← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 64

Sashe 33

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hanyar fita daga ɗakin ya nufa da ƙarfi ya ji ta ce "Abbaa" jikinsa na rawa ya juya yana tambayar mene sai ta ce "Ina son ka Abbaa"

Girgiza kai ya yi ya fita cike da karyewar zuciya da tunani kala-kala a ransa ya nufi titi neman me napep ya É—auke su zuwa gida.

Haysaam.
Yana zaune a cikin ofis ɗin likitan ya zuba masa ido tare da sauraran abin da yake cewa cike da zallar nutsuwa da fahimta. Dr ya gyara zama ya ce "Wannan yarinyar Allah ne ya yi tana da sauran kwana Sam, ga binciken da muka yi abin da ya nuna" ya tura files ɗin gaban Sam ya ɗora da faɗin. "Bincike ya nuna ta samu tabo a mahaifarta dalilin dukan da akai mata, wanda a turance muke kiran matsalar da SCAR wani gurɓataccen nama ne da jiki ke ƙirƙira bayan rauni ya warke. Idan aka samu duka, ita kuma ta samu Scar a MAHAIFA (uterus) wanda zai haifar mata da miscarriage, ko ta samu wahala wajan samun ciki, wahala wajan saduwa. Zubar jini mai yawa (internal ko external bleeding) don haka disvirging nata zai wahala, kamar yadda ɗaukan ciki zai mata wahala. Wannan serious issue ne Haysaam, yana da kyau duk wanda zai nemi aurenta ya san da wannan matsalar Please"

Wata zufa ce ta shiga tsastafowa Haysaam ta tsakiyar goshinsa, ya yi shiru bayan ɗora kan shi da ya yi a saman table ɗin dake gaban likitan, jikinsa duka rawa yake yi kamar an watsa masa ruwan ƙarƙara wanda ya yi daidai da lokacin hunturu ƙofofin da suke lulluɓe gargasar jikinsa, ya yi shiru.

"Haysaam....

Likitan ya kira shi da kulawa. "Naga ka damu da Chocolate girl ɗin nan, ka yi haƙuri kowa da ƙaddararsa, ka dai ja mata kunne akan wasan banza ko don lafiyar jikinta"

Haysaam ya kasa magana, dr ya dafa ƙafaɗarsa "A kula sosai da jikinta, a faɗawa wanda zai aure ta" a hankali Sam ya ɗago kan shi ya watsa rinannun idanunsa a fuskar Dr a kasalance ya ce "Ina son maganar nan ta zama sirri, kar yarinyar ta ji haka mahaifin yarinyar ka bar ta daga ni sai kai" Dr ya buɗe ido da mamaki "Amma ta ya ya wannan matsalar zata zama sirri, bayan dole ta yi aure ta zauna a gidan mijinta?" Haysaam ya ce

"Dole ta zama sirri Dr "

"Ok tell me how? Tayaya......

"Saboda ni ne mijin, ni zan aureta" ya nuna kan shi da yatsa

"What!" Dr ya furta da sauti na zallar mamaki.

"Haysaam baka yi mini kala da wanda hankalinsa ya bar jikinsa ba, kana son sadaukar da lafiyarka saboda ita ne?"

A ɗan harzuƙe Sam ya ce "Ok Kamal, Ka faɗa mini ya kake so ayi, ya kake so yarinyar ta fahimci rayuwarta zuwa nan gaba? Wannan ba zai zama hujja kaɗai ba, bai zama hujjar da zaka gina na cewa na yi Sacrifices ba, idan sadaukarwa zan yi mata nawa ke buƙatar hakan, na je gidan gyaran hali, ko gidan karuwai, ko gidan marayu zan iya ruskar matan da zan iya zaɓa na yi Sacrifices akan su" sai ya yi baya kaɗan ya taka a hankali zuwa gaban Dr Kamal ya ce "Wannan daban yake, dalilin ma daban na, is difference Kamal ina fatan zaka fahimta" Dr Kamal ya ce

"Matsalar soyayya?"

"I did say it.....

