← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 64

Sashe 61

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Engineer ya ce "Asad, why? Ai ka bari a yi bikinmu me ya sa zaka É—auki yarinya ka tafi da ita? Har ta kwana a wajanka, this is wrong" again, Liman shiru ya yi saboda wani shock da tsoro kuma da ya ratsa masa cikin zuciyarsa. A hankali ya ce "Wajena?"

Ya ɗora da "ta ce za ku je Abuja, har ta nemi izinin tafiya a wajena, Yaya ya zan ɗauke ta ta kwana a wajena, bayan a gida nake rayuwa ban taɓa yi nini a hotel ba. I thought ma ita ta kira da lambarka" Engineer ya ce

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"

"Lafiya menene ya faru?"

"Asad, bamu da yan'uwa a Abuja, ba mu da kowa a Abuja, asalinmu Æ´an Maiduguri ne, a sanadin boko haram muka rasa Æ´an'uwanmu, Ahlam ba ta da kowa da za ta ziyarta idan ma akwai suna rayuwa ba mu san ina suke ba, Ahlam ita ta rage mini, nima ita kawai nake da ita, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Ko wani abu ya faru ne wanda ban san dashi ba? An shigo har gida an sace mini baby, su waye wannan? Me ta yi musu? Ina baby take yanzu wanne hali za ta shiga ne don Allah?" Liman ya yi shiru.

A hankali ya ce "Bari na zo gidan Yaya"

Ya kashe wayar.

Engineer da ƙyar ya ja jikinsa zuwa cikin gidan ya zauna saman kujera kan shi a ƙasa, wasu hawaye masu zafi suka shiga bin fuskarsa, duk yadda yake tunanin abin da fasalta shi a zuciyarsa ya kasa fahimtar cewa she run away from the house, zuciyarsa ta cunkushe ta shiga buga masa. Anty Jiddah ce take sakkowa daga saman bene wajan faɗin "Engineer ga abin da Ahlam ta bari akan gadonta, tabbas gudawa ta yi, amma yarinyar nan ba ta kyauta mana ba, idan auren ne ba ta so me ya sa ba za ta faɗa ba, sai ta ɗauki hanya ta gudu ta bar gida? Haka aka ba ta tarbiyya ko haka shine mafita a gare ta, ina za ta? Ina take fisabilillahi?" Ya amsa takadda har biyu, ɗaya an saka sunan Yaya a jiki ɗaya kuma Liman, wanda yake nuna tabbacin bashi da ikon dubawa balle ya karanta. A hankali ya buɗe tasar ta fara karantawa inda ta fara rubutun da; "Yaya zan tafi ba tare da yadda da izininka ba, saboda na san ba za ka amince mini ba, kai ba kawai Yaya bane a wajena, kai ne uwa kuma uban da nake gani ƴan'uwana gabaɗaya. Ina son ka sosai ina gudun ɓacin ranka, na kuma amince da auren da ka yi mini saboda ina son Asad sosai Yaya, zan kuma dawo gare ku a kai ni gidansa na aure na yi rayuwa kamar yadda kowacce take yi a gidan mijinta. Ina da buri sosai akan aikina, ina son aikin jarida Yaya ina jin ƙaunar aikin a jinin jikina, ina son na kawo sauyi a harkar jarida musamman a ɓangaren mata Yaya. An yi taron karrama ƴan jarida ban fuskanci komai ba sai baƙinciki da baƙinciki, na yi kukan da zuciyata ta kusa samun matsala, ban taɓa takaicin nakasar da nake da ita ba sai yau. Na tafi Yaya, zan dawo a lokacin dana amsa sunan ƴar jarida cikakkiyar, zan dawo idan na samu ɗaukakar da nake fata, zan dawo da abin mamaki kuma bazatar da duniya za ta yi mamaki da ita. Kar ki yi mummunan tunani a kaina, zan tsare kaina da mutuncina ba zan taɓa yin abin da zai taɓa ƙimata da taka ba. Ka yi haƙuri Yaya ka yafe mini kuma ka yi mini addu'a, ka bawa mijina haƙuri ka rarrashe. Ahlam Abdallah Kurmi"

Tun kafin ya gama karantawa idanunsa yake zubar da hawaye, ya ji kamar ya samu matsala da zuciyarsa da kuma jikinsa, ya yi shiru yana sauraran bugun da zuciyarsa take. Aunty Jiddah ta saki salati tana fashewa da kuka. "Ahlam me ya sa za ki mana haka, duk irin abin da za ki fuskanta ba gwara kin zauna kusa damu ba?"

Muryarsa mai sanyi ta sauka a cikin parlourn yana yin sallama, shine na farko sai Mu'allim da yake bayansa, hannunsa manne da kanuna yana sanye shadda mai ruwan duhu data amshi jikinsa sosai ya rame ya sake haske. Liman kuma tattausar Jallabiya ce a jikinsa wacce ta yi kwance a fatar jikinsa, tunda ya je masallaci Baffa ya ja su jam'i ya dawo gida ya ji wannan tashin hankalin kasa motsi ya yi, da ƙyar ya iya faɗawa Al'ameen, duk da Al'ameen ɗin babu lafiya shine ya yi ƙoƙarin yin driving nasu zuwa.

