← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 64

Sashe 60

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannu a hankali ya zame jikinsa daga nata, ya kwantar da ita a saman laddumar ya ja Hijab ya rufe ta. "Babban Yaya Innti?" Yaya ya juya ya kalle su da nutsuwa da fahimtar daya arowa zuciyarsa da jikinsa, ba don bai firgita ko ya zauce ba, sai don a yanzu shine wanda suke kallo a matsayin Innti ɗin, dole ya zama jarumi. Ya riƙo hannayensu cikin ƙasa da murya wacce take fita da ƙyar ya ce "Na san ku Musulmai ne, kuma dukkan cikakken musulmi an san shi da imani da Allah, tare da Mala'iku da mazanni, tare da imani da ƙaddara me kyau ko kasin hakan. Duk wanda bai yadda da ƙaddara ba, kai tsaye yana faɗa da Ubangiji ne, kuma imaninsa yana da rauni" ya yi jim kafin ya ɗan rufe idanunsa, fishaa kuma ya buɗe su.

"Jaheed, Jadid mun rasa Innti kamar yadda muka rasa Iftihal, kar ku yi kuka, domin yinsa yana saka mamaci cikin azaba, kar ku yi baƙin ciki, domin wanda ya halicci Innti shine ya ɗauki ranta, rayuwarta a wajansa ta fi wacce take yi a wannan gidan. Za ku iya cewa Allah don me ya yi muku haka? Idan ba Ubangiji ba, wane zai ɗauki ran uwa kuma ya ɗauki na ƴa a taƙin lokaci? Kuna da ikon question ɗinsa akan hakan? Ya kamata mu yi farinciki, Iftihal ta yi shahada, ta rasu a cikin ruwa, Innti ta rasu yayin da take ganawa da ubangijinta, ranar juma'a kuma"

Ya É—an fesar da iska "Akwai raÉ—aÉ—i tabbas, akwai É—aci, ciwo ne kuma a zuciya ta tafi ta bar mu dashi. Mu yi mata addu'a, kar ku yi kuka, idan ya zama dole ku zubar da hawaye" kallon Babban Yaya kawai suke yi, sun ji me ya ce kuma sun gamsu, amma tambayar da suke da ita, yaushe za ta sake dawowa rayuwarsu a karo na biyu a matsayin uwa mahaifiya? Suna son sake fitowa daga cikinta, su sake rayuwa da ita.

"Bango ya faÉ—i Yaya" cewar Jadid.

Ya É—ora da "Ni ya kamata na mutu ba ita..,"

"Shhha, ita Ubangiji ya yi niyya, domin ya gwada imanin da muke dashi, babu lokaci ina son a yi mata sallah a kaita gidanta yau"

Gabaɗaya zuciyoyinsu sun yi nauyin gaske, wani abu mai girma ya danne musu kirji, Jaheed da Jadid suka nemi hawaye suka rasa a idanunsu, rawa da kakkarwa da wata tsuma kawai jikinsu ke yi, basa ganin ko gabansu, su ka ji kamar basu taɓa walwala ko farinciki a duniya ba, komai ya ƙare.

Wata sabuwar rayuwa suke hangowa, tare da wata sabuwar ƙaddara me girman gaske.

"Jeka faÉ—awa Maman....

Jadid ya gane me Babban Yaya yake nufi, kamar an zare masa lakar jikinsa ya nufi gidansu Haysaam. Yaya ya miƙe ya nufi ɗakinsu. Yana shiga ya ja ƙofa ya rufe, wanwar ya faɗi a ƙasa ya dinga haɗawa jikinsa da bango, baya son yin ihu saboda kar su gane ya karaya ko kuma su yake hanawa kuka. Ya saka haƙori wajan datse harshensa, idanunsa suka zazzago, ya ji wa kan shi rauni a harshe. "Innti me ya sa? Za ki tafi ki bar Ana? Ke da kanki kike faɗin yadda take damuwa da ku ko kanta bata damu dashi ba, ke da kanki kike faɗar taurin kai da rigimarta, Innti ba zan iya da rigimar Ana ba, ba zan iya ɗaukan wannan nauyin ba, Abbaa ba zai iya kulawa da Ana ba, ba tare da kina a kusa damu ba, Innti ba zan iya faɗawa Ana cewa bakya duniya ba, wallahi ba zan iya ba, ta ya zan rufe mata wannan maganar? Ta ya zan iya wannan?"

