da ake yi duk ƙarshen shekara wajan bada karramawa ga ƴan jaridun da suka fi kowa hazaƙa. A wannan shekarar ne kuma take son nunawa Yussy cewa za ta iya, zata nuna mata nakasa ba zai zama kasawa ba.
"Allah Ya bawa me rabo sa'a Anees"
"Amin. Allah Ya sa ki samu Outstanding Journalist Award a ɓangaren mata baby"
Maganar award da taron da Anees ya yi ya sake saka Ahlam cikin damuwa, a hankali ta ciro wayarta saboda wani program da zata fara gabatar tana buƙatar bincike sosai. Data ta kunna, ta shiga Chatgbt ta fara bincike a hankali take dubawa, sai idanunta ya sauka akan wata kalma da bata taɓa gani ba, kuma ta kasa fassara ma'anar ta. "Kwagh" shine kalmar sai ta sake tambaya, mene fassararta wanne yare ne wannan?
Nan take ya bata amsa da "Tana nufin Almara a harshen Tiv, wanda yana cikin harsunan Bantu/Congo"
A hankali ta furta "TIV?" Anees ya juya ya kalle ta, sai ya yi murmushi ya cigaba da driving domin shima bai san mene Tiv ɗin ba. Ta samu kanta da buƙatar son sanin mene Tiv.
Chatgbt ta sake tambaya ta ce "Mene Tiv?"
"Tiv wata kaɓila ce a Nigeria, sun fito daga yankin da yake kusa da Kamaru"
Taɓe bakinta ta yi, a hankali kuma ya fice daga cikin application ɗin bayan ta karanta, haka kawai kuma kalmar Tiv da son sanin su waye su ya shiga yi mata yawo a cikin kanta.
Har suka ƙarasa Bright Fm bata sake cewa komai ba, saboda abubuwan da take ji sun fi ƙarfin ta faɗe su. Parking Anees ya yi a harabar gidan rediyon ganin Ahlam ta fito tana ƙoƙarin amsa kira ya ɗan yi gaba saboda akwai aikin da zai yi a ciki. Da murmushi ta amsa kiran ta ce
"Zainab Alƙali"
Ta cikin wayar Zainab Alƙali ta ce "Golden voice, ya naga har yanzu ba ki shigo ba ko ba ki da duty ne yau?" Cikin jin daɗi ya ce "Kin ganni a haraba yanzu zan shigo reception. Shegiya ki ce yau akwai labari, wanne littafi kika samo za ki fara karanta mana Besty?"
Zainab Alƙali ta yi dariya.
"Ke dalla ki shigo ciki tukunna"
"Please bama Æ´ar haka"
"Ban wani duba littafin ba, amma naga sunan wai ko INUWAR GIGINYA. Akwai labari ki ƙarasu ciki"
"Ok....." Cewar Ahlam.
Kashe wayar ta yi tana ƙoƙarin juyawa taga mutum tsaye a gabanta yana ɗan zazzare idanu "Malam lafiya ya zaka tsaya mini a gaba kamar ka haɗiye taɓarya?" Ya ƙura mata jajayen idanunsa yana watsa mata wani irin malalacin kallo zata tafi ya ce
"Kece Ahlam Abdallah Kurmi?" Ta É—an dube shi kaÉ—an "Yeah, ni ce ya aka yi?"
Ya jinjina kai ya ce "Ƴar jarida fa Golden voice?" Siririn tsaki taja saboda ta fara gajiya da rainin da wayon da yake yi mata. Duk ni ce. Malam ka faɗi mene matsalar aiki ne dani a ciki kuma ka tsayar dani waje guda" ya yi baya yana murmushi da ɗaga kai. "Relex..... Relex.... Relex"
"Ina nufin wacce ta saka labarin matar da aka ƙonawa jariri fa?" Ya tambaya.
"Ni ce, kana da matsala ne?"
"Eh babba ma" ya bata amsa.
Kafin ta ce komai ya ciro wata lafiyayyiyar wuƙa a ƙugunsa tana wani irin sheƙi ya yanki Ahlam da ita a hannunta ta fasa wani gigitaccen ihu ta yi baya ya sake yi mata wani lafiyayyen yanka a wuyanta ya ce
"Hukuncin ɓatawa mahafinmu suna" Yana faɗin hakan ya juya a guje ya fice daga cikin wajan. Wani gigitaccen ihu Ahlam ta kurma tana dafe wajan da hannunta, jini tuni ya wanke mata wuya da rigarta har jiri ya fara ɗaukanta, ta kasa motsi ta ƙanƙame wajan da hannunta tana jin kamar ranta ne zai fita idan jininta ya ƙare, kai tsaye rayuwarta aka nema, rabata da duniya aka so yi ta ƙarfin gaske akan case ɗin da bata da laifi a kan shi. "Wayyo wuyana, don Allah taimaka mini zai kashe ni, Anty Jiddah, yayana, wuyana" da ƙarfin gaske take kiran sunayen nasu.
Sannu a hankali yake murza É—an Bluetooth É—in hannunsa daga inda yake tsayen, waya yake yi don haka dukkan attention É—insa yana ga wayar da yake yi ne. A hankali ya ce