← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 64

Sashe 50

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga cikin bukkar Batty ta kumbura murya ta ce "lalle, ga Ramu da Innarta, ga Shatu Æ´ar rakiya, ga ciwo nan da mutuwa suna binki Ramu, ga lahira nan dab dake Ramu"

Ramu ta ƙanƙame Innarta tace "Inna kin ji ko mutuwa zan yi, daman na faɗa miki Batty ta ce bani da lafiya kin ƙi yadda dani gashi yanzu bokanya karaba ta faɗa sai ki yarda"

"Yanzu Bokanya mene abin yi?" Batty ta maƙale murya

"Kin san ciwon Taifot? Shine yake damun Ramu hanjinta ya fara taɓowa yana fashewa kuma shikenan. A samu tafashasshen gayen zogale ko neem (dogon yaro) ta dinga shan ruwan akai akai sai a dinga yi mata surace, in sha Allah zata samu waraka magani sadidan daga wajan Bokayan karaba" Innar Ramu ta ce "Na gode sosai, na gode Bokayan karaba mene kuma abin sadaƙa" Batty ta yi shiru ta rasa me zata ce, cikin sauri Shatu ta ce "Dubu uku ake bata ai" jikin Innar Ramu na rawa ta ɗauki kuɗin ta tura ta ƙasa, ta riƙe Ramu suka tafi. Suna tafiya Shatu ta yi wuf ta faɗa ciki ta ce

"Mutuniyar....

"Na'am, masoyiyar"

Batty ta amsa tana cire ganyen kanta ta ce "Wash Masoyiyar yunwa nake ji sosai wallahi" Cike da damuwa Shatu ta ce "Yau ma su Lami basu sammiki abinci ba? Suke barinki da yunwa haka?" Batty ta jinjina kai ta ce "Ai don fara cin mutane ba, da sai na lashe kurwarsu tas. Jira nake kaÉ—o ya dawo mu yi aure irin wanda za'ayi wa Hawwa tunda kin ce mijin mutum yana bashi abinci"

Shatu ta ce "Sosai ma. Amma waye kaÉ—o?"

"Wani fari, dogo kyakkywa, me gashi a gefen fuska, me suma har wuyansa shine mijina shi nake so ba Saleh ba, kyakkywa ne sosai don ki ji" shiru suka yi, Batty ta lumshe idanunta tana hasaso yadda taga mutumin.

"Ya sunansa?"

"KaÉ—o.....

"Ke sunan gaskiya za ki waÉ—e mini?"

Sai Batty ta watsa hannunsa alamar rashin sani. Daidai nan Hawwa ta ƙarasu da sauri tana hakki ta ce "Ke Shatu maza zo, Mado ne ya mutu gashi can an cika a gidan Moddibo ana ta kuka, duka abokan Mado na birni sun zo har da Sambo" jikin Shatu ya ɗauki rawa, domin tana da alaƙa da gidansu Moddibo. Jikin Batty ma ya ɗauki rawa sosai da ɓari hawaye ya ɓalle mata a fuska ta ƙanƙame jikinta tana jin kamar ta fasa wani irin gigitaccen ihu haɗe da birigma. "Wallah bani na cinye shi ba, bani bace...," Hawwa ta ce

"Batty me kika ce?"

Cikin sauri Shatu ta ce "Babu komai, mu je mu gani" Batty taƙi yadda ta je gani take kamar asirinta ne zai bayyana. Sanda suka je, shirin yi wa Mado jana'iza ake yi, Shatu ta hangi Sambo yana alwala a hankali ta ce.

"Laa ashe da gaske dai Hawwa take yi?"

Idanun Sambo akan abin da yake yi ya ce

"Da gaske me?'

"Da gaske ka zo binne Mado"

Ya ɗago idanunsa a hankali, ganinsa ya sauka akan Batty, ya ƙura mata idanunsa da suka sha farin ƙwalli ya jima yana kallon ta kafin ya zame idanunsa ya ce "E, babu jimawa" Shatu ta ce "Allah sarki, ya aiki kuma?"

"Kazo da Lemo da biredin yau ma?" Kafin ya ce komai Batty ta ce "Nima ka bani idan ka zo dashi, zaka bani ko yaya ne ko?"

