← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 64

Sashe 29

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke don ƙaniyyarki munafurci kika koya irin na uwarki? Mugun abu take koya muku ashe?"

Ta girgiza kai a hankali ta ce

"A'a Daada...

"Makaranta zani muna exam ne" A hargitse ya ce "Dake da makarantar da uniform É—in makarantar, da Malaman, da wacce ta saka ki makarantar Allah ya yi wadaranku tsinannu marasa amfani a duniya har ma da lahira, duk wani mugun abu kuma gama lashe shi a nonon uwarku"

Wani irin runtse idanu Innti ta yi idanunta sun yi jajur ta kasa motsi, idan cin mutuncin Daada ne ta saba amsar shi a koyaushe a gaban yaran nata. Babu ranar banza ita ta rasa yadda wannan ƙiyayyar ta samo asali da tushe. Kamar ba haka yake ba, kamar kuma haka ɗin yake tun fil'azal. Ta fuski numfashi da ƙyar ta tuna kamar ta tuna. Zata iya tuna dalilin faruwar komai.

"Bana son haihuwa Innti, bana son zuri'a Innti ban shirya mata ba, yara basa ɗaya daga cikin abin da yake birge duniyar Daada. Daga wannan cikin kar ki ƙara sakin jiki wajan ware ƙafa ki ɗauki ciki, shima wannan ɗin bana murna dashi, kuma ba zan ɗauki alhakin kulawa dashi ba na faɗa miki"

Wannan sune kalaman shi na farko, lokacin data samu cikin Babban yaya ne, tun bata san me zata haifa ba a lokacin cikin yana watanni bakwai ne dab da zuwa duniya yaso zubar dashi ma, haƙarsa bata cimma ruwa ba. Tunda aka wayi gari da labarin cikin komai ya sauya komai ya zama labari.

Zata iya tuna raddin data yi masa ma a lokacin. Kamar cewa ta yi "Daada ƴaƴa ai Rahma ne baka san me jin ƙan ka ba"

"Assalamu Alaikum"

Sallamar da aka yi ya katse ta daga tunanin abubuwan da suka shige, wata sabuwar faɗuwar gaban ce ta sake ruskarta. Uwar mijinta ce da kuma yayar mijin da ƙanwarsa.

"Ina yini Emama?"

Wani irin gatsine wacce aka kira da Emama ta yi ta dubi tukunyar da Innti ta dafa taliya ƴar murji jallof wacce ta ji ganyen albasa sai ta riƙe baki ta ce "Babu shakka ashe abin da nake ji na cewa kin shanye Daada gaskiya ne, ya tare a gindinki ke da yaranki har taliya kuke dafawa da wannan sanyin hantsin?" Innti ta kalli tukunyar tana mamakin shi Daada ne ya ce shi ya yi cefanen ko me? Sama da shekaru rabon da taga sisin kwabo nashi? Duk abin da yake dashi ko ya mallaka ya tafi a caca. Taliyar fa Haysaam ne ya kawo da saffafe ya ce su dafa a kai wa Shalale asibiti daga baya ma ya kira ya ce ya siya mata Rufaida da Shawarma. Shine za su azabtar da zuciyarta da wani baƙin cikin na dangin miji? Ita kam tana tunanin da ƙyar idan takaici da baƙin cikin namiji bai yi ajalinta ba.

Ƙoƙarin magana take yi Baba ta kalli babbar ƴarta me suna Hanna ta ce "ke jeki juyo mini taliyar nan a faranti gabaɗayanta kin ji"

"To Emama" Hanna ta faÉ—a cikin sauri.

"Wallahi Emama Daada ya zama mijin tace a gidansa, komai ya samu yana gidan wannan matar data zame mana bala'i. Haka jiya dana biya ta wajan abincin Bala yake bani labarin cin mutuncin da wannan me suffar Aljanu ta yi masa, Ana" Emama ta riƙe haɓa ta ce "Ba shakka iskancin yarinyar nan da rashin kunyarta haka ya bunƙasa?"

