← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 64

Sashe 1

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*H I Y A A M*

Page 1
Bright pens

More pages on ArewaPen. Ku yi searching sunan littafin za ku samu.

Yota/001

Bari na yi amfani da wannan damar na yi miki godiya Yaɗɗo am, kina daga cikin alherin da media ta bani, Ubangiji Ya cika miki muradanki ya raya miki zuri'a Falmata 😂Every time I see you, I see you as family, even though you're the one I love. You'll always be my favorite person, Yaɗɗo, and my best friend forever. Even if I’ve never said it before, I can proudly shout it to the world through a loudspeaker: you're so special to me. Daga farko har ƙarshe wannan littafin sadaukawa ce a gare ki Jikar Nashe. Dedicated to NAZEEFAH SABO NASHE. Fans ɗinta zanga adadin capacityn da za ku nuna mini a tafiyar HIYAAM.

NOTE: A baya ban taɓa faɗa ba, a yanzu na ce, duk wanda ya sake ya yi mini amfani da littafi a YouTube Shari'a zata rabani da mutum in sha Allah, ban fara ba sai dana samu Copyright. Ta kowacce fuska kar a juya mini littafi.

MY WORDS: Wani labari da zai yi dai-dai da abin da kuke buƙata wani labari ne dana fara rubutawa tun 2/5/2025 bani da tabbacin zai muku amma ina da yaƙinin ba za ku yi danasanin karantawa ba. Duk abin da ya yi dai-dai da rayuwar wata ko wani ayi mini lamunin cewa bincike ne ya kawo haka, ƴar jarida daku nake a yi mini afuwa, iyayen ƙasa ayi mini afuwa da masu ruwa da tsaki abin da kukai makkuwa ne na dawo dashi, idan kina sake da addu'a ko tarbiyya ba ki wahala ki zo mu sasanta lamarin tare. Iyaye mata wanda suka riƙe responsibilities na gida wannan ma naku ne. Ƙirƙira ce amma labarin ƙabilar da za ku ji da wasu abubuwan masu kama da almara duk gaske ne, kawai na yi ƙari kaɗan akan wasu kuma zuwa gaba zan faɗa.

THANK YOU: Kafin na fara zan godewa marubutan da suka taimaka mini wajan haɗa information waje guda, na sha wahala na kasa sukuni akan tattara bayanai ganin kar a baku abin da hankali ba zai ɗauka ba. Marubuta sun mini ƙoƙari tabbas, Lubnasufyan, Sumayya takori, Zuwairiyyah Adamu gerie, Autar manya, Mai dambu, MeerahGee thank you all sun mini ƙoƙari wajan tattara bayanai da ganin na kammala komai.

BRIGHT PENS: Dear Ayushercool na gode sosai my zizi Zee Kumurya Allah Ya baku aljanna ina son ku sadidan yan'uwana abokan🤭... Da na ce ba zan rubutu ba sai 2027 sune suka tasoni gaba😄. My pple YOTAWA dangina duniya da lahira Allah ya sakawa jama'ar Young talented writers association wannan page ɗin naku ne.

_Bisimillahir Rahmanir Rahim_

A ƙa'ida a kuma tarihi, maza ne kawai suke yin aiki a gidan, sun tsani mata basa son su sam, suna ganin alaƙa da matan da suka ƙetare iyaka daka waje zuwa cikin gidan, kamar zai zama tubalin rusa dukkan wani al'ada, tsafi, ƙarfin ikon da sukai shekara da shekaru suna ginawa, domin kyautata goben da har yanzu suke zaman jiran ganinta. Kakanninsu ne suka damƙawa iyayensu, bayan sun cinye wa'adin da ƙaddara ta shimfiɗa wanda kowanne mai numfashi a ƙirji yake rayuwa tare da zanen tasa ƙaddara, mai kyau ko akasin hakan, sai suka tattara ragamar komai suka damƙawa ƴaƴansu, wanda ƙarfin iko, isa, izza, jinin ƙifaɗin dake gudana a jikinsu ya zarce waɗanda suka shuɗe. Sun rayu akan mafarki, sun wanzu da tsoron da mafarkin ya saka musu, wanda kuma shine zai zame musu jagoran da zai sanya su samu haske a cikin duhun da suke. A bisa wannan tsoran suka zartar da hukunci na ma'aikatan da za su dinga hidima a cikin TAJMAHAR. Jadawalin maza kusan 150 ne masu aiki kowacce rana, safe da yamma.

