← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 64

Sashe 13

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Oh; Yes, na duba komai ya yi kyau kin yi aiki me kyau kuma me muhimmaci, ni kaina hankalina ya tashi dana saurara ban yi ƙasa a qwiwa ba na tura shi bayan na tace komai" ya ce yana yin baya da juya kujerar.

Ahlam ta fiddo idanunta wajan faÉ—in.

"Ina ka tura shi Sir?"

"Editor-in-Chief, is there any problem?"

Shiru ta yi har zata miƙe tsaye ta ce "Sir ka gyara zaman tea cup ɗin zai iya faɗuwa ya zube maka a ƙafa, idan ka ƙone ai muna cikin wani hali" kallon cup ɗin ya yi sai ya kalle ta.

"Babu wani faɗuwa....," bai ƙarasa faɗa maganar ta tsaya masa ta dalilin rikitowar cup ɗin da shayin zuwa ƙasa, Ahlam ta hangame baki cike da tsoro ta yi baya tana faɗin

"Sannu sir, bari na...,"

"Hold on please Ahlam, ki faɗa mini gaskiya ya akai kika san cup ɗin zai faɗi da shayin? Da faɗar da kikai ko minti uku ba'ayi ba ya kifo mini a ƙafa" kai ta shiga girgiza wa da alamar jarumta a tattare da ita ta ce "Kawai na faɗa ne bana nufin hakan" Wani kallo ya yi mata wannan shi ne karo na uku tana musu a gidan rediyon nan yana faruwa wani abu kamar camfi "kina nufin bakya tsafi?"

Ta girgiza kai sai kuma ta yi saurin tashi tsaye ta yi masa godiya ta fita, cikin sassarfa bata ganin ko gabanta ta nufi office ɗin Editor-in-chief, tana ƙoƙarin yin corner ta ji ta yi ƙaro da ƙirjin mutum, a kiɗime ta yi baya tana rarraba idanunta, tare da dafe goshinta, ya tsaya cak daga tafiyar da yake yi yana juya idanunsa a kanta, wacce take biye dashi ce ta yi siririn tsaki wajan furta "Kin fita daga cikin hankalinki ne da za ki dinga tafiya anyhow, duk yadda zuciya ta raya miki kamar a filin gidanku?"

Ahlam ta zubawa Yusraah idanunta, kamar da biyu take mata faɗan, kamar bata lura cewa abin da ya faru unexpected ne ba, ba da gangan ta yi ba, ta ya ya zata tsara buge mutumin daya girme mata, ya zama sama da ita a gidan rediyon, yake sama da kowa ma. Dukkan su ai suna ƙarƙashinsa ne, a ƙasan MD suke shi kuma yake ƙasan Founder, kamar bata lura shima ya yi mata rauni da buɗaɗɗan ƙirjinsa ba, ko ita Yusraah bata gani ne, bata kuma fahimta.

"I'm very sorry Sir"

Shine abin da ya suɓuce daga cikin bakinta, ba tare data lura daya jima da barin wajan ba. "Ga iyayi ga nakasa, a dole sai an ɗaukaka wai, mu zuba mu gani ni dake babu wani cigaba da za ki kawo wanda zai iya moving level ɗinki daga yadda kike ɗaukaka sai dai ki ga ana yi wallahi"

"Yussy, ai ban É—auka kina halitta ba" Yusraah ta ce

"Kar ki mini rashin É—a'a yanzu na miki illa"

Ahlam ta yi murmushi tana cije bakinta tana kallon Yussy ta ce "Bayan rashin aji dake É—awainiyya dake ashe hadda rashin ilimin addini ne ke damunki Yussy."