Daada dai ya yi shiru yaƙi cewa komai.

"Liya ki daina suffanta Æ´ata da Aljanu"

Kau! Daada ya É—auke Innti da wani irin mari yana nuna ta da manuniyya ya ce "Ahir É—inki. Ke kuma......" Ya juya kan Iftihal da take ta rusar kuka ya ce "Daga yau na haramta miki zuwa makaranta, kuma zuwa dare ki shirya akwai inda zamu dani dake"

"Ba mu yi haka dakai ba, duk abin da za ka yi don Allah na roƙe ka sbd Allah ka tsaya iya kaina. Kar ka rusa goben yarana na sadaukar da komai saboda su yi karatu"

"Wacce gobe? Har wata gobe suke dashi a nan? Ai indai cigaba ne a rayuwa sai dai su yi na me haƙar rijiya. Har abada yaranki ba za su taɓa zama wasu ba a rayuwa tunda suka fito daga cikinki"

Kuka Innti ta fashe dashi tana wani irin fidda numfashi da kiran sunan Allah, yadda take kuka haka ma Iftihal ke kuka ta rarrafa wajan Daada ta riƙe ƙafafuwansa ta ce "Muna da buruka a karatunmu Daada za ka ji daɗi ta dalilinmu, kar ka bari mafarkina na zama ƴar jarida ya rushe, kar ka bari mafarkin Ana na zama marubuciya ya zama tarihi mun rayu akan mafarkanmu da burinmu don Allah kar ka tarwatsa mana su" ƙafa ya saka ya shure ta ya nunata da yatsa ya ce. "Har wani mafakar kike dashi?"

Ya yi ƙwafa "Ni na riga na saka ki a caca kuma rashin sa'ar uwarki ta shafe ki wacce taja mini asara babu kuɗin kuma aka ciki"

Cak! Numfashin Iftifal ya tsaya a ƙirjinta dumm haka ta ji wani abu yana mata amo a kunne kallon Daada kawai take yi da kallo na rashin fahimta. "Ka.. saka..ni a caca Daada?" Ta yi maganar a rarrabe tana dafe ƙirjinta.

"La shakka kuma an ciki zuwa dare zan kai ki gidan Alhaji Baita, ban sani ba ko auranki zai yi ko kuma dai ajjiye ki zai yi kawai a gidan"

'Alhaji Baita?' ta maimaita sunan ba wannan tsohon bane me baki duk dauɗa wanda goro ya gama cinye masa haƙori har wata tsotsa ce take gani a bakin wannan Alhaji Baitan mai ciki kamar name shirin haihuwa shi ne za'a kaita gidansa a matsayin me?

"Na shiga uku Daada ka yi mini rai"

Ta fasa wani gigitaccen ihun daya saka Jadid dake kwance tun ɗazo saurin runtse idanunsa ya saka hannu ya dafe kai, fitowa yake son yi daga ɗaki abu ya ci tura saboda nauyin da jikinsa ya yi masa ga tashin zuciya da hakki da ƙyar yake iya buɗe idanunsa. A hankali hawayen da suka cika masa idanu suka silalo ta gefen idanunsa. "Allah ka ɗauki raina ko zan huta da ganin kuncin dake zuciyar Innti da ƴar'uwana"

"Ka aurar dani idan kana buƙatar hakan amma Daada don Allah kar ka kai ni gidan mutum nan mutuwa zan yi, kar ka saka ni a caca. Ka duban girman Allah ka tuna mu jininka ne, ƴaƴanka ne ka tuna mu amana ne a gare ka watarana Ubangiji zai tambaye ka. Ka ji tsoron haɗuwa da Ubangiji Daada wallahi muna son ka muna ƙaunarka kai mahafinmu koyaushe muna jiran sanda zaka dawo mana da soyayyar da muke maka" ya ɗauke kai zuwa gefe bai ce komai ba. Emama ce ta kalle shi bayan ta tattara wasu kayan miya data gani a wajan ta ce

"Zuwa na yi a siyar da rabin gidan nan a bawa Liya kuÉ—in zata tafi Saudia aikatau"

"Wanne gidan?"

