Sashe 18
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Me kake yi a nan? Kai ma ɗan gidan Moddibo ne? Ina naggenka? Ina Innarka ta mutu ko tana raye? Kuma kai ma kana ganin kayan cikin mutane? Mutum nawa ka taɓa ci? Ka taɓa fita maitar dare? Wa aka taɓa cewa ka kawo aci? Kai kaɗai kake kama kurwa ko haɗin gwiwa kuke yi?" Tambaya take ta yi masa daga wannan zuwa wannan, shi kuma ya juya mata baya.
Ɗan zabura ya yi kaɗan jin ta cakume shi sai ta yi baya. "Innalillahi!" Ta lumshe idanunta "Jikinka laushi kamar burudin da Saleh yake bani idan ya taɓa ƙirjina" Sannu a hankali ya juya ya kalle ta, don tsayi tana da tsayi amma bata kai Anarsa tsayi ba, kyau kuma bai san waye yafi wani ba, wannan akwai surutu kamar aku, ana kuma maganarta a sanyaye take kuma babu ƙuruciya a tattare da Ana magana cikin hikima take yi. Ana ta zama budurwa completely, wannan yanzu take girman.
"Baffana makaho ne, amma sarai da idanunsa Yaaye ce ta makantar dashi saboda ta kasa cinye shi, ta É—ora masa lalura ita a tunaninta duk ban sani ba, ta manta muddin mayu suka kama mutum idan É—an'uwansa ya gani yana gane tambarin mayen" ganin ko tari bai ba, ya saka jikinta yin sanyi ta ce
"Laa kaÉ—on baya magana Allah Sarki"
Ta zuba tagumi ta tallafi haɓarta. "Ka dinga shan ruwa sosai zaka samu kuzari da ruwan zogale ka saka madara a ciki
***
BRIGHT FM REDIO.
Ta gefen ido ya sake watsawa Ahlam wani irin miskilin kallo wanda yake nuna kin rainawa kan ki hankali. Ita kam gabaɗaya jikinta wani irin rawa yake yi yana ƙoƙarin bada ita, da yadda tsoron MD ɗin ya bayyana ƙarara akan fuskarta, ta kasa ɗago kai ta kalle shi, gashi zuwa yanzu tasan Yussy ta fara karanta labaran, gashi bata son ta saka auren matar can a cikin matsala.
A hankali ta ɗago kai kamar zata kalli fuskar MD ɗin sai kuma ta yi saurin mayar da idanunta zuwa gefensa, ta shiga kame jikinta da tattauna laɓɓanta wanda ta gama jiƙasu da yawon bakinta ba tare data sani ba. A iya tsayin lokacin data shafe a BRIGHT FM ɗin bata taɓa kallon cikakkiyar fuskarsa ba, bata da wani dalilin da zata kama wanda zai zama hujjar ƙin kallon fuskar ta MD.
Kawai dai tana da yaƙinin bata da alaƙa dashi da dukkan abin da ya mallaka a ciki har da fuskar da zuwa ke janta wajan kala, ko zata iya yango bambancin da yake tsakaninsa da sauran maza, wanda ya saka shi irin wannan ƙifaɗin da jin kai har haka.
MD da yake tsaye kamar an dasa shi wayarsa kawai yake dannawa, yatsunne kawai suke operating wayar, amma duk wani motsi na Ahlam yana ankare dashi, tare da sanya su cikin ma'adanan sirrin shi.
"Don Allah....,"
Ta kasa yin maganar a lokacin daya ɗago idanunsa ya watsa a saman fuskarta, jiran abin da zata ce yake yi, sai kawai yaga ta fashe da kuka ta haɗe kai da jikin ƙofar Studio ɗin jikinta na wani irin ɓari tana girgiza kai, a firgice kuma ta juya tare da zubewa a wajan ta haɗe hannunta biyu waje guda ta ce "Sir don Allah, don girman ka tsayar da Yussy daga karanta labaran nan, na shiga uku idan ta karanta na kaɗe har ganye na" da ƙyar take yin maganar ma. "Bana son matar nan ta rasa igiyar aurenta akan son raina, akan son ɗaukakata don...,"
"Baby mene haka? Get up please"
Anees ya furta yana ƙarasawa wajan idanunsa ya rine saboda ɓacin rai da ganin yadda Ahlam ta durƙusa a gaban MD ta zama wulaƙantacciya a wajan mara gata.
