Sashe 11
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya jinjina kai, bayan ta fita ya miƙe shima ya fita zuwa waje, babu jimawa ya dawo hannunsa ɗauke da leda, ya ɗauki kwano ya saka tuwo da miyar ya shiga ɗakinsu Ana, ita kaɗai ce Ifti ta fita aike zuwa maƙota. Ya zauna saman ƙafafuwansa irin zaman raƙuma ya ja kwanon gabanta, tun kafin ta yi magana ya zura yatsunsa ya ciro tuwon ya saka mata a baki, ta ɓata fuska haka ya dinga bata tuwon a bakinta da hannunsa ganin kamar za ta yi amai ya wanke hannunsa ya miƙa mata ledar, indomie ta gani dafaffiya tun kafin ta yi magana ya fice daga cikin ɗakin yana rufe idanunsa. Daman tun asubar fari Daada ya fice nasa waje, su kaɗai ne a gidan.
***
Ƙuri ta yi wa jaririn da yake kwance jikinsa kamar kwando saboda saɓulewa da ya yi, bata iya taɓa shi an baɗe masa jiki da wani garin magani. A hankali ta kai hannunta zuwa fuska ta share hawayen idanunta, bata taɓa ganin aure irin wannan ba, ko da ta taɓa gani nata yana da tarin bambanci, mijin ya aureta amma kamar kishiyarta ce ke riƙe da igiyoyin auren, da ƙuruciyarta da komai amma baƙincikin aure da zaman kishiya ya sako rayuwarta gaba, haihuwa ta yi ko kunun kanwa wannan bai ga cikinta ba, balle ƙaurin da ake yi wa me jego. Ɗan kara kunnenta ta yi sai ta ji numfashin babyn na fita da ƙyar.
Labulen É—akin aka É—ago yana daga tsaye ya ce "Wato Maryama ba za ki je ki hana me rahotan can sakawa ba, wallahi Allah muddin ta saka a bakin aurenki makira munafuka" kasa motsi Maryama ta yi, jikinta É—anye ne sosai abarka da farar mace ta sake yin fari shar kamar mara jini a jika, gefe da gefen fuskarta duk gashi ne kwance haka ma girarta kyakkywa ce sosai bata shige 21 ba gabaÉ—aya.
Cike da tsoro ta ce "Ai ban santa ba, bani na faÉ—a mata ba. Kar ka sake ni don Allah wallahi za'a iya kashe ni a gidanmu"
Da hargagi ya ce "Ai gwara su kashe ki tunda gashi za ki jazamin shiga masifa da zarar hukuma ta ji na kaÉ—e har ganyena"
Wacce take gefensa ta yi ƙwafa "Malam burinta ba a rufe ni na bar gidan ya zama daga kai sai ita, na faɗa maka ba ƙaunata take yi ba, da zaka sake ta da yafi" sai ya yi mursisi da idanu saboda yana ƙaunar tarayya da ita "A'a bata kai ga haka ba, ki duba duk ayyukan gidan nan Maryama ce ke yi miki idan ta bar gidan yaya kenan"
Wani irin malalacin kallo ta watsa masa "Na fahimci kamar son ta kake, bana hanaka ce mata Maryama ba idan ba zaka ce ƴar aiki ba kawai ka yi shiru kaima fa Malam jarababbe ne" tusa ƙeyarsa ta yi suka fice daga ɗakin. Maryama ta bisu da idanu tana fashewa da kuka a hankali ta ce "Ubangiji ka kawo mini mafita ta alheri"
***
NIGER/MINNA.
Jihar Niger tana Arewa ta Tsakiya (North Central Nigeria). Ita ce jiha mafi girma a faɗin ƙasa wanda babban birninta ya kasance Minna, suna maƙwabtaka da Zamfara, Kebbi daka Arewa, sai Kaduna, FCT Abuja daga Gabas, sai kuma Kogi, Kwara daga Kudu, Benin Republic daga Yamma.
