← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 64

Sashe 37

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Saboda ƙarya ce tsantsa a rahoton naki" Jiki a saɓule ta miƙe tare da ficewa daga cikin ofis ɗin, hawayen daya ciki idanunta ya tilasta mata tsayawa a wajan tana share su da shanyayyen hannunta, a daidai lokacin ne kuma ta ji sautin dariyar Yussy shine ta ɗora da wancan maganar ta sake faɗin. "Ki koma ki nemi tabarma da roba ki fara zaman bakin titi Ahlam, trust me za ki samu sadaƙa sosai. Nakasassu basu da wata sana'a ai bayan wannan. Amma kinga aikin jarida?" Sai ta yi shiru tana cije lips ɗinta da kallon Ahlam na wani lokacin. "Za ki ji fa kamar muguwar shawara nake ba ki, ki saka a zuciyarki ni me son ki ce, idan kuma kika tilasta a wannan sabgar to haƙarki ba zata taɓa cimma ruwa ba, babu inda za ki je a aikin jarida, ki duba kamar haka.....,"

Ta nuna ofis É—in da Ahlam ta fito, tare da nuna rahotannin da suke hannunta ta ce

"Haka ce zata dinga faruwa dake daga nan har a kore ki daga aikin jarida wallahi"

Wani irin murmushi Ahlam ta saki bayan ta gama goge hawayen kallon sama da ƙasa ta yi wa Yussy ta ce "Ashe kina tara sani da Allah Yussy, ashe kin san me gobe zata haifar ko?" Cikin sauri Yussy ta ce "Ke kam gobenki ai ta jima da bayyana a idanun jama'a" A wannan karan ma murmushi Ahlam ta yi ba ta ce komai ba ta yi gaba.Har ta tafi ta ɗan tsaya ta ce

"Yussy ki rubuta ki ajjiye in sha Allah muryar Ahlam sai ta kare duniya ba iya jihar nan ba, ba iya ƙasar nan ba, duniya gabaɗaya. Na yi miki alƙawarin sai muryar Ahlam ta hanaki bacci Yussy, idan kin shirya na shirya shege ka fasa" tana faɗin hakan ta yi gaba abinta.

*Ajjiyar zuciya Ahlam ta sauke bayan ta gama tuna kaɗan daga cikin wulaƙancin da Yussy take ba, ta dubi hannunta dake maƙale a fili ta ce "Kai ina, Impossible wannan hannun ba zai taɓa hanani cimma burina ba" duk abin da zai faru tana buƙatar samun Outstanding Journalist Award. Sai ta fara tunanin wanne irin abu za ta yi in few days da zai saka ta samu wannan Award ɗin? Ta runtse idanunta ta sake buɗe su.

"Think Think.....

"Ahlam think"

Wayarta ta É—akko ta kira Anees tasan yana da night duty bai yi bacci ba yanzu ba. Bayan ya É—aga kiran ta cikin wayar ya ce "Baby ya jikin naki?" Da nutsuwarta ta ce

"Da sauƙi"

"Ma sha Allah. Akwai wani abu ne?" Ta sauke ajjiyar zuciya

"Anees"

Calmly ya ce "Na'am"

"Kana ganin idan na yi Interview da Sayyadi Baffa zan iya samun karramawa ta musamman?" Anees ya yi shiru domin a bazata ya ji maganar tata. "Ka yi shiru"

Ya ce "Wa kika ce baby?"

"Sayyadi Baffa"

Wani ƙarfaffan numfashi yaja a ƙirji ya fesar mata dashi ta cikin wayar, da ƙyar ya ce "Kin taɓa ganinsa ne? Kina da hanyar da za ki ganshi har ki yi Interview dashi? Hakan ba mai yiyuwa bane baby, ki sauya idea ba za ki taɓa samun dabar yin hira da Sayyadi Baffa ba" jikinta na wani irin rawa da ɓari cikin karyewar murya kamar za ta yi kuka ta ce "Don me ya sa? Shi ɗin ba mutum bane?"

