← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 64

Sashe 6

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruwan daya taro a cikin kwarmin idanunta ta haÉ—iye su, tare da mayar dasu ta hana su zuba a saman fuskar da babu tabo ko guda.

Butar ta saki ruwan ya mamale ta shige É—aki abinta, sai da duk suka fita zuwa masallacin su uku, kana ta fito kanta babu kallabi ta shige banÉ—aki, a bakin banÉ—akin ta yi addu'a ta shiga. Alwala ta É—aura ta yi sallah a sakar gida kusa da MahaÉ—inta wato, 'Ifti'.

Bayan sun idar sun yi azkar wanda Innti take nanata musu muhimmancinsa, sukai sabuwar shimfiɗa aka saka Tuwon a babban faranti da ruwa a babban kofi wanda ake sha ɗaya bayan ɗaya. Ana sai tsinewa Tuwon albarka take yi, wanda takaicin ya saka ta miƙe ta shige ɗaki bacci ya ɗauke ta.

ÆŠabi'ar zuri'ar Innti ce, cin abinci a faranti É—aya tare da iyalanta, safe, rana da dare.

"Innti, Daada ya amshi kuÉ—in kitson dana bawa MahaÉ—ita ta siyo taliya Æ´ar murji"

"Daada?"

Jaheed da Jadid suka maimaita.

Ita dai Innti ba ta yi magana ba, kalmar Daada kawai ya tsayar da bugun zuciyarta na wani lokaci, a ƙarƙashin tsayuwar bugun zuciyar, ta nemo fargaba da tashin hankali, zullumin abin da zai biyo baya, akan abubuwa da suka riga suka shuɗe ya sakata tsame hannunta daga cikin jerin hannu huɗun da yake faranti, biyar cif idan aka haɗa da nata hannu. "Ifti, kici abinci ki bar Ana kawai, samu ne wanda yafi rashi ɓarna, ganin Tuwon ya saka take wannan, da Allah bai hore na ɗora tukunyar bafa?" Ifti za ta yi magana, yatsun Babban yaya daya motsa ya saka ta yi shiru.

Har akai sallar issha'i Ana na bacci, da ƙyar ta miƙe ta fito kan nan babu ɗan ƙwali gashi sumar ta mimmiƙe kamar sabon kamu, bata kitso bata son dukkan wani tashin hankali da zai saka a taɓa mata kai, kamar me gyambo a kan, suka zuba mata idanu, Babban yaya kallon ta kawai yake yi ya ƙudurce abin da zai mata idan ta shiga banɗakin babu kallabi, Innti ta tsaya da tatsuniyar da take basu, da labarin iliya ɗan me ƙarfi. Ana ta nufi banɗaki bayan taja ruwa a rijiya, a magagin bacci take ko addu'ar shiga banɗaki ba ta yi ba, tana saka ƙafafuwanta cikin banɗakin, ta yi arba da me kama da ita kwabo da kwabo zaune a banɗaki ta zuba mata manyan idanunta.

Da fari ta ɗauka Ifti ce, sai ta tuna yau ba kaya iri guda suka saka ba, Ana ta murza idanunta, sai taga matar itama ta murza nata idanun, ta ɗauka ko bacci take yi har yanzu, tana a duniyar mafarki ne wataƙil

Sai ta girgiza kanta sumar ta baje.

Nan take matar itama ta girgiza kanta.

Wani gigitaccen ihu Ana ta saki sanda ta tabbatar gamo ta yi a banɗakin, ta zube a wajan a sume babu numfashi a ƙirjinta.

Babban yaya, ya riga su miƙewa, taku ɗaya biyu dugwayen ƙafafuwansa suka ƙarasa dashi banɗakin,a bakin ƙofa yaga Ana bata motsi, ya zuba mata idanunsa da suke iri ɗaya sak da nata kafin ya saka hannunsa ya ɗakko ta zuwa harabar gidan. Salati Innti ta fara a gigice tana ɗaukan carbi, cikin rikicewa Ifti ta fashe da kuka, Jaheed da Jadid suka rufu a kanta suna kiran sunanta. Hijabin Innti dake gefe Babban yaya ya ɗauka ya zurawa Ana, a zuciyarsa ya dinga addu'a yana tofa mata, da yayyafa mata ruwa a fuskarta zuwa wuyanta sosai

Ajjiyar zuciya ta sauke me ƙarfi. Sai kuma ta zabura tana sambatu da surutai, suka danne ta suna sake yi mata addu'a a haka har ta dawowa daidai.

