← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 64

Sashe 62

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haan ya kasa yadda da maganar da Kaka yake yi na cewa sun rasa Anum da Jarumi. Ya yi cikin gidan da sauri, har lokacin iska me ɗauke da guguwa na tashi yana ɗaukan mutane sosai. Sanda ya shiga sai ya ga cikin inda su ka yi gininsu a gaɓar kogin ya tsira ya shiga yana duba inda Dooshima ya ɓoye Anum da Jarumi. Cikin sa'a ya ga ramin ƙasan ya buɗe, daga Anum har jarumi babu me numfashi a ƙirji haka ya ɗaƙƙo su yana kiran sunan Kaka da ƙarfin gaske, kwantar da su aka yi a gefe aka shiga yi musu magani. Anum ta riga farfaɗowa a gigice ta shiga girgiza Jarumi tana kiran sunansa, wata soyayya ce me ƙarfin gaske a tsakaninta da Jarumi, soyayyar da ko iyayensu basa yi wa hakan. Kaka ya sauke numfashi ya ce "Uwa"

"UWA MAMA kina ina? Ki kawo mana É—auki ki, maganarki muke jira, furucinki muke jira"

Haan ya ce "Kaka anya ba za mu fita neman uwa mama ba? Yaushe za mu jira zuwanta? Yaushe za ta zo garemu? Tana ina? Tana kusa da mu ko tana nesa da mu? Tana duniya ko ba a haife ta ba? Ya kamaninta suke Kaka?" Kaka ya yi shiru na wani lokaci kafin ya ce "Haan, ba a faɗa mana suffarta ba, haruffan sunanta kwai aka bamu, sunan Uwa Mama za a iya samun a haruffan A, ko H, ko F, Mama tana ɗauke da Tsav ne, Tsav wani tsohon tunani ne na gargajiya a al’ummar Tiv wanda yake da alaƙa da:bikon asiri, sihiri, ƙarfin ruhaniya,ko wata baiwa da ake ganin mutum yana da ita ta ɓoye.
A fahimtar gargajiyar Tiv: ana ganin wasu mutane suna da “Tsav” a jikinsu wanda zai iya ba su ikon yin abubuwa na al’ajabi ko cutarwa, waɗannan mutane su kan su basu son suna da wannan baiwar ba, wannan baiwar ita mu Tubabe muke so da buƙata"

Haan ya ce "Yanzu kaka yaya za mu yi?"

"Dole mu jira bayyanar Uwa mu roƙi Aondo ya kawo mana ita, bana son Akombo ya sake yin fushi damu Haan, wannan shine"

Dare ya yi, cikin dare suka farka da wani sabon tashin hankali, gabaɗaya gonakin da suke noma a ciki wuta ta kama a cikinsu, komai ya ƙone tas, ga gawarwakin mutane da suka gani zube. Sati ya shuɗe haka watanni babu Dooshima babu labarinsa, hankalin Anum ya tashi sosai, kaka ne ya shafe mata tunanin Dooshima tas kanta da zuciyarta, ta mance ta dinga kallon Haan mahaifin Jarumi a matsayin nata uban.

Sojoji suka dawo, a wannan lokacin babu tashin hankali. Suka kalli kaka suka ce

"Ya muke ciki daki ne?"

Kaka ya ce "Mun amince da sauyin da za ku kawo mana, ina roƙan Aondo ya baku damar dawo mana da Dooshima da aminci"

Sojan ya ce "Dooshima? Bai dawo ba?"

"Kun sake shi ne?"

Sojan ya kalli Haan ya ce "Me zai saka mu riƙe shi? Baya wajanmu, tun a lokacin ai mu ka saka a kawo shi kan iyaka damu"

Uji da Terhemba suka kalli juna.

A 1976 aka sake ƙafa tsarin Mulki na TOR TIV aka naɗa Kaka matsayin shugaban Tubabe. Wannan mulkin ya baƙanta ran Imande family sosai, aka yi shagali akai Swange dance Kwagh-hir (wasan kwaikwayo da al’adar Tiv) Tsarin Tor Tiv, ba sai ka mutu ba, akwai adadin da ake ɗauka a yi juyin mulki zuwa wani family, don haka Imande suka matso ƙwarai mulkin ya ƙare daga hannun Ikur family. Kaka ya mutu, nan take aka ɗauki muƙami aka bawa Terhemba.