Anees ya ce "Of course mutum ne, amma ba gamagarin mutum ba, to cut the conversation short da ace hira da Sayyadi Baffa abu ne me sauƙi to da tuni Bright Fm ta yi hakan. Daga nan jiharmu da ƙasar babu wata gidan jarida daya taɓa yin hira dashi wallahi Allah, mutumin da ko ganinsa ba'a taɓa yi ba, saboda taka tsantsan irin nasa" shiru Ahlam ta yi domin ita Sayyadi Baffa shine target ɗinta akan shi ta ɗora duka hope ɗinta. A hankali ta ce "Amma Anees mene dabarar hakan da yake ɓoye kan shi? Na ji ance kamar yana da raya ko?"

"Nima a haka na ji wai yana tagwayen yara amma babu tabbaci, domin babu wanda ya taɓa ganinsu. Kin ɓaro aiki babba baby"

"Uhmmm" ya ji taja numfashi ya yi saurin lumshe idanunsa yana sosa ƙirjinsa a nutse

"Trust me Anees zan yi shira da Sayyadi Baffa, zan zama ta farko zan É—aga Bright Fm da hirata da Sayyadi Baffa ka yi mini addu'a"

"Best of luck baby, ki yi a hankali kuma"

"I will.... Definitely"

Ta sake cewa "Anees, I'll make my words"

"Idan ya tabbata haka ne daga Bright Fm za ki shige Special training opportunity NIJ Lagos, kina kammala sai BBC yin attachment" idanunta ya cicciko da hawaye cikin rawar murya ta ce "da har abada bani da bakin yi wa Ubangiji godiya daya ƙaddara mini cikar burina ina raye ina kallo, maƙiyana za su kalli ɗaukakata babu yadda suka iya, Anees bani da burin daya shige na ganni a BBC ko VOA" cikin ƙasa da murya ya ce

"Za ki cika burinki da yardar Allah baby" Ta ce

"Allah Ya sa. Good night"

"I love you... I so much love you Ahlam"

Ƙit ya ji ta kashe wayar ya yi murmushi yana ajjiye wayar shima. A hankali kuma ta shiga tunanin kalmar Tiv dake mata yawo a cikin kanta da zuciya.

**Tana tsaye a harabar masarautar jikinta sanye da wani ƙyalle da kuma wasu ganye manya, manyan mutane maza da mata sun kewaye ta suna mata kirari da kuka tare da roƙo da magiya, ga wani kaɗe-kaɗe da suke yi. Da rawar ɗari ta ce "Su waye ku? Me kuke buƙata a wajena, ina ne nan waye kawo ni nan wajan" ta shiga tambayar su, da alama basa jin hausa koma suna ji alamun hakan bai nuna a tattare dasu ba, ita sai taga kamar ma naman mutane suke ci. Wani daga cikinsu ne ya zube a ƙasa daidai ƙafafuwansa ya ce "Kakanninmu sun shuɗe suna zaman jiranki, Iyayenmu sun tafi da baƙinciki rashin ganinki, mun rasa rayuka da dama saboda ƙin bayyanarki, mun rasa dukiya mun rasa ƙarfi da iko, mun shiga cikin fushin Akombo. Ki cece mu MAMA ki dawo mana da kima da martabar TAJMAHAR, kece UWA MAMA a gare mu"

A kiÉ—ime ta yi baya ta ce "Wallahi bani bace, ni ban san wata uwa mama ba, sunana Ahlam ku rabu dani bani bace wallahi" ihu da kuma kawai take yi

"Subuhanallahi baby ke da waye haka?"

Engineer ya shigo cikin ɗakin da gudu yana riƙe ta ganin yadda take fusge fusge tana cewa ba ita bace ihunta ya cika gidan nasu.

"Abban Mufeed anya ba za'a haƙura da aikin nan na Ahlam ba, mijinta me rufin asiri ne zai iya kulawa da ita, na fara jin tsoro gaskiya" girgiza kai Engineer ya yi yana rungume da Ahlam tare da tofa mata addu'a yana jin yadda ta ƙanƙame shi kamar ance za'a ƙwace ta daga wajansa sai numfashi da ajjiyar zuciya take saukewa.

