← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 64

Sashe 2

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jerin kalmomi guda biyar kawai ta samu zarafin rubutawa a cikin fejin littafin dake hannunta, idan ta irga haruffa a jimilance a yau ta samu ƙarfin zuciyar rubuta harafai har Talatin cif, saɓanin baya da iya HIYAAM kawai take rubutawa a tsayin kwanaki talatin har yinin yau kenan, kalmar da a yanzu bata san me take nufi ba, bata san bigirin da zata ajjiye ta ba, ta ci karo ne da ita a cikin mafarkan data saba a kullum.

Ta shiga juya biron hannunta, tana tunanin da zuciyarta, da tambayar kanta a hikimance.

"Zan zama marubuciyar kuwa?Zan iya rubuta abin da nake ji yana mini yawo a cikin kaina wanda baya barin ƙwaƙwalwata samun nutsuwa? Wanda yake gallabar zuciyata..Haka rubutun yake dama?"

Ta ja numfashi ta sauke.

"Haka kowacce marubuciyya take ji?" Sai ta sake ɗora biron akan takaddar akaro na babu adadi, wannan karan ma haƙarta bata cimma ruwa ba, duk yadda ta saƙa zaren labarin daka farko har ƙarshe, data zo rubutawa komai yake daburce mata, ta kasa.

"Wataƙila bani da basirar zama marubuciya"

Ta furta a fili cike da sangarta da shagwaɓar da take jin kamar da ita aka haife ta, luuu ta ja manyan idanunta ta lumshe su, saboda iskar bishiyar darbejiyar dake kaɗata, wacce ta kasance zaune a ƙasanta saman tabarma.

Sai kuma ta saki dariya me sauti. "Ƙila rabon zama ƴar jarida ya daƙusar dani daga kasancewa marubuciya, irin shahararrun marubutan nan da suke tashe, amma ba masu rubutun lalata tarbiyya ba" Idan zaman banza ne da rashin abin yi ya riga ya gama zama a jikin Ana, hankali kwance cike da sabon nishaɗi ta juya bayan littafin nata, ta fara rubutu sannu a hankali.

"Sunana Ayshatul-Haleeym, da yawan mutane basu san asalin sunana na Aysha ba, irin sunan Nana Aysha Matar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama. Ban san ina Babana ya samo sunan ba, a kaf danginmu na uwa da uba babu wata mai suna Aysha....Au dangin Babanmu basa son mu na manta ban faÉ—a muku ba, bayan Aysha, ana kirana da Haleeym irin sunan Æ´an gayu, duk da ni talauci ya É—aurawa iyayena riga, bayan Haleeym ana kirana da ANA. Sunan Mamata INNTI, wanda ya amsa sunan uba a gare ni ana ce masa DAADA, Muna zaune a garin Kano, a cikin local Government ta Municipal, a wata unguwa da ake kira da Kankarofi. Mu biyar ne a wajan Iyayenmu, haka Innti ta haife mu duk da Talaucin da take fama dashi, amma masu kuÉ—i yara biyu kawai suke haifa, Babban yayanmu ana ce masa BABBAN YAYA, bayan shi ta haifi tagwaye duk maza Yaa Jaheed da Yaa Jadid, amma nafi son Yaa Jadid, saboda shi yana taje mini kaina, yana yanke mini farce, shima Yaa Jaheed ina son shi saboda yana da kirki, yara uku kenan, sai mu da muka kasance Æ´an auta, tagwaye ne muma, dani da mahaÉ—ita, rana É—aya aka haife mu, bamu san waye babba ba, Innti ta ce bata cikin hayyacinta ta haifo mu, don haka kowa babba ne. Sunan abokiyar haihuwata IFTIHAL, wasu na ce mata Iftin Innti, ni kuma Shalelen Innti Itama sunanta Aysha, ni ANA ita IFTI...

Sai ta dakata daga rubutun tana bin jerin kalmomin da bata san yaushe ta rubuta ba, ba tare data san hakan shi ne tubalin zama marubuciya a gare ta ba, baiwar kalaman da suke fitowa daka ƙasan zuciya na zahiri.

Iskar ta cigaba ta kwasarta dara-daran idanunta ya fara lunshewa alamar bacci.

