Sashe 30
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Batty na rakuɓe a cikin bukkarta ta yi shiru tana kallon saman rufin wajan idanunta ya yi jajur saboda tsananin azabar da take jin tana yunƙuro mata, bata taɓa jin kanƙarar maita na mata yawo a ciki irin yau ɗin ba. A hankali ta juya ta kalli inda ta ajjiye kurwar Mado data kamo a jiya data fita maitar dare. Miƙewa ta yi a hankali ta isa wajan randar ruwan dake ɗakin, randar ta yi sanyi sosai ta miƙa hannu zuwa ƙasan randar ta buɗe wani ɗan ƙyalle idanunta ya sauka akan ƴar tsokar kurwar data kamo ta zubawa kurwar idanu tana jin kamar ta ci kamar kuma hakan ba dai-dai bane ba. Wasu hawaye ne suka shiga sakkowa daga cikin idanunta ta mayar da kurwar ta ajjiye. Wata baƙar leda ta ɗakko barkono ne ɗanye shar a ciki haka ta dinga damƙa tana kaiwa baki tana ci ga hawayen a zama na cika idanunta bayan ta gama ci abin da take ji ya ɗan lafa mata sai ya miƙe ta fito zuwa tsakar gidan turus ta yi ganin jama'a fal ta manta yaron Kulu ya rasu. Sadiatu ta ce "Batty kin fito ne?"
Ta jinjina kai alamar
"Eh"
"To jeki waje wajan yara muna amsar gaisuwa ne" nan ma ba ta yi magana ba kanta a ƙasa cike da nutsuwa ta fito sumar kan sai ɗaukan ƙyalli na dauɗa take yi a haka ta nufi waje cikin sa'a ta samu yara sa'aninta suna ta wasa tana zuwa ta shiga tsakiya aka fara wasa da ita. Kamar an ce ta ɗaga kai ta hango cikin Shatu fal wainar gero har da albasa bata gama narkewa ba.Caraf ta ce
"Sammin wainar geron kin ji"
Shatu ta fiddo ido ta ce
"Wa É—in?"
"Ke, gashi nan kin ci wainar gero"
"Laaa ha'ilallah wallahi kin cinka waina na ci"
GabaÉ—aya yaran suka zagaye Batty. "Ni me ma ce?"
"Rogo da gyaÉ—a" ta bawa Hawwa amsa.
Wani irin daɗi da murna ya kama yaran su basu taɓa sanin ana sanin me mutum ya ci ba sai yau. "Ni ki faɗa mini me na ce to"
Ramu ta yi tambayar a hankali tana kallon Batty cike da tsoro. Batty ta zubawa cikin Ramu idanu komai da komai dake cikin Ramu na kayan ciki tana gani, daman duk wani maye da kallo É—aya yake kallon ka tsirara musamman idan babu dafa'i a jikinka. Madadin Batty taga abin da Ramu ta ci sai taga hanjin cikinta ya motse kuma ya yi kore. ÆŠauke kai ta yi zuwa gefe guda ta ce
"Ai ba ki da lafiya, ga hanjinki nan ya ta mushe ya yi kore ki nemi magani idan ba haka ba za ki mutu wallahi ina faÉ—a miki"
Fashewa da kuka Ramu ta yi tana riƙe cikinta. "Na shi gangaɗi" ta faɗa gigice.
Su Shatu ne suka dinga bata haƙuri har ta yi shiru juyi kaɗan tana dafe da cikinta tana jin kamar hanjin nata ne zai fito ta cikinta.
Shatu ta ce "Kin zama ƙawarmu daga yau za ki dinga faɗa mana me muka ji kin ji ko?"
"To za ku dinga sam mini?"
"E, sosai ma. Ya sunanki?"
