← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 64

Sashe 32

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki fita daga maganar nan, kin san bana shiga sabgar kowa bana son raini at all"

Ya yi shiru alamar saurare can ya nisa ya ce "Zan sake faÉ—ar the same abin da na ce, babu ruwana ok?" Wanda yake wayar dashi zai sake magana MD ya yi saurin dakatar dashi da faÉ—in.

"Hold on....."

Ya kashe wayar tare da saurare na ihun da yake ji tun ɗazo, ya juya idanunsa sai kuma ya ɗan taɓe bakinsa tabbacin bashi da ruwa da tsaki akan me ihun da dalilin ihun. Addu'arsa ɗaya ce, kar hargagin ya saukar masa da ciwon kai mara tushe. Amma me? Takalmi macen daya gani da jaka a yashe sune abu na farko daya ja hankalin nasa. "Wace wannan?"

"Ta kuma rasa wajan yin taɓararta sai a nan? A gidan rediyonsu? Ta ɓata musu suna?" Gently ya fara tafiya hannunsa ɗaya cikin aljihu, idanunsa cikin glasses wanda ya amshe shi ya yi daidai da faɗin fuskanta me ɗauke da zagayayyen sajen daya kwanta. Yana isa idanunsa ya sauka akan ta tana durƙushe jini na zuba daga wuyanta gashin kanta ya tarwatse a bayanta kamar zautaciyya. MD yaja numfashi ya sauke sbd bai yi tsammanin ganin jini ba, ya kuma fahimci wacece tunda ga Id card ɗinta nan a yashe. Bayan ya ƙarasa ya ɗan miƙa ƙafarsa kaɗan yana zungurinta. A gigice Ahlam tace "Don Allah kar ka kashe ni, nifa matar aure ce, ko tarewa ban yi ba. Kar ka cutar dani"

Idanunta ya faɗa a kan shi, sai ta miƙe tsaye da ƙyar tana layi idanunta na shanyewa, a firgice ta ƙarasa kusa da MD ta miƙa hannunta ta damƙi nasa ta ce "Na san ni da kai bama shiri, amma kar ka bari na mutu saboda jin haushina da kake, bana son na mutu banga ƴaƴana ba, yau aka yi mini aure ko mijin ban sani ba, wayyo yaya za su kashe ni" Ta sake damƙo MD ta ce "ka taimaka mini ka kira mini yayana, wallahi bana son na mutu, ina da buri akan aikina, ina da burin ganin na ɗaukaka ina da burin naga na haihu na tara zuri'a masu yawa" da ƙyar take yin maganar saboda fitar hayyaci.

"Help me.....

"Please!"

Ta ce cike da raunin murya.

Taɓe bakinsa kawai ya yi ganin ta sulale zata faɗi a wajan ba numfashi ya saka hannunta ya riƙo nata, ɗaukarta ya yi gabaɗaya ya sakata a cikin motarsa, daidai nan Baba driver yazo wajan ya ce "Yallaɓai ina zaka?"

Hannu MD ya ɗaga masa alamar babu buƙata. Baba driver har ya juya ya ji MD ya ce "baka ji ba?" Sai Baba driver yaja ya tsaya

"Na'am, ka ce wani abu ne?"

A nutse MD bayan ya shiga mota ya ɗan murza key ya ce "Ka faɗawa officer muna buƙatar police a cikin Bright Fm right now"

"Police? Ƴan sanda fa Yallaɓai?"

"In sha Allah" cewar MD.

Yana faÉ—in hakan yaja motar a guje ya bar cikin gidan rediyon.

***
"Mita 119 bright Fm kuke so sauraro. Au yau ne hukumar ma'aikatar ilimi ta jiya ta sanar da sabon tallafi da gwamnati ta fitar ta ƙarƙashin hukumar, inda za'a ɗauki adadi ɗaliban jami' kimanin mutane dubu ɗaya aikin Gwamnati, tare da bada tallafi ga wasu. Za'a fara tantance ɗaliban a ranar Litinin me zuwa, ɗaliban zasu taho da takardun makaranta wanda dama ta iya wanda suka fita daga first class ne" sai aka ɗan dakata da maganar aka sako taken gidan rediyo. "Labaran Duniya" muryar na namiji ya fito.

