← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 64

Sashe 52

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Masarautar ta yi shiru sai kukan tsuntsaye da sauran nau'in dabbobin da suke ciki, girma da faÉ—in masarautar ya kai a yi kwantance da masarautar Tajmahar a cikin jerin masarautun da suka africa, ba lokacin bayi bane, amma har yanzu Tajmahar suna bautar da jama'a kamar sune suka halicce su, yawanci kuma sun fi É—ora tsananin dokar tasu ne akan mata, suna siyan bayi mata daka ko'ina, musamman suke ranar kasuwar bayi a naÉ—a shugaban bayi ya je ya siye duk matan da aka kawo kasuwar, a cikin farashi me tsananin tsada.

Akaf cikin Tajmahar, babban part guda shine ya zama daban, komai na part É—in daban, tsarin fari da ash ne, sai ya zama very different da sauran kuma yafi É—aukan idanu saboda tsarin shi

Yana zaune akan kushin ya ɗan tanƙwashe ƙafafuwansa, daga shi sai three qauter, duk da farin fatar jikinsa da yadda take ɗauke idanu, wani sahihin fari na burge wa, bai hana gargasa kwanciya a saman cinyarsa ba, ta lulluɓe fatar sai sheƙi take yi baƙa suɗik da ita. Babu riga a jikinsa, A hankali ya miƙa hannunsa idanunsa rufe ya ƙaro gudun acn, bai san me saka shi dawowa Tajmahar a dai-dai irin wannan lokacin ba, da alama kafin ya fita sai ran kowa ya ɓaci daga ciki kuma har dana Mai girma Deborah. Yaja numfashi ta cikin bakinsa ya cika bakin da iska ya fesar a hankali.

Wannan karon ma yana ji ana sake knocking ƙofar da za'a shigo haɗaɗɗan ƙaramin parlourn nasa da yake hutawa ya yi burus.

Wayarsa ce ta shiga haske, saboda baya son ringtones a silent take kodayaushe kuma a DnD. Number Tor Tiv ya gani da ya yi saved da "World" kiran ya katse a karo na farko. Aka sake kira, ya miƙa hannunsa kaɗan ya shafi screen ɗin wayar ya saka a hands free, dakakkiyar muryar Tor Tiv me cike da iko da izza ta ratsa cikin kunnensa. "Idan ba ka yi haka ba, ai ba zan kalle ka matsayin jinin Tajmahar ba, jinin Imande, zuciyar Imande, ƙaunar Uji"

A hankali ya sake sauke ajjiyar zuciya saboda muryar abin da yafi ƙauna a zuciyarsa ta ratsa cikin wannan zuciyar dai.

"Our next Tor Tiv, Me Tajmahar gabaÉ—aya"

"World.....

Ya ce a kasalance.

"No agreement, my prince"

Tor Tiv kuma Uji ya yi saurin tare shi da faÉ—ar hakan, babu hayaniya cikin muryar shugaba, a nutse take cikin zallar iko da isa da kuma izza na jinin mulkin Tajmahar dake gudana a jinin jikinsa yana kwaranya a zuciyarsa. Bai sake cewa komai ya yi shiru.

"Me ya samu Madaki yake hargagi a sashin Mai girma Deborah?"

Madaki ya ji tambayar da aka yi masa, wato har an kai maganar zuwa fada gaban Shugaban Tajmahar? To shi duka duka, da Tor Tiv É—in, da kingmakers, ciyamomin fadar, da dattawan cikinta akwai me zummar tarar shi ne ya masa wannan birkitacciyar tambayar bai É—aure mutum ya saka shi a kurkuku ba, shi kan shi Tor Tiv yana da zummar tambayarsa ne kawai ta cikin wayar ba fuska da fuska ba. Yi masa wannan shirman tambayar daidai yake da sabon tashin hankali a Tajmahar. Sai ya É—an yatsuna zagayayyiyar fuskarsa me É—auke da kwantaccen saje me laushi da kyawun gani.

