← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 64

Sashe 3

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ba mu mallake ku ba” ya faɗa a hankali. “Ku ne kuke riƙe mu.” Ya ɗauki ɗan gishiri ya zuba a ƙasa. Ya shafa ruwa a ganyen, ya ɗora su a gefen wuta. Murmushi mu kaga yayi, akan hadayar da ya yi wa Akombo.

Itayo ya ce "Akombo ya yarda da zamanmu a nan, bai amince da zubda jini ba, duk wanda ya karya doka bala'in Akombo zai saukar mana, don haka a kiyaye kun ji?"

Ikur da Imande sun yanke shawarar a zauna a nan, saboda ruwa mai yawa, mun samu ƙasa me laushi da albarka ga kuma sauƙin noma. Aka kafa tanti Ikur suka keɓe haka Imande, muna murna mun samu makoma me kyau muna tsaka da bacci, wata mummunar masifa ta afko mana, wanda ya haddasa mana rashin mutane wajan ashirin a cikinmu, farmakin da ƙabilar Jukun suka kawo mana.

1976.
TIVLAND.

Shigowar Dooshima ne da sauri ya dakatar da Kaka daga Tarihin da yake bawa jikokinsa na asalinsu wanda yake bin tarihin shekara-shekara na abin da komai ya faru, tunda daga asalin Tiv har zuwa yanzu da yake shekarar da sukai ƙaura a 1500/1700. Kaka ya bi ɗansa Dooshima da idanu, shima kallon mahaifin nasa yake kafin da hanzari kuma ya ce "A ɓoye mata da ƙananun yara"

"Ɓoyewa? Dooshima lafiya?"

Kaka ya tambaya da tsoro saboda gudun wani bala'in da Akombo zai jefo musu.

Anum na É—an juya fararen idanunta masu kyau da tsari irin na mahafinta Dooshima.

Dooshima ya kalli Kaka ya ce

"Sojoji ne, sune sukai mana ƙawanya kar su sake kashe mu, kamar yadda Junkun suke bin mu kowacce farar asuba su kashe mu"

"Na rantse da Akombo babu abin da zai faru da dukkan jinin Ikur alƙawarina ne wannan, ka hanzarta ɓoye yaran nan yanzu"

Anum ta ce "Kaka me ya saka za'a ɓoye mu?" Ya shafa kan ta cike da damuwa ya ce

"Za mu iya rasa ku a yau ɗin nan Anum ɗin kaka, jeki wajan Babanki ya ɓoye ki kin ji?"

Rashin yadda ya bayyana a tattare da Anum, ita a dole sai ta fita taga Sojojin da ake magana akai. Haan ne ya shigo hannunsa É—auke da baka da kibbau, yana ganin É—an'uwansa Dooshima ya furta

"ka shirya?"

"Zan ajjiye Anum da Jarumi"

Tashin hankali ya wanzu a saman fuskokinsu, tsoro suke ji da gaske, sun É—auka sun samu Æ´ancin kai bayan zuwan turawan Biritania, amma hakan duk ya tafi a busar sarewar Audu. Haan ya furta

"Yaushe za mu daina fuskantar matsi da rikin ƙabilanci, anya ba za mu yi magana da gawar Kakanku ba Ortyom?"

Kaka ya ce "Ba za mu daina shiga masifa ba, har sai MAMAA ta bayyana wacce za mu samu TSAV a tattare da ita, dole sai ita"

Cikin gwaranci Anum ta ce

"Kaka yaushe Mamaa zata zo?"

"Yau ne, gobe ne, jibi ne ko gata, wannan shekarar, wannan zamanin ko sai bana raye ban san yaushe ne Mamaa zata bayyana ba, amma komai daran daɗewa Uwa Mamaa zata zo, kuma za ta cece mu" ƙarar Kibbau suka ji, da sauri Haan ya yi waje yana kare ƙofar shigowa gidan duk da a tsakiyar dokar daji suke a gaɓar kogin da bashi da suna.