"Ina da ƙanin uba, amma fa shi ɗan daudu ne, ana kiran shi da suna Sukunbiya, don Allah ba sunan kifi ne haka ba? Bala sunansa na gaskiya... Sai kuma Yaa Sam, abokina aminina kuma yayana maƙocinmu ne, kyakkyawa ne sosai yana da grey eyes amma talaka ne irinmu, wasu da yawa suna cewa wai saurayina ne, bayan babansa ya yi masa zaɓen matar aure, kuma ni bana son ma ya zama mijina. Ina son namiji kyakkyawa,bani da burin daya shige na auri kyakkyawan namiji a duniya, fari, dogo, mai zubi da tsarin halittar Ubangiji, irin kyawun da bana damuwa ko da na Aljanu ne, talaka ne, gurgu ne, ko da me cutar ƙangamau ne (Hiv) muddin kyakkyawa ne ajin ƙarshe, irin kyawun mazan novel to zan aure shi, ko da ace zai dinga gutsirar naman jikina yana soyawa tare da cinyewa ne, kai ni ko da maye ne ina so. Wannan shine ra'ayi da tsarin ANA....

Bacci ne ya ci ƙarfinta a daf da lokacin da limamin Masallacin unguwarsu ke ƙwalla kiran sallar la'asar, haka ta cusa littafin a rigarta ta ɓingire wajan ta fara bacci.

*
1500 / 1700.
TIVLAND NA FARKO

Sau tari ana cewa, idan masifu suka yi yawa a inda kuke, yin ƙaura tare da yin nisa shine yafi zama alheri, a kwanakin baya na faɗa muku asalin su waye Tiv, na san kuma kun fahimci daga ina iyaye da kakanninku suka samu tushe, Hausawa sukan ce, Tushiya masomin dawa, haka kuma kowa ya bar gida, gidan zai bar shi. Mun samu matsin rayuwa, na rashin doka, bamu da shugaba ko wanda suke jagorantarmu, kowa yana cin gashin kan shi ne, mun yi imani da Akombo fiye da yadda kuke tunani, mun wayi gari cikin fari da talauci, har muka yanke shawarar yin ƙaura, ashe Akombo ya yi fushi me tsanani damu, hakan yasa komai ya rikici mana. Muka ɗauki hanya me nisa.

A cikin wannan shekarar a hanyarmu ta yin ƙaura saboda yawan jama'a sai aka rabu kashi da kashi, kowanne rukuni suka kasance Ahhali guda, kamar yadda muma muka kasance iyali ɗaya ta hanyar kaka ɗaya daya haifi iyayenmu, ni na fito daga ɓangaren Ikur ɗan'uwana ya fito daga ɓangaren Imande, ma'ana babana shine Ikur babansa kuma Imande, muka tashi dangi biyu a bisa jagorancin kakanmu. Mun yi wannan ƙaurar saboda yawan jama'a, da kuma neman ruwa da kuma Dazuzzuka sai ƙasar da za ta iya yin noma. Akan hanyarmu ne wa'adin mutuwar kakanmu ya yi, dare ya tsala babu gida gaba, babu baya, muna tsakiyar daji ne. Mun yi kukan rashi sosai, domin shine muke gani matsayin Dattijon da yake jagorancin Ikur da Imande. A cikin wannan daren muka fara shirin bikin jana'izar kakanmu, muna yara amma har yanzu ina hango yadda al'amarin ya faru.

Aka haɗa ganye da ruwa da ƙasa, aka fara watsawa gawar kakanmu tare da wasu kalamai na tsafi, an lulluɓe shi da farin yadi.

Ba'a ɗauki minti biyar da fara wannan tsafin ba, mu kaga kakanmu ya miƙe saman ƙafafuwansa, na ɗauka idan mutum ya mutu shikenan tashi ta ƙare, bisa ga mamakina sai na ga gawa ta miƙe da ƙafafuwanta tana tafiya, haka muka dinga binsu gawa na tafe muna bayanta ana kiɗa da waƙe, har zuwa inda aka haƙa ramin, kakanmu na zuwa zai shiga cikin kabarinsa, sai mu kaga ya tsaya cak, wani baƙin hayaƙi na fita ta cikin idanunsa, wanda alama ce na cewa, yana son bayar da saƙo ne kafin ya kwanta a cikin kabarin nasa, wanda zai zama gidansa na ƙarshe, sai idan dalili ya zama babban dalili za'a iya tayar da shi ya bamu haske akan abin da ya shige mana duhu muka kasa samun mafita mai ɓullewa.