"Ina son barin Tajmahar"

Shine abin da ya fita daga cikin bakin Madaki kamar baya son yin maganar, ya saka hannu ya tura gashin gaban goshinsa zuwa baya. Tor Tiv ya yi shiru, don baya jin zai sake bawa Madaki damar barin Tajmahar masifun da suke bibiyarsu kaÉ—ai sun isa.

"Za ka iya banda yanzu"

"World amma....," bai ƙarasa faɗa ba, Tor Tiv ya kashe kiran gabaɗaya da ita kanta wayar.

Wani abu ya caki zuciyar Madaki, tsigar jikinsa ta shiga tashi tana mimmiƙewa da zubewa a farar fatar jikinsa, ya tsani hakan baya son hakan, wannan shi ne ƙarshen raini kashe waya mutum waya a fuska. Ajjiye wayar ya yi, ya miƙe tsaye yana saka kyakkyawan takalmi a cikin farar ƙafarsa, fuskarsa kamar zai ce ya shiga uku haka ya nufi ƙofar fita daga cikin sashin nasa, yana fitowa ƙofar farko gabaɗaya sojojin da suke gadin ƙofar suka yi saurin zubewa akan ƙafafuwansu, kan su a ƙasa, ko numfashi da suna da iko da kan su ba za su iya jan shi ba, da sassarfa yake tafiya, saboda kuzarin da ya yi wa jikinsa yawa, ba'a ganin fuskarsa sosai saboda gashin daya kwanto masa, a jinin jikinsa yake jin Tajmahar, amma deep down akwai abin da yafi Tajmahar muhimmaci a zuciyarsa a yanzu, ji yake kamar ana kiransa ana jan zuciyarsa zuwa wani waje daban, wani waje me muhimmaci.

Fada ta jima da tashi, don haka kai tsaye sashin Shugaba Tor Tiv Madaki ya nufa, daga shi sai gajeren wandon da yake jikinsa buɗaɗɗan jikinsa na motsawa, sojojin ko inuwar Madaki basa kuskuran gani balle shi da kan shi Madaki, ya fito a suffar da ba kowa ke ganinsa da ita ba, kamar yadda ba kowa ne ya san ya shigo cikin Tajmahar ɗin ba. Madaki yana middle of the age ne, amma arziƙi da gata haɗi da gidan sarauta, da sangartar da aka nuna masa, sun buɗe masa jiki sosai ya zama fiye da age ɗin nasa. Yana zuwa ƙofar da aka rubuta TOR TIV da manyan haruffa yaja ya tsaya.

Wani soja ne ya kira Tor Tiv ya ce "Shugaba, ga gudan jinin Tajmahar a ƙofar Tor Tiv da kan shi" ta cikin wayar da wata kasalalliyar murya Tor Tiv ya ja numfashi

"Kar a bar shi ya shigo"

Yana faɗin hakan ya ƙare da wani sauti na fitar hayyaci. Duk yadda ka kai da jin kan ka muddin Tor Tiv bai baka damar shigowa sashin ba, dole ne ka haƙura ko waye kai. Madaki ya juya zuwa can gefe, jikinsa ya ɗan fara ɗaukan rawa. Kamar ance ya ɗago kai sai yaga matar daya taɓa gani an fito da ita daga sashin Tor Tiv jikinta ɗaure da sarƙa, ya ware kasalallun idanunsa ya cigaba da kallon yadda ake janta kusan duk kayan jikinta a yayyage yake. Can wani waje da ake ajjiye dabbobi suka cillata sojojin kana suka juya. Ya ɗan taɓe jajayen laɓɓansa yana zura na ƙasa a cikin bakinsa ya tsotsa, kamar zai shige sai ya nufi wajan, da wannan karsashin nasa. Yana zuwa ya yatsuna fuska wajan ya yi datti da yawa, duk da ko tsinke babu. Yana shiga ya ganta ya rakuɓe tana cirar ciyawa tana ci kamar mahaukaciya, ya zuba mata maganaɗisun idanunsa kafin ya saka yatsu biyu ya murza

A gigice ta ɗago kai, cike da tsoran ko wajan Tor Tiv za'a sake mayar da ita, ta shiga girgiza wa Madaki kai tana ja baya kamar ma tsoran mutane take yi. Ya durƙusa inda take ya dinga kallon yadda fatar jikinta take duk shatin duka, faratanta ma duk an cire su. "Ka tafi, ka tafi ka bar nan ba zan koma ba" a tsorace take maganar tana girgiza kai da wani firgice ta ce

"Kar ka mayar dani....

