← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 64

Sashe 39

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daidai ne Daada ya fito suna ganinsa suka ƙanƙame juna, Ana ta dafe hannun Iftihal ta ce "Daada zani a madadin Mahaɗita zan bika" kallon tsaf ya yi mata sai ya ce

"muje"

Ya miƙa mata hannunsa, hannun ta kalla sai ta miƙa nata zata ɗora akan nasa kenan ya cafke hannun ya fito da sabuwar reza ya kama tafin hannunta ya shiga tsaka hannun, wani ihu Iftihal ta kurma, ihun daya dawo da Innti daga hayyacinta ta miƙe ta ce

"Daada! Mene haka ka sakar mini Æ´ata"

"Kina matsowa a bakin aurenki wallahi"

Cak ta tsaya, ta zubawa jinin da yake tsiyaya daga hannun Ana yana sauka a ƙasa, Ana ko motsi ta kasa kamar yadda ko tari ta kasa, ta kafe Daada da manyan Idanunta, sai daya kammala rubuta sunan Daada a tafin hannunta sannan ya fusgeta ya cillata a wani ɗaki me masifar duhu ya rufe ya saka ɗan makulin a alijuhu da ƙarfin gaske kuma ya shiga jan Iftihal tana tirjewa haka ya jata har ƙofar gida inda Alhji Baita yake tsaye yana sake shanye haɗin tsumin da ya yi, duk da wannan robar ya sha kusan roba goma ta tsumin maza. "Gata riƙe ta ku tafi" Daada ya ce yana tura Iftihal waje yaja ƙofa ya rufe....

*H I Y A A M*

Page 11: The Price of Betrayal

Bright pens
Yota/001

NAZY's KITCHEN me abincin ƴan gayu, duk wani nau'in ƙwalam da maƙwalashe, da kayan jiƙa maƙoshi da fita kunya za'a samu a wajanta.
08033748387

Iftihal ji ta yi kamar ana jan zuciyarta daga cikin ƙirjinta, ta kasa kuka sai haɗiyar zuciya idanunta rufe haka Alhaji Baita ya damƙi hannunta ya riƙe yana washe bakinsa. Daada ya kalle ta yana nunata da yatsa ya ce "kuma wallahi kika sake kika bar gidansa sai na tsine miki albarka kin bi duniya, gargaɗi nake miki" har ya rufe ƙofar ya buɗe takanas domin ya yi mata wannan gargaɗin. Bata san me yake cewa ba, balle kuma ta fahimta, cikin wani irin farinciki da jin daɗi Alhaji Baita ya zura hannu a aljihu ya damƙo kuɗi ya bawa Daada yana godiya tare da jan hannun Iftihal sukai gaba hankalinsa kwance.

*
BIYA.
Juyi take kamar macijiya a cikin bukkarta ta kasa bacci Idanunta sun yi jajur saboda tsananin azabar da take ciki, idan ta runtse idanunta sai ta buɗe da sauri, zuciya ke kai komo na son tilasta mata cinye Mado, tana ƙaunar ɗanɗana zaƙin naman mutumin da ita ce ta yi farautarsa, ta kama shi, ta danne ta kuma soya, saɓanin lokutan bayan da ake yin haɗin gwiwa da ita wajan kama kurwa tun kafin ta kai adadin lokacin da take a yanzu. Zuciyarta ke rarrabewa tare da cure mata a ƙirji idan ta tuna kamar akwai rashin kyautawa a abin da take shirin yi ɗin a yau.

A nutse ta miƙe tsaye ta nufi ƙofar bukkar tana leƙawa sai taga dare ya tsala amma akwai hasken watan dake haske sararin subuhana da Ubangiji Ya halitta. Tana cikin wannan halin ne ta ji kukan mage da wani irin sautin da har abada ba zata taɓa mance shi ba, wani irin faɗuwar gaba ya ruske ta, haɗe da wani irin firgitaccen yanayi me kama da tsoro. Jin wannan kukan masifa ne a gare ta, kuma babban bala'in da zai iya sakawa a yi mata korar kare a rugar Biya ɗin. Har inda Batty ke tsaye magen da ƙarasu baƙa da ita jibgegiyya sai huci take yi tana zare manya manyan Idanunta, ta raɓa ta gefen Batty ta shige zuwa cikin bukkar. "Batty, zo nan ciki Batty" Ta ji muryar Gana na kiranta da sautin da ita kaɗai zata iya jinsa. Jiki a matuƙar saɓule Batty ta ƙarasa inda Gana take tsaye wacce ta dawo asalin suffarta ta mutane. Kanta a ƙasa cikin rawar murya ta fara ƙoƙarin gaisar da Gana, da azama ta ɗaga mata hannu ta ce "Bana buƙata, ki bani kurwar Mado da kika kama, ita na biyo sawu" Batty ta ware ido tana kallon Gana da rashin fahimta. "Kurwar da kika kama ta Mado na ce ki azo mini ita na shige yanzu" a hankali Batty ta shiga ja da baya tana girgiza kai wasu hawayen tsoro suka shiga bin fuskarta. A tsorace ta ce

"A'a.... A'a ki bar Mado a raye......."Na roƙe ki, zan sakar masa kurwarsa"

Gana ta ce "Ai wallahi sai na yanka kurwar Mado, sai na yi watanda da ita a irin wannan lokacin tunda har kika riga kika kamata" sosai ƙafafuwan Batty suka shiga rawa da kakkarwa suna ƙoƙarin gaza ɗaukan gangar jikinta, wani irin nauyi ta ji sun yi mata, kamar yadda ta ji wani rikitattaccen yanayi yana saukar mata tare da shirin rikita lissafin dake riƙe da rayuwarta, idan lissafinta ya cika cif da cif, Gana zata cinye Mado a zuwan ita ta cinye shi, duk sanda me afkuwa ta afku asirin dake lulluɓe ya bayyana ita za'a zubawa jakar tsaba kaji su bita, kamar yadda a baya ta yi mata tuggun daya saka zaman rugar Yari ya fi ƙarfinta, kamar yadda a dalilinta ne ya rayuwarta taso lalacewa duk da har yanzu bata da amsar da ƙwaƙwalwata ke tambayarta na ma'anar rushewar rayuwa ko gurɓacewarta. Ta ɗauka kishiyar uwa, a rubuce a haka lissafin yake itama uwa ce? Balle matar da take wa kallon jininta madadin uwa, ƙanwar mahafiyarta da suka sha nono guda, innarta ta saki nono Gana ta kama, shine take yi mata rashin kyautawa.