"You don't need to say it ai dama, baka buƙatar ka ce ma, your action shows. Soyayya kaɗan ke rufe idanunta mutum ya gaza gane gaskiya, ta ya zaka auri yarinyar da zaka iya ƙare rayuwarka babu haihuwar ko kuma ka ƙare rayuwar ba tare daka taɓa saninta a matsayin mace ba?' ƙuri Sam ya yi da jajayen idanunsa akan fuskar Kamal. "Ai ya zame maka dole ka kalle ni, ba zan ɗauki wannan rubbish ɗin ba, akan wannan yarinyar ko farcen da zaka sosa jikinka wallahi sai ka neme shi ka rasa, ka ɗauki responsibilities ɗin daba naka ba, ka ɗora wa kanka kazar tsaba haka za ta yi ta binka. Kai ne suttura, kai ne kayan abinci, kai ne kayan ƙyale ƙyale na mata. Babban takaicin ma, yadda ta fito daga maragurbin gida, kallon turɓaya nake mata, gidan da basu da tarbiyya ko ta misƙala zarratan........,"

"Kau.... Kau!" Haysaam ya ɗauke Dr Kamal da wasu maruka lokaci guda, wanda ƙarfinsu ya bada wani irin sauti. Ya dafe kunci yana kallon Haysaam ya ce "Mari?"

"Marina ka yi akan yarinyar can fa Haysaam?"

"Zan iya yi maka fiye da mari akanta. Sai dai wannan marin ya sha bambam da tunaninka. Rayuwarta kake kallo kawai, mahaifinta kake dubawa kawai, baka san wacece ita da irin tarbiyyar data samu ba"

A zafafe Kamal ya ce "Tarbiyya banza da wofi, tarbiyya idan irin ta gidansu ce Allah Ya tsine mata, ko kyauta za'a bani auren mace a gidan nan banga uwar da zan yi da ita ba. Har shine kake da zafin zuciyar marina akan ta?" Da wata irin zafin zuciya shima Sam ya yunƙuro kan Kamal ya ce "Kasan zafi da raɗaɗin da yake cikin muzanta ɗiya mace? Idan maganar tarbiyya kake akaso ɗari na tarbiyyar yarinyar nan kaso talatin nawa ne, kashi hamsin na babarta kashi ashirin na Yaa Marwaan"

"Matse muku ta yi kai dasu, amma alamu yana nuna shaiɗaniyya ce alaƙarka kai da ita babu alheri tunda har ka iya marina akan ta" wani irin huci su biyun suke fitarwa kamar masu ganin hanjin juna, fuuuu kuma Sam ya juya. "Kazo ka bani kuɗin treatment ɗin da na yi mata don ubanka ni ba bawa bane" cewar Dr Kamal yana ɗaga murya amma ko ta kan shi Sam bai bi. Ko da ya fito daga ofis ɗin sai daya tsaya ya samawa kan shi nutsuwa ya saita fushinsa kafin ya ƙarasa room ɗin da take ciki a nutse abin shi

Bacci ne ya ɗauke ta tana rungume da hannunta a ƙirji kanta a tsakiyar katifar gadon gashin ya barbaje numfashinta na sauka a ƙirjinta a hankali tana sakin ajjiyar zuciya kamar wacce ta yi gudun tsira da rai. Haysaam ya jima tsaye a kanta ya zuba mata idanunsa a cikin jinya take amma sosai ta yi masa kyawun gani a cikin idanunsa. Yaja nasa idanun ya lumshe yana haƙaito lokacin, da ranar daya fara sanyata a cikin idanunsa, ranar daya fara ganinta.