Suna amfani da maza ne, domin kafin haihuwarsu an sanar musu mace ita zata zama hujjar rarrabuwar kan su gabaÉ—aya.

Kamar kullum yau ma ma'aikatan sun yi layi a babbar ƙofar da zata fitar da su daka cikin Tajmahar, jerin maza ne, sanye da kaya iri ɗaya wanda ke bawa wanda ya kalle su, tabbacin uniform ne.Kowanne akwai numbersa a jikin rigarsa, duk wanda zai fita akan caje shi domin tabbatar da bai yi sata daga ciki ba zuwa waje. Zuciyarta ce ta cigaba da bugawa a ƙirji, wanda ya haifarwa da jikinta amsar yanayi, duk ƙoƙarinta ta kasa daurewa, a kullum da wannan tsoron take shigowa Tajmahar kuma take fita, Allah yana tarfawa garinta nono wajan fita salin alin. Sanda binciken yazo kanta numfashita ne ya ɗauke tsaf, kamar wacce wa'adinta ya yi a sa'ilin zufa na yanko mata a duk wata ƙofa da Ubangiji ya halitta a kyakkyawan jikin da wahala ta gama muzanta shi, zuwa siffa ta daban, siffar da ita kanta tsoran kallonta take yi a madubi, bata sha'awar ganin ma.

"No 089" aka nanata kiran sunanta.

Cikin hanzari ta ƙarasa tana shanye tsoran da ya gama cinye dukkan zuciyarta sai rawar ɗari take yi, a zuciyarta take furta; “Allah ya cece ta yau ma”.

Aka fara caje ta, aka cire hular kanta domin tabbatar da babu komai a ciki, aka tarar da santalelen kanta daya sha ƙwal kwabo babu tsoruwar suma ko guda ɗaya sai ƙyalli yake. Bayan an duba aka mayar da hular kan nata, aka caje har cikin takalminta har zai sallame ta, sai ya lura da ƙirjinta kamar ya tasa, tunaninsa ko wani abu mutumin ya sato, zato ko tsammani balle hasashe bai taɓa kawo masa ita ɗin macace ba, tunda ta fara aiki har kawo yanzu da sunan namiji take amsawa “TERSEER”. Ya yi mata kallon tsaf kamar zai cinye ta a dake ya furta "089"

Sannu a hankali ta jinjina kai alamar amsawa. "Cire rigarka, umarni nan take"

Ta ji umarnin har tsakiyar kanta, kamar an sanar mata da ranar mutuwarta, ƙoƙarin magana take yi, amma ta kasa, muryarta zata fallasa sirrinta na jinsin ƴa mace, ya sake yi mata tsawa "Terseer 089!" Fafur taƙi cire rigar, sauran ma'aikatan da basu fita ba, suka fara yi mata ban baki akan ta yi abin da aka ce, domin a cikin abu biyu za'ayi ɗaya, ko ta rasa ranta nan take, ko dai ta tabbata a cikin kurkukun “GBANDE AONDO”

"Guards! Guards!"

"Umarnin kira nan take......!"

Cikin ƙaramin lokaci dukkan wasu Guards da suke tsaron ƙofar suka bayyana, aka zagaye ta. Babban cikinsu ya ce "Wannan mutumin ya yi sata, akwai kaya a ƙirjinsa, a ƙwace a yi masa bulala hamsin a kore shi"

"Kashina ya bushe!" Ta furta a zuciyarta.