Girgiza kai ta yi ta ce "Ya zan yi Anees?"
"Wataƙila idan na durƙusa za'a fi fahimtata"
Anees ya ce "Ba dole sai kowa ya fahimci ki ba baby, saka labarin nan baya nufin tsayuwar rayuwarki, wani ko wata basu isa su yi miki abin da Ubangiji bai ƙaddara ba"
Hannu Anees ya miƙa zai ɗagota ganin yadda shanyayyen hannunta yake ta rawa shi kaɗai, shi dai sosai yake jin tausayin Ahlam har ƙasan zuciyarsa ba tare daya san wani dalili ba. Kafin ya saka hannunsa Md ya yi baya kaɗan da waya kare a kunnunsa
Ya ce "Idan room zaka kama mata a hotel bani da damuwa, Bright Fm bai zama dandalin Æ´an iska na mamajos ba Please"
Daga Anees har Ahlam wani abu suka ji ya tokare musu a maƙoshi ya tsaya waje guda, wani irin duhu kawai Ahlam take gani, ta rasa dalilin daya saka MD yake mata kallon ƴar iska ko kuma me buɗewar ido, bata san abin daya taka ba da yake jin ko a gaban Ubangiji zai iya maimaita wannan kalaman masu muni a gare ta dama rayuwarta gabaɗaya. Ko dai ya taɓa kamata tana aikata abin da ba shikenan ba? Ko wani namijin ya taɓa gani ya rungumeta, ko ya sumbace ta, ko kuma kamata ya taɓa yi turmi da taɓarya? Tana buƙatar sanin dalilin wannan ƙazafin wanda yake shirin rusa mata dukkan farincikin rayuwarta.
Mijinta take wa tanadin kanta, jikinta na wanda Allah ya bawa ita ne matsayin mata
Da ƙyar ta miƙe tsaye, kanta a ƙasa daidai nan Yussy ta fito daga Studio kuma ya yi wa'adi da lokacin da HR ya ƙarasu wajan.
HR ya ce "Na je office É—inka baka nan, so you're here ashe. Na ji kana kirana?"
"HR daga yau kar ka sake É—aukar mana shirmammun mutane a gidan rediyon nan, waÉ—anda basu san komai ba sai shirme da tsoro, wanda basu da wani amfani sam"
Cikin girmamawa HR ya ce "In sha Allah"
MD ya juya a hankali, Yussy ma ta yi wa Ahlam wani irin ƙasƙantaccen kallo kafin da sauri tabi bayan MD tana riƙe masa hannu da faɗin "MD yaushe aka mayar da taron?"
Ahlam tabi bayansu da kallo, ta dubi yadda shafaffen ƙugun Yussy ke mannewa ita a dole murguɗa shi take yi, sannu a hankali kuma ganinta ya sauka akan hannun Yussy da yake cikin na MD. "Ɗan iska akwai" Ahlam ta furta a sanyaye tana jin cewa daman ɗan iska ne kawai ke yi wa wasu kallon ƴan iska. Da ƙyar Anees ya rarrashe ta suka nufi office ɗinsa tana ta murmushi tare da juya manyan idanunta, bayan sun shiga office ɗin ya ja mata kujera ta zauna.
"Anees"
"Na'am baby"
A hankali ta ce "Anees ina buƙatar ɗaukaka a aikin jarida kota wacce hanya ce, ina buƙatar na samu ɗaukaka ko hakan zai saka Yussy ta daina yi mini kallon da take yi mini na wacce ba zata iya ba, ina son nunawa duniya nakasa ba zata taɓa zama kasawa ba" ta ƙare maganar a hankali tana yin ƙasa da kanta saboda kallon da Anees yake mata.