"Ni kike faÉ—awa haka"

"Na faɗa miki ki saka mini gas idan za ki iya, wacece ke da za ki fara mini ihu a saman kaina, da faɗan zan ji ko da muryarki dake neman tarwatsa dodon kunnena, maganar nakasa da kike, na yarda ina da nakasa, amma nakasata bata taɓa zama kasawa a gare ni ta zama hujjar zama raunin Ahlam ba, kina ji kina kallo da wannan nakasar Ahlam zata kafa tarihin da har abada Yusraah bata kafa ba, kuma ki faɗawa me sama cewa bai iya halitta ba, ƙarshe kenan"

Tana faɗin hakan ta shige office ɗin Editor-in-chief ta bar Yussy tsaye shanye da baki."Kamar fa daƙiƙiya take ƙoƙarin haɗani da kalmar, kan uba, yaushe tazo gidan rediyon?" Ta saka hannunta a baki tana ciza sai kuma ta yarfe hannun, ba zata taɓa zuba idanu Ahlam ta shigo ta fita farin jini ko ƙoƙari a cikin BRIGHT FM, Radio ba, wacece Ahlam yaushe ta fara koyan aikin? Ta tuna ranar data fara zuwa gidan rediyon, ranar data saka idanunta akan Ahlam sai ta ji kamar wacce zata kawo ƙarshen farin jininta a gidan rediyon ce tazo. Tabbas ta tuna, ta tuna komai.

Daga office É—in HR ta fito sukai karo a hanya

"Sunana Ahlam Abdallah Kurmi, matashiyar Æ´ar Jarida me koyan aiki yau na fara aiki" Ta ce da golden voice É—inta tana kallon Yussy, wacce ta yi tsaye tana kallon ta, bafa mata Æ´an jarida ne bata saba gani ba, ana yawan yin mata masu koyan aiki, kuma ta dalilin Yussy suke barin BRIGHT FM É—in.

Sai dai me? Akwai bambanci.

Tarin bambancin dake tsakaninsu da Ahlam, a suffa, kyawun sura, nutsuwa da kamala, da zallar kyau irin na kanuri. Da farko, muryarta ita ta fara ruɗa Yussy, irin muryar dake hawa da kowanne kalar program a gidan rediyon, News, interview, Boardcast, kowanne kalar abu muryar Ahlam zata ɗauka. Hakan ya bawa Yussy tabbacin Ahlam za ta yi nasara na shiga kowanne kalar program, ita kuma za ta yi ƙasa ne. Hujjar farko daya zama dalilin tsanarta da Yussy ta yi, hujjar da bata zama ƙwaƙƙwara ba, bata zama dalili babba ba. Tana da kyawun da za'a so ta, sai dai tana da tabbacin ko kallo bata ishe MD ba, kamar yadda burin Yusraah shine maza matar MD ɗin.

Sai ta kalle ta sheƙeƙe ta watsar, tana taunar chewing gum, ƙas ƙas ƙas ƙas.

Al'amarin da ya yi wa Ahlam zafi kenan.

"Ina fatan na samu ƙawa, wacce zata koya mini abubuwa da ya kamata na sani game da aikin daya kawo ni ko?".

"Sai da bana abota da nakasasshe, da zan ba ki shawara da kin koma gida kin É—auki roba ki bi sawun mutanen gefen titi, amma wannan aikin bana mutane masu nakasa bane irinki" ta faÉ—a tana watsawa Ahlam harara, har zata juya sai kuma ta tsaya ta ce

"Yusraah Yassar Yakasai, shine sunana, matashiyar Æ´ar jaridar da ake ji da ita"

Tana faɗin hakan ta juya tana rangaji kamar wacce zata bi iska ta yi sama, siririya ce sosai, irin masu shafaffan ɗuwawun zaman nan, ga ɗamammun kaya da take son sakawa, wanda ke fitar da jemammen kwankwason nata a fili, zanƙaleliya ta ita tana da yalwar ƙirji da kyan fuska sosai

Ahlam sai ta fito da hannunta data ɗan rufe da mayafi, ta kasance me duhun fata, irin me hasken nan sosai da akewa laƙani da

'Chocolate colour'

Bata da tsayi can, kuma ba gajeriya bace, tana da kakkuran jiki ko'ina a murje kamar ita ta zaɓin yadda zata kasance, abu uku dake fito da asalin kamarta da Kanuri shine, manyan idanunta farare tas, sai jajayen laɓɓanta wanda suke koyaushe kamar ta shafa musu lips lamp peach kuma. Hannun daya shanye take ta kallo, yatsun hannun wani yafi wani, wani dogo wani gajere, sai ɗan kaifi da suka yi, wanda ya kasance manuniyya shine ya yi zabgege a ciki, sai fatar hannun da ta yi yaushi da tattare waje guda, bata taɓa iya motsa hannun yana maƙale kodayaushe, da hannu guda take yin komai na rayuwa, wanda ya zama na damanta, bata samun gazawa na yin abu.

