← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 64

Sashe 41

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana tsaye taga Babban yaya ya fito daga cikin ɗakinsu abin ya girgiza ta bata san yaushe ya shiga ba, data lura dashi sai taga kamar bashi ba, taga kamar idanunsa bana Muraad ɗinta ba, data ci-gaba da kallonsa sai taga kamar gashi ne ya mimmiƙe a jikinsa har ya zame masa riga data sake kallon yatsun hannunsa sai taga kowanne yatsa ya ruɓanya kan shi sau biyar a tsayi. Ɗago kai ta yi suna haɗa ido taga ya yi mata kyakkyawan murmushi kuma ya zubawa ƙofar ɗakin da Daada ya cilla Ana a ciki idanu yana girgiza kai.

SHEKARUN DA SUKA SHIGE A BAYA.
YEARS AGO.

Ana ta ƙwala kiran sallar magariba a lokacin tana zaune kan dakalin ƙofa da cikinta da ya yi kimanin wata huɗu kanta babu ɗan kwali. Yau ɗin da fara'a ya shigo gidan ya juya ya kalle ta da kulawa sai ya girgiza kai ya ce "Na fahimci a kwana biyun nan ba ki da aiki sai zaman kan dakali kuma dab da magariba kike wannan ɗabi'a" ta kalle shi kawai sai ta ce

"Zaman yana mini daɗi ne sosai" Ya jujjuya kan shi kafin ya ce "duk faɗin tsakar gidan ki rasa wajan zama sai dakalin ƙofa? Gaki da juna biyu ga kai a buɗe" Ta yatsuna fuska ta yi tamiƙe da ƙyar tana nufar murhu shimkafa ƴar Hausa ta tace tana jin yana ta mita shi kaɗai kamar zai ari baki amma bata ce ci kan ka ba. Bayan ta gama tace shinkafar ta mayar ta turara, ruwan da tatar da yake azabar turiri ta nufi bakin rariya dashi. Kafin ya yi magana ta zubar da ruwan a wajan tsananin azabar ya saka fuskarta haɗa zufa. Ya yi zumbur ya ce

"Subuhanallahi! Ya za ki zubar da ruwan zafi a bakin rariya da irin wannan lokacin madadin ki tsahirta ya sha iska ba kyau"

"Ina ake zubar da ruwan zafi idan ba bakin rariya ba masoyi?" Ya kalle ta sai ya girgiza kai ya ce "Allah Ya kyauta"

*Back. Iskar da ta ji an kaɗa mata ya dawo da ita tunaninta, kafin ta yi magana ya fice daga cikin gidan gabaɗaya. Fargabar rasa igiyar aurenta ya saka Innti ɗora ruwan zafi a wannan lokacin. Sai yanzu take sanin anahin inda take samun ciwon sanyi (Infection) idan Daada ya ɗauke mata ƙafa da zarar ta fara amfani da maganin sanyi na haɗin shayi da Maman Haysaam ke bata, wanda take siya a wajan BloomHer Wellness ingantaccen haɗin maganin sanyi ne da ake tafasa shi kamar shayi, sha ɗaya ka yi masa zaka san ka sha maganin sanyi tsaftacce ne, iya ƙamshinsa abin sha'awa ne, tana aikawa ko'ina cikin ƙanƙanin farashi, Maman Haysaam har maganin sanyin ƙashi take bata. Duk sanda ta sha haɗin shayin na sanyi wasai take jinta, amma da zarar Daada ya raɓeta sanyinta zai dawo ashe a wajansa take kwasa shi kuma a wajan Tani yake ɗauka. Ruwan ya yi zafi ta juye a tukunya.

A tare suka fito manne da juna suka shige banÉ—aki zuciyar Innti na ayyana mata ta É—auki ruwan zafin ta kwara musu gabaÉ—aya.

Sukai wanka suka fito, daga nan suka fara buɗe ƙofar shaiɗanci, wajan busa sigari da yin wasan karta.

"Mijin Innti"

Cewar Tani sai ya watsa mata harara. "Zan miki rashin kirki Tani ki daina haÉ—ani da wannan salamatun matar na faÉ—a miki"

Tani ta ce "Ina da shawara, me zai hana ka kamawa Ana shago a cikin gari irinsu ake ya yi a wannan zamanin, tunda kaga yadda cacarku da baita ya kasance, ni zan dinga kai wa manyan mutane tallanta mu dinga samun kuɗi da ita, yarinyar ba ƙaramar kasuwa za ta yi ba"

Daada ya numfasa.

"Kina ganin hakan me yiyuwa ne daman shiga cacar da na yi da Iftihal a wajanki na nemi shawara?" Ta maka masa duka

"Me zai hana shi yiyuwa? Kafin kama ɗakin za'a fara bata wasu magunguna, za'a koya mata makirci, salon ƙwace ɗa namiji, da salon tafiya da yaudara"

"Shi ya sa nake son ki gidan albarka, ko ni zan iya koya mata ina da sauran magungunan dana ba ki jiya bari na É—akko na danne Æ´ar banza a bata" Innti ta ce

"Wallahi ƙarya ne, idan kun isa na zama ƴar albarka" wani wawan mari ya yi mata ya saka ta a cikin ɗaki da ƙarfi ya rufe ta a a ciki. Maganin ya ɗakko da suka kasance masu ƙarfi, ya buɗe ɗakin ya shiga tana kwance bata cikin hayyacinta Tani ta riƙe ta suka tuttula mata maganin ta ce "Yarinyar ta zama budurwa ma. Ka ce basu fi 17 ba"