Da hannu ɗaya Dooshima ya saɓa Anum a kafaɗa, ya saka hannunsa ya ɗauki yaron dake wajan kaka yana bacci ɗan wajan Haan. Can cikin gidan ya shiga wajan wani ramin ƙasa inda suke ɓoye mata da yaran, Anum na kuka da ihu haka ya dannata cikin ramin ya ɗauki Jarumi ya saka mata a cinya, ya mayar da ƙofar ya rufe tare da ƙaton dutse, cak ya tsaya yana goge hawayen idanunsa bayan ya zubawa ramin ido, yana jin kukan Anum dake ratsa kunnunwansa, babu tabbacin zai sake sanyata a cikin idanunsa. Ya ɗaga kai sama ya ce "Na bar Anum da Jarumi a hannunka Akombo, an yi maka laifi har yanzu Uwa bata bayyana ba, waɗannan ɗin yara ne ka kula dasu Akombo" yana faɗin hakan ya fice da sauri yana tushe kunnunwansa daga jin kukan Anum ɗinsa.

***
Mafari.
11/8/2025.
KANKAROFI/ KANO MUNICIPAL.

Kankarofi na daga cikin tsofaffin unguwanni da ke cikin birnin Kano. Tana cikin Kano Municipal LGA. Yammacin ranar Asabar ne wanda ya yi dai-dai da Shaɗaya ga watan takwas, shekara ta dubu ashirin da ashirin da biyar, kasancewar watan Nuwamba ne, farkon shigowar sanyi ya saka iska me daɗi da sanya nutsuwa take kaɗawa a lungu da saƙo na cikin garin, har zuwa unguwar Kankarofi da mutane shige da fice.

Ƙarar ihunta ne ya ja hankalinsu zuwa ga ƙasan bishiyar da take kwance tana bacci a saman tabarma, ba ihun ke basu mamaki ba, face yadda take kiran sunan Anum da dukkan ƙarfinta zufa na yanko mata, bayan sunan Anum har sunan jarumi take kira.

"Kar ku bar su a ramin nan, shikenan za'a kashe Anum na shiga uku, Anum, Anum...

Wanda yake alwala ya juyo ya kalle ta, sai ya girgiza kai ya ce "Ina fa'ida a baccin La'asar daman, ba dole mutum ya yi mugun mafarki ba, tai ta bacci kamar kasa haba"

Matar dake ta tsinke zogale da ya yi kore shar saboda rani, ta ajjiye zogalen tare da zuba tagumi sannu a hankali kuma take bin yarinyar dake ƙwance wacce bata fasa kiran sunan Anum da Jarumi ba da kallo, can ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Tashe ta daga baccin nan Jaheed" ya ajjiye butar hannunsa. Tsaye ya yi a kanta, fuskarta ta yi sharkaf da zufa ta kuma yi ƙyalli ya saka ƙafa yana shurinta a hankali

Ya ce "Ana"

Jadid ya kalli Jaheed yana dariya ya ce

"Wannan uwar baccin, da shegen nauyin bacci kake wa wannan kiran Jaheed?"

"Wallahi takaici ne ya kamani, wannan ihun kamar mahaukaciya sabon kamu har ina"

Jadid ya ce "Ko kuma sabuwar amaryar da ake shirin sawa a lalle ba, zaune zaka tashe ta, idan ba haka ba, ba tashi za ta yi ba".

Duk yadda Jaheed ya yi ƙoƙarin tashin Ana kasawa ya yi, ya juya ya kalli mahaifiyarsu data mayar da kai zuwa ga aikin tsinke zogalen ya ce "Innti taƙi tashi, anya lafiya?" Bata kalli Jaheed ba ta miƙe zuwa inda Haleeym ke bacci da sambatun kiran sunan Anum da Jarumi, ta zubawa kyakkyawar fuskar yarinyar idanu kamar tana karantar yanayin da take ciki, ta fara kiran sunanta.

"Ayshatul Haleeym!"

Ta nanata "Ana, Haleeym"

Sallama ya yi a nutse cikin kamala ya shigo gidan, amma duk basu san ya shigo ba, ya jima tsaye hannunsa cikin aljihu ya watsa idanunsa akan fuskar Ana ganin yadda Innti ke ta kiran sunanta amma ko motsi ba ta yi. Ya juya zuwa bakin rijiya, ruwan da ya gani a cikin bokici ya ɗakko tare da ƙarasuwa wajan da suke, duk suka matsa shi kuma ya ɗaga bokicin ya sheƙa mata ruwan.