Haan yana ɗaya daga cikin dattawan masu zartarwa duk da haka ya zama ɗan kallo, ya bada shawara akan yadda Terhemba ya fara sawa na kawo masa mata yana lalata budurcinsu akan neman Uwa Mama da yake. Jarumi yana da shekaru goma a duniya, ya fara kulawa da Tor Tiv da dukkan zuciyarsa, duk rikicin da za a kawo musu yana ɗaya daga cikin jaruman da suke kare tubabe. Ya zama zakaran gwajin dafi wajan faɗa da wasa da kibbau, yana da sha'awar wasan ruwa, kodayaushe yana gefen ruwa ƙafafunsa a ciki, ga wata soyayyarsa da aka ɗorawa jama'a, duk inda aka ce ga Jarumi nan sai an cika. Murmushinsa ya fi maganarsa yawa sosai.

Watarana aka wayi gari rikicin manoma da makiyaya ya ɓarke, Jarumi ƙoƙarin kare al'ummar Tiv yake, koda wasa baya taɓa zubar da jini, ko Fulani ya gani yana basu hanya. Rikicin ya yi tsanani domin jar da Junkun a kawo musu hari. Bayan komai ya lafa jikinsa duk jini ya nemi Anum ƙasa da sama ya rasa babu ita babu alamar ta, ba ƙaramar ɓarna Fulani sukai musu ba.

Jarumi ya yi kukan rashin Anum ya sake zama shiru shiru a wannan lokacin kuma dukkan Tiv suka amshi addinin kiristanci, aka fara daina gargajiya mutane suka fara zuwa cuci, aka gina makarantu da kasuwanni. Amma duk da haka wasu ba su daina gargajiya ba, kamar yadda ba su watsar da tsafi ba. A wannan lokacin Terhemba da Uji da Haan su ka yi tafiya, sanda suka tashi dawowa babu Haan sai gawarsa da ta ƙone sun yi tsari kuma shi kaɗai ne ya rasu. Maraici kota ina ya rufe jarumi.

Shekarar 1976 tana da muhimmanci sosai a tarihin yankin Tiv. Najeriya a 1976 A lokacin soja ne ke mulkin Najeriya. Shugaban ƙasa shi ne Olusegun Obasanjo (bayan mutuwar Murtala Muhammed a Fabrairu 1976).Babban Abin Da Ya Faru a 1976 1. Local Government Reform (Gyaran Ƙananan Hukumomi) A 1976 gwamnatin soja ta yi babban gyara: an ƙarfafa ƙananan hukumomi, an tsara shugabancin gargajiya,
an ba sarakuna rawar hukuma. A yankin Tiv:
an ƙara ƙarfafa matsayin: Tor Tiv da kuma:
Tiv Traditional Council.

Ba a kafa Benue State ita kaÉ—ai ba tukuna.
A lokacin: Benue-Plateau State ce.

Sai a 1991 aka raba: Benue State da Plateau State Benue ta zama jiha mai zaman kanta

Inda Tiv sukai rayuwa ya zama River Benue.

***
Sannu a hankali take juya kanta da yammacin, mafarkin da ta yi a yau na rashin Anum ya sake saka mata nauyin zuciya. Da ƙyar ta buɗe idanunta da suka kumbura sosai, kwananta huɗu kenan a haka, hakan ya yi daidai da kwana uku da rasuwar Innti.

"Abbaaa" ta ce a hankali tana yi masa murmushi me kyau, domin a fuskarsa ganinta ya sauka, kanta a kan cinyarsa yana gyara mata sumar kan da a kullum baya rabuwa da gyara mata. Jadid ya sauke ajjiyar zuciya ya ce "Finally, gudan jinin Abbaa ta farka" sai ta masa murmushi.

