← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 64

Sashe 16

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ana kallon Dattijon ta yi, sannu a hankali ta kalli gefen hijabin nata inda ya riƙe mata. Runtse idanunta ta yi, ƙirjinta yana yi mata wani irin nauyi kamar an saka mata dutse a ƙirjin, wani zafi-zafi take ji haɗe da yaji-yaji.

Ta buɗe baki da ƙyar ta ce

"Ina ganin darajar furfura ko bata mahaifina bace, ka cire hannunka a jikina Baba"

Dattijon ya ce "Rashin kunya za ki mini?" Ya ɗora da "Ke anya ke kuwa mutum ce? Ban taɓa ganinki a wannan unguwar ba, ko irin ƴan iskan yaran nan ne masu barin gaban iyaye zance su biyo saurayi har unguwarsu?"

Takaicin da ya yi mata yawa a zuciya tana jin kamar ta yi bindiga saboda yadda take jin wata wuta na rura kanta a cikin zuciyarta sai ta ka da bakinta ta ce "E, ita ce. Ka sake ni"

"Waye ubanki a unguwar nan?" Ta ce "DAADA"

Sunan ya fita ta cikin sirriyar muryarta mara son hayaniya da ihu ko kaÉ—an bata so.

"Kan uba! Wannan tantirin tsohon shine uban naki? Me caca da garta kike nufi?"

Cewar wani matashi, da ya yi maganar yana riƙe haɓa saboda tsananin mamakin daya cisa. A wannan karon Ana watsa firgitattun idanunta ta yi akan matashin, idanun da tunda take bai taɓa fita daga hayyacinsa irin yau ba, kanta wani irin ciwo yake mata yana juyawa tana jin kamar zai rabe mata biyu.

A tausashe ta ce "E, shine ubana"

"Babangida wai Daada me shan barasa yana yawo tsirara a kwararo idan dare da ya yi kake nufi? Me bin matan banza yana aikata aikin banza dasu, kamar yadda ya kasance É—an banza? Wannan shine uban yarinyar nan?" Kai tsaye Babangida ya bashi amsa da

"Wallahi shine, ai Daada É—aya ne unguwar nan" ya tuntsire da dariya ta mugunta.

Kallon tsana Dattijon yake bin Ana dashi kafin ya sake ta yana ɓata fuska kamar yaga kashi ya ce "Sannu ƴar nan, na tayaki baƙinciki da kuma takaicin samun mahaifi irin wannan, ashe yana da yarinya data girma har haka yake aikin banza da wofi a gari babu kunya babu tsoran Allah? Ashe yana da zuri'a mace yake bin manta banza? Yarinya kin yi kyawun ɗan maciji, kyawun da kike dashi ya tashi a banza ya kuma tafi a banza, babu uban arziƙi da zai yadda ɗansa ya aure ki domin baki kasance tsatson arziƙi ba" Babangida ne ya ce "Gaskiya kam baba"

"Abin ya muku yawa wai shege da hauka, ke maita, Ubanki Dattijon banza, ƙanin ubanki wanda Allah Ya tsinewa me shigar mata"

Sai a lokacin ne wasu azababbun hawaye masu masifar zafi da raÉ—aÉ—i suka kwace mata tare da bin kyakkyawar fuskarta suna sauka da gudu saman kumatunta, cikin sauri ta saka bayan hannunta ta goge su.

Ba'a taɓa bin Ana bashin magana. Saboda haka ta kalli Dattijon ta ce

"Na gode Allah da baka da gidan wuta balle na Aljanna, Ubangiji shike fitar da iri daga matacciyyar shuka, kuma shike raya wannan irin har ya zama ganye kore shar wanda kowa yake birge shi, na yarda ubana yana shan giya, yana caca, amma ƙazafin bin mata da kukai masa Allah shine zai mana sakayya daku, ban taɓa jin tsanar shi ba, soyayyar da nake masa ce ta saka kai tsaye nace muku shine ubana, babu wanda ya isa ya saka na sauya sunana daga nasa"

Za su yi magana Jaheed daya rufe shagon ya ƙarasu wajan, idanunsa zube akan shalelen Innti ya dube ta tsaf kafin ya ce

"Meya fito dake?"

"Au ɓoye ta kuke yi saboda mugun iri ce ko?" Jaheed ya kalli Babangida ya ce

"Sai dai ban fahimce ka ba"

Babangida ya ce "Borin kunya daman da hauka ake naÉ—e shi, yaron mutane ta kama"

"Kar ka sake ce mata Mayya!"

Furucin Yaa Sam ya fito a nutse a tausashe yana bubbuÉ—e grey eyes É—insa zuwa waje.

"Na faɗa a saka kaina gabas a yanka, wallahi ni dai kurwata kur nafi ƙarfinta"

Cikin zafin rai da raÉ—aÉ—in kalaman Babangida da yake jifan Ana dasu wanda kai tsaye suke sauka a zuciyarsa suna kartar naman dake sarrafata ya nuna shi yana tattare hannun rigarsa ya ce "Ka yi kuskuren jifanta da wannan kalmar wallahi sai na maka illa mutumin banza da wofi, yunwa duk ta cinye muku yara babu mamaki ma olser gare shi, shine za ku zo kuna ihun banza bara a kufai" ganin da gaske Yaa Sam naushin Babangida yake shirin yi ya saka Jaheed saurin matsawa gabansa yana faÉ—in

