← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 64

Sashe 57

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ja hancinta kaɗan ya ce "Ina son ki Halimatul Sadiya, ina son ki Ahlam ɗin yaya, ina son Babyn yaya, ina son Golden voice. Ina son ki tun ranar dana fara ganinki Ahlam, na zuba idanu ne naga yanayinki da tarbiyyarki, duk abin da nake miki tsakanin kishin Anees ne ya ja, domin da ace na furta ina son ki ko bakya so na, yake shige miki ko ban karya ɗan mutane ba, jikinsa zai faɗa masa. Sannu a hankali na fahimci kema kina ra'ayina. Kar ki mini musu ke kin sani nima na sani, Yussy kuma bani da business da ita, ina barinta ne ta yi abin da taga dama akan idanunki saboda na kunna ki, kuma Alhamd ina yin nasara" ya yi shiru yana sassauta riƙon da ya yi mata, kanta a ƙirjinsa tana rera masa kuka ya shafa kanta kaɗan ya ce "Ni ba zan tauye ki akan aikinki ba, zan barki duk abin da kike so ki yi muddin bai saɓawa koyar war musulunci ba, zan tayaki aiki wajan cimma burinki"

Cikin sauri ta ce "Za ka yi inviting Sayyadi Baffa na yi Interview dashi don Allah?"

Md ya yi shiru yana kallon ta.

Ta daki ƙirjinsa ta ce "Please Liman"

A hankali ya ce "Ƙarewa ki ce Asad Hafiz Baffa" ya ɗora da "Ba zan miki ƙarya don ki so ni ba, Md ne ni a Bright Fm, Bilal ne Founder a Bright Fm, shine me rediyon, kuma muddin yana nan Sayyadi Baffa ba zai taɓa zuwa nan ba, ke ko bashi bane i don't hakan zai faru, even Nadiyaah da Diyanaah ba ki da zarafin hira dasu" ya kalli cikin idanunta yana goge mata hawaye ya ce

"Tunda kika amsa sunan Mrs Asad Hafiz Hafiz, dole ki yi Interview da Sayyadi Baffa"

Ahlam ta ce "Yaushe?"

"Not now"

Ta zame a jikinsa ya tayar da motar ya jata suka fice daga cikin gidan gabaÉ—aya.

***
Bayan azahar jama'a duk suka watse a gidan Innti, da an shigo an yi gaisuwa mutum yake komawa gida. Jaheed ta bawa kuɗin aikin da za'ayi Jadid a asibiti ta ce ya je ya zauna kusa dashi, saboda kada a shigo ba'a same ta ba daman shi ai namiji ne, gwara ya saba da jinyar ɗan'uwansa tun yanzu. Ita ta kewa Jadid komai, hatta wanka da alwala idan ciwon ya tashi, bata jin nauyinsa kamar yadda shima yake jin bashi da kamar Innti a duniya kuma uwa ce, labulen sirrinsa ce. A hankali ta miƙe tun bayan dawowarta daga waje babu wanda ta cewa komai, komai da idanu take binsa dashi. Duk yadda zata faɗi raɗaɗin da take ji a zuciya ba kowa zai fahimce ta ba, nauyin da zuciyarta ta yi mata ita kaɗai ma sai ta saka ta jinya, ga tijarar da Daada ya yi a cikin jama'a akan kuɗi, Emama tazo ta tusa.

"Wai ai ita ce ta kai Iftihal gidan masu kuɗi, kuma idan Innti ta bata kuɗin sadaƙa za'ayi"

Hanna ta ce "Ta ina kike zaton zata ba ki kuÉ—i, tana kallo mugun abin da take jifanmu dashi, da kuma Daada ya fara komawa kanta, gashi nan Æ´arta ta faÉ—a rijiya ta mutu"

"Ai shi sharri kan me shi yake bi, kuma alhaki É—an tsako ne" ita kanta ko karin maganar bata gama iyawa ba. Innti da idanu kawai take bin su dashi, bata ko tari.

Maman Haysaam ta ce "Haba bayin Allah, wanne irin tozarci ne wannan? Ɗiyar cikinta ta rasu saboda baku da lissafi ku dinga binta da waɗannan munanan malaman? Shi ɗan'uwan naku me ya tare mata da har zata yi asiri saboda shi? Wallahi baiwar Allan da tana jin shawara ta da tuni ta jima da kashe aurenta ta rungume ƴaƴanta ta rufawa kanta asiri. Banda gantalallen ɗan'uwan naku yana yi mata yadda yake so, saboda tunanin tana masa biyayya ko wani dalili nata can mara tushe, ai tuni Innti ta sha kwana ta zama abar data zama. Jaheed yana shago, duk wata ana masa albashi ko babu yawa ne, Muraad yana zuwa farm centre ko babu yawa dai yafi zamam gidan, matar nan tana koyarwa a makaranta, tana ɗaukan albashi, ga ɗinki ta na yi, ga ƙananun sana'a ta hannu da mata suke yi. Ita kenan faɗi tashi wajan ganin ta rufawa kanta asiri bata bar yaranta cikin yunwa da datti ba. Motsi kaɗan sai ya sace kuɗi ya shiga caca, komai na Innti a sace yake a wajan ruɓaɓɓan mutumin can, ga shegen bin mata kamar uwa ɗaya ta haife su da ɗan taure, tunda ta daina koyarwa ta shiga matsin lamba, ga ciwon Jadid dake lashe kuɗi, ɗaukin nawa kika taɓa kawo mata a matsayinki na uwar mijinta, kuma jininta? Wanne tallafi kikai mata?" Maman Haysaam ta ƙare maganar tana miƙe tsaye idanunta na zazzagowa kamar zata hau iska jikinta sai rawa yake.

