← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 64

Sashe 49

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Au har kuÉ—in sun samu shine babu labari? Daman ai saboda aikin nake tausayin yarinyar idan kuma ka yi ai shar dani" Baita ya watsa mata wani lalataccen kallo ya ce "Macuciyya uwar Kasko da Marka. Ki É—auki yarinyar nan ki mata wanka yanzu zan dawo domin har yanzu a sama nake jin kaina"

"Kasan aiki kuÉ—i nake, bari na yi mata yanzu na dawo mu tsadance, akwai wasu magungunan ma"ya ce "ki haÉ—u mini dasu". Fita waje ta yi, shi kuma ya yi shirim yana danna waya, wata number ya kira ana É—agawa ya ce "Ranka ya daÉ—e, Allah Ya taimake ka. Aiki ya kammalu a É—akin da na ce ka ware, yanzu kana shiga zaka ga zakara me abun mamaki" shiru ya yi alamar saurare ya ce

"Ka bada Biliyan goma ya wadatar ai kai ne, dole mu tsaya maka a komai, idan aka kafa ai damu ake komai. Thank you Sir na gode"

Ya kashe kiran yana sakin murmushi.

Jummai ta dawo tana kallon Iftihal dake cikin jini, yarinyar sai surutai take ita kaɗai tana cewa Ana ta rungumeta, ji take yi kamar ana fusgar naman jikinta, ji take yi wata wuta na rura kanta a fatar jikinta, ƙoƙarin buɗe baki take yi wajan yi wa Ana bayanin irin ciwon da take ji, amma ta kasa. Jummai ta tattare hannu ta ɗago Iftihal sama wani gigitaccen ihu Iftihal ta saki tana zabura jini na sake ɓalle mata ta cakume Jummai tana kafa mata haƙori a hannu saboda wani irin raɗaɗi da take ji a ƙasanta. Jikinta ya ɗauki zafi sosai kamar gaushin wuta. Ta shige banɗaki da ita a cikin wani ƙaton ruwan zafi ta saka Iftihal, daga nan kuma bata sake sanin inda kanta yake ba, sai farkawa da ta yi da wata sabuwar azabar data ninka ta baya. Ɗis haka idanunta ya buɗe ya kumbura sosai kamar zai faɗo, Baita ta gani a kanta yana yi mata abin da ya yi jiya, ta yi masa ƙuri da idanunta, deep down na zuciyarta sunan Allah kawai take kira jikinta ya saki zuciyarta ta tsaya, daga nan numfashinta ya ɗauke bata sake sanin inda kanta yake ba saboda tashin hankali.

Yadda azaba ta sumar da ita, haka wata azabar ta sake farkar da ita. Ɗakin shiru, ba iya ɗakin ba, kusan duka gidanne shiru, Ana take son gani, Anarta take buƙatar kwanciya a jikinta, ta san dole raɗaɗin da take ji a zuciyarta zai ragu, ta shiga kiran sunan Allah guda ɗari babu ɗaya, cikin hukuncin Allah ta samu zarafin yunƙura wa ta miƙe zaune, ta ɗauki hijabin data gani a gefe ta saka, ya saukar mata har ƙasa jikinta ko wando babu, ta shiga daddafawa ta miƙe, taga kuɗi da yawa ta saka hannu ta ɗauki dubu ɗaya, da taimakon Ubangiji ta fito tsakar gidan, tas kamar an share, har zata fice sai taji wata ƙara da ɗan ihu daga gefen ɗakin da take tsaye, ɗaki da akaf mutanen gidan har matan Baita hatta Jummai babu wanda ya taɓa shiga, kodayaushe a rufe yake, yanzu bata san mene ya saka ya zama a buɗe ba. Taja ƙafafuwanta a hankali ta nufi ɗaki ta buɗe ta shiga, sandarewa ta yi kanta ya sara gabanta ya yi mummunan faɗuwa, wata ƙaramar yarinya ta gani tsaye cur an kafeta, tana kyautata zaton Anisa da Baita ya bata labari ce. "Anisa?" Iftihal ta kira sunanta, madadin Anisa ta amsa sai ta shiga ambaliyar kuɗi ta cikin bakinta.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"