"Barka da asuba" cewar Mu'allim yana miƙawa Engineer hannu su ka yi musabaha ya gaida Anty Jiddah. Liman kasa magana ya yi

"Gashi, saƙon da ta bar maka"

Liman ya amsa ya buɗe, shima a nutse ya fara dubawa da; "To my one and only Zauj, Mr Asad Hafiz Hafiz Hafiz. Na rubuta maka wannan a lokacin da bani da wani zaɓi bayan abin da nake jin zan aikata shi ne daidai. Na rubuta maka wannan a sanda zuciyata ta cika da so da ƙaunarka, yes, ka fahimci ina son, kusan kai ne confidence ɗina a Bright Fm, ina tsintar kaina cikin tsananin kishi idan na ganka tare da Yussy... Na maka ƙarya na ce zan ji Abuja haƙiƙanin gaskiya ba mu da kowa a can, na yi haka ne kar na tafi da haƙƙinka na fita ba tare da izininka ba. Abin da Yussy ta mini zai iya saka mini ciwon zuciya, na kasa haƙura na kuma kasa mancewa. Na ji sanarwa BBC a jiya da Hausa France International RFI suna neman wani sabon tarihi da za su wallafa a ranar Hausa ta duniya, na tafi zuwa ga neman abin da zai dace da su, ina da tabbaci za su buƙata kuma duniya za ta san dani a wannan rana, ta HAUSA INTERNATIONAL DAY. Wallahi Liman i so much love you, I love you with all my heart and soul, I love you to the Extra Liman. Zan kare maka kaina da mutuncina, za ka same ni yadda kowanne miji yake samun matarsa, ba zan taɓa kallon wani namiji a bayanka ba, ina fatan kafin na dawo zaka soyayyata a cikin zuciyar danginka, ina fatan daga nan har na dawo na tsaya a gabanka mijina ba za ka taɓa kallon wata mace da irin kallon da kakewa Halimatul Sadiya ba. A ranar dana dawo a wannan rana ba zan kwana gidan kowa ba, sai gidan mijina Mr Asad Hafiz Hafiz fa, a gadonsa zan kwana rungume a jikinsa. I love You Md, Liman, Asad. I'll be back sooner or later bye. Ur wife Ahlam"

Ya naÉ—e takaddar ba tare da ya ce komai ba, wannan shirun kuma har gwara ya ce wani abu ko babu yawa. Engineer ya ce "ka yi...,"

"No need Yaya, i can wait for her"

Ya yi shiru yana jan numfashi da sauƙewa yana jin zuciyarsa ta yi masa nauyi sosai.

"Bani da wata mata a duniya sama da Halimatu, zan jira ta, zan jira ta jira na iya adadin da za ta É—auka kafin ta dawo Yaya"

"Amma Asad....,

"No please, na fahimci uzurinta, akwai wauta da ƙuruciya a tattare da ita. Ka yi addu'a za ta dawo da nasarar da take fata, ina addu'ar Ubangiji Ya sa ta je a sa'a. Ni na san ba za ta iya jurewa ba tare da ta yi notifying ɗina ba, zan jira ranar daga sanda ta neman a sannan zan yi tracking numberta zan bita zuwa inda take" ya yi ƙasa da kan shi a hankali ya miƙe tare da kama hannun Al'ameen da yake jingine da jikin Liman ɗin yana riƙe da hannunsa ya ce

"And please, kar ka yi cigiyarta, saboda tana da ɗaukakar da zuwa gaba zai iya taɓa ɗaukakar data samu. Thank you Yaya"

Engineer yana jin tausayin kanshi, amma ganin Liman ya ji kamar shi ne abin tausayi, yana son Ahlam sosai yana ƙaunarta Allah ya bashi haƙuri da juriya kawai. Anty Jiddah ta kawowa Engineer shayi ya ce "Ga tea ɗin"

"Bana jin yunwa Hawwa'u"

Ta yi shiru na wani lokaci.

Wayarta ce ta fara ringing, ganin sunan matar abokin mijinta ya saka ta É—auka ta ce "Firdausi ina kwana ya kwanan yaran?"

Ta cikin wayar Firdausi ta ce "Alhamdlh Jiddah, daman akan maganar ƴar aikin da kika ce kina so ce, ga wata an samu, ba su jima da zuwa Kano ba, wai ƴar gudun hijira ce daga Barno shine na ce bari na kira ki" Jiddah ta yi jim ta juya ta kalli Engineer ta ce "Firdausi zan kira ki zuwa anjima, amma batun aikin nan kamar na fasa ɗauka fa, idan na yanke shawara za ki ji ni in sha Allah" kashe wayar ta yi, ta shiga lallashin Engineer daya lumshe idanunsa yana ta kokawa da numfashinsa ya kasa jure rashin Ahlam a kusa dashi. Wayarsa ya ɗauka ya kunna data ya shiga page ɗinta ko zai ga ta yi update na wani abu, madadin hakan sai ya ga vedion Ahlam ne tana kuka sosai kanta a ƙasa, wacce ta yi posting ta saka caption na. "Ƴar jarida Ahlam Abdallah Kurmi, a wajan taron ƙarshen shekara na karrama ƴan jaridu. Tana yin kuka saboda bata samu award na Outstanding Journalist ba"

Vedion ya je viral, ya samu a ƙalla viewes wajan 5M. Ga sharing da comments kamar hauka, ya miƙe da ƙyar yana shirin fita daga gidan ya yanke jiki ya faɗi a tsakiyar parlourn.

***
TIVLAND 1976
Chapter 61 · 0% Book details