Sashe 7
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Allah Ya kula mini da rayuwarki Shatuna, Ubangiji Ya miki zaɓi da mafi alheri ke da ƴan'uwaki gabaɗaya. Riƙe ana nemanki a waya" wayar ta bata ta amsa ita kuma ta juya zuwa inda take yankan atamfa.
Sannu a hankali ta manna wayar a kunnenta tana lumshe idanunta, shima shirun ya yi saboda gabaÉ—aya ya ji hirar da suke yi da Innti. Ciki ciki tana kumbura fuska ta ce
"Hello.....
"Assalamu Alaiki"
Muryarsa me cike da kamala ta sauka a kunnenta ajjiyar zuciya ta sauke tana jingina da bango. Bai jira ta amsa ba ya ce
"Me kike buƙata?"
Shiru taƙi amsawa.
"Nanaah....."
Ya kirata da sunan da yake kiranta, madadin ta amsa sai ya ji kamar tana ɗan shessheƙar kuka. "Nanaah mene?"
"Ni yaushe zaka dawo kuma ka ƙi kirana sai yanzu"
Ya yi jim yana jin damuwarta na sauka a ransa kamar ba zai ce komai ba sai ya ce "To ni da ba kyakkywa ba mene za ki ƙwarzaɓi ranki don ban dawo ba?" Bai bari ta amsa ba ya ɗora da "Ba zan dawo ba, ki faɗa mini me kike so zan aiko miki dashi, idan kinga dama ki yi ta yin rashin kunya Nanaah. Kina faɗawa Innti ke handsome kike so"
"To kai ma ka É—an fara shafa man bilitin mana, kana saka kaya masu kyau ni kawai.....,"
Cikin tsawa ya ce "Heee queit!" Yana faÉ—a ya kashe kiran gabaÉ—aya ta ji tsawar har cikin kanta tabi wayar da kallo tana tura bakinta gaba zuciyarta kuma ta ji babu daÉ—i.
***
Ahlam na zaune a parlour tana bawa yayanta labari na rahotan da ɗazo da taje ɗauka, cikin sanyin muryarta me ɗauke da wani 'sounds' wanda duk ƙarshen harafi sai ka ji kamar tana fitar dashi da sauri ne.
Tana da ƙin-ƙina sosai a saman harshenta, wata baiwa ta Ubangiji muddin akan aikinta ne ko karatun Alkur'ani bata yin ƙin-ƙinar.
"Yaya wai me kishiya ta É—auki abokiyar zamanta ne? Wasu mutanen basu da imani da tausayi sam a cikin lamuransu yaya"
Ya murmusa kawai ya ce
"Ahlam me kika gano ne?"
Cikin damuwa ta ce "Yaya ɗazo da naje ɗaukan rahoto, wata ce mijinta ya yi mata kishiya, yanzu kishiyar ta haihu sai ta ɗauki jaririn ta saka shi a cikin ruwan zafi, kar kaso kaga babyn gabaɗaya ya saɓule"
Engineer ya ce
"Subuhanallahi!"
"Babu kyan gani, da ƙyar bai mutu ba" Anty Jiddah dake zaune kusa da mijinta tana sauraran hirar yaya da ƙanwa cikin raunin murya da damuwa irin ta uwa ta ce "Ai wasu matan basu da imani, wannan ya fita daga kishi ya koma hauka ya kamata hukuma ta shiga cikin lamarin a bi mata haƙƙinta, ban san yaushe ne mutane za su yi hankali ba a wannan rayuwar, kodayaushe wa'adinmu ƙarewa yake, yanzu zaka mutu, yau ne, gobe ne bamu sani ba, da muna da masaniya wataƙila mu yi hankali da wasu abubuwan rayuwar" Ahlam idanunta ya cika da hawaye muryarta na rawa ta ce "Anty abin baƙin ciki mijin yace muddin tai ƙarar kishiyar zuwa hukuma a bakin aurenta, duk wanda ya shigo cewa ake yi ruwan zafi jaririn ya faɗa, mace ɗaya ce abin ya faru akan idanunta ita ce wacce ta fito da maganar ta fara hawa iska kamar wutar daji, da ƙyar ta bani haɗin kai na yi Recorded muryarta, kuma na ga hakan ma babu fa'ida kar na saka a Redio na yi sanadin aurenta, auren fari ne"
"Allah buwayi gagara misali, Allah mun tuba. Zata iya sauya miji amma É—anta fa?"