Duk wani kira da Iftihal ta yi wa Anisa kuɗi ke zuba, cikin ƙaramin lokaci kuɗi ya taru sosai. Ta shiga ƙarewa ɗakin kallo sosai, da sauri ta juya ta fita jiri na kwasarta haka ta samu zarafin bin wani lungu ta fice daga unguwar. Ina zata je? Ba zata iya komawa gida ba a wannan halin da take ciki ba, tana buƙatar ganin Ana akwai abin da take son faɗa mata akan Alhaji Baita, amma gidan a yanzu ya haramta da ita. Ta tsayar da me napep da ƙyar ta shiga ta ce masa "Mai taɓa sule, Baffas estate zai kaita, please ka kaini har bakin gate ɗin Baba driver ka ji?"

"In sha Allah yarinya" yace yana jan napep É—in zuwa kan titi hankali kwance. Iftihal taja jikinta kaÉ—an ta kwanta jikin kujerar napep

***
Yana zaune a saman dakalin yana danna wayarsa ya ji motsi kusa dashi, a hankali ya É—aga kan shi zuwa gare ta, ya watsa mata idanunsa masu laushi, sai yanzu take farkawa. "Anji daÉ—in katifata irin bacci haka"

Ta É—an dube shi kamar za ta yi magana kuma sai ta yi shiru, idanunta ya yi wani irin jirkicewa fuskarta a haÉ—e babu walwala da wata sanyin murya ta ce "Abbaa yazo?"

Haysaam ya girgizar kai ya ce "Jaheed dai"

"Abbaa bai zo nema na ba?"

"Sure, ai kamar baya nan fa"

Ana ta juya manyan idanunta wanda sannu a hankali suke sake rinewa, ta ɗaga hannunta wajan dafe ƙirjinta ya ce "Ya akai? Ciwo yake miki ƙirjin?" Ta yi tsaida idanunta akan Yaa Sam bata kuma sake masa magana ba ta shige cikin gidansu, sallama ta yi ta shiga Jaheed dake ta aikin kuka ya tusa Jadid dake cinyarsa yana suma ya amsa mata. Da wani irin rawar jiki idanunta na firfitowa ts durƙushe ta riƙo hannun Yas Jadid ta ce "Masoyi, don Allah ka tashi haka nan, ka daina wannan ciwon, ina jin fiye da abin da kake ji, idan na tuna kuna kusa dani sai na ji duk wani ciwona ya yafi. Haba nawan"

Jaheed ya share hawayensa ya ce "Masoyiyar jeki gidan Emama ki kira Innti kar Jadid ya mutu bata nan, nima mutuwa zan yi idan É—an'uwana baya raye a duniya wallahi"

"A'a......." Ta shiga girgiza kai, gabaɗaya Ana bata san me take ji a ranta ba, tana jin ciwo tabbas, tana jin raɗaɗi tabbas, idan taga sunan Daada a tafin hannunta ji take kamar ta cire hannun ta yar, babu wani abu data tsana a duniya fiye da Daada da kuma hannunta, ta ɗauki alƙawarin goge wannan sunan ta kowacce hanya.

"Abbaa fa?"

Jaheed ya ce "Ban san ina yake ba" Bata sake magana ba, ta miƙe tare da yin waje bata ganin ko gabanta, kamar wacce ta yi wani mugun abu duk inda ta shige sai taga ana kallon ta, a haka ta isa gidan Emama tana shiga ta same su suna cin shinkafa da miya da nama ga lemo a gefe.

Daga tsayen ta ce "Sannu Emama, Innti fa?"

Liya ta ce "Ke don uwarki a haka uwarki ta koya miki yadda ake gaida na gaba dama?"

Tana saukewa Ana ta ce "Ke don uwarki a haka uwarki ta koya miki yadda ake yi wa mutum gyara dama?" Liya ta juya ta kalli Hanna da wani irin mamaki ta ce

"Ni yarinyar nan take zagi da mayar wa da magana Hanna? Ni yaushe aka haifi Ana?"

