Sashe 15
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai ya yi ƙwafa kawai.
"DaÉ—in ciwo nishi, inda me maka sannu"
Inji Ƴar Beauty.
Caraf Abar ƙauna ya amshe da faɗin.
"Ni dai ki yi sauri yaya, ina da aikin suyar waina zani yinin suna kuma, kar a yi mini asarar haɗuwa da ƙawayena masu capacity"
"Heeee riii" suka sake saka shewa da haÉ—e kwankwaso waje guda abinsu.
Sukunbiya ya ce "Daman kuÉ—in adashi na kawo gashi, ina neman alfarma a bani zubi na gaba, saboda bikin Æ´ar aminiyata za'a yi"
Ya ranƙwafar da hannu wajan miƙa mata kuɗin, ganin Innti bata amsa ya dire kuɗin ya ce "Na rasa ta cewa, wai uwar gulma ta yi cikin shege, sai aron rigar mamakin za ki bani zani suna yau, naga size ɗinmu ɗaya dake matar Daada, kema dai tubarakallah"
Abar ƙauna ya riƙe zancen da faɗin.
"Kallabi tubani, wai anwa uwar kwarto fyaɗe ya ce mama riƙe mini wando ina zuwa"
"Riiiii!" Suka sake yin shewa.
"Ya naga kina mini kallon hadarin kaji, abin fa duk the same me, wai Ali ya ga Ali"
Cewar Sukunbiya.
Innti ta ce "Bala ka yi haƙuri, bana bada kayan sawata, kar ka sake mini haka"
Ya riƙe haɓa ya ce "Oh ni Sukunbiya abin zubawa a miya, ina ruwan gayyar tsiya arna a idi abin arziƙi bai amshe ni ba ni dai kam"
Ƴar Beauty ya ce.
"Yaya muje don Allah, na ji kamar al'adata ce take bin ƙafafuwana, muje muje ni"
Suka rankaya tare da ficewa suna sakarwa Innti habaice-habaice ita dai bata kula su ba. "MahaÉ—ita Yaa Sam ya dawo fa"
"Me ƙarya?"
"ÆŠan aljanna, yana waje ma"
Cikin sauri ta zura hijab É—inta, rabon data fita waje har ta manta makaranta ke fitar da ita, kuma kwana biyu bata je kwata-kwata.
Sanda ta fita bata same shi a waje ba, sai ta shiga gidansu ta tarar da Mama zaune tana suya gyaÉ—a ta ce "Barka da yamma mama?"
Mama na dariya ta ce "Ana manya, muddin naga ƙafafuwanki a gidan nan mutuminki ne ya dawo, yanzu ya fita yana shagonsu na waje ai" murmushin kawai Ana ta yi ta nufi waje, a bakin shagon ta tsaya tana bubbugawa, yana jinta bai amsa ba, ta gaji ta bugawa ta leƙa sai taka ya miƙe tsaye yana gyara rigarsa ya fito.
"Yaushe ka dawo?"
Ya dube ta tsam ta grey eyes É—insa ya sake yin fresh fuskarsa na É—aukan ido sai ya ce "ban sani ba"
"Au sorry faÉ—a muka yi ne? Naga ka yi fari ko bilitin É—in ka fara ne, ina yini ya hanya?" Bakinta kawai yake kallo.
Ƙafarta ya kalla yaga takalminta ya lalace sosai kafin ya ce " kin rame"
Kamar me jira ta shawagaɓe masa fuska blue eyes ɗinta ta juya ta ce "To ba kai bane"
"Ni?" Ya nuna kan shi da yatsa.
"Baka sake kirana a wayar Yaa Jaheed na duk na damu"
A kasalance ya ce "Ban niyya ba"
Sai ta fara yarfe hannunta tana shirin yi masa kuka abin da ba ɗabi'arta ba, ya tsuke kyakkyawar fuskarsa ya ce "Kar ki mini banso" sai ta yi ƙasa da kanta kawai.
"How many times zan ce ban son shawagaɓar nan Nanaah?"