Zuciyarta ta ji tana sake tsagewa da fargabar halin Gana ta durƙushe a wajan tana haɗewa hannayenta biyu alamar roƙo kafin da ƙyar ta iya buɗe laɓɓanta da suka bushe ta ce "Ki yi mini afuwa, ki mini rai kar ki kashe Mado, yana da kirki mutumin arziƙi ne....," bata ƙarasa maganar ba Gana ta saka ƙafa ta shure Batty ta hantsila baya.

"A irin wannan lokacin da nake jin kamar na ci babu kike cewa na bar Mado? Ƙanƙarar data yunƙuro mini na yi yaya da ita kuma?"

"Kici barkono, zata lafa miki"

"Abin da nake ji yafi ƙarfin na ci barkono, ya yi kaɗan ya lafa mini, ki gwada kama kurwa ki bata wahala daga ƙarshe ki danne ki yanka kici za ki faɗa mini daɗin da yake cikin hakan" ƙuri haka Batty ta zubawa Gana ido, tana ta lissafi a zuci, idan Gana ta ɗauke kurwar Mado za'a wayi gari babu mado a duniya, ita kuma ba zata iya zama silar wa'adin wanda ya yi mata alheri ba rayuwa.

Da ƙyar da wani irin nauyin zuciya dana jiki Batty ta buɗe baki wajan tambayar Gana.

“Mi waawi ƴamde maa, Yaaye?” (Zan iya tambayarki Yaaye?) tana kiran Gana da sunan Yaaye wani lokacin wanda yana nufin ƙanwar uwa a Fulatancin Kontagora, ko kuma Gwaggo. Gana ta dubi Batty ba tare da ta yi magana ba. Cikin rawar murya ta ce

"Me ya sa Inna ta zaɓe ni ta bani maita? Me ya sa taga nice fi dacewa na zama mayya a kaf zuri'arta? Yaaye mene maita do Allah waɗe mini?"

Ta saki wani kuka "Me ya sa muka zama mayu ni dake? Da kuma Inna? Baffana ma yana yin maita ko shi ba maye bane ba.... Me ya sa?"

"Yaaye ki waÉ—e mini batun gaskiya"

Cikin fusata Gana ta ce "Sai ki matse mini bakina na faɗa miki, ko kuma ki je kabarin Innar taki ki haƙe ki tambaye ta batun maitar ta amsa ki muga idan zata iya"

A ruɗe ta ce "Bani da ƙarfi, ni ba babba bace ba zan iya haƙo kushewar Innata ba, da zan iya taso ta daga kabarinta da a yau ba zan kwanta bacci ba sai na ji amsar tambayoyin da kaina yake mini, sai ta amsa mini abin da nake girma dashi yana addabata da ci mini nan ɗina" ta nuna saitin ƙirjinta hawaye na cigaba da zuba daga cikin idanunta ta ƙanƙame ƙafafuwan Gana. "Ni mayya ce na yarda, na yarda wallahi na yarda na amince" Ta runtse idanunta ƙirjinta na buɗewa yana yi mata wani irin bugu "Amma bana so, Yaaye bana son maitar nan, don Allah ki kai a cire mini bana iya bacci, bana son ganin kayan cikin mutane da abubuwan da suke ci, da jinin da yake gudana a jikinsu. Ki taimaka mini kar a sake korata daga wannan rugar idan gaskiya ta bayyana a bayan ƙaryar da muke rufe wa. Tsoro nake ji, fargaba nake ji, damuwa nake ji, tashin hankali nake ruskar kaina a ciki. Yaaye ki cire mini maitar nan bana so, ba zan iya cin mutum ba. Na shige su na lalashe."

Ta rusa wani irin gigitaccen ihu ta faɗi a ƙasa tana birgima da riƙe cikinta. "Wayyo ni Batty me gani har hanji na shiga uku na barinkaɗi"

Ganin tana shirin janyo hankalin jama'ar gidan ya sanya wuf Gana ta ɗauke kurwar Mado dake cikin wani tulo ta fice daga cikin gidan. Abin ka da rugar Fulani basu da ƙofa tuni ta bar unguwa tana yin tuƙar baƙi da ƙifta idanu, zuciyarta fal murna zata ci wata kurwar me zallar tsokar nama a jikinta.

Batty ta jima tana birgima da ihu da kuka tana kirin sunan Innarta da bata duniyar, ba ƙaramar azaba maitar kenan bata ba, da wata wahalar da bata saba da ita ba. Bayan ta yi me isarta ta miƙe tsaye tare da fitowa daga bukkar ta ɗan kewaye, cure jikinta ta yi waje guda tana rawa da juyi da katantanwa da surutai a hankali jikinta ya fara sauyawa zuwa kuliya baƙar ƙirin Idanunta mai matsagaicin ja ta yi shiru tana kallon rufin bukkokin Sadiatu, Kulu da Lami sai ta Dikko.
Chapter 39 · 0% Book details