Kokawa suka shiga yi da ita, sai dai kasancewar ta macace ita dole ta bada kai bori ya kar boka, bugun zuciyarta ya tsananta lokacin da suka zare rigar wata razana suka yi tare da yin baya, nan take kuma iska ta fara tashi a wajan, arba da halittun ƙirjinta na ɗiya mace da suka yi a lokacin ya fi komai muni a tarihin masarautar Tajmahar, wani abu ne da ko a mafarki ba'a taɓa tunanin zai faru ba, rashin sani ga Guards ɗin, domin bayyanarta zanannen labari ne tun iyaye da kuma kakanninsu har zuwa yanzu.

Ta saka hannu wajan kakkare tsaraicin ƙirjinta, hawaye na taruwa a cikin idanunta.

Bayyanar abin da ya faru ya zama abu me sauƙi, kamar wutar daji a cikin Tajmahar, kafin ka ce wane aiki, Shugaban da kan shi da jama'arsa sun ƙarasu wajan, ya shiga bin kowa da idanu, yana ɗora idanunsa a kanta, jikinsa na matsanancin rawa da ɓari ya yar da sandan dake hannunsa ya zube a gabanta wajan ƙafafuwanta ya furta "Lale, barka da zuwa uwata, barka da zuwa Mamaa, barka" ya ce da rawar ɗari.

Allah Subhanahu wata'ala shi kaÉ—ai ake bautawa, ita musulma ce mene ya haÉ—ata da abin da suke yi? Su waye su É—in? Mene hakan? Me kalma Uwata, da Mamaa suke nufi a tattare da ita? Ta shiga girgiza kai

"Bani bace, bani bace" ta faÉ—a a sanyaye, jikinta na rawa

"Mun fi shekaru muna dakwan zuwanki Mamaa, kar ki yi fushi damu, ki albarkaci wannan masarautar, an ce, kalmar ki É—aya na iya sauya mana rayuwa, ki yi furuci akai na Mamaa, ki buÉ—e bakinki Mamaa, ki yi..,"

"Ban kasance wacce kuke nema ba"Ta rushe da kuka

"bani kuke jira ba....

Nan da nan suka fara rawa da kiɗe-kiɗe hatta Shugaban rawa ya fara cikin waƙe yake maganar "Kece ruhinmu Mamaa, kece gatanmu Mamaa, abar bautarmu kece Mamaa, kece"

Suka shiga watsa mata wasu abubuwa aka.

Sham ya ce "Mu fara tabbatarwa ita ɗin ce, an bamu haske na yadda za mu gane Mamaa, an baka umarnin kasancewa da ita a dare ɗaya, idan ka samu nasarar keta budurcinta, to ba ita ce Mamaa ba, idan alƙalaminka ya gaza keta budurcinta to tabbas Mamaa ta bayyana a wannan karon"

Jin haka ya saka ta mance da tsaraicin ƙirjinta dake bayyane, ta saki hannunta ta juya zata fara gudu ya ce "A ɗakkota, akai ta kyakkyawan gadon da nake kwajin budurci domin tabbatar da zuwan Mamaa, ku kasance a bakin ƙofa, idan kuka ji ihu to na samu budurcinta, sai a fara tunanin yadda za mu kashe ta, idan kuka ji shiru baƙin hayaƙi ya bayyana, to Mamaa ta bayyana, sai mu shirya inda zamu ajjiyeta mu dinga yi mata bauta" duk yadda ta yi ƙoƙarin kiran sunan Allah ta kasa, komai nata ya kunce ta durƙushe a wajan, wani badakaren mutum ya zo ya saɓa ta a wuya ya nufi da ita cikin ɗakin Shugaba. Ya ajjiye ta ya fito, Shugaban ya shiga jama'ar wajan sun fi ɗari suka tsaya a bakin ƙofa ana dako, tare da sauraro zuƙata cike da fatan Allah Ya sa ta kasance MAMAA ABAR BAUTA wace suke jira tsayin shekaru.

***
H I Y A A M.
Littafin Haleeym Ana Daada.
Chapter 1 · 0% Book details