"Jikinsu ne me fushi amma yara ne su fa"

Ta ce "Ina yara a nan duba ka gani" Ta faɗa tana yaye masa rigar Ana har zuwa ƙirji, sanda idanun Daada ya yi arba da ƙirjin Ana har yawu ya haɗeye, duk da yana ƙoƙarin haramtawa kan shi hakan. "Ka dubi ƙirjinta ai wannan ta riƙa sosai a gida ta zama riƙaƙƙiyyar kuɓewa, idan baka yarda ba duba" ta ce tana haska masa ƙirjin Ana ta fitila, duk tsalle tsallen Daada da yadda yake shigewa lungu da zarar magariba ta yi yana tarfa yaran jama'a da laƙume musu baiwarsu gane ganensa bai taɓa gano masa lafiyayyen ƙirji irin wannan ba, wani abu ya ɗarsu a ransa wanda yake kokawa dashi a hankali ya kai hannu kamar zai shafo su sai ya yi saurin janye wa ya ce "Muje waje"

*

Tun 7 saura Yaa Sam ya shirya cikin farar shadda me kyau ya ɗora a saman kan shi, ya yi kyau sosai nutsuwa da kamalarsa ta fito, sai ƙamshi yake yi. A nutse ta dube shi ta ce "Har ka shirya? Gashi ban kammala abin kari ba, ko zaka jinkirta?" Ya duba lokaci, sai ya girgiza kai alamar tafiya zai.

"Yanzu a can gidan Gwamnati za'ayi muku interview ko ma'aikatar ilimin?"

"Both, wasu a Government house wasu ma'aikatan ilimi" ya faÉ—a a nutse yana gyara zaman hular kan shi tare da juya grey eyes É—insa.

"Allah Ya taimaka ya bada sa'a, Allah Ya sa ka samu aikin nan ko zaka mure da ilimin da ka yi ko?"

"Amin" ya ce yana ficewa daga cikin gidan.

*
Washegari da safe a gurguje Ahlam ta shirya cikin kamilalliyar shigarta duk da still tana jin raɗaɗin ciwon amma burinta yafi ƙarfin ta tsaya sanya ta ci sa'a Engineer baya nan ta nufi waje tare da tarar napep ta ce Hisba headguater zai kai ta don Allah ita kaɗai.

Ya ce "To hajiya amma drop za ki biya" "No problem"

Suna isa ta biya shi kuÉ—insa ya dinga godiya ita kuma ta shiga cikin babban headguater É—insu tana addu'ar fatan alheri wa kanta.

*
GANDUN ALBASA.

Yana tsaye inda ya yi parking motarsa ya jingina bayansa da jikin motar idanunsa cikin glasses kamar koyaushe, farar single ce a jikinsa data kama shi sosai, sai jeans wanda ya dace da rigar jikin nasa, ya É—ora p.cap a kan shi yana É—an kaÉ—a key É—in motar dake hannunsa. Wanda ke kusa dashi ya ce

"Seriously idan na ce kana da problem baka yadda dani, yanzu kalli yadda kake ɓata time ɗinka akan wasu ƙazaman mutane" ya yi maganar yana jan siririn tsaki tare da hurgawa MD uwar harara, duk abin da yake yi ta wutsiyar idanu MD ke kallon shi. Ganin yadda ya yi masa banza ya masshe shi ɗan banza ya saka Anwar yin ƙwafa ya ce "Amma dai ka san ni ba ɗan banza bane da zaka je har office ka ɗakko ni ka yi tunanin zan zauna free time muna shan iskar gari, iskar ma mu rasa ta shan ko'ina sai ta Gandun Albasa for God sake" yadda ya yi maganar shi kaɗai shi kaɗai ya sake bawa kan shi amsa da

"Are You deep?"

"Ubanka kake so na yi maka Anwar?" Ya ce a slow voice

Anwar ya zare glasses ɗin idanunsa ya ce "Kar ka faɗa mini mun fito don kawai muzo ƙofar gidan dattijon nan mu kalla mu koma?" Taɓe baki kaɗai MD ya yi cikin husky voice ɗinsa ya ce "Anwar idan ba zaka iya jira ba you can go please, ba kyauta na ɗakko ka ba aiki za ka yi mini na kuɗi officer"

"Aikin kuÉ—i"

A daƙile MD ya ce "Yeah"

Kafin Anwar ya yi magana dattijon ya fito bayan ya yi musu sallama ya ce "kune kuke sallama dani?" MD ya yi shiru sai Anwar ne ya ce

"Mune baba". Wanda aka kira da Baba ya ce "To lafiya dai? Naga baƙin fuskoki ne ban waye ku ba"

MD ya ɗan yunƙuro ya ce "amm ina jin lafiya ba zata kawo mu gidanka ba, tunda baka da wani abu da kake na business ɗin da zamu zo gare ka. More especially daya kasance ina tare da mai uniform ɗin police" a gadarance ya ce "Ina ɗanka daka aika shi ya yi kisan kai? Ka fito mana dashi mu shige station" a rikice ya ce

"ÆŠana? Kisan kai fa ka ce yaro?" MD ya dubi kan shi sosai jin ya ce masa yaro kafin ya tsuke fuska ya ce "Kasan me nake magana akai. ÆŠan'daban yaronka daka tura shi ya kashe ma'aikaciyarmu saboda ta saka rahotan abin da matarka ta yi wa amarya"

Baba ya ce "Assha assha yaro ban san zancan ba, ban san anyi ba wallahi"
Chapter 41 · 0% Book details