Akwai mabanbanta mutane a jihar Niger zuwa Minna, Nupe a ɓangaren Bida, Lavun, Agaie. Sai Gwari/Gbagyi daka ɓangaren Suleja, Tafa, Minna. Sai Hausa Fulani a yankin Kontagora, Rijau, Wushishi, haka sauran ƙabilun kamar Kamuku a yankin Mariga, sai Kambari a yankin Agwara, sai
Basa a yankin,Katcha haka kuma Dukawa a yankin Borgu. Niger na daga jihohin da suka fi kabilu haÉ—uwa a Najeriya.
BIYA.
Wani yanki ne a Nijer ƙauye ne sosai, wanda mutanen ƙauyen suka dogara da Noma, farauta da kiwo sana'ar hannu, suna da ɗan yawa gasu da soyayyar juna ta mutunci.
"Wai har yanzu bata sauka bane?"
Lami ta yi tambayar tana kai komo hannunta riƙe da zaninta saboda tashin hankali. Jin an yi mata shiru ya saka ta sake cewa
"Sadiatu, magana nake yi"
"Kika ce me Lami?"
Sadiatu ta yi maganar tana É—ago labule daga É—akin da take ta fito fuskarta babu walwala saboda damuwa.
Lami ta ce "Har yanzu bata juye bane?"
"Sai dai Allah Ya saukar da alheri, ban taɓa ganin naƙuda irin wannan ba Lami, abu tun jiya? Har hantsi ya fara kawo kai?" Sadiatu ta faɗa idanunta cike da hawayen halin da Kulu take ciki, suka yi jingum jingum. "Ai Malam ne da kalar tasa masifar, a kira me karɓar haihuwa amma bafur yaƙi ba dole ba" Sadiatu ta ce "Kin san shi da kafiya kamar kuturu haka yake".
"Ai har gwara kuturu dashi"
"Gafaranku dai"
Suka ji an yi sallama daga bakin ƙofa.
"Maraba lale da Gana, yau kece a tafe?" Cikin fara'a da walwala Gana ta ce "Wallahi, ai tafiyar dole ce shi ya sa na yi babu sanarwa" ta ƙare maganar yanayin fuskarta yana sauyawa zuwa damuwa can kuma ta juya a fusace ta ce "Ba za ki shigo ba ƴar kusun uwa, munafuka makira me ido a tsastsaye, mahaukaciyar banza da wofi"
Lami da Sadiatu suka shiga leƙawa zuwa bayan Gana domin ganin dawa take sai suka hangota tsaye rakuɓe da jikin katanga. Tana zazzare idanu, tare da murza gashin kanta dake tufke tana wasa dashi, sai murmushi take yi tana girgiza kai da nunna abu a sama, ita kanta bata san me take yi ba, ba kuma tana yi saboda hauka bane bata son ganin matan gidanne
"Au wai Batty ce, ince dai lafiya yaushe ta fara hauka kuma ni Æ´ar nan?"
Gana ta yi ƙwafa cike da takaici ta ce
"Ina lafiya? Ai Baffan Batty ne ya ce a dawo da ita gabanku, wataƙila za ta yi hankali, ta dage sai an sata a makaranta" mamaki ya wanzu a fuskokinsu. "To ina Fulani ina zuwa wata makaranta, arna ne kawai suke zuwa bokoko, ya yi mini daidai ai"
"Wata sabuwa ni Lami" ta sake faÉ—ar haka Gana taja kujera tana zama.
"Me ta yi ne? Me ya sa Baffan Batty ya ce a kawo ta Biya wani abu ta aikata a can yarin?"
Cikin fillatanci Gana ta ce “Ko Batty woni jokka waɗude jango mo, sabu ɗum jokkaare makko.†ma'ana a yaren Biya ana nufin “Batty ce ta fara ɗauko masa zance, ai iskanci ne ke tuka ta.†Lami ta shiga salati
"Na boni, me ta É—akko?"
"Zuwa ta yi ake taɓa mata matasan ƙirjin saboda iskaci, shi ya sa shekarunta be ɗakko ba, zuciyarta ta ɗakko nan da nan ƙirji ya haye" Sadiatu ta girgiza kai kawai.