"Abbaaa....

Ya ji muryar Ana ta kira shi da wannan sanyin nata, da wannan silent voice É—in nata

Ya juya kaÉ—an, sai ya ga har yanzu ba ta farka ba, amma sai kiran sunansa take yi. A hankali ya ja jikinsa ya matsa kusa da ita, sai ya ji tana surutai. "Abbaa kaga Iftihal ko, Abbaa wai ba za ta yi wasa dani ba da Innti za ta yi, Abbaa ka ga sun tafi sun barni suna mini dariya, Abbaa kalli kaya iri É—aya zan saka. Nima ka siya mini irin kayansu ka ji"

"No" ya ce cikin sauri yana girgiza kai.

"Ba za ki saka irin wannan kayan ba, ba yanzu ba, ba nan kusa ba in sha Allah Shetty" ya riƙota jikinsa gabaɗaya ya rungumeta sosai kamar zai mayar da ita ciki ya sake haifar ta haka yake ji, wata sabuwar soyayyar Ana ce me zafin gaske ta shiga huda zuciyar Yaya, wani irin hope, da wish tare da dreams me girma ne suka shiga yawo a cikin zuciyarsa. Dole ya ɗauke Ana ya kaita inda ake buƙatarta, inda za ta yi farinciki da jin daɗi, amma ba za ta iya farinciki ba idan babu Iftihal da Innti a cikin rayuwarta. Dole ya shafe mata tunaninsu gabaɗaya a cikin kanta da zuciyarta, ta yadda za ta mance ta yi rayuwa dasu. Saboda nutsuwar zuciyarta zai yi hakan.

A hankali ya sumbaci goshinta, ya sake sumbatar gefen kuncinta, a nutse ya zura yatsun hannunsa guda biyar cikin nata ya haÉ—e su gam. "Rayuwarki ta zama tawa, Abbaa ya zama naki ke É—aya, zan sadaukar da komai nawa saboda ki yi farinciki, sbd ke" ya yi shiru yana kallon fuskarta me kyau

Ya É—ora fuskarsa a saman tata ya ce

"Ina fatan ba zan zama mai laifi a gareki ba a sanda kika tuna matsayin Innti da Iftihal a rayuwarki, ina fatan ba za ki guji Abbaa É—inki ba. Rayuwata taki ce Shetty, ina rayuwa dominki ne a gidan nan shettyyy"

Ya ƙanƙameta for a while.

A hankali ya kwantar da ita, ya miƙe ya nufi wajan wata jakarsa ya ɗakko turare ya dawo gabanta, ya haɗe hannayensa biyu sai ga wuta ta kama ya saka turaren, ya fara shaƙa mata, cikin fitar hayyaci ta fara tari sosai ƙirjinta na ɗagawa sama, jikinta ya ɗauki rawa ta shiga girgiza, da ƙarfi ta yi ihu sai kuma ta kira sunan Allah, maganarta ta ƙarshe shine ambaton sunan Iftihal da Innti.

Jikinta ya ɗauki zufa ta wanke mata fuska ya miƙe ya fice. Yana fitowa Maman Haysaam da shi kan shi Yaa Sam da wasu matan maƙota suna shigowa cikin gidan, Maman Haysaam ta fashe da kuka tana salati.