Shiru ne ya biyo baya, tun tana jiran ta ji amsar da Anees zai bata har ta gaji ta miƙe ta nufi ƙofa zata fita tana ƙoƙarin buɗewa
Ta ji ya ce "Ahlam"
Cak ta tsaya kuma bata juya ba, tana jin sanda ya miƙe ya tsaya a bayanta ya ce
"Wata ɗaukakar masifa ce, ki yi addu'ar samun abin da yafi zame miki alheri. Aikin jarida ba abu bane me sauƙi, yanzu kika fara ba balle ki fahimci me nake son faɗa miki ba. Amma ɗaukaka ga ɗiya mace hatsari, kar ki damu da abin da Yussy ke miki, ki mata uzuri na wani lokaci kin ji?"
A hankali ta jinjina kai ta ce
"Thank you Anees"
"Bari na ajjiye ki a hanya nima tafiya zan"
Office ɗin ya rufe fuska fito tare, tunda ta fito Baba driver yake mata kirari irin wanda ya saba. "Allah Ya taimaki Golden voice, maƙiyanki fadawanki an buga dake an barki sarauniyar murya ta Bright Fm gabaɗaya"
Ta murmusa ta ce "Duk ni kaÉ—ai Bana?"
"Haka za'a ganki a bar ki, bangon sigari kowa ya jingina dake sai ya lasa Wallahi"
Anees ne ya ciro walet É—insa ya ce
"Wannan kirarin ya zama dole na biya"
Jiki na rawa Baba driver ya saka hannu ya amshi kuÉ—in yana faÉ—in "Sarauniya sai da Sarki, Allah Ya baka Golden voice ka ji"
"Amin Ya Allah, Amin Ya rabb"
Anees ya furta cikin sauri yana lumshe idanunsa, cikin sauri Ahlam ta kalle shi sai ya yi saurin kashe mata ido ya yi waje.
Ta saman bene MD ya hango shigar Ahlam cikin motar Anees har suka fice sai kawai yaja siririn tsaki yana mai da sunglasses É—insa zuwa saman fuskarsa.
***
Ya murmusa kaÉ—an ya ce "GiÉ—aÉ—o ikon Allah masu Gwamantin da kan su, to ya ake ciki ne?" Wanda aka kira da GiÉ—aÉ—o ya gyara zaman shi a nutse fuska a kame cike da kwarjini ya ce.
"Barde, Gwamnati ai taku ce" Barde ya jinjina kai yana faÉ—in
"Shi ya sa naga nine na hannun daman Gwamna. Na ji abin arziƙi na offers data fito daga hukumar Ma'aikata ta Jiha, kuma dai kai ne Kwamishinan ilimi, dole na yi kamun ƙafa da akai" Giɗaɗo ya buɗe fararan idanunsa ta cikin glasses ya kalli Barde kamar ba zai magana ba, sai ya ce "Mun tattauna da Indabawa jiya, an ware naku da za ku bawa iya family ɗinku, Offer ɗin me kyau ce, hatta salary duk da ba'a kammala yanke nawa za'a bada ba. Waɗanda za'a bawa Allowance ma daban suke. Don haka za'a dinga siyar da Offer ɗin akan dubu ɗari uku, ba zamu rabawa yaran talakawa a aikin banza ba, ba sanin darajar ilimin sukai ba duk sune ƴan iskan gari"
Barde ya ce "Allah mutumina? Shi ya sa nake yinka ba, masu Gwamanati da kan su" Giɗaɗo ya miƙe tsaye yana gyara zaman suit ɗin jikinsa wacce ta yi masa kyau sosai.
"You're not nice Barde. Zuwa anjima zan shige Qatar dani da Madam, wai tana buƙatar hutun sati biyu ne kawai a can"
"Dole Madam ta huta da yawa, kuɗi yazo Alhaji" taɓe baki Giɗaɗo ya yi, mutum ne me ji da kan shi uwa uba ilimi da izza professor matakin ƙarshe kuma Dr. Suka ɗan fito harabar babban wajan. Barde ya ce
"Yanzu airport zaka shige kenan GiÉ—aÉ—o?"