Ita dai ba ta yi magana ba, ya ce
"Muje"
Ta ce "Ina?"
"Siyar dake"
***
A gurguje Gana ta shige cikin bukkarta tana sakin assabari, ajjiyar zuciya ta sauke kafin ta sunkuya ƙasan ƙaramin gadonta ta janyo wani kasko ta fito da baƙin ƙyalle a hankali ta kuntu gefen zaninta ta ciro ƴar tsokar kurwar jaririn ta ɗaure da baƙin ƙyallen, sai kuma ta saka a cikin kaskon ta zura cikin wata kwarya ta rufe. Wani kwano ta ɗakko me ɗauke da mai fal ciki, ta saka yatsa ta lashi man a bakinta tana jin garɗi da daɗin man na ratsa cikin kunnuwanta saboda daɗi
"Allah ka sake haɗani da mai maiƙo a jiki kamar Hansai, wayyo daɗi wayyo daɗi"
Ta sake laso man ta kai bakinta.
"Kamar na sayarwa da Alhaji kurwar nan, kamar na yi watanda a kanta" ta fara tunani.
Sai kuma ta ɓata fuska sosai
"Ina son kuÉ—in kuma"
Can ta yi tsaki ta ce "Ina son jaririn ma"
***
A bakin shagon Ana ta tsaya Yana Sam kuma na can gefe yana yin waya hannunsa cikin alijuhu yana daga inda yake yana hangota. Ita bata saba tsayuwar shagon katin nan ba, gashi ko ta kira sunan Jaheed ba ji zai ba. A cikin cunkoson wajan ta ji an zura hannu ana shafo ta, sai ta yi banza ta sake jin an shafo bayanta cikin sauri ta juya idanunta na rinewa ta kalli yaron ta ce "Ajjiyar me ka yi a jikina da kake shafani, É—an iska ne kai? Uban me kake nema?"
Gabaɗaya mutanen wajan suka juyo suna kallon Ana, kamar basu taɓa ganin mace ba sai a kanta musamman yadda take juya manyan idanun nan nata, sai ya ce
"Ni za ki wa sharri?"
Tai wani irin luu da idanunta kamar za ta yi bacci ta buÉ—e su akan shi, fuskarta ta haÉ—e ta watsa kamilallun idanunta akan shi.
"Ashe ban ji sanda kake taɓa ni ba"
Ta sake faÉ—a kamar bata son magana.
Wani ya ce "Ke yarinyar nan me zai taɓa a jikin naki, ko dai ba ki ji dai-dai bane?"
"Me namiji yake taɓawa a jikin mace?"
Caraf yaron ya ce "Sharri ma take yi mini"
Wani irin haske ne ya bayyana a idanun Ana ya sauka akan yaron jikinta har wani irin rawa yake yi ta ce "Ban taɓa yi wa wani sharri ba, ban yafe ba ɗan iska kawai, in sha Allah sai kaga abin da zai same ka"
Wani irin ɗaci take ji a maƙoshinta, ta tsani a ƙaryatata, ta sani a nemi cin zarafinta, gata da wata baƙar zuciya da riƙe abu a rai
"Kake cewa na maka sharri?"
Ta runtse idanunta, ta sake ware idanun wannan hasken me kama da magic ya sake sauka akan yaron "Zaka gani"
Ganin abin na neman zama rigima aka ce yaron ya tafi zuwa wani kantin, ita kuma ta cije a wajan jikinta sai kakkarwa yake yi.
Yaron na ƙoƙarin juyawa kawai ya faɗi a wajan yana murɗewa idanunsa suka kakkafe, cikin sauri ta kalli yaron domin itama ta tsorata sosai sai ta juya caraf wani ya riƙe hannunta ya ce "Mayya ina za ki bayan ki kama yaron mutane shine za ki gudu?" Da rashin fahimta Ana take kallon cikin idanun mutumin ranta ya sake ɓaci ta rasa abin cewa, da alama yau bata da sa'a. Wani ya ce "Daman ta ce zai gani"
"Kuma zai ga abin da zai same shi" in ji wani.