To ai ita ma ba haka aka haife ta ba.

Kamar cutar ƙyanda ta yi.

"Baby na kusa rasa ki, fara ce ke sosai, ƙyandar nan da kikai ta saka kin yi baƙi"

Cewar Engineer.

Yussy ta sauke ajjiyar zuciya bayan Ahlam ta shige cikin office ɗin Editor-in-chief, ta yi ƙwafa tana bin bayan MD zuwa office ɗinsa.

TJ ya kalli Ahlam ya ce

"Golden voice ya akai ne?"

"Sir, na je wajan Director of News akan batun rahoton dana tura masa jiya da daddare, shine ya ce ya turo maka ai"

"Rahotan matar da aka ƙonawa jinjiri?"

Cikin rawar murya Ahlam ta ce.

"Yes Sir, shi nake magana"

"Ok ya akai Golden voice?"

"Sir Tj akwai matsala ne akan rahoton, ina buƙatar a dakata wajan ɗora shi, kar a gabatar dashi Please don Allah sir Tj"

Ya yi baya ya ce "A dakata?"

Ta ce "E, don Allah"

"Na riga na turawa News editor, zai wahala idan ba'a kammala ba, domin a labaran 12 za'a saka shi, sai dai ki je can ki duba muga...," bai ƙarasa faɗa ba, ta yi saurin miƙewa jikinta na rawa ta fita ta nufi office ɗin News editor, a hanya ta haɗu dashi, tun kafin ta ƙarasa ya dinga yi mata kyakkyawan murmushi yana lumshe idanunsa tare da daidaita tsaiwarsa yana jiran zuwan nata, daman wajanta zashi sai kuma gata tazo.

"Baby ya aka yi?"

Ya furta kamar yadda Engineer yake faɗa, sai ta kwaɓe fuska idanunta ya yi rau rau muryarta na rawa domin bata so ya dinga ce mata baby sam.

"Shikenan, Ahlam"

Ya É—an matsa kusa da ita yana jin numfashinta na sauka. "Anees, rahoton dana turo yana ina? Ka cire a cikin rahotanni da za'ayi ina cikin matsala ne sosai Please"

"Problem?"

Ta jinjina masa kai.

"11:52 fa baby"

Anees ya faÉ—a yana duba agogon hannunsa.

"News Anchor tana studio yanzu haka, ki yi haƙuri ki bar shi baby, ai labari ne me kyau"

"Na shiga uku"

Shine abin data samu zarafin faɗa tana jingina da jikin bangon. Anees ya ɗan matsa kamar zai riƙe hannunta daga bayansa ya ji an furta "Kana iya ɗaukanta zuwa hotel, nan bai zama dandalin yin iska ci ba" kafin su juya tuni ya bar wajan, ƙirjin Ahlam sai ɗagawa yake yi kamar wacce Asthma ɗinta ke ƙoƙarin tashi, ta dinga riƙe ƙirjinta, bata san zirga-zirgar da MD yake yi yau ɗin nan ba, tana lura sai shige da fice suke yi shi da Official & Professional department, tare da Events & Outside Broadcasts (OB) Unit.

"Anees ka taimaka mini, idan aka saka abin nan ina cikin matsala ba zan yafewa kaina ba, ka taimaka mini" Anees ya zuba mata idanunsa da sukai ɗan laushi da kalaman da MD ya jefe shi da su, da ƙyar ya iya cewa

"Baby bana shiri da
Yussy kin riga kin san hakan"

"Yussy ce zata gabatar da labaran?"

Ya ce "Yes, Zainab Alƙali bata shigo ba"
Chapter 13 · 0% Book details