"Yau naga abin da ya ishe ni, sau nawa zan ce ki dinga saka kallabi a kan ki Ana?"

Inji Innti tana riƙe haɓa.

Jaheed ya ce "Babu mamaki gamo ta yi"

"Idan gamo ta yin ma ai da sauƙi muddin basu shafe ta ba, yarinya ce da shegen taurin kai da miskilancin jaraba kamar matar kuturu, ƙila ko addu'a ma ba ki yi ba"

Wata uwar harara ta watsawa Jadid. Ya ce

"Oh, hararata ma kike?"

Ya juya yana kallon Innti ya ce "Anya Innti Shalelenki ce wannan ko wata ce daban?"

"In sha Allah ita ce. Tashi maza É—iyar albarka ki yi sallah ki ci abinci kin ji Shalelen Innti"

Ana ta miƙe kamar ka ce mata ƙyat ta gudu saboda tsoro, ta marairace fuska ta ce "Mahaɗita rakani banɗakin don Allah?"

"Ai ya zama dole rabin jiki"

Ifti ta ce tana miƙewa, bayan ta yi alwala ta yi sallah yin duniya aka yi taci abinci amma taƙi a haka bacci ya ɗauke ta, bayan ta shiga ɗaki Ifti baccin itama ta yi, Innti dake tsaye a ɗakin ta bisu da kallo, a hankali ta zauna gefen katifar da rabi duk ya cinye, kallon fuskar Ana take yi, kyawun fuskarta tsoro yake bata, wannan tsoran shine yake cin zuciyarta, wannan tsoran shine yake damunta, dashi take kwana take yini, wannan tsoron shine yake hanata sakin jiki da fitar Ana, shine yake hanata sakin jiki da barin Ana ta yi ƙawaye, wannan tsoron shine yake sawa bata barinta fita waje. Ta ja numfashi me ɗauke da damuwa da yawa, na makomar yaranta, da tarbiyyarsu. Ta jima tana yi musu addu'a sosai ta shafa musu sannan ta fice daga cikin ɗakin. Sannu a hankali suka juya a tare, Ifti da Ana, suka rungume junansu cikin bacci.

Basa iya bacci sai sun yi wannan rungumar kamar ibada, wannan numfashin junan. Shine ke riƙe da zuciyoyinsu.

Ɗakin mazan ta shiga ta tarar Jaheed ya yi bacci, Jadid riƙe da azkar, Babban yaya na duba wata waya a can gefe wajan shimfiɗarsa, ma kwanci biyu ne a ɗakin.

Jadid da Jaheed, sai ta Babban yaya.

"Jadid"

Ya ce "Na'am, wani abin zan miki Innti?"

Ta zuba masa idanunta wanda suke faÉ—ar abubuwa da yawa a hankali ta ce

"Magani"

"Kasha maganinka na dare?"

"Ina cin abinci na sha ai Innti"

Ta ce "Ma sha Allah, Allah Ya ƙara lafiya"

"Amin Ya Allah, Allah ya ja kwana Innti"

Ta yi masa murmushi.

"Yaya" ta kira sunan Babban yaya.

Fararen idanunsa sune suka fara shiga cikin nata kafin kyakkywan duhun fatar fuskarsa, ya yi jim ta ce "Zo, ka saman a waje" tana fita ya bi bayanta a nutse

A tsaye ya sameta tsakiyar hasken wata, haskensa da yake nuna cewa ya shiga 14 ko 15. Ya durƙusa har ƙasa cike da ladabi.

"Yaya, kai ne Babba bana son yi maka faɗa a cikinsu shi ya sa na rabu da kai, kar ka sake ranƙwashi Ana a tsakiyar kanta, ita macace tarbiyyar mace akwai wahala a wannan matakin bana son ka yi mata sabon duka, idan ya zama dole gwara ka ɗauki bulala ka zane ta akan ranƙwashi nan ka ji?"

