← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 64

Sashe 22

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ana mahafin naki kike faɗawa haka? Babu kyau fa ki tuna abin da Innti take faɗa mana akan Daada. Ni dai ina son Daada ina matuƙar son shi sosai a cikin zuciyata"

Ana ta sake ware idanunta da mamaki ta ce "Kai haba? Shine mahaifin nawa kenan ashe?" Iftihal bata iya bawa amsa ba. Ana ta É—an cije lips a hankali ta ce

"Kuma kin taɓa ji na saka muku baki idan kuna batu akan shi? He's never been headache wallahi"

"Kinga Iftihal, za ki iya son Daada har ƙarshen rayuwarki idan kin so, amma ba'a tilasta Ana yin abin da ba ta yi niyya ba. Idan ba ki ba sani ba, bari yanzu ki sani. Mahaifin Ana ya jima da rasuwa tun tana cikin Innti"

Tana faɗin hakan ta miƙe zata je ta kwanta cikinta na yi mata wani irin ciwo saboda azababbiyyar yunwa, amma data ci tuwo ta gwammace ta kwana da ƴar gusau.

"Yaa Sam ke kiranki a waya"

Wayar ta amsa fuska ba walwala ta kara a kunne da wannan sanyin muryarta ta ce"Uhm...

Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Yaa Sam ya sauke tun ɗazo yana jin yadda take surutu na masifa saboda ta yi niyya. "Dawa kike?"

Ta yi masa shiru ta yatsar fashi.

Shirun da yake azabtar da zuciyarsa wanda baya so baya buƙata shi ta yi masa. Ba zai jure sai ya tattaro dukkan nutsuwarsa ya sake fesar da numfashi da ta ji sautinsa ya shiga kunnenta ya saukar mata a zuciya, ta ƙanƙame wayar tana lumshe idanunta tana jin wani abu yana yi mata motsi a ƙirjinta.

"Nanaah"

Ta yi masa shiru wannan karon ma. "Zan koma Lagos gobe idan rai ya kai mu, naso ganinki kafin hakan ta kasance kin ji?" Sai ta yi shiru tana sake saka ƙarfi wajan riƙe wayar da kyau, Lagos ke ta yi mata kai komo a kunne, ba yau ta saba jin sunan Lagos a bakin Haysaam ba, ba yau bane kawai, wannan bai zama na farko ba, babu tabbacin zai zama na ƙarshe. Akwai wani abu da take ji game da sunan Lagos, da duk sanda ya furta a kunnenta, menene shi? Menene abin? Bata sani ba, ko wuƙa aka saka a wuyanta akan sai ta faɗi me take. Tabbas sai dai a ɗauki ranta.

"Na.......

Ya kasa ƙarasa kiran sunan nata.

Kamar yadda ta yi shiru shima shirun ya yi, duk wani bugun zuciyarta yana tafiya daidai da bugun tasa zuciyar. Ta É—auka ya kashe kiran sai ta ce "Yaa Sam.....

"Na'am"

"Zaka tafi dani? Ka tafi dani Please" ta ce kamar za ta yi kuka

"Nanaah, ya zan tafi dake garin da babu dangin uwa balle na uba, ke ba matata ba?"

Ta ɗan narke masa ta cikin wayar "To ba sai ka ce ƙanwarka bace ni, ka yi maganin munafukai ko?" Ya yi jim sai kuma ya ce "A baki kike jin Lagos Nanaah, ba irin garinku Kano bane, kuma inda nake ɗaki ɗaya ne da Banki suka bani, ko zan dinga kwana dake muna using one bedroom?"

"E, na yarda nikam"

"Ba za ki ji komai ba, mu kwana tare?" A hankali ta ce

"Me zan ji to?"

"Think dear, yi tunani ko?"

"Na yi, ba zan ji komai ba"

Sai kawai ya share ta, yaja matsagaitan idanunsa ya lumshe.

"Yaa Sam"

"Nanaah"

"Kai za ka ji?"