"Daga gefe guda, wasu da ba'a san ko su waye ba, suna shiga rugar Fulani tare da yi musu kisan gilla, bayan kisan suna tattare kan jama'ar su yi gaba dasu, an fasa Fulani adadin da ya kai 75. Duka ina jami'an tsaro da gwamnati suke ake wannan abin? Aka ce, kowa ya ji daɗin gemu bai ka maƙoro ba. Ahlam Abdallah Kurmi ke tare daku"

A hankali ya kashe radiyon tare da yin baya ya lumshe idanunsa yana jin zuciyarsa na bugawa sosai, tun rahotanni da ta yi jiya da daddare ne sai yau aka saka. Ya numfasa ya ce.

"Ba wani bayani akan yarinyar ne?"

Wanda aka tambaya ya ce "Akwai, Ahlam Abdallah Kurmi sunanta, amma asalin sunan shine Haleemah, iyayenta sun rasu tare zaune a wajen yayanta Engineer Abdallahi. Shine ya tsaya mata tun daga primary har zuwa secondary da jami'a, karatu me kyau ta yi a makaranta me tsada a ɓangaren aikin jarida. Tana da ƙoƙari da jajircewa a aikinta, amma a nutse take, bata da hayaniya tana da kamun kai, ba irin sauran da suke mata aikin jarida bane. Sir i wonder why kake son ganinta, is there any problem da ba zaka iya sharing ɗinsa dani ba?"

Ya ware idanunsa, kallon yaron kawai ya yi ta cikin glasses É—in idanunsa ba tare da ya ce masa komai ba.

A ɓangaren Maryama a wannan dare a tasha ta kwana, mutane sai kallonta suke yi, wanda tana da tabbacin kallon mahaukaciya suke yi mata, ƙudaje suna ta binta saboda jinin haihuwar daya ɓata mata jiki, zuciyarta ta yi mata wani irin nauyi a ƙirjinta, ko kuka ta kasa idanunta ya bushe sai yawo take yi da gawa a hannunta wacce ta ɗan fara wari. Mutane na ganinta suke matsawa zuwa gefe.

A hankali taja jaririn ta ƙanƙame a ƙirjinta sai a lokacin ta samu damar sakin wani irin raunataccen kuka me cin zuciya, ta yi ta gama ta lallashi kanta ta faki idanun jama'a ta ajjiye gawar a gefen kwata dake tashar ta tashi da sauri ta bar wajan tana dafe ƙirjinta.

***
Ana ce kwance a gadon asibitin da take, ta yi shiru idanunta a rufe tana sauraran bugun zuciyarta daya ruɓaya fiye da yadda take ji a lokutan baya, a hankali ta miƙa hannunta zuwa saitin zuciyar da nufin ta danne ta da tafin hannun, sai ta ji haƙarta bata cimma ruwa ba, tamƙar tana saƙa ne zaran baya data tufke yana warware kan shi. A dalilin bugun dake ratso ƙirjin yana haɗawa da hannun da take ganin ta ɗora da nufin bata kariya. A kowacce daƙiƙa ta shigewar lokaci ƙara nisanta zuciyarta da Daada take yi, nisan da take murna dashi domin da gaske bata buƙatarsa a rayuwarta, ace da uba ake gado, ita kam bata yarda da wannan gurɓatacciyar kalmar ba, bata yi believing da ita ba, kuma bata jin ko nan gaba da abada zata yarda cewa da uba ake ado har ta bawa jimilar muhalli nada ban a zuciyarta. Da Innti take yin ado, ita ce sahibarta abar adonta, abar ta ɗauki abu ta yi shelan irin tarin soyayyar da take yi mata, sau tari ta kan rasa sanin adadin soyayyar da take yi wa Innti da Mahaɗinta, soyayyar kunnen doki ce, kowanne ba zata iya shaƙar wadataccen numfashi ba idan babu shi.... Bayan su sai waye next? Yaa Jadid, da Yaa Jaheed jaruman yayyinta a ɓangaren uba kuma Babban yaya shi ne ubanta shine abu mafi ƙauna a ranta a ɓangaren maza. Shine duniyar Ana.