Wata ranar talata ce, da farar safiya ya fito sanye da fararan kaya wanda suka kasance uniform, ranar da zai rubuta jarrabawar ƙarshe a Rumfa College lokacin yana Sakandire. Yana tsaye ya zubawa gefe guda ido yana lissafin yadda zai taka a ƙafa daga nan Kankarofi zuwa Rumfa College ɗin. Murmushinta ya ji, murmushinta ya fara ji ya sauka a cikin kunnensa, idan ba zai mata ba abu biyu daya gani a tattare da ita bayan murmushinta shine yatsun hannunta, wanda ta yi amfani dasu wajan riƙe tsinke tana yin zane na haƙa rami za ta yi ƴar carafke ake cewa, bai ba gama sanin sunansa ba. Kasancewar ɗaukewar ruwan sama kenan, wanda yana daga cikin abin da ya saka shi yin latti a makaranta. Bayan yatsun hannunta sai sumar kanta wacce aka rabata gida biyu aka tufke. Babu takalmi aƙafar kamar yadda ya lura da koɗewar kayan jikinta. Bai mata magana ba, ya nufi shigewa ta ƙofar gidansu a sama ya ji ta ce

"Ramina... Wayyo ka rufe mini ramina"

Ya ji wannan karaÉ—in, ya ji slow voice É—inta.

"Ƴaƴana na wasa suna ciki, wayyo ni" Cak ya tsaya a wancan lokacin ya juya ya kalle ta, bashi take kallo ba, hankalinta yana kan abin da take ƙorafin ya yi mata ɗin.

"Ƙazama" abin da ya furta kenan. "Ba ƙazama bace ni, mahaɗita nake jira ta fito mu yi wasa shine ka cike mini ramina"

Sai ya dakata gabaÉ—aya fuska a tsuke ya ce

"Tashi a nan wajan"

Sanda ya fara ganin ƙwayar idanunta sai da ya yi tasbihi a cikin ransa, ba ƙwayar ido ce bai saba gani ba, hasken daya fito daga cikin nata ya shiga nasa shine abin da bai taɓa fuskanta ba a rayuwarsa, bayan hasken shine manyan da ƙwayar idanun nata suka kasance dashi, sai kuma shuɗiyar kala madadin baƙa. "Idan ba ƙazami ba, wake wasa a turɓaya?" Ita dai kallonsa take yi, kallon da bata taɓa tsayawa ta yi wa wani ba, idan aka ɗauke ƴan gidansu.

"Kana da kyau"

"You're very handsome"

Ya ji kyau ɗin, ya kuma yi mamakin fitar turanci daga cikin bakinta. Miƙewa ta yi tsaye sai ya lura jikinta ya girme wa shekarunta, ya kuma lura da yadda take ƙyanƙyamin turɓaya kamar ma akwai abin da ya fito da ita daga cikin gidan. Ya nisa yace "Ina takalmanki? Kallabinki?"

"Suna gida" bata bari ya sake yin wata maganar ba ta shige cikin gidansu a nutse.

Motsin da ta yi a saman gadon ya tilatsa Haysaam dawowa daga tunanin abin da ya shuɗe, gani ya yi tana jujjuya kanta zufa na yanko mata a goshinta sai ya ranƙwafa kaɗan ya kalle ta, har numfashinta na sauka a saman fuskarsa. "Nanaah.... Nanaah..."

"Kai na....

"Kaina Yaa Sam zai cire"

Da farko ya rasa abin yi, domin yana avoiding duk abin da zai haɗa shi da ita wanda yake a haramce. Amma alaƙar shi da Ana tafi ƙarfin haka, mu shi da kan shi shaiɗan zai ji kunyar kunno kan shi cikin su. Hannunsa biyu ya ɗauka ya ɗauki kanta ya ɗora a cinyarsa ya ɗora tafin hannunsa yana murza kan nata. Babu jimawa ta sauke numfashi tare da buɗe idanun. "Nagode"

Ta ce a sanyaye. Ya yi mata ƙuri da ido.

"Ya jikin naki?"

"Allahamdulilah"

Ya jinjina kai ya ce "Sakko muje"

"Lagos?"

Harara ya watsa mata ya ce "Ba za ki raba kan ki da zuwa Lagos ba?" Sai ta ɓata fuska taƙi cewa komai. Rufaida fura ya ɗakko ya saka cokalin ya nufi bakinta ya ce "Sha tukunna sai mu yi magana" ƙin kula shi ta yi.

"Niko?" Ta yi shiru.
Chapter 33 · 0% Book details