Sambo ya sake juyawa ya kalli Batty can ya ɗauke kai yana miƙewa ya ce "Ina dawowa"

A hankali Batty tabi bayansa da kallo.

***
Anty Jiddah ce ta tura handle ɗin ƙofar ɗakin Ahlam magana za ta yi sai ta fasa, ta zubawa bayan Ahlam idanu ganin yadda faffaɗan waist ɗinta ya zauna a riga da skirt ɗin data saka, ya yi mata wani irin kyau sosai atamfar, ta murza ɗauri na gaban goshi, fat fat haka ƙirjin Anty Jiddah ke bugawa. Sai ta ƙirƙiri murmushin dole ta ce

"Golden voice da kanta, kwaliyyar tarbar mijin ce har yanzu bata ƙare ba?" A hankali Ahlam ta juyo idanunta ya yi jajur saboda kukan da ta yi, ba ta yi kwaliyya ba, amma skin ɗinta ta yi fresh ta goge hannunta ɗaya maƙale a hammata. "Kuka kike Ahlam?"

"Kuka akan me subuhanallahi!"

Ta ƙarasa tana kama Ahlam zuwa jikinta ta ce "Haba kakata, mene abin kuka a aure? Na ɗauka za ki fi kowa farinciki, kin san a duniya bayan ganin kin samu nasara akan aikin ki, babu abin da Engineer yake so irin ya ganki a ɗakin mijinki. Haba Hali dubu, kakata ta kaina ya isa haka daina kukan" Ahlam ta narke tana shagwaɓe fuska ta ce "Anty Jiddah wanene shi? Ki faɗa mini ko sunansa ne, Allah tsoro nake ji bana son fita, bana son auren, na amince saboda Yaya ne kawai, fargaba da faɗuwar gaba nake ji idan na tuna ina da aure. Burina, farincikina, nasarata duk za su rushe fa Anty Jiddah, ɗaukakar da nake son yi fa?" Anty Jiddah ta share mata hawaye ta ce "Haba Babyn yaya, aure ai ni'ima ce kuma ba zai hanaki cimma burinki ba, idan bakya son ran yaya ya ɓaci maza tashi ki sami mijinki yana parlour" da rawar ɗari Ahlam ta ce "Yazo ne? Innalillahi!"

Anty Jiddah ta fashe da dariya tana sake fesawa Ahlam turare, taja hannunta suka sakko ƙasan bene daga nan Anty ta juya.

Yana tsaye a tsakiyar parlourn, ya bata baya sanye yake da yadi kaftan brown wanda ya haska fatar jikinsa, ya ɗora wula a saman kan shi, hannunsa ɗaya sanye cikin aljihun wandonsa. Kan shi a sama ya zubawa photon Ahlam dake manne idanu baya ko ƙiftawa. Ya ji sanda ta tsaya a bayansa nesa dashi, kamar yadda gabanta ke faɗuwa haka shima nasa yake yi, bai sani ba ko zata amince masa, zata karɓe shi a matsayin mijinta, ya aureta ba tare da amincewarta ko neman soyayyarta ba. Amma bashi da iko da kan shi, kamar yadda bashi da control da zuciyarsa akan soyayyarta. She loves her so much. Sannu a hankali ya shiga juyawa zuwa inda take, wata ajjiyar zuciya ya sauke sanda ya ɗora idanunsa a kanta, a yanayin da bai taɓa ganinta ba. Kanta yana ƙasa bata son ya juyo ba, bata san ya ƙarasu inda take ba. Sai nunfashinsa ta ji yana sauka a fuskarta. Kadin ta yi motsi ya zaga hannunsa biyun zuwa bayanta daidai ƙugunta ya ɗora ya janyota kaɗan ya sakata a tsakiyarsa. Wani irin rawa jikinta ya fara.

"Assalamu Alaiki Halimatul Sadiya.....

"Hello my Ahlam Abdallah Kurmi....

"Fine baby, my wife"

Ahlam ta sandare ta kasa motsin kirki zuciyarta ta fara gaza É—aukan yanayin, tsigar jikinta ya shiga tashi, dum haka take jin saukar muryarsa kamar dalma kamar kuma ruwan sama, ta kasa yadda da abin kunnenta yake jiye mata a yanzu É—in.