"Sannu kakata, tsofan ne ya motsa?" Da ƙyar ta yi maganar saboda wani abu daya tsaya mata ganin yadda Abban Mufeed ya rungume Ahlam. Ahlam ta ce

"Tsoro nake ji Anty Jiddah"

"Baby ko za ki haƙura da aikin nan?" Engineer ya ce "Hawwa'u Ubangiji baya jarabtar bawa sai ace yabar abu? Sakaci ne irin na yaran zamani wataƙila haka ta kwanta babu alwala balle addu'a ba dole mutum ya dinga mugwayen mafarkai ba" ya duba lokaci ya ce "Zan tafi masallaci kar na makara ki tashi ki yi alwala ki tabbata kin yi lafila tare da azkar" Anty Jiddah ta ce

"Baka jin firgitar da na yi ba, har cikina ne ya juya na É—auka ko biyota aka yi har gida" Bayan mijinta tabi suka fita a tare Ahlam ta yi shiru tana tuna mafarkin da ta yi.

*
Sanda Mu'alim ya sauke Iftihal akan corner ɗin unguwarsu bata jira sun yi magana ba, shi ɗinma da yake ƙoƙarin cewa wani abu sai ya samu rashin kuzarin tanka ta, ya fahimci tsoro da firgici a tattare da yarinya, bai san dalili ba, kamar yadda bai san wani abu na musamman da ya fusgi ra'ayinsa akan ta, ya ji ta yi masa, ya kuma gamsu ta yi ɗin, ya ji ta cancanci ta zama Mrs Al'ameen Hafizz Baffa, mata a wajan Mu'alim. Kamar ma bata taɓa shiga mota irin wannan ba idan ka ɗauke batun napep yana kallon yadda take takawa a hankali har ya isa corner. A hankali ya sauke gilashin motarsa ya ɗan leƙa, shi kamar ji ya yi ta ce "My Mu'alim" daidai lokacin itama ta juyo suka haɗa idanu sai ya jinjina mata kai alamar ta shige ciki.

Ashe dai kiran nasa ta yi, ba kira na baki ba, kira dake tsakanin zuciya da zuciya. Ya ɗauki lokaci kafin ya iya kunna motar ya yi reverse ya bar Kankarofin gabaɗaya ya nufi Maitama Sule, da zumuɗin ƙara ganinta.

Kamar mara gaskiya haka Iftihal ta shiga gidan nasu da sallama suka amsa mata, a cikin muryoyin da ta ji babu ta mahaÉ—inta cikin damuwa ta shiga rarraba idanu ta kalli Innti ta ce "Ina mahaÉ—ita Innti?" A sanyaye ta ce

"Tana ciki, sai yanzu Iftihal?"

"E, ya gida Sahibarmu? Ya aiki da jikin mahaɗita?" Innti ce ta miƙa hannunta wajan riƙo hannun Iftihal ta zaunar da ita kusa da ita ta ce "Ita kam da sauƙi naga, Yaa Jadid ne jikin nasa sai godiyar Ubangiji, wankin ƙoda yake buƙata, babu kuɗi wajena na kuma rasa mafita da abin yi, ɗazo ma jikin tsoro ya bani, ganin yarona na sha wahala ga abu bane me sauƙi da zuciyata zata jure"

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Iftihal ta faɗa tana runtse idanunta, another banger, another problem. Su kam me rayuwa take nufi da tasu rayuwar ne. A hankali ta ce "Innti kuɗin dashi, ki ari kuɗin dashin mana tunda daman Baba Bala za ki bawa ɗauka, zai yi miki lamunin rance zuwa ki samu ko?" Innti ta yi shiru domin bata son tace an sace kuɗin, babu ɓarawo a yaranta kai tsaye za su ce Daada ne
Chapter 37 · 0% Book details