Mutumin ya ce "Bidiri kashin rana da kiÉ—a, gashin nan tun ba'a yi nisa ba ta kame shi"
Nan da nan wajan ya cika ana faÉ—in.
"Mayya ce Mayya ce"
Mene kuma mayya? Wani abu ne hakan da bata san dashi ba har ake jifanta dashi?
Gabaɗaya sai ta rasa fahimta ta zama confused lokaci guda, ta haɗiye wani abu mai ciwo a ƙirji taƙi barin ruwan daya taru a cikin idanunta zuba, wanda ya sake sawa idanun nata suka sake zama manya.
"Ni ba mayya bace, me na yi masa?"
"Ai wallahi babu inda za ki sai kin tsallaka shi" cewar yayan yaron daya ƙarasu.
Jaheed bai san meke faruwa ba, domin ko da wasa bai taɓa tunanin Ana zata fito ba, balle har ta ƙarasu kantin nasu.
"Kul, kurwata kur ina faÉ—a miki" mutumin ya sake furtawa yana jefa wa Ana harara
"Idan kun su ko kashe ni, babu wanda ya isa na tsallaka yaron nan, ku kuka san wata mayya kamar wani man shafawa aikin banza" sannu a hankali Yaa Sam ya ƙarasu wajan saboda hayaniyar da ta yi yawa, kuma ya hango Ana a tsakiyar mutanen, ya dubi mutanen kaf ya kalli Ana sai ya ce "Menene?" Cikin rawar murya ta ce
"Wai ni ce Mayya zai na tsallaka yaron nan"
"Mayya?" Yaa Sam ya nanata sunan a ƙasan ranshi. Sai ya kalli mutanen wajan ya ce
"Kun yi kuskuren fahimta, ba ita bace"
Yayan yaron ya ce
"Wallahi sai ta tsallaka ƙanina sau uku, ko mu ƙone ta da taya a wajan nan a rage iri, wato a bari ta tafi gida, idan yaso ta cinye shi a can ko?" Ana ta kalle shi sosai.
"Idan baka ƙona ni baka cika ɗan halak ba"
Yaa Sam kallon ta ya dinga yi
Daman ana cin mutum ne?
Ganin al'amarin ya zama babba ya saka Yaa Sam sassauta murya yana kallon Ana
Ya ce
"Tsallaka shi, ki goge shakkun ransu"
Sai a lokacin ne ruwan idanunta ya yi kamar zai sauka da sauri ta haÉ—iye hawayen ta ce
"Kaima kallon mayyar kake mini? Wallahi tallahi sai dai su kashe ni amma ba zan taɓa tsallaka shi ba....
*H I Y A A M*
Page 5: Six Worlds Around Me
Bright pens
Yota/001
“I pray that Allah grants you Jannah together with your parents.†Nazeefah Sabo Nashe.
Page É—in yau naku ne, Rabi'ahtu Achadu Fulani gal tare da Hiyaam book channel Allah Ya saka muku da alheri ya biya ku da Aljanna.
"Ko duka garin nan gatanki ne, wallahi sai kin zo kin tsallaka yaron nan ya tashi, mayyar banza mayyar wofi masu cinye kurwar mutane a duhu" wani irin kallon gefen hagu ta yi wa yayan yaron ta ce "Bani da gatan daya shige na Allah da kuma mutanen shidan da suke tare dani, maita kuma kai ne mayen bani Æ´ar gidan Innti ba"
Yadda take furucin a hankali ɗaya bayan ɗaya, da yadda idanunta sukai jajur wajan sauya launi amma taurin zuciya ya hanata zubar da hawaye zai tabbatar wa duk wanda yake wajan ranta ya kai maƙura wajan ɓaci. A nutse ta sake juya idanunta akan Yaa Sam, kafin ta mayar da ganinta kan yaron dake kwance har yanzu, sai ta yi baya kaɗan tana ƙoƙarin juyawa ta bar wajan. Caraf wani dattijo ya riƙe gefen hijabinta yana faɗin "Guduwa za ta yi"