Hanna ta ce "Ki bar shegiya da idanu irin na Aljanu, mugun duka za mu yi mata wallahi"

Ana ta juya sosai sai ta saki dariya ta ce "A haba? Ƙarya kike wallahi Hanna, sai dai mu daku kuma kar ki yi kuskuren taɓa Ana, don wallahi ko wannan bugaggen yayan naku a yanzu ya ce zai taɓa ni sai ya san ni ƴar wahala ce, sai ya san ni cikakkiyar ƴar halak ce gaba da baya. Idan kina ganin ƙarya ne bisimillah try me za ki gani a fayyace" Liya ta miƙe tsaye tana yin ɗamara, cikin azama Ana ta cire hijabin jikinta ta cire ɗankwali ta yi ɗamara, gashinta da Babban yaya ya yi mata gida biyu dasu suka sauka har baya, wasu kwantattun suma ne daga gaban goshinta masu ɗaukan idanu, gefe da gefen fuskarta sumar ce ta kwanta gwanin sha'awa. "Ƙashi ɗaya ne dani, idan kun fasa baku haifo cikin Emama ba dukanku"

Kanta suka yo, Hanna ta shaƙe wuyan Ana, Liya kuma ta shiga jan gashin kan Ana. Idanun yarinyar ya yi jajur jijiyoyin kanta suka firfito waje, wani ihu da kururuwa Ana ta yi saboda azama ta kai wa nonon Hanna cafka ta matse, azaba ta saka Hanna sakin wuyan Ana, tana sakinta Ana ta juya ta buga Liya da ƙasa da wani irin ƙarfi daya zo mata, idanunta rufe ta shiga dukan Liya da naushi ta fasa mata baki. Hanna ta ɗakko taɓarya zata makawa Ana a kanta ta ji an kwarfeta ta baya, ta yunƙura zata miƙe ta sake jin an kwarfeta ta zube a wajan wanwar a ƙasa.

"Innalillahi, Muraad uban me ya kawo ka cikin gidana? Kashe mini Æ´a za ka yi?"

Babban yaya bai ko kalle ta ba, ya ciri wayar caja daya gani a tsakar gidan ya shiga zararawa Hanna tana ihu da birigma ya farfasa mata jikinta, ganin ta yi laushi ya kalli Ana yaga har yanzu tana kan Liya hannu ɗaya ya saka cak ya ɗauke Ana, ta ɗauka Hanna ce da ihu ta juya zata dake ta ya yi saurin riƙo hannunta. "Abbaa....," ta ce da rawar murya.

Rungumeta ya yi sosai yana jin tana sauke ajjiyar zuciya, ya ɗauki ɗan kwalin ya saka mata ya zura mata hijab, idanunsa zube cikin ƙwayar tata idanun. "Abbaaa...

"Ina ka je na dinga nemanka..,"

"Shhhh" ya ce yana É—ora yatsarsa a bakinta alamar ta yi shiru yana ta shafa kanta.

Emama ta ce "Shegu haihuwar asara, uwar taku tana can wajan police sun garƙame shegiya a can" dam! Zuciyar Ana data Yaya ta buga lokaci guda, cikin sauri ya riƙe hannunta suka fice daga cikin gidan Emama.

***
BIYA.
Shatu na gaba Innar Ramu na biye da ita, ta riƙo Ramu a hannunta a haka suke tafiya, har suka shiga cikin dajin sosai kafin suka isa inda bukkar take. Innar Ramu ta ce "Shatu kin tabbatar me bada magani ce? Yama sunanta kika ce mini jiya da yammaci?" Shatu ta murmusa sosai ta ce

"Bokayan karaba sunanta"

Ta ƙarasa jikin bukkar a hankali ta ce "Muna gaisuwa zuwa ga karaba, muna muki jinjina yake bokanyan rugar Biya da kanta gamu"
Chapter 49 · 0% Book details