Sashe 47
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina gurasar bani abata na cinye" bai kalle ta ba ya miƙa mata Yougurt ɗin bayan ta kafa baki tasha ya miƙa mata hannunsa ta ce "ba siya mini ka yi duka ba Yaa Sam?" Bai tanka ta ba ta dire masa Yougurt ɗin tana ajjiye ya miƙa mata Apple ɗin daya ciro a bakinsa sai ɓata rai take yi bai bi ta kanta ba, ya ɗauki Yougurt ɗin ya sha ya sake miƙa mata, karɓa karɓa suka dinga yi har ta ce ta ƙoshi ya rufe ya ajjiye. "Oya tashi ki koma gida kar Abbaa ya neme ki" ta yi shiru
"Nanah.....
"Ina ganin Abbaa a cikin mafarkina ta wata siga sai ya dinga ce mini shi mijina ne. Innti bata gida Mahaɗita ma haka" ya yi jim. "Ina Iftihal ɗin ta je ta bar ki?" Kwanciya ta yi a gefe tana hamma "Mijin Innti ne ya sakata a caca, wai zai ci miliyan ashirin shine Alhaji Baita ya ci cacar aka bashi Mahaɗita, Innti ta ce koda wasa na je gidan xan haɗu da fushinta, kuma kar na faɗa maka" ta ɗan yatsuna fuska tana jujjuya kai ya saka hannunsa ya riƙe kan, zafi sosai ya ji ita kuma ta zuba masa ido har bata san lokacin data ɗora kanta a cinyarsa dake miƙe ba. "Abin dai sai ita da mijin nata, i told Iftihal Daada shi zai zama ajalinta but she refused to understand that" tana faɗin hakan ta rufe idanunta ruf babu jimawa ya ji saukar numfashinta alamar bacci ya ɗauke ta. Ya dinga kallon fuskarta ta torchlight ɗin daya kunna ya ja numfashi ya sauke ya ji ta mirgina a hankali ta shige can ƙurwar ɗakin tana riƙe hannunsa sosai a cikin nata, ya wanzu yana kallon ta sosai, yana sake tuna ƙuruciyarta da ta yi akan idanunsa ya ɗan ranƙwafa goshinsa ya sauka akan nata a hankali ya mayar da idanunsa kan laɓɓanta....
*H I Y A A M*
Page 13: The Night of Reckoning
Bright pens
Yota/001
Sending you lots of love, my Pixie 😘NSN the great NAZY's KITCHEN
Ya jima yana kallon fuskarta me cike da rauni, ƙuruciya da rashin mafita goshinsa yana shafar nata, a hankali ya janye goshin nasa sai kuma ya sake ɗorawa ya sumbaci goshinta da kulawa kafin ya gyara mata kwanciya ya miƙe tare da fita daga cikin shagon nasa, a dakalin gidansu Ana ya zauna ya yi shiru yana harɗe hannu a ƙirji.
***
A karo na biyu ta sake ɗago kanta daga kan t.v da take kallo, ta juya kaɗan ta kalle shi sai taga ya harɗe ƙafarsa ɗaya kan ɗaya hannunsa ɗaya riƙe da hot coffee yana sha. "Liman ko baka ji me na ce maka bane?" Bai ɗago kai ba, sai ajjiye cup ɗin da ya yi a center table ya ce "Me kika ce Umaimah?"
Wani irin kallo ta watsa masa me cike da gargaɗi kafin ta mai da hankalinta gabaɗaya gare shi ta ce "Ina magana akan yarinyar da zaka aura wacce Alhaji Sadi suka je kai maka kuɗin auren, auren da tunda Baffa yaƙi zuwa kai kuɗin jikina ya bani akwai matsala a tattare dashi bawai baki na yi maka ba Allah Ya tsare" ta ƙarasa maganar tana sauya yanayin fuskarta. Wanda aka kira da Liman kallon ta kawai yake yi, ya ji me ta ce kuma zai iya maimaita kalaman da Umaimah ta ce, amma ko za'a saka masa wuƙa ba zai ce ga abin da take son nuna masa ba. Sai ya zaɓi yin shiru akan bata amsa. "Ya zama last time da zan sake maimaita kaina akan batun nan Liman"
Ya numfashi ya ce
"Me kika ce ne?"
Ta dube shi ta ce
"Ina magana akan yarinyar ne" Da rashin fahimta ya ce
"Who?"
"Why are you answering my question with a question ne Liman? Yarinyar da zaka aura wacce aka kai sadakinka gidansu, ina buƙatar ka kawo mini ita na ganta da kaina" da wani irin yanayin na rashin jin daɗi Liman ke kallon Hajiya Umaimah yafi seconds sha biyar kafin ya iya cewa "Umaimah ina jin I already told you that the girl is visually impaired, so I can’t bring her to Baffas Estate by myself.†da mamaki tace
"She's visually impaired? Mugunta zan mata ko naman jikinta zan dinga yanka ina ci da zaka wani sauya mood kana ce mini wani visually impaired, au daman da gaske kake makauniyya zaka aura Liman? Kana da cikakken hankali kowa? Me ya sa kai É—in nan abin da ka yi ra'ayi kawai kake mana a cikin gidan nan? Haka kaga Mu'allim yana yi ne?"
Liman ya miƙe tsaye fuska a kame, Hajiya Umaimah ta ce "Zauna ban gama magana ba" daga tsayen ya kalle ta sai ya yi kamar ba zai zauna ba a hankali kuma ya yi baya tare da sake zama akan kujerar daya tashi akai ya fara kallon wani direction daban. "Zan sake magana, ina fatan ta zama ta ƙarshe ina son ka kawo mini ƴarinyar nan gidan nan, domin ba zaka auri wacce zan zo ina kasa nuna ta a dangi ba. Ban ma dai gama gamsuwa da uban nata ba, ƴar waye? Matsayin mahaifinta, mene matsayin karatunta? Ƙasashe nawa ta je? Ta je Saudia? Musaɓaka nawa ta ci, ta Jiha ko ta ƙasa? Sau nawa tana sauke Alkur'ani?"