"Bana so, ba zani ba"

Ya buɗe idanunsa, a karo na farko daya taɓa tsayawa da wata baiwa a cikin Tajmahar har ta ji muryarsa, murya a shaƙe da slow ya ce

"Wacece ke?"

Da sauri itama ta ce

"Wacece ke?"

"Ina nufin sunanki?"

Itama ta ce

"Ina nufin sunanki?"

"Huh!" Ya fesar da iska me zafi. Ya jima yana binta da kallo kafin ya taɓe bakinsa ya miƙe ya bar wajan. Yana barin wajan kuma aka fara kuke-kuke, yana ji bai bi ta kai bai ba, bashi da wani ra'ayi sosai akan Tajmahar ɗin. Gashi kuma shine namiji guda ɗaya wanda ya zama magajinta.

Kukan da ake yi ya saka shi miƙewa daga saman lafiyayyen gadon da yake kwance, mata guda uku suna yi masa tausa, ya sakko ƙafarsa, ɗaya ta miƙo masa rigar bacci ya saka, ɗaya ta shiga rufe masa botiran rigar, da wata sabuwar izza ya shiga takawa wajan bakin ƙofarsa ya fita zuwa wani part ɗin duk a ɓangare guda.

Yana shiga yaja ya tsaya ya kalli wacce ke shimfiɗe a ƙasa kafin ya yi magana ace

"She's died, ta mutu mun rasa ta itama"

Ɗaya yarinyar ta girgiza kai ta dawo kusa dashi ta riƙe shi ta ce "Yaushe Uwa Mamaa zata bayyana? Bana son na mutu kamar yadda Zizi ta rasu, yaushe Mama zata zo?"

Yaja idanunsa ya rufe.

"Terhemba, kana gani dai kana ji komai dake faruwa?"

A hankali ya ce "Mun ta ganin masifa kenan har sai Uwa Mamaa me É—auke da Tsav ta bayyana a Tajmahar, Mama yaushe za ki zo?"

***
"Abbaaa.....

Ana ta daddage ta kurma ihun kiran sunan Abbaa, bisa mamakin Innti sai Babban yaya ya fito daga cikin É—akinsu, yana tafiya a hankali idanunsa zube akan Ana wacce ya ji kiran da take masa yana fusgarsa, a nutse ya mayar da ganinsa kan Innti yana juya ido. Kafin ma ya yi tambaya Yaa Jaheed yace

"Daada ya cilla Iftihal a cikin rijiya" wani zaro ido Yaya ya yi waje yana yin baya kamar zai koma É—aki a guje ya taho ya faÉ—a cikin rijiyar, daidai lokacin Yaa Sam ya shigo shima cikin shigar bacci, idanunsa bai gama buÉ—ewa ba, ya kalle du É—aya bayan ya ce "Jaheed meke faruwa ne? Ko jikin Jadid ne?"

Jaheed ya kasa magana sai rawar jiki yake yi. "Ai hukuncin bijirewa umarnina da ta yi kenan, tana fitowa kuma zata goma gidan Alhaji Baita. Idan ta yi rai a cikin rijiyar kenan" nan take Yaa Sam ya fahimci abin da yake faruwa, ya saurin leƙa rijiyar baya ganin komai saboda duhu amma yana jin motsin ruwa. Ya runtse idanunsa ya shiga addu'ar Allah Ya sa Iftihal ta fito lafiya, ya san kusancin dake tsakanin zuciyoyi biyu idan Ana ta rasa Iftihal akwai matsala, idan Iftihal ta rasa Ana nan ma wata sabuwar matsala ce. Ana na jikin Innti, da alama tsoron kallon rijiyar ma suke yi, Jaheed da Yaa Sam suna wajan rijiyar suna leƙawa, Daada kuma na tsaye sai surutan iska yake.
Chapter 52 · 0% Book details