Bayan su sai wa zata saka a lissafin nata?"

“Haysaam"

"Yaa Sam.....

Ta faÉ—a a fili tana sakin lallausan murmushi.

Motsin da ta ji ya saka ta buɗe gajiyayyun idanunta wanda sukai laushi saboda ciwo da galabaitar da zuciyarta ta yi saboda tunanin 'future life' ɗinsu ita da Iftihal. "Abbaa" ta kira sunan a tausashe tana faɗaɗa murmushinta. Kallon ta ya yi na wani lokaci, jikinsa sanye da sabbin kaya wanda sukai masa kyau sosai, ya ɗan sake yin fresh, lallausan sumar kansa da take har baya ta dinga ɗaukan idanu a nutse ya ƙarasa ya zauna daidai kanta ya zuba mata ido, ita ɗinma kallon shi take yi da manyan ƙwayar idanunta jin shiru ya saka ta miƙa hannunta ta riƙo nasa ta ce

"Abbaa...

"Abbaana"

Ya É—an buÉ—e ido bai magana ba. "Ina ka je? Tun jiya baka dawo ba in ji Yaa Sam" bai bata amsa ya juya idanunsa alamar

"Kina jin ciwo?"

Ta ji ya furta da silent voice É—insa me sanyi a cikin shurunsa da maganarsa ta body language.

Ta jinjina kai lokaci É—aya ta ce

"Eh"

Ya zauna kusa da ita ya damƙe hannunta dake cikin nasa ya shafa gefen kanta ya zuba mata ido alamar saurare. Ana ta ce "Abbaa ka yi mini alƙawarin ba zaka zama irin mijin Innti ba, ba zaka dinga cutar da matarka ba, da yaran da Allah zai baka, ka yi mini alƙawarin zaka dinga sakawa yaranka albarka daga cikin yaran na zama ɗaya daga ciki, ka zama babana ni na riga na zama ƴarka Abbaa. Zan yi addu'a Ubangijin Ya yi mini yalwar arziƙi na siya maka gida babba mu koma can ka yi aure ka buɗe babban shago a Farm center. Ina son ka Abbaa kaina hope ɗina, kai na nake gani na ji ka cike mini gurbin uba, ina ƙaunarka Abbaa"

Ya shafa goshinta alamar "Idan ba Ubangiji ba, waye zai maka kyautar É—a babu aure?"

Ta washe masa jerarrun fararen haƙoranta. Ya shafa hannunta tabbacin "Idan Ubangijin Ya ara mini rai da kuma dama, zan cike miki duka gurbin da kika rasa, In sha Allah"

"Da gaske kake Abbaa?"

Ya jinjina kai alamar

"Me kike buri a rayuwa?"

"Na yi rayuwa daku ta har abada, naga na zama cikakkiyar marubuciya idan na kammalawa karatuna, idan Allah ya yi mini arziƙi na kai ku hajji da umara na siya muku gida, na dinga ajjiye kayan abinci akai akai"

"Kayan abinci?"

Ta matse hannunsa a nata tana jin relief yana sauka a gangar jikinta yana samar mata da nutsuwar zuciya. "E. Saboda kada mu ji yunwar da muka rayu a cikinta, kada mu sha wahalar rayuwa My Abbaa" Ya ce "Na fahimta"

Ƙuri ya yi mata da nasa idanun dake nuna maganar
"Ba ki yi maganar aure ba?" In seconds yaga mood ɗinta ya sauya, damuwa ta maye gurbin walwalar wani abu ya tukare ƙirjinta ya tsaya mata tana jin ya yi mata nauyi.

"Kodayake you're still my baby"

Ta yi murmushi "I'm always been your baby"

"Your favourite daughter"

Sai ya sumbaci goshinta yana faÉ—in "In sha Allah!"
Chapter 32 · 0% Book details