"Yanzu ni da aka kawo mini ita nan na yi yaya da ita? Salon ta dinga É—aukar mini zance, Biya fa ba kamar can yari bace"
Gana ta ce "haka za ki haƙuri Lami"
Sai ta juya ta kalli Batty wacce kanta yake sama tana ta murmushi, a nutse yarinyar take sosai, idan ka ɗauke ƙuruciyar dake addabar kanta kayan saƙi na fulani ne a jikinta an ɗaure sumar kanta kamar alkaki.
"Shai Baffan daya turo ta nan me za'ayi mata? Kiwo zata dinga yi ko farauta?"
"Idan an samu me son ta a bayar da ita sadaƙa" sai a lokacin ta ɗago dara-daran idanunta ta zuba akan Gana tana jin duk abin da suke cewa, da sauri kuma ta faɗo cikin gidan, a hankali kuma ta kalli Sadiatu, ba ita take kallo ba, jinin da yake gudana a jikinta yana kai kawo take kallo, da kuma kwantaccen kitsan da yake cikinta, ta zubawa cikin idanun sai ta hango dafaffiyar masarar da Sadiatu ta ci ɗazo wacce bata gama narkewa ba, wani irin numfashi ta fuska idanunta yana rinewa saboda ja da kuma abin da ya motsa mata, tana ta kallon abin da yake yawo a ƙasan ƙafafuwan Sadiatu. Kafin su yi magana sun jiyo kukan jariri cikin sauri Sadiatu ta nufi ɗakin Gana kuma ta ce "Waye zai haihu?"
"Kulu ce"
"A'a tubarakallah ma sha Allah, kulu Allah ya yi kenan" Gana ta ce tana washe bakinta. Suna zaune aka gyara jaririn mutane suna ta yi wa Kulu murna haihuwar da har ta fitar da rai da ita. Gana ce ta shiga cikin ɗakin tana ƙifta idanunta, bayan ta ɗauki jaririn da yake fari tas ƙato dashi, sai motsa baki take, can dai ta miƙe tana faɗin "Allah Ya raya Kulu sai mun dawo raɗin suna, sannu kin ji haihuwa me daɗi" Kulu na murmushi
Ta ce "Yaya Gana har za ki shige?"
"Wallahi, Batty na kawo ai"
Tana faÉ—in hakan ta laso bakinta kamar za ta yi magana sai ta haÉ—a da kurwar jaririn ta yi sauri ta fito. "Gana tsaya mu yi magana"
"A'a Sadiatu, zan dawo ai in sha Allah"
Ta faɗi hakan tana ficewa, sai data je waje ta tsaya ta ƙulle kurwar a bakin zaninta....
*H I Y A A M*
Page 4
Bright pens
Yota/001
*"A resilient heroine;* Nazeefah Sabo Nashe
Ganin rana ta buɗe ya saka ta ƙara ɗaure bakin zaninta inda ta ƙulle kurwar jaririn tana tafe tana juyawa har ta ɗauki hanyar shiga rugar Fulaninsu da ake cewa Rugar Yari, idanun nan nata jajur babu kyan gani sai motsa bakinta take, tana yin tiƙar baki.
Daga can cikin gidan Kulu na zaune da jaririn a hannunta sai murmushi take yi yau Allah ya azurtata da samun É—a, bayan shafewar wasu shekaru da aurenta, mai rai baya fida tsammani a rayuwa, a wajan Kulu har ta cire rai da ganin jininta a duniya, banda gorin haihuwa, dana kishiya da kuma dangin miji, ana kiranta da juya babu kalar cin kashin da bata gani ba. Duk tafiyar minti guda sai ta juya ta kalli jaririn da zuwa yanzu ta kwantar dashi akan ka katifa. "Kulu kallon yaron ya isa haka" In ji Sadiatu
Murmushi ta yi can kuma ta ce "Yaa Sadiatu ji nake kamar ba daka cikina ya fito ba, me zan yi na nuna wa Ubangiji godiyata daya share mini hawayena? Yau ni na haihu? ÆŠana na kaina nake gani a gabana?" Sadiatu ta ce
"Haka Allah yake ikonsa"
"Haka ne Yaa Sadiatu"