"Mrs Asad....

"Matar MD da kanta"

Ya saka yatsu biyu ya É—ago kanta, idanunta da yake zubar da hawaye ta watsa akan fuskar Md wani abu na cakin zuciyarta. "Md ne mijina?.....

"Md yaya ya aura mini? Me Md zai yi da Æ´ar iska matsoraciyya? Anya Md take gani?" A zuci take wannan maganar jikinta duka rawa yake ta kasa furta komai, ji take kamar ba Ahlam ba, yau ita Md kewa dariya? Bata dawo daidai ba ta ji ya jata jikinsa ya rungumeta kaÉ—an, ta rasa dalilin daya hanata hana shi, ko yatsa ta kasa motsawa ta yi wani irin hooking gabaÉ—ayanta.

Ya sumbaci goshinta ya riƙo hannunta ya ce

"Let's go.....

"Mu je" ya jata suka fita har inda ya yi parking motarsa ya buɗe mata tare da sakata, ya zagaya ya shiga. Tafiya suka yi me tsayi hannunta yana cikin nasa, ta kasa motsi, ta kasa magana, ta kasa daina zubar da hawaye. Daidai Napep na tsayawa a bakin gate ɗin daidai lokacin da motar Md ta ƙarasu, aka buɗe masa gate ya shiga, itama a dai-dai lokacin ta sako ƙafafuwanta da babu ko takalmi a cikin makeken gidan.

Md ya buɗewa Ahlam ƙofa ya riƙo hannunta, Ahlam kuma ta juya sai kallon wacce take tsaye dafe da cikinta ta kasa motsi take yi. Ya ja hannun Ahlam zuwa babbar ƙofar shiga gidan daidai nan Mu'allim ya fito saboda saƙon Mamy da zai amso, na magani, idanun Nadiyaah ke ciwo sosai tun jiya sun jajur. Mu'allim ya dakata.

"Finally, ni ne wanda ya fara ganinta" in ji Mu'allim

Md ya kalli Mu'allim ya yi shiru.

"Ahky Liman, Allah Ya sa Albarka ashe staff É—inka ka É—akko, wannan ai na sha ganinta a Bright Fm idan na je wajanka, Am right?"

Md ya ce "Al'ameen, ina zaka by this time?"

"Nadiyaah Sayyadi Baffa zan amsowa magani a asibiti wajan family Doctor"

"Sayyadi Baffa?"

Ahlam ta maimaita a zuciyarta, Md yaja hannunta zuwa ciki shi kuma Mu'allim ya yi gaba. Har yazo daidai inda take bai lura ba, sai da ya ji ta cakume shi kamar daman wani take jira, ya É—ago kai gabansa ya faÉ—i ya ce "Iftihal? Me kike a nan wajan?"

Bata iya buɗe ido, bata ko ware laɓɓanta ta kifo jikinsa, nan take kuma jini ya ɓalle mata, a firgice ta ce "Ana.......

"Ana, kai ni wajan Ana zani gida" Laɓɓanta ne kawai ke motsawa idanunta a rufe suke. "No bari na kai ki asibiti"

Ta damƙe hannunsa tana girgiza kai "Don Allah ka kai ni wajan Mahaɗita don.....

Gabaɗaya jinin ya ɓata shi, ya sunkuce ta gabaɗaya ya saka a mota suka nufi Kankarofi. Ana ta kira magariba sanda ya isa, ya ci sa'a Babban yaya yana shirin shiga Masallaci, suka gaisa cikin kulawa, Mu'allim ya yi wa Muraad bayanin komai, har yadda yake son Iftihal ya shirya aurenta, Yaya ma ya yi wa Al'ameen bayani har batun cacar, nan take ya ce zai biya miliyan ashirin ɗin a bawa Alhaji Baita, zai turo Mahaifinsa gobe a ɗaura masa aure da Iftihal ɗin. Yaya ya yi na'am da hakan sukai exchanging number.

Ya ɗauki Iftihal a hannunsa zuwa gida, Innti ta dawo gida da ƙyar bayan alƙawarin da yaya ya yi zai biya Bala Sukunbiya kuɗinsa.
Chapter 50 · 0% Book details