"Batty me gani har hanji"
Hawwa ta dafe ƙirjinta ta ce "Laa wallahi haka ne gashi nan ta hango hanjin Ramu"
Hira suka fara yi Batty ta shiga cewa "Ita fa ta kusa fara cin mutane tana shan wahala, ta taɓa shan man wani da babarta ta zuba mata man a cikin abinci akwai daɗi sosai. Kuma tana ganin jinin mutum da kayan cikinsa ita fa har mage tana iya zama" suka fashe da dariya suna jin abin kamar alamar.
Bayan sun gama hirar la'asar sakaliya ta koma gida tana ta zuba idanun a bata abinci amma shiru. Sai ma hira suke yi "Ai Kulu haƙuri ya zama dole, kinga samu kinga rashi amma hakan yin Allah ne. Yanzu fa mutuwar fuju'a ake yi babu ji babu gani ana ta zuba"
Lami dake ta wanki ta ce "Wallahi Sadiatu al'amarin har tsoro ya bani sosai"
Ita dai Batty jinsu kawai take ta san wannan mutuwar da ake yi rabinta mayu ne sanadi. Mutane za su ga ana ta rasuwa irin mutuwar abin mamaki nan, daga ciwon kai sai ace wane babu ko ciwon ciki, ko kuma mutum da lafiyarsa da komai sai aji ya yanke jiki ya faÉ—i shikenan sai tashin lahira. A cikin wannan watan ne na dab da babbar sallah Mayu suke sharafi a cikin watan ne suke yanka duk wanda suka É—aure kurwarsa da niyyar shagalin babbar sallah. Don haka duk wanda yake fama da jinya ta Mayu a irin wannan watan Allah ne kaÉ—ai me tsallakar dashi sai idan ya dage da addu'a da neman tsari da taimako.
Miƙewa ta yi ta sake shiga bukkarta, kurwar Mado ta ɗakko ta riƙe a hannunta sosai ta nufi hanyar rafi tana addu'ar Allah ya sa yau ma taga kyakkywan Kaɗo har mafarkinsa ta dinga yi tana isa ta haƙa rami a gefen rafin ta adana kurwar a ciki ta shiga wasa da ruwa can kuma ta fashe da kuka lokacin data tuna kisan gillar da akai wa Innarta
A can gidan Moddibo suna zaune a tsakar gida, suna ta amsar baƙin da suke zuwa duba Mado. Wani ihu suka ji Mado ya kwarara yana faɗin "Wayyo ga ruwana zai cinye ni ga kifi nan, ruwa ne zai tafi dani"
A razane suka shiga ɗakin suna masa sannu. Hanne ta ce "Moddibo anya ba iska bace ta kama Mado? Wanne irin ruwa zai tafi dashi ana zaune ƙalau Moddibo?"
Moddibo ya ɗan taɓa jikin Mado ya ce "Kuma jikin sanyi ƙalau. Bari zan kira me ruƙiyya in sha Allah sai a yi masa a gani"
"To da dai yafi" Hanne ta ce tana yin takumi.
***
Aikin yamma ne da ita yau bayan ta kammala shiryawa ta fito hannunta riƙe da jaka da damuwa ta bayyana sosai a tattare da ita. Engineer na zaune a parlour shi da matarsa Jiddah ta ɗan durƙusa ta ce "Barka da yammaci Abba" saboda da yawan lokaci tana bin bakinsu Mufeed wajan kiran Engineer da Abba. Itama ta yi imani da Allah bata da wani uba bayan Engineer ɗin nata.
"Baby an fito kenan?"
"E, Abba. Anty Jiddah sannu da aiki"
Jidda ta murmusa ta ce "Yawwa babyn mijina" murmushi kawai Ahlam ta yi.