Ruwan sanyin da aka kwarara a jikinta ya haddasa mata farkawa daga nauyayyen baccin yamman daya ɗauke ta, ta shiga mustsikka manyan idanunta, ƙoƙarin komawa take yi ta kwanta tana surutai irin magagin baccin nan wanda bai gama sakin mutum ba, daman gata da nauyin bacci.

A fusace ya ɗauke ta, ya dire a wajan. Ganin ta tsaya akan ƙafafuwanta ya saka ya juya ya zauna akan Benci yana duba agogo.

Littafin dake rigarta ya faɗo ƙasa

"Wayyo Anum, ki yi shiru kin ji jikalle" cikin magagin baccin ta sake furta hakan idanunta na lunshewa jikinta na zubar da ruwan daya kwara mata saboda yadda ta ishe su da ihun ana saka Anum da Jarumi a cikin rami, garin kayan takaicinta ta kwasuwa kanta mutanen ɓoye ita kaɗai ta sani sai Allah, yin duniya ta tashi daga bacci amma fafur taƙi sai mimmiƙe hannu take.

Daga gefe aka ce "Wai uwar wace Anum ɗin nan, da kika cika mana gida da kiran sunanta a cikin baccinki? Ƙawarki ce ko?"

Jadid ya girgiza kai ya ce.

"Ko kuma ta yi rigima da wasu, suka biyo yammaci wajan shaƙe wuyanta wallahi"

"Babu mamaki" in ji Jaheed.

Sai kuma ya miƙe yana kakkaɓe yadin da yake jikinsa da furta "Duk hankalina ya tashi, na ɗauka Shalelen Innti aka kawo wa hari, gashi na rasa jami'in la'asar dole a gida zan gabatar na yi na koma shago yanzu"

"Kar ka sake ka yi mini sallah a gida" Innti ta furta a sanyaye idanunta zube akan yarinyar da aka tayar daga bacci. Sai ɗacin rai take yi tana kukkumbura kamar wata kububuwa, fuskar nan na ƙyallin kyakkywar baƙar fatarta ga shatin tabarma da ya yi mata zane a kumatu

Jaheed ya ce

"A gafarce ni Innti"

Ya furta yana ficewa daga cikin gidan.

"Mutum yana baccinsa me daÉ—i kawai sai a katse shi fisabilillahi? Kun san me nake gani?" Jadid da Innti suka zuba mata idanu, wanda ya tashe daga baccin kuwa har yanzu ko tari bai yi ba, bai ma sake kallon inda take tsaye ba, tuni ya koma ya zauna ya cigaba da duba wayar hannunsa daya kunce. Ta juya ta kalli Jadid suna haÉ—a ido ta murguÉ—a masa bakinta, ta kalli Innti ta ce

"Innti wanne me tsautsayin ne ya tashe ni?"

"Gashi can" Jadid ya bata amsa yana nuna bayanta. Ta juya zata fara masifa idanunta ya sauka akan Baban yaya, nan take ta ji zufa na karyo mata duk da iskar bishiyar darbejiya dake kaÉ—awa tana bada yanayi me daÉ—i. Ta haÉ—iye yawon baccin daya tarar mata a baki. Ta nufi tabarmar zata zauna ta ji kamar daga sama ya yi gyaran murya.

Sai ta kwaɓe fuska ta ce

"Nifa aka zalunta bance komai ba, kun san a tarihin gidan nan ko Tv ta wasa ba'a taɓa yi ba, balle ta gaske ɗan kallon nan dake saka nishaɗi ba'ayi, kowa keyboard ce a hannunsa, shikenan na samu ana haska mini film a cikin baccina sai a tashe ni saboda mugun abu? Yanzu ba lalle na sake yin wannan sa'ar ba, gashi ina son sanin yadda ƙarshen abu zai kasan da rayuwar Anum data Jarumi...," bata ƙarasa maganar ba, ta miƙe a zabure ta yi cikin ɗaki ganin Babban yaya ya ciro darbejiya tasan tsaf zai zane ta, ba imani ne dashi ba wallahi ga mugun abu.
Chapter 3 · 0% Book details