Innti ta faɗa tana buɗe jajayen idanunta da ƙyar saboda faɗuwar gaba. Ta ɗora da faɗin

"Kar ku siyar da gidan nan don Allah, idan Babban yaya ya tashi aure a nan zai zauna bamu da komai ku tausaya mana don Allah"

Emama ta ce "Gidana ne sai an siyar shi Muradun É—in aure aka ce za'a bashi? Wani É—an iskan uba ne zai bawa wannan mara lakar É—iyarsa? Da wacce sana'ar zai yi auren?"

"Emama, wannan gidan gidana ne bawai na Daada ba, ki tambayi Daada ki ji" tana faÉ—in hakan ta shiga É—aki tana dafe saitin zuciyarta dake mata ciwo da raÉ—aÉ—i.

"Ohho dai. Ke kuma tashi aikatau na samo miki a wani gida, ko na kwana biyu ne ki yi kafin akai ki can gidan Baita É—in, ba zan É—auki wannan fitsarariyyar da zata iya ja mana bala'i a gidan jama'a ba" ta saka hannu ta fusgi Iftihal za su yi waje Daada ya ce

"Kin san Baita bashi da mutunci fa?"

"Ka bashi uzurin shirya yarinyar ake yi" Tana faÉ—in hakan ta fice daga gidan suka nufi titi napep ta shiga ta ce masa Maitaima Sule Baffas Estate kai tsaye.

Bayan fitar su zama Innti ta yi ta dinga kuka har sai da ta yi me isar ta tana kukan tana cewa. “Rabbanaa hab lanaa min azwaajinaa wa dhurriyyaatinaa qurrata a’yunin waj‘alnaa lilmuttaqeena imaamaa”
(Surah Furqan: 74). Ta É—ora da faÉ—in.

“Allahumma ihdihi wa-shrah ṣadrahu lil-ḥaqqi, Allahumma habbib ilayhi al-īmāna wa zayyinhu fī qalbihi, wa karrih ilayhi al-kufra wal-fusūqa wal-‘iṣyāna, waj‘alhu minar-rāshidīn.” Ma’ana: “Ya Allah, Ka shiryar da shi, Ka buɗe ƙirjinsa ga gaskiya, Ka sanya ya so imani Ka yi masa kwalliya da shi a zuciyarsa, Ka tsanar da shi da kafirci, da fisqanci, da saba wa Allah. Ka sanya shi daga cikin masu samun shiriya.”

Wani irin numfashi take fitarwa me ɗauke da ciwo tattare da damuwar da ta yi shekaru a cikinta ba tare data buɗewa kowa cikinta ba. Idanunta na buɗewa da lumshe ta ce “Allahumma aslih lī zawjī, wa aslih līhi, waj‘alhu qurrata ‘ayni, waj‘alnī qurrata ‘aynih.” ta ɗan ja idanunta ta lumshe su.

Sama-sama ta ji kakarin amai tana fitowa taka Jadid ne ke kwara amai gabanta kuma ya faɗi ganin yadda fuskarsa ta kumbura sosai da ƙafafuwansa da hannayensa. Bayan ta wanke masa baki da fuska ta ce

"Ina maganinka?"

"Ya ƙare" ya ce da ƙyar.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"

Shimfiɗa ta yi masa ya kwanta ta dinga kallon shi tasan da ƙyar idan ba dialysis za'ayi wa Yaa Jadid ɗin ba.

"Babu komai, Allah duk abin da ka yi daidai kuma na amsa. Bari na ɗakko kuɗin adashin nan na jama'a siya maka magani kafin aje asibiti idan Allah ya hore mana" ko data miƙe ta nufi ɗaki tana zuwa inda take adana kuɗin jama'a na adashi taga babu komai kusan dubu ɗari biyu da hamsin an kwashe

***
BIYA.
Chapter 29 · 0% Book details