Sashe 35
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A wannan rana har party zan haɗa a gida" Tana faɗin hakan ta cire password ta miƙawa Ahlam wayar. Sun ɗauka wani nata zata kira ko gidansu zata sanar wa tsautsayin daya sameta. Sai su kaga akasin hakan, domin camera ta buɗe ta saita a kanta ta fashe da wani irin matsanancin kuka ta shiga faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Kamar yadda kuka sani sunana Ahlam Abdallah Kurmi matashiyar ƴar jaridarku wacce aka fi sani da Golden voice. A yau na tashi da babbar jarrabawa a sanadin aikin jarida, shigowata Bright Fm kenan wani ɗan balaja'u riƙaƙƙen ɗan daba ya kawo mini hari, wanda rayuwata ya nema kai tsaye Allah Ya kiyaye ni, ban san me na yi masa ba, amma ya yi iƙirarin ganin bayana kuma yace saboda rahotan matar da aka ƙonawa jariri ya yi mini haka. Kai ɗan'daba idan kana jina ka saurare ni da kyau, ni ƙadangaren bakin tulo ce ban fito ba sai dana shirya, aikin jarida yanzu na fara ko da kowa shi ne silar barina duniya ba zan tsagaita ba sai na cimma burina, yadda ka yi mini abin nan ka sake rura wutar abin, sai an ƙwatar wa matar nan haƙƙinta idan ma ubanka ne ya sa ka yi mini abin. Na gode jama'ata a tayani da addu'a hakan ma alamun nasara ne da ɗaukaka, zan zo muku da cikakken bayanin abin da ya faru da matar. Har kullum Golden voice ce taku"
Tana kammala vedion ta miƙawa Nurse wayar ta ce
"Na gode sister "
"Babu komai. Allah Ya cigaba da tsare wa" cewar Nurse É—in
"Wayyo yayana, zan mutu wayyo Anty Jiddah" ta cigaba da ihu da yarfe hannunta saura kaɗan likitan ya fashe da dariya. Dukkan kuma abin da yake faruwa akan idanun MD baya ko motsi daga ƙarshe ma, juyawa ya yi yabar cikin room yana amsa kiran wayar da ake ta yi masa a lokacin. Treatment aka yi mata da allurai da drip Allah Ya taimaka yankan babu zurfi a jikinta
*
"Kan uba amma annarka uwar dukiya a gidan nan, Allah ka bamu mu taɓa, wasu sukan ce arziƙi kashi baka kwana dashi ba, sai ka tashi dashi. Kamar gidan ƴan Film" Tunda Emama ta shigo Baffas estate ta kasa yin shiru da bakinta saboda sambatu ganin daular gidan girma da arziƙinbgidan masu Jiha da juya wasu rassuna na ƙasashe. Gidan da ake ado da addini da taƙama da Musulunci gidan cikakkun mabiyan Izala (Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa lqamatis sunna). Ganin babban parlorn da ake ajjiye baƙi babu kowa sai su ya saka Emama zungurin Iftihal ta ce "Kalli gida ɗan ubansu, ba irin na gidanku ba wanda uwarku ta ja mana jarfa, ai Allah Ya isa tsakaninmu da Innti sau cikin carbi gantalalliyya matsiyaciyya" Iftihal ta runtse idanunta daga zaunen da take tun ɗazo ta ƙanƙame jikinta waje guda, wasu hawaye masu zafi suka shiga bin fuskarta. Idan ta buƙaci lallashin kanta da zuciyarta da zarar ta tuna wai an sakata a caca Alhaji Baita ta cita sai ta ji tsakanin rayuwarta da mutuwa babu tazara, walwala da farinciki sun sake nesanta kan su da ita. Iya rumbun cikin Alhaji Baita tsoro yake bata, balle ta kalli cikin bakinsa, gashi bata ma san ya kalar gidansa yake ba, babban abin da yake mata yawo a kanta bai shige rashin sanin aurenta zai yi ko kuma farkarsa zata zama a gidan?