Ya É—an murmusa, sautin murmushin nasa ya saka ta sakin nata kyakkyawan murmushin da zuciya ke ayyana masa kamar ya ji É—umin bakinta ne a fuskarsa.

"E, zan ji" ya bata amsa.

"To faÉ—a mini me zaka ji É—in, na ji ko nima zan ji irin shi mu yi anko ni da kai abokina"

“Abokina” ya maimaita sunan a ran shi.

"Please Yaa Sam, say it"

"Zan faÉ—a, not now"

Ta ce "Sai yaushe?"

"Sanda Shalelen Innti ta girma"

"Yaa Sam.. Yaa Sam...

Ƙit ya kashe wayar. Bayan ya kashe wayar juyi kawai yake yi a saman ƴar yaloluwar katifarsa, yaja idanunsa ya lumshe ya sake buɗe su, ya ƙara rufe su ji ya yi zuciyarsa na yi masa motsi. Ya zai yi ne? A aboki ta ɗauke shi Madam, kuma kamar she's too young ta fahimci abin da yake ji, wata ƙilama ita bata jin komai ma. Yaushe ya san Ana ne? Kamar zai iya tuna sanda ya ganta? Idan ya rufe ido tsaf zai ga tarihin daya shuɗe akan Ana

Sanda ya fara ganinta a duniya.

***

Rediyo take saurara amma taƙi tsayar da hankalinta waje guda, daga ta danna nan sai kuma ta danna nan cikin sa'a takai inda ake maimaicin labarai. Ta yi shiru tana saurara. Sai ji an ce

"Wannan kenan. A yau ne wani rikicin kishi tsakanin matan Malam Sani dake Gandun Albasa ya barƙe, barƙewar data tashi barƙewa ta haɗa da jaririn da aka haifa wanda yake a shaƙi iskar kwana ɗaya a duniya, inda kishiyar Maryama wato uwar gida ga Malam Sani ne suna Talatuwa ta yi juyin waina a tanta da jaririn Maryama a ruwan zafin, kai ka ce kaza ake shirin figewa wajan yin tagomashin arziƙi a baki" me yin labaran ta ɗan yi shiru ta ɗora da; "Duk yadda gidan rediyon bright Fm yaso ganawa da Maryama abin ya faskara, ga abin da ya faru a taƙaice daga bakin wanda idanunsu ya gane musu"

Muryar wata mata aka sako tana kuka sosai ta ce "Ban taɓa ganin azababben kishi fara fa'ida irin wannan, akan idanuna ta ɗauki jaririn amaryar ta cilla a ruwa, Talatuwa ta yi haka ne da gayya da tunanin hukuma ba zata ɗauki mataki ba, sun auro yarinyar suna gallaza mata hatta mijin bayan Talatuwa yake bi shi ya hana Maryama ta kai ƙara. Alkur'anin Allah akan idanuna komai ya faru"

Ɗif aka ɗauke muryarta. "To daman kowa ya sai rariya ai ya san zata zubda ruwa, Allah kasa mufi ƙarfin zuciyarmu. Me rahoto Yussrah Yassar Yakasai"

Sai aka ɗan sako take da muryar namiji a background sound ana faɗin "Labaran rana kuka Saurara daga bakin Yussrah Yassar Yakasai....," bata bari ya ƙarasa faɗa ba ta yi cilli da rediyon hankali tashe ta fito tana faɗin "Malam malam fito ka ji muryar Asabe a rediyo ta yi bayani dalla dallah mun shiga uku Malam" fitowa ya yi daga ɗakinsa domin shima yanzu yaga ma ji ya kalli Talatuwa data rushe da kuka daidai nan Maryama ta fito tana kuka sosai "Malam na rasa ɗaya ya rasu na shiga uku, an kashe mini yarona"

A fusace ya ce "To allahamdulilah da hakan ma, maza tattara kayanki da gawar ki fice mini a gida na sake ki saki uku cif kar na sake ganin me kama dake. Ba za ki ja mini masifar zaman gidan yari ba billahi"