Daada ne ya ɗaga hannu zai mare ta, Emama ta riƙe hannunsa ta ce "Rabu da ita"

"Basshi ya taɓa ni, wallahi da sai na masa sanadin da zai koma bakin titi da yin bar"

Ta juya kan Emama ta ce "Ke kuma ba wayo kike dashi ko dabara ba, tunda ga ƴaƴa mata nan kina dasu, tun a nan duniya za ki fara ganin HUKUNCIN ALLAH, Saboda kin riga da kin zama INUWAR GIGINYA mara tsoran Allah da son zuciya, a halin da matar nan take ciki ga yaro can a asibiti ba'a san ina kan shi yake ba, shine nan kuka wanko jiki a baku kuɗi, daman ba jana'iza ta kawo ku ba. Jarrabawa ce kawai irin ta aure amma Innti ba tsaran Daada bace in sha Allah farincikin da kuke baƙincikin ta yi kuna ji kuna gani za ta yi yaranta za su zama zama abin sha'awa ga jama'a. Ƴan wahala kawai"

Tana faɗin hakan ta saka kai ta fice, zuciyarta na yi mata raɗaɗin rashin hankalin jama'a. Suma ɗin juyawa suka yi tare da ficewa. Daada ya kalle ta ya ce "ƴar daba kika kawo mini cikin gidana ashe bani da labari? Har tana iƙirarin zata sabauta ni ko?"

Ya jinjina kai, yau fes yake cikin hayyacinsa tsaye akan ƙafafuwansa ya ce "Ina jin igiya ɗaya ta rage tsakanin auren da bashi da wata ma'ana a wajena, face ni na rufa miki asiri kamar yadda mahaifinki ya nema ko?"

A hankali ta É—ago ta kalle shi, ta zuba masa rinannun idanunta bata ce ci kan ka ba.

Ya ce "Tunda babu abin da za ki yi dani kuma kina da wanda zai iya aurenki, ki je na sawwaƙe miki. Nima yau zan yi sabuwar amarya. Na yanke sauran igiyar da ta yi saura" yana faɗin hakan ya juya ya fice da takun isa da ƙasaita. Ta zubawa bayansa idanu, a hankali ta ɗora hannunta a ƙirji ta danne sai kuma ta saki yalwataccen murmushi. Duk abin da yake faruwa Babban yaya yana ɗakinsu kusa da Ana wacce har yanzu babu inda yake motsi a jikinta, kanta a cinyarsa yana shafa sumarta a hankali hannunsa ɗaya ya damƙe nata hannun dashi. Bai sani ba, amma ya samu kan shi da hamdala bayan sakin da Daada ya yi wa Innti ɗin, ya ji wani sanyi na musamman, ya ji relief na musamman a zuciyarsa yana sauka a hankali, hakan ya yi masa daɗi shi ya shirya, daga Ana har Innti yana da inda zai kai su da baza su ta gayyara ba. Yana wannan tunanin Jaheed ya kira shi a waya, ya zubawa wayar ganin number da baya so a kira shi da ita yana yawo a screen ɗin wayar bayan katsewar kiran na Jaheed, ya kuma fahimci filashin daman Jaheed ɗin ya yi masa. Don haka numbers ya kira kai tsaye yana ɗagawa

Ya ce "An fito da Jadid yanzu daga wankin ƙodar" Babban yaya ya yi shiru for a while

Sai kuma ya kashe kiran.

Innti na zaune har yanzu ta kasa motsi, ita da kanta bata san meke damunta ba, duk abin data furta kusan zata iya cewa ba shine ainihin abin da yake mata yawo a zuciyarta ba, carbi kawai take ja tana istigifari, a ranar sai da suka saukewa IFTIHAL Kur'ani ita da Yaya da Jaheed, ta san da idanun Ana biyu ita kaɗai zata iya sauke Kur'anin da kanta cif. A nutse ya shigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, ƙamshinsa me sanyi ya mamaye tsakar gidan, yana sanye da yadi me laushi ash colour ya ɗora a akan shi.

Ya durƙusa ya ce "Ina yini ya ƙarin haƙuri?"

"Allahamdulillah Haysaam" ta ce da ƙyar.

Ya yi shiru kan shi a ƙasa, ta dube shi ta ce

"Ya aka yi ne Haysaam?"

"Daman Offer É—in aiki da gwamnati ta raba Allah Ya yi na samu, yanzu ma daga can ma'aikata ilimi nake, an sake tantance mu wajan Hamsin akwai wani interview da za mu ke Abuja, wannan kuma shine Finally Interview da za mu yi, shine na ce a tayamu da addu'a mu tsallake idan da rabonmu"

Innti ta ce "Khairan in sha Allah Haysaam, Allah Ya taimaka ya basa sa'a isa rabo ne"

Ya ce "Amin Ya Allah"

"Amma yaya bai san da Offer É—in ba, link aka cike ko e-mail ne? The offer is still available?" Ya girgiza mata kai kafin ya ce

"A Redio aka sanar, kuma masu first class"

"Yaya ma first class gare shi. Babu rabo ina maka murna ƙwarai da gaske. Yau za ka tafi?"

"Nan da 2 days masu in sha Allah"

"Ma sha Allah" ta ce a nutse.

Ya yi jim kafin ya ce "Nanaah ta farko?"
Chapter 57 · 0% Book details