Tana cikin wannan tunanin Emama ta ce "Idan kina so a soke batunki da Alhaji Baita ki yi ƙoƙarin sace zuciyar wani namijin a gidan nan, ko me gidanne ma. Ina nufin magajin gidan, idan hakan bata faru ba, da zarar kinga an ajjiye kuɗi ki yi wuf ki saka su a hammata ko cikin wando ko cikin hular kan ki, su basa jin kuɗin a iska suke ganinsa ina faɗa miki. Ɗan raguye-raguyen abinci da nama duk ki haɗo kan su ki juye a leda ki kawo mini har gida. Ke ko wani ne ya nuna yana buƙatarki ki amince" sai ta yi saurin rufe bakinta ta ce "Asstagafirullah! Nan gidan malamai ne na manta ba za'a samu me bin mata ba" ita kaɗai take da surutunta ci kan ki Iftihal bata iya cewa ba. Ina zata iya magana? Bayan ƙirjinta ya jima da yi mata nauyi yana rinjayar zuciyarta, ji take kamar zuciyar ce zata tarwatse gabaɗaya ta huta.
"Assalamu alaikum"
Wata kyakkyawar yarinya ta yi sallama ba tare data shigo ba.
"Maraba waye?"
"Zan iya shigowa?"
"Bisimillah"
Shigowa ta yi ta gaishe da Emama ta ce "Mamy ta ce ku shigo É—aya parlorn"
"To to to babu laifi, ke tashi muje" tana faÉ—in hakan ta juya abinta. Emama ta ce tana kallon Iftihal dayin gaba.
Iftihal bata san ya aka yi ta iya miƙewa ba, balle tasan yadda aka yi ta iya taka ƙafafuwanta taje bakin ƙofar kamar yadda bata san mene ya tsayar da ita a wajan ba. Ta ji ƙamshi na dukan hancinta ta kuma ji ƙwayar idanu na bin jikinta wanda ya sake sakar mata da lakar dake riƙe da gadon bayanta zuwa ƙafafuwanta. Idanunta rufe kamar yadda ƙofar zuciyarta yaja ya rufe bata san kuma mene ya haddasa mata rawar ɗari ba, gabaɗaya ta yi baya ta nemi zubewa a wajan.
"Ki bi a hankali ko?'
Ta ji sautin muryarsa ya sauka a kanta. Ta buɗe idanunta da ƙyar ganinta ya sauka a farar fuskarsa me ɗauke da nutsuwa da kamala, nutsuwarsa kaɗai ta isa ta nuna yadda ibada ta zauna masa domin ta tabon sallah nan a tsakiyar goshinsa, wanda hakan ya tuna mata da nata tabon ta miƙa hannu kaɗan ta shafi nata tabon hakan ya saka ya kai dubansa ga nata.
"Ma sha Allah"
Ya ce a fili yana bin gefenta ya shige. Iftihal ta ƙarasa ta zauna kanta a ƙasa ta ce
"Ina yini?"
"Allahamdulillah"
Mamy ta amsa da kulawa.
"Ita ce me aikin?"
"E Hajiya ita ce kamar yadda kika nuna yarinya kike buƙata itama bata shige 17 ba"
"Age mate É—in Nadiyaah da Diyanah ce ashe ma"
Mamy ta furta a fili kafin ta ce. "Shukrà n alaiki. Waɗanda za ta yi wa aikin sa'ointa ne. Zata dinga musu breakfast, lunch da dinner. Ina ga iya lunch ne dinner bai wani dame su ba. Sai mahafinsu idan ya dawo" idanunta akan azkar ɗin hannunta take yin maganar. Da kamala a tare da ita. Emama ta ce
"Duk zata iya babu assha"
"Makaranta ta?"
"Na'am........?
"Bata zuwa makaranta ne?"