"Ka yi haƙuri ka rabu dashi Yaa Sam. Ana dai ba mayya bace kuma banda Innti ta hana mu faɗa da mutane wallahi yau da ya ɗauki kashinsa a hannu babu wanda ba ɗan iskan kan shi bane, da ita mayya ce da mune farkon waɗanda zata fara cinyewa I'm telling you this"

"Kuma da mayyar ce me zan yi da naman mummunan mutum irinsa jiki duk basir da sanyi ya yi masa illa" Jaheed ya ce

"Gaya masa dai tawan"

Yaa Sam ya juya ya kalli Jaheed sai ya mayar da idanunsa akan Babangida ya ce "kuma wannan maganar shari'a ce zata rabani da kai, tunda ko mugun abu kukai iya da tsinanne sa ido wa jama'ar unguwa"

Cikin shakku dattijon ya dubi Yaa Sam yana nuna shi da yatsa ya ce "Wannan ba É—an gidan Malam Usmanu bane? Shi Usmanun ya barka kaka mu'amala da zuri'ar Daada?"

Ko inda dattijon yake Yaa Sam bai kalla ba. Jaheed da ya shiga mamaki da takaicin fitowar Ana ya dube ta a hankali ya ce

"Me ya fito da Shalelen Innti?"

Ta ji shi sarai amma ko motsi ta kasa yi balle ya yi tunanin zata ɗago ta kalle shi har ta bashi amsar da kunnuwansa suka mace wajan jiran jin abin da yake faruwa, shi dai a tunaninsa da iya lissafin ƙwaƙwalwarsa a shekarun nan ɗaiɗai har shekaru goma sha Bakwai, tun daga haihuwar tawayen Innti, Iftifal da Ana, tun daga rainonsu zuwa girma idan kaga Ana ta fito waje a cikin biyu ko uku akwai ɗaya, babban dalili zuwa makaranta, boko, Islamiyya sai ta dare, dalilin dake bayan neman ilimin shine kiran Yaa Sam idan ya dawo gari. Wannan sune.

Ƙawaye bata dasu, sau tari ta kan ce;

"Duniyoyi shida ne ke zagaye da rayuwata, ina jin sanyi daga kowacce kusurwa Innti"

Zata ja numfashi a hankali ta sauke manyan idanunta na sauyawa zuwa yanayi na ruwa, ruwan dake ƙara musu nagarta da kuma sahihin kyau, wanda yake sake fitar da kalarsu na “sexcy eyes” bata fiye kallon mutane da wannan suffar idanun ba.

Babban mutum kawai take iya kalla dasu kai tsaye ta ji ta yi na'am da kallon har ranta.

Da wannan nauyin zuciyar take riƙe hannun Innti da Iftihal musamman a ƙasan bishiyar dake ƙara musu ƙaunar juna saboda sanyinta. "Innti ni kaɗai nake jin idan na rasa ku kamar Ana ba zata iya rayuwa ba? Ina jin kamar nima wa'adina zai zo ɗaya da naku ne, zan jure komai, zan haƙura da komai, zan fahimce komai, zan yarda da komai, a cikin komai ɗin nan banda ku...,"

Ta lumshe idanunta ta É—ora da,

"A cikin komai ɗin nan ban da rashinku a duniyata, kune ƙawayena, aminaina na cikin zuciyata, farinciki da walwalar Ana"

A irin wannan lokacin Iftihal ke damƙe hannun Ana ƙam hawaye na sauka a saman fuskarta ta ce "Ita kanta mutuwa na san za ta yi mana halarci mahaɗita, zata ɗauke mu ne tare, dani dake da Inntinmu, yadda muka zo duniya a rana ɗaya, a kusan daƙiƙa ɗaya, a mahaifa ɗaya, daga cikin nagartacciyar uwa ɗaya, ina roƙan Allah ya amshi rayukanmu su yi wa'adi ɗaya tare da uwar data kawo mu duniya" Ita kanta Innti wannnan ranar ta rabuwa kashe ta take yi tun kafin mutuwarta, tana rayuwa da mutuwa da tunanin rabuwa dasu watarana dole. Idan ta tuna su yarana sai ta ji ta mutu, idan ta tuna su mata ne sai ta sake yin wata mutuwar, idan ta tuna dangin mahafinsu sake macewa take yi, babban dalilin dake sawa ta ji ta zama matacciyya shine; halin mahafinsu Daada.

Bayan macewar tana farfaɗo wa da ƙarfin zuciya da shauƙin tuna cewa akwai, wani jigo a rayuwarsu bayan ita. Akwai garkuwarsu. Suna da Babban yaya a tare dasu tabbas..... Ta yi nisa cikin tunaninta

Jaheed ya sake maimaita mata tambayar

"Mene ya fito dake Ana?"

Bata iya bashi amsa ba, saboda yadda ƙirjinta ke ɗagawa tana jin wani zafi da raɗaɗi kiranta da mayya, kalmar da bata san ma'anarta ba, bata kuma san me take nufi ba. Tambayar duniya Jaheed ya yi mata ganin kamar zata haɗiye zuciya ya saka Yaa Sam ya yi gyaran murya ya ce

"Ka barta"

"Shikenan, amma....,"

Bai ƙarasa faɗa ba, su kaga yaron ya miƙe a guje yana ihu ya yi lungun gidansu yana faɗin

"Cikina, yunwa....yunwa zata kai ni lahira"

Babangida ya yi saurin É—auke kai jiki a sanyaye, haka dattijon ma ya bar wajan.

Jaheed ya ce "Bari na koma shago Yaa Sam"
Chapter 16 · 0% Book details