Cak kukanta ya tsaya ta zubawa Malam ido jikinta duka rawa da ɓari yake yana zata da gawa cikin daren nan? Ina za ta yi? Ba zata iya komawa gidansu ba, ta shiga uku. "Ka tausaya mini Malam na yarda ka sake ni amma kabar ni na zauna a gidan nan don Allah, na shiga uku. Ka tuna ɗan nan na kane ko jana'iza ayi masa"

Talatuwa ce ta shiga ta ɗakko jaririn a hannu, Malam ya shiga jan Maryama tana turjewa sai da ya kai ta bakin ƙofa Talatuwa ta ajjiye mata gawar ƙasa suka ja ƙofa suka rufe babu ko mayafi a jikin Maryama.

***
Juyi kawai Ahlam take yi a saman gadon dakinti, ta ɗauki a ƙalla awa ɗaya da daƙiƙo a haka tana juyin da bashi da amfani, idan ta yi niyyar bacci baya samo, maganganun MD da suke neman saka mata ciwon zuciya kawai take tunawa a cikin kanta, ga matsalar baiwar Allah da bata san halin da take ciki Bama, ga matsalar Yussy da kanta.

"Na shiga uku! Ko dai bani da rabo ne a aikin jarida?" Ta saka hannu ta dafe kanta.

Da sauri ta miƙe zaune tana faɗin "No! Ba zai yiwu ba, dole na ɗaukaka akan aikina, ɗaukaka nake so ko ta wacce fuska wacce zata saka tauraruwar Yussy ta disashe" ta saka tafin hannunta wajan goge hawayen idanunta, shanyayyen hannunta ta kalla. "Ko nakasata ce silar komai? Ko ita ce ta hanani ɗaukaka ni Ahlam?" Sannu a hankali ta miƙe tsaye bayan ta sakko daga kan gadon, safara da marwa ta shiga yi a cikin bedroom ɗinta. "Anees" ta kira sunan.

Wayarta ta É—auka ba tare data duba lokacin kiran ba, idanunta rufe ta fara neman number. Kira biyu ta yi ba'a É—auka ba, ana ukun aka É—auka sai aka yi shiru.

"Hello....

Babu martani. "Hello...

Nan ma shiru sai ta ce

"Anees, akwai matsala ina buƙatar taimakonka Please" babu raddi ko numfashi balle sauti a ɓangaren Anees ɗin. Wayar ta ciro daga kunnenta tana ƙoƙarin sake kira, da firgici ta yi baya tana zaro ido ganin number MD ta makawa kira a cikin daren.

***

Wajejen gotawar uku da kwata na dare, Innti na zaune saman laddumar da ta yi lafila hannunta riƙe da carbi tana azkar. Ta jima zaune iska na kaɗata. Hannunta ta ɗaga sama bayan ta ajjiye carbin da karyayyiyar murya me raunin gaske, buɗaɗɗiya me cike da buƙatu a wajan Ubangiji ta ware hannayenta wajan furta. "na sani Ubangiji, ina da masaniyar babu abin da zai faru da rayuwar bawa face abin da ka ƙaddara masa, na amshi jarrabawata da hannu bibbiyu, burina, fatana addu'ata akan ƴaƴana ne da mijina. Mijina shine gatana ƴaƴans sune farincikina, Ubangiji ka shirya mini zuri'a, ka shirya mini su. Allah ka haɗa su da alherin da yake cikin wannan duniyar, ka nisanta su da sharrin dake cikinta.. Allah ga autata nan Ubangiji ka shiga cikin rayuwar Ayshatul-Haleeym, ka shirya mini ita, ka shirye ta ka tausashi zuciyarta, ka cire mata zafin zuciya da taurin kai. Ka daidaita tsakaninta da mahafinta" taja ajjiyar zuciya me ƙarfi ta sauke ta ce "Mijina...
Chapter 22 · 0% Book details