Ya jinjina kan shi alamar “Eh" Dubansa ta yi da kyau bata san me ya sa shurunsa ke ninka maganarsa ba, yana yaro kamar karsashinsa yafi haka. Hannunsa ta riƙo cikin nata ta damƙe, ajjiyar zuciya ya sauke saboda wani daɗi da nutsuwa da ya ji, ya ɗauki hannunsa ya ɗora a nata. "Hausawa suka ce babban wa magajin uba, ina jiye maka kula da tarbiyyar Ana zuwa ɗakin miji idan haka zaka dinga mata, na san kana da zafin zuciya wacce a lokutan baya har tsoro nake ji, na ji da ɗabi'arka ta sauya. Ka yi haƙuri Yaya ka sake haƙuri watarana sai labari, za kaga babu Ana babu Iftihal duk suna ɗakin mazajensu, kaima kana tare da matarka wataƙila da yara, be patient yaya"

"Har Ana? Itama auren kenan za'a mata?" Ya shiga zance a zuciyarsa ransa kuma ya ɓaci nan take. Ta ce

"Saboda lafiyar idanunka, ya kamata ka kwanta don Allah, kar na leƙo naga kana wani aikin na daban kuma yaya"

Tsoro Innti take ji!
Taka tsantsan take yi!
Tana ƙoƙarin tilasta musu yin bacci, bayan dole sai sun farka kamar kullum.

Ya sake bata tabbacin zai kwanta ta hanyar jinjina mata kansa kana ya miƙe ya koma ɗakinsa. Tsakar gidan ta dawo da zama hannunta riƙe da carbi zuciyarta sai bugawa take yi, na rashin sanin dalili gashi bata jin bacci sam, kamar wacce akai wa farraƙu dashi, tunawa ta yi tana da ɗinki sai ta ɗakko atamfar da almakashi ta fara yankawa.

Tana zaune Yaa Jaheed ya fito hannunsa riƙe da waya zai nufi ɗakin su Ana. Innti ta ce "Jaheed me za ka yi a ɗakinsu a yayin da suke bacci" ya yi sak sai ya ce "Ana zan bawa wayar ne Ana nemanta" kallon wayar ta yi har za ta yi magana kuma ta fasa. Ta miƙe ta amshi wayar shi kuma ya juya zuwa ciki. Kamar me jiran wayar haka Innti ta samu Ana zaune akan katifar ta ɗora kan Iftihal a cinyarta tana shafa kanta a hankali, idanunta yana kallon sama ta yi shiru.

"Shalele me ya farkar dake yunwa ko?" Sai ta girgiza kai a hankali cikin sautin muryarta mara ta ce "Sumar kaina Innti don Allah kar Babban yaya ya aske mini na san halinsa da ƙeta wani lokacin, ina son sumar kaina ba zan samu mijin aure me kuɗi da kyau ba idan bani da gashi wallahi"

"Oh! Wannan kyau da kuÉ—i Ubangiji ya sa ya zame miki alheri Aysha. Wani kyawun masifa ne"

Ta ɓata fuska kaɗan "Ki yi mini addu'a kawai Sahibarmu, addu'arki kaifiyance. Yanzu da Daada yana da kyau sosai irin na mazan novel da Zainab Alƙali take karantawa a redio wallahi da wani takaicin nasa bai sarƙi zuciyarki ba, da ya shigo kinga kyakkyawan mijinki ko yunwa kike ji za ki mance"

Innti bata san lokacin da ta yi murmushi ba ta ce "Au yanzu idan na ganshi bana farincikin kenan Shalele" ta ce tana ɗan jingina da ƙofar yin hira da Ana na sata nishaɗi yana ƙara mata son yarinyar. "Nifa ban taɓa ji kince masa I love you ba, kinga Miftaa na cikin littafin Allah Yana gani matarsa kullum sai ta ce masa I love you, shi ma ya faɗa mata ai soyayya duniya ce Babarmu"

"Oh really?"

"Wallahi Innti"
Chapter 6 · 0% Book details