Ahlam ta kalli Anty Jiddah.
"Bari kawai Anty, ina ganin goge recorded É—in zan yi, kar tsautsayi ya saka na turawa News editor" Alhaji Abdallah ya dubi Ahlam cikin nazari da tunani da nutsuwa ya ce
"Amma wannan kamar opportunity ne kika samu da za ki moving level É—inki a gidan rediyon naku, nasan kece kika fara samun rahoton jaririn, ya kamata ki kai musu"
"Yaya...
"Yaya ina jin tsoro ne"
Ta fashe da wani irin raunataccen kuka, jikinta har rawa yake yi nan da nan hankalin yayan nata ya tashi, ya dawo kusa da ita yana riƙota da kulawa, ganin yadda shanyayyen hannunta ɗaya ya fara rawa shi kaɗai. "Tsoron me kuma kike Ahlam, ki tuna ina tare dake a koyaushe dukkan abin da kike buƙata ko kike so zan miki, ke ƴar jarida ce, matakin farko a fara aikinki, ki tuna daga shigarki kika samu award a 2024, ina ganin wannan labarin zai iya sawa ki samu wani award ɗin a ƙarshen shekarar nan, ki ƙarfafa zuciyarki, ki cire tsoro, daman kun saba ɗaukan kasada, tsoro ko ja da baya bana ɗan jarida bane, wannan mafarkinki ne, burinki ne, ba daga sama kika samu aikin ba, karanta kikai, karatunki ya kai ki wannan matakin, kar ki sare kin ji?"
"Idan na yi mata sanadin igiya uku fa? Idan na yi sanadin aurenta a gidan mijinta fa?"
Ya yi jim, sai ya ce "Hakan ba zai faru ba"
"Idan ya faru fa? Zaka aure ta?"
Anty Jiddah kallon Ahlam kawai take yi tana girgiza ƙafarta hannunta rungume a ƙirjinta ta cije leɓenta, zafi da ɗanɗanon da ta ji ya shiga cikin bakinta, ya bata tabbacin ta datse leɓen da haƙoranta, ta jiwa kanta rauni ne. Miƙewa ta yi da murmushin data ara ta shimfiɗa a fuskarta ta ce "ƴar gatan yaya rigima ake ji yau, ni dai mu kwana lafiya" Abdallah ya bi bayanta da kallo har ta shige cikin part ɗinsu kafin ya sauke nauyayyiyyar ajjiyar zuciya yana kallon ta
Ya ce "Ki je ki kwanta, kinga gobe da wuri za ki tashi, idan na kunna rediyo ina son na ji wannan rahoton daga cikin golden voice ɗinki" rarrashinta ya dinga yi har ya rakata ɗakinta ta je ta kwanta tana tunanin yadda ta bar jaririn matar a saɓule tas ko asibiti anƙi kai shi. A daren ta turawa Editor recorded ɗin tana son amincewa daga wajansa
***
Tsaye ta yi a gaban room ɗin hotel ɗin cikin shigar after dress data ɗora a saman kayan jikinta, ta rufe fuskarta da face mars. Babu jimawa aka buɗe ƙofar da fararan idanunsa ya bita da idanu kafin ya yi baya wajan bata waje ta shige ciki.
"Na fara gajiya da wannan mu'amalar, ni ba matarka ba ni ba budurwa ba nama kasa gane ina muka dosa. Yaushe ne zaka daina yi mini barazana jikina ya fara gazawa"
Jallabiyar jikinsa ya zare ya zago ta bayanta ya rungumeta yana ɓalle after dress ɗin ya ce "Kin samu abin da kike so, nima dole ki bari na yi yadda nake so, tunda nine na kai ki matakin da kikai kai. Don haka quiet ki haɗiye duk wani complain ki bani farinciki a nan" ya ce yana nuna mata gadon ɗakin.