Caraf ta ce "Lahaula bokoko a wuta? Ai tuni suka yi mata korar kare bata fahimta sam a karatun data samu mijin aure za'a yi mata"
Daidai nan ya sake shigowa parlourn cikin sabuwar shiga wagambari ya saka ruwan sararin samaniya wanda ya kwanta a jikinsa ya É—ora hula me kyau ta zauna a sumar kan, bayan ya sake yin sallama ya nemi waje kusa da Mamy ya zauna. Mamy ta kalli Iftihal lokaci guda ta ji yarinyar ta shiga zuciyarta. "Ok. Per month kuke son salary É—inta ko per year or daily? Wanne a ciki"
Emama ta zazzaro idanunta waje. Mamy ta É—auki a Æ™allla minti uku tana duba azkar kafin ta ce "duk wata za'a dinga bata dubu É—ari da hamsin in sha Allah, ki je ita zata dawo gida anjima ko?" Sallama Emama ta yi musu ta tafi. Bayan tafiyarta aka nunawa Iftihal wani kitchen daban da zata dinga aiki a ciki. Mu'allim ya dubi Mamy ya ce "Baffa be sanar dake garin da yaje da'awa ba ne Mamy?" Kai kawai ta girgiza. Bai sake cewa komai ba, domin ya lura itama Mamyntasa bata da ra'ayin cewa wani abu a yanzu É—in. Don haka sai ya tattara nutsuwarsa wajan jan idanunsa ya lumshe yana sauraran kiran Liman duk da babu tabbacin zai kira shi a yanzu É—in kamar yadda ya ce. Kasa haÆ™uri ya yi ya dubi Mamy ya ce "MÄ ismuhÄ?" (Ya sunanta)" A hankali ta juya ta watsa masa fararan idanunta ta ce "kana da business da ita ne Mu'allim?"
"Mamy kika sani ko a haÉ—a bikina dana Akhy" azkar É—in hannunta ta ajjiye ta kalli jaridar dake saman table ta miÆ™a hannunta tare da faÉ—in "NÄwilni" (MiÆ™o mini" ya É—auki jaridar ya miÆ™a mata yana rusunar da kai gefe cike kuma da ladabi. "Mamy don Allah...," ta yi saurin katse shi da faÉ—in "Ina ga kamar ka san hanyar shiga kitchen ko Al'ameen?" Ya É—an cire hularsa yana shafa kai bai sake magana ba, ya nufi saman bene Mamy ta bishi kallo har ya shige a hankali ta sauke É“oyayyiyar ajjiyar zuciya me nauyi.
Tana tsaye a gaban haÉ—aÉ—É—an madubin dake cikin bedroom É—in tana yin rolling da mayafin abayar hannunta, silver ce irin wacce bata da nauyi a jiki tabi jikinta ta kwanta. A hankali ta É—an yatsuna fuska saboda ciwon dake É—arsarta har yanzu. Daga bayanta aka ce "Ukhty ina zaki ne?"
Nadiyaah ta juya ta kalli Diyanah dake kwance saman kujera wacce take jikin gado, kayan shan iska ne marasa nauyi a jikinta sai data gama ƙare mata kallo ta ce
"Abinci"
"Yunwa nake ji.....
Taja idanunta wanda suke sak irin na mahaÉ—inta ta ce "Sosai nake ji Ukhty" Diyanah ta sakko daga saman kujerar ta ce "Muje na tayaki girkin ko noodles ce"
"Noodles dai?" In ji Nadiyaah.
"Yeah. Kin yi waya da Baffa?"
Girgiza kai kawai ta yi alamar a'a tana sake jan idanunta wajan lumshe su. Diyanah ta kama hannunta suna Æ™oÆ™arin fita aka yi knocking cak suka tsaya. "Assalamu alaikum" a tare suka amsa sallamar. Ya É—ora da "Ina neman izinin shigowa wajanku" Diynaah na shirin tambayar waye Nadiyaah ta rigata da faÉ—in "KhÄlÄ« Al'ameen, Mu'allim"
"Bisimillah..." Ya buɗe ƙofa ya shigo. Gabaɗaya suka miƙa masa hannunsu alamar musabaha suka gaisa ya ce "Baffa fa?" Nadiyaah ce ta ce "Ya dawo ne? Ban ji Ƙamshinsa ba, jikina bai bani Baffa am yana kusa damu ba" Mu'allim ya girgiza kai ya ce "Bai dawo ba, ina tambayar ko kun san garin da yaje da'awa" Nadiyaah ta ce
"Ask Ukhty Diyanah" tana faÉ—in hakan ta fita. Diyanah ta ce