Ya yi shiru daga basu tarihin kakansa, ya dubi ƙananun yaran da suke gabansa, basu fi shekara biyar biyar ba, sai namiji da ba zai fi shekara biyu ba a cinyarsa ya yi luf yana bacci. Yana shafa kan wata mace ya ce

"Na san kuna son jin me kakana zai ce ko a lokacin?" Suka jinjina masa kai alamar "eh"

Ya ɗora da; Ikur da Imande, muna tsaye muna kallon kakanmu, Iyayenmu na kallon mahaifinsu suna sauraro daga gare shi. Cikin abin da bai gaza daƙiƙo ba, gawar kakanmu ta buɗe bakinta cikin damuwa da murya irin ta kuka da tashin hankali, ta ce

“Haƙiƙa kun karya dokar Akombo, bala'i da masifu za su faɗo muka, ba za ku taɓa samun sauƙi ba, har sai UWA MAMAA ta bayyana, zata bayyana ɗauke da TSAV, kalmarta ɗaya waraka ce a tattare daku, albarkarta ceto ce a wajanku, kada ku neme ta, ita da kanta zata kawo kanta inda kuke, domin bata kasance ɗaya daga cikinmu ba, tana wata uwa duniya, wata nahiyar ta daban, kar ku neme ta, zata zo har inda kuke ta same ku, duhu da iska,da baƙin hayaƙi da kukan Akombo shi ne zai baku shaidar cewa, MAMAA tazo, kalmanta shi ne misali na biyu, babu yankan shakku a duk wani furucinta, harshenta bala'i ne ga ƴan'uwanta, ku kuma haske da tabarraki ne a gare ku, idan kun samu MAMAA kar a yadda a kuskura ta kasance da ɗa namiji, balle ta ɗauki ciki, MAMAA tsarkakkiya ce, na san Ikur da Imande da maitar mace. Akwai alama ta uku da zata sake bayyana zuwan MAMAA, idan an yi mata gwajin budurci, Alƙalamin ba zai taɓa shiga jikinta ba, babu wani daya isa ya amshi kimar MAMAA, zaku sadaukar da budurcinta ne zuwa ga Akombo, Tsav ɗinta zai cece ku”

"Kaka mene Akombo da Tsav?"

Anum ta yi tambayar cikin rashin fahimtar tarihin kakan nasu na zamanin daya shige.

Ya dubi Anum ya ce "Anum, Akombo yana nufin ikon ruhaniya da aka gada daga kakanni, yana warkar da cuta, kariya daga bala'i, gano me laifi, warware rikicin dangi a taƙaice Akombo shine haskenmu da muka yi imani da shi Anum. Tsav shi ne ikon sihiri mugun iko a al’adar Tiv. Ana danganta shi da Mayu, masu shan jini, masu cutarwa ta ɓoye ana cewa Tsav yana cikin jinin mutum ko ruhinsa. Ba kowa ke da Tsav ba masu Tsav suna iya, haddasa cuta, kashe mutum a ruhaniya, rikitar da al’umma hakan na faruwa ta harshensu, a kalamansu"

Ya cigaba da basu labarin asalinsu; Bayan mun kammala sauraran Kaka, yana gama faɗa ya faɗa cikin kabarinsa muka binne shi. Muka cigaba da nausa tafiya a tsakiyar daren har muka samu yada zago a gaɓar wani ƙogi. A lokacin Itayo daga ɓangaren Imande shine ya amshi jagorancin tafiyar. A hannunsa akwai ganye da aka ɗaure da zare,da ƙasa a ƙaramar ƙwarya, da ruwa daga kogi. Ya durƙusa a wajan yana duba ƙasa kamar me nazari cikin girmamawa ya ce
Chapter 2 · 0% Book details