Ya ɗan kalle ta sai kuma ya ce "Wannan baby hijab ɗin baya miki kaɗan ne a jiki Ahlam?" Ta dubi Hijab ɗin, abaya ce a jikinta me ɗan faɗi ruwan ƙasa sai ta ɗauki hijab ta saka madadin mayafin abayar. "Idan akwai kuskure a shigar zan je na sauya Abba"
"Matsayin naki ne ya sauya daga yadda kika sani. Ahlam na taɓa miki maganar fitar da mijin aure har na yi tunanin wannan yaron na wajan aikin ku ko son ki yake yi. Yama sunan nasa?" Kanta a ƙasa ta ce "Anees ne"
"Good, Anees"
Ya ɗan ɗaga filon kujera ya ciro kuɗi bandir bandir ya damƙa mata ɗaya ya ce "Wannan kuɗin na gani ina so ne naki dana amsa da safe. Ke da kan ki kika bani damar zaɓar miki mijin da nake ganin zai iya kulawa da nake. Nasan komai na zartar a rayuwarki ba za ki yi mini musu ba, ba za ki ce a'a ba. Daga ni har ke marayu ne, amma ke ba za'a taɓa miki kallon maraici ba, dukkan abin da zai zo ya tuna miki ke marainiyya ce bana son shi Ahlam ɗina. Na bada ke, na bada aurenki ga mijin daya kwanta mini kuma ina da yaƙinin ba zai cutar dake ba baby"
Sak Ahlam ta yi tana juya kuɗin a hannunta jikinta ya yi sanyi ba damuwarta waye mijin ba, saboda ba soyayya ce a ranta ba, cikar burinta shi ne gaba da komai a rayuwarta. Tambayoyin zuriyarta bai shige zai barta aiki ba? Ba zai tauye mata rayuwa wajan hanata zuwa aiki ba? Ya san cewa ita nakasasshiya ce? Waɗannan tambayoyin sune suke damunta a yanzu. "Baby " da ƙyar ta ce
"Abba ba zan tambaye ka waye ba, ba kuma zan bijire maka ba, na amshi abin da ka zaɓa mini na san ba zai taɓa cutar dani ba"
Sai ta É—an yi shiru tana mai da murmushi.
"Ya san ina da nakasa Abba?"
"Ya san abin da ba ki sani ba don gane da rayuwarki ma Ahlam. Matsalolin suna bibiyarki wanda ni ban san su ba, ya ɗauki ɗamarar yaƙi da wannan matsalolin ne"
"Amshi nan....
Ya sake damƙa mata wasu kuɗin ya ce "Sadakinki an ɗaura aurenki a sanda suka kawo kuɗin baiko, ni ba zan iya wannan ba tsarina daban shi ya sa na buƙaci ɗauren auren daga baya a yi maganar tafiyarki"
Ji ta yi kamar Engineer ya saka igiyoyi ya sarƙafe rayuwarta da ita ne, komai ya tsaya mata. Yana nufin yanzu ita matar aure ce? Yana nufin igiya uku ke ɗaure da rayuwarta. An yi mata ɗaurin da sai hanata sakewa da zai kawo mata matsala a cikin burinta? Ta rufe ido ta buɗe yafi sau shurin masaƙi wajan tabbatar da abin mafarki ne amma da alama gaske ne. Wata faɗuwar gaba ta ruske ta, aikinta shine gaba da komai, ɗaukarta shine burinta. Ta yi aure bata cimma komai na rayuwa ba, Yussy ta samu sararin yi wa ƙaddararta dariya? Girgiza kai ta shiga yi wajan faɗin "Impossible....
"... menene impossible É—in? Auren ko kuma mijin Ahlam Abdallah Kurmi?"
Sai ta ƙirƙiri murmushin ta ce "A'a Abba"
"Kina farinciki?"
"Sosai. Na gode sosai my 001 madakina"
"Nima na gode ƙwarai my happiness"
Wani abu ya caki zuciyar Jiddah ta yi saurin shaƙar iska ta fesar tana jifan Ahlam da wani irin kallo. Kishin yarinyar kamar ya kashe ta dannewa kawai take yi for more than a years yanzu ya fara cin ƙarfinta sosai.
"Tashi ki je a kiyaye kula wasu samarin tunda dai kina da naki zaɓin Baby Ubangiji ya yi miki albarka ya sa tafiyarmu ta yi nisa"
"Amin na tafi"
"Allah ya tsare Kakata" inji Jiddah.