Da aka sanar da Daada ƙin zuwa ya yi, sai Emama da Liya da Hanna ne suka shigo, suna fashewa da kuka. "Baiwar Allah, mace mai haƙuri da kawaici Allah Sarki Innti" a cikin wannan lokacin Jaheed da Jadid da Yaya suka sauƙewa Innti Kur'ani tare da Yaa Sam daya zama kamar jininsu. Babban yaya da kan shi ya yi wa Innti wanka, ƙamshi sai tashi yake a jikinta, ya sha kuka saboda duk inda ya juya jikin Innti, shatin dukan Daada ne. Ya zubawa ƙasan cibiyarta idanu, saboda zanen wani tambari daya gani, ya rasa kuma wanne tambari ne wannan? Ya wanke ta tas, ya shirya ta, da aka zo tafiya da ita sai ya samu kan shi da riƙe gawar ya kasa saki, da ƙyar Yaa Sam ya zame hannun Babban yaya. Jaheed tun bayan maganar Babban yaya ko tari ya kasa, idanunsa ya bushe gabaɗaya bai san me yake ji a ransa ba. Bayan an yi mata sallah, sanda aka binne Innti Jadid ya yanke jiki ya faɗi a jikin Babban yaya babu numfashi haka Jaheed.

***
Asuba a tasha ta yi wa Ahlam, ta shiga motar da za'a kaita zuwa Banue state. Ta yi kuka har ta gaji idanunta sun kumbura sosai, amma taja ji this is the only way, da zata iya samun damar cika burinta, zata samu damar amsa sunan cikakkiyar ƴar jarida kuma ƴar gwagwarmaya. Ta san Engineer dole zai yi baƙinciki, amma tana hango farincikin da zai yi idan ya ganta ciki matsayin da za ta taka. "Liman?" Ta ƙira sunansa a hankali tana dafe ƙirjinta, ta so Md, ta ƙaunaci Md, kuma tana fatan rayuwa dashi ta har abada, za ta dawo tabbas.

Ta lumshe idanunta, tana sauraran waƙar “Im coming home" tare da binta a hankali.

6:00 motar ta ɗaga tare da barin tashar, Ahlam ta ji kamar rayuwarta ta bari a kano kacokan, dukkan wani farinciki da jin daɗi sannu a hankali ta ji suna yin ƙaura a jikinta.

Yana daga bakin ƙofar hannunsa riƙe da casbaha ya ce "Wai Jiddah tashin baby ne haka?" Daga cikin ɗakin Anty Jiddah ta ce

"Abban Mufeed, Ahlam bata É—akin fa"

"What?" Ya ce yana shigowa da sauri.

Aunty Jiddah ta ce "Wallahi, shigo ka tayani ganin ikon Allah, har banÉ—aki bata ciki fa"

Engineer ya shiga duddubawa, ya fita waje ya shiga kiran sunan Ahlam amma shiru, duk inda suke expecting ganinta bata nan. Da aka mira me gadi yana duba gate ya ganshi a buÉ—e, gaban Engineer ya faÉ—i, hankalinsa ya tashi sosai. "Abban Mufeed ko dai kidnapers ne suka shigo suka É—auke Ahlam, da za ta kwanta bacci sai da ta yi mini sai da safe fa. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Engineer ya ce "Kidnapers?"

Ya girgiza kai "Kuma su É—auki iya baby kawai? Duk mutanen gidan sai ita kawai?"

"Abin ne da ɗaure kai, amma ka ƙira Asad ka ji, ko suna tare da ita da" ya kalle ta ya ce

"Jiddah, kin san me kike nufi, by this time ki ce wai Ahlam na tare da wani? GabaÉ—aya yaushe aka idar da sallar Asuba ne?" Ta ce

"Naga mijinta ne, ba abin mamaki bane" Ance ba'a ƙin ta mutum sai ya juya zuwa cikin gidan kai tsaye ɗakinsa ya shiga ya nemi inda ya ajjiye wayarsa, number Md kuma Liman ya nemo, a ringing ɗin farko ya ɗauka kamar me zaman jiran ƙiran ya ce "Wify, ina kika ajjiye wayarki kika ɗauki tasa?" Jin hakan ya saka Engineer dafe kan shi da ƙyar ya ce "Asad, Engineer ke magana" Liman ya yi ƙasa da murya ya ce "Afuwan Yaya, good morning ya hanya?"

"Allahamdulillah. Nace Ahlam fa?"

"Ahlam" Liman ya maimaita a kan harshe, ya kuma kasa bawa Engineer amsar tambayar da ya yi masa domin bai fahimta ya san by now shi da ita ai suna tare a hanyar Abuja.
Chapter 60 · 0% Book details