Jaheed da yake ta firfita wuta idanuna cike da hayaƙi yana ƙoƙarin dafa taliya ya ce

"Sannu da turmushe wa Abbaa cinya"

Ana ta miƙe a hankali ta kalli Abbaa shima kallon ta yake, ta tsorawa cikin idanunsa ido sai ta shagwaɓe fuska ta ce "Abbaa wai haka?" Ya girgiza kai ya ce "Ko goyo kike so zan miki shi har ki sake yin wani baccin"

Jadid ya kasa dauriya ya ce "Ba ki tambayi Iftihal da Innti ba" ta yi shiru alamar tunani zuciyarta ta buga da gaske kanta ya sara ta ɗan rirriƙe kanta ta ce "Su waye haka?"

Su ka yi shiru suna kallon ta, Jadid ya juya yana share hawaye. Sai ta juya idanunta ta ce "Nifa ban san so ba, Allah da gaske"

Daidai nan Yaa Sam ya yi sallama yana ganinta zaune kusa da Babban Yaya ya ja idanunsa ya lumshe yana jan numfashi da saukewa. Su Jaheed suka gaishe shi, idanunsa akan Ana ya amsa. Ta gaishe shi ya ce "Ya jikin nakin?" Ta juya idanunta ta ce

"Abbaa wai ya jikina bani da lafiya ne?"

Bai amsata ba, bata da sukuni yanzu komai ta ce Abbaa. "Ya ƙarin haƙuri kuma?"

"Waye ne ya rasu kuma? Daada? Allah Ya sa shine ya mutu Allah Ya sa babu shi a raye"

Babu wanda ya san meke faruwa da Ana sai Abbaa gabaɗaya ya shafe mata tunanin Iftihal da Innti. Yaa Sam ya yi musu sallama ya fita Ana ta yi kwanciyarta akan cinyar Abbaa yana ƴan wakoƙinta deep down tana jin kewa me zafin gaske, tana jin kamar bayan ita akwai wasu daban da suke tattare da ita. Jaheed ne ya yi musu girki suka ci, da dare ya yi a ɗaki ɗaya suka kwanta, Jaheed da Jadid shimfiɗa ɗaya, Ana tana shimfiɗar Babban Yaya ta shige jikinsa sai bacci take.

Idanunsa biyu, suna haka Daada ya shigo a yadda ya saba shigowa, duk suka farka har Ana ta fito. "Ki shirya gobe zan kai ki wajan Alhaji Baita, a madadin Æ´ar'uwarki dana saka a caca, ya ce dole sai na biya shi"

Ana ta sheƙi da dariya ta ce "Ko ba biya ba"

Ta san cacar, fresh komai yake kanta matsayin Innti da Iftihal da kasancewar su a gidan duk ta mance bata ma san so ba.

Daada yayo kanta Abbaa ya shiga tsakiya, shi dai ya san yana ɗora hannunsa akan Daada tsaf za'a ɗauke shi babu rai, kuma hukuncin zai hau kan shi, duk abin da zai raba shi da Ana baya so. Kuma har yanzu yana riƙe da umarnin Innti akan Daada.

"Muddin kaga ban bawa Baita ita ba, ka É—auka bana raye a duniya ne wallahi"

Sannu a hankali Ana ta fara tuna irin makamancin wannan maganar da ya yi a baya. Rawar da zuciyarta take yi, ya haddasa wa jikinta amsar ta yin da zuciyar ke yi masa. “kuɗi ya fi mini komai akan ta, farincikin da nake ciki idan na ga jaka guda, ya fi mini kallon ta, matsayin ɗiyar cikina, ba ita ba, hatta uwarta zan iya sadaukar da ita muddin za a cika lalitata da kuɗi wallahi”

Sannu a hankali, maganganun suka shiga dawo mata tare da kai komo a cikin kanta. Suna yi wa ƙwaƙwalwarta tuni!

“Bani da ko sisi, ina kuma buƙatar sulalla na gaji da zama da dattin aljihu, na shiga caca, na kuma yanke shawarar sanya Ayshatul-Iftihal a cikin cacar, idan na ci za ta cigaba da rayuwa a gidan nan, akasin hakan na sadaukarwa da Alhaji Baita ita akan cacar”
Chapter 62 · 0% Book details