"But sir....
"But what? Fitowa kike so na yi na ce ba ki cancanta ba, ko kuma ba karantar ɓangaren kikai ba, ko kuma ana daƙile wasu ne saboda ke"
Sai ya girgiza kai da faÉ—in "I'm not in the mood ne sir" yana shafa fuskarta ya É—an murmusa kaÉ—an "Never mind, zan dawo dake mood yanzu" yana faÉ—in hakan ya kashe hasken room É—in
***
Cikin dare Ana ta dinga firgita saboda gamon da ta yi a banɗaki ta hana Ifti bacci sam, sai ta dinga rungumeta tana mata addu'a kuma taƙi kiran Innti bata so ta dame ta. Har kusan 1:36 na dare Innti na zaune a tsakar gidan tana yankan ɗinki.
Garam! Sautin bugowar ƙofarsa ya bayar a cikin kunnenta, addu'a ta fara idan ka shiga tsoro da firgicin gamuwa da wata halitta ta Ɗan'Adam. Jin bata ji motsin shi ba, ya saka ta juya a hankali bayan ta ajjiye yadin landin ɗin da take saita kafaɗa zata yanka, zumbur ta miƙe tsaye, a tsakanin miƙewa da tsayuwar bugun zuciyarta na wani lokacin ba zata lissafa wanne ya zarce wani ba.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"
Ta furta a gigice da sautin daya cika gidan ganin Daada tsaye a tsakiyar gidan zigidir haihuwar uwarsa, idan ya miƙe tsaye sai ya sake yanke jiki ya faɗi yana layi da tangaɗi, ko irin ɗan kamfan da maza suke sawa babu a jikinsa, bata san tun yaushe ya kasance tsirara ɗin ba, wandonsa da zabgegen tazugen wandon da yake lilo har ƙasa, ya yi amfani dashi wajan ɗaure wuyansa da tunanin al'aurarsa ya rufe, furfurar kan shi da wacce hazo ya ƙara masa sun yi haɗin gwiwa wajan sake fito da tsofan nasa.
Sambatun giyar bata sake shi ba, a cikin can tsakiyar kan shi jijiyoyin da suke sarrafa tunanin Ɗan'Adam, su sanar da ƙwaƙwalwa halin da gangar jiki take ciki, sune suke aikinsu a tattare da Daada, ya ɗauka har yanzu yana cikin ɗakin Tani suna aikata abin da suka saba. Wani mokaɗe kwankwaso yake yi yana tura shi gaba zuwa bawa.
"Tani ke duniya ce,
Tani zumata, me zaƙi,
Tani kin fi reza kaifi,
Tani kinfi Innti amfani da garÉ—i!"
Jerin baitocin waƙar duka a kunnen Babban yaya da Ana dake ƙoƙarin buɗe ƙofa ta fito waje, cikin sauri Babban yaya ya saka headphone a cikin kunnensa yana juya zaibar idanunsa zuwa shimfiɗar su Jadid da Jaheed, yaga bacci suke yi ɗaya ya yi filo da hannun ɗaya, abin mamaki hannunsu damƙe dana juna a haka suke yin baccin
A gigice Innti ta nufi ƙofar ɗakinsu Ana tun kafin ta fito, karo suka yi. "Ana"
"Na'am" ta faÉ—a a hankali.
"Me za ki fito yi cikin daren nan?"
"Innti na kasa ganin film ɗinsu su Anum da Jarumi a ɗaki, zan kwanta ƙasan bishiya ne"
"Ƙasan bishiya?"
Ta ce da mamaki "Ana anya ba zan kwana ina faÉ—awa Ubangiji lamuranki ba?"
Innti ta maimaita tana buÉ—e mata idanu.
"A daren nan? Bakya tsoron mutanen ɓoye ashe ba ki ɗauki darasi a banɗaki ba Ana?" Ta zubawa Innti manyan idanunta masu saƙar baƙi kamar me son karanto gaskiyar maganar Innti a fuskar tata.
"Koma cikin É—aki"
Da ƙyar ta ce "Bari na sha ruwa"