Ya yi jim a daƙile ya ce
"Ba ko É—aya"
Murmushi Azizah ta yi ta ce "Stop beating around the bush Liman, ka fito ka ce ƴar talakawa kawai zaka aura, duk kewaye-kewayen naka da gujewa ƴaƴan ƴan'uwa sai ka ƙare akan ƴar talakawa haba Liman?" Tunda ta fara magana yake binta da wani irin masifaffan kallo yana sauke numfashi akai-akai idanunsa sukai jajur ya dunƙule hannunsa dake masa rawa. Hajiya Umaimah ta ce "Ga dukkan alamu Azizah, ki yi shiru kar ya kawo mana duka naga yana rawar ɗari" Azizah ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya
"Ko burkutu yake sha ai bai isa ya taɓa ni ba balle ke Umaimah da kika haife shi ko?" A hankali ya ce
"Bata da iyaye a haka kuma nake son ta"
"Kutumar uba, marainiyya zaka aura?"
Daidai nan wanda ya sako ƙafarsa cikin parlour ya tsaya cak kamar wanda aka yi wa umarnin hakan, ƙafar ta daɗe a yadda ya ɗage ta cikin wani kyakkyawan farin takalmi na saƙi me ɗauke da gashin ɗawisu daya kwanta, sannu a hankali kuma ya shiga yin baya da ƙafar hakan ya bawa wanda yake tare dashi tabbacin ya fasa shiga gidan a yanzu. Ya yi tsaye akan ƙafafuwansa hannunsa ɗaya ya juya shi zuwa bayansa ɗayan kuma ya ɗora a saman goshinsa ya saka yatsu biyu yana murza tsakiyar goshinsa idanunsa a lumshe suke, kamar yadda zara-zaran gashin idanun suka bi fatar wajan suka kwanta, iya idanun daman kawai ake iya gani a fuskarsa da zarar ya saka glasses suma ya yi wa jama'a rowar ganinsu, ilahirin gargasar jikinsa sai data mimmiƙe wani irin sanyi ya shiga ratsa farar fatar jikin nasa, yaja numfashi da saukewa sau babu adadi. Babban yatsarsa na ƙafa sai rawa yake yi shi kaɗai hakan ya faru ne a dalilin zagin da Azizah ta yi a daidai sanda Sayyadi Baffa yake sako kan shi cikin parlourn.
Fuskarsa ta rikiɗe ta yi jajur laɓɓansa yana wani irin rawa da ɓari, a cikin zuciyarsa ya furta “A’udhu billahi minash-shaytanir-rajim†yana kame jikinsa da kyau cike da kulawa ya ɗora da;
“Allahumma ighfir li wa lahum wahdina sawaa’as-sabeel†ya maimaita a zuciya.
Ya ɗauki a ƙalla minti guda tsaye yana addu'ar nemawa Azizah gafara wajan Ubangiji da kuma tsari da neman afuwa wajan Allah akan jin zagin da ya yi. Bai san wacece ta yi zagin ba, bai ɗauki murya ba kamar yadda bai damu da sani ba, ba murya kowa ya haddace ba, yadda jikinsa ke rawa ya sake tabbatarwa Mu'allim akwai matsala. Juyawa ya yi yabar sashin gabaɗaya baya mistake a sauke ƙafa sai ya cire ɗaya yake ɗora ɗaya saboda nutsuwa.
Ta ƙofar baya yabi har zuwa babban sashin da yake mallakin Sayyadi Baffa, a nan ƙofa Mu'allim ya ja ya tsaya yana cewa "Allah ya huci zuciyar Baffa, ya ƙarawa Baffa lafiya" Wannan karan ko zarafin jinjina kai bai samu ba, ya buɗe ƙofa da yatsu biyu, sai da ya yi addu'ar shiga ɗaki kafin ya saka ƙafarsa da Bisimillah ya shiga zuwa ciki.
Mu'allim ya juya kai tsaye cikin gidan ya shiga idanunsa ya sauka akan Azizah dake zaune har yanzu ita da Hajiya Umaimah saboda Liman ya fita.
"Ukhty Azizah me ya sa kike son yi mana zagi a gidan nan ne? Wa kika ji yana yi?"
Ta ce "Mu'allim ban fa san na yi ba?" Al'ameen ya watsa mata fararan idanunsa
"Ko?" Ya tambaya cike da takaici. "To a kunnen Baffa kikai, kuma ya ce ko wacece ya bata minti ashirin ta bar gidan nan, yana da tabbacin ba zuri'ar Hafiz Hafiz Baffa ce da aikata wannan saɓon ba" wani irin sandarewa Azizah ta yi, sunan Baffa ya saka zuciyarta bugawa da matsanancin farinciki har ta kasa ɓoyewa ta faɗaɗa murmushinta tare da lumshe ido ta buɗe. "Da gaske Baffa ya dawo? Yana cikin gidan nan Please Mu'allim ka nema mini iso wajansa, don Allah ina kamon ƙafa da kai"
"Allahumma yahdiki. Is like kamar ba ki fahimci me nake cewa ba ko Ukhty Azizah?"
"No, na ji. Na san bai sanni ba, ka rufa mini asiri idan ya tambaya ka ce baƙuwa ce kuma ta tafi, sai ka nema mini izinin ganin nasa Please"