Sashe 24
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Me ya sa kamar bakya so na ne Innti?" Ta faÉ—a da rawar murya
Bata farfaɗo ba wasu kalaman na Ana suka sake cakar zuciyar Innti da yi mata wani irin rauni me zurfi. Da rawar murya Ana ta ce "Naga kamar bakya so na ne, a tunanina abin ƙwarai na yi ai, abin azo a yaba. Taya kike tunanin zan jure ganin ana cin mutuncinki da na dinga ganin haka gwara na bar muku duniya, gwara na bar wa mijin naki duniyar"
"Kept quiet Aysha!"
"Ki bari na faɗa Innti,naga kamar kin fi son mijin naki akan yaran naki, naga kamar ya fimu muhimmaci a rayuwarki. Ko babu komai muna saka ki farinciki, muna sawa ki yi alfahari damu, muna sawa ki ji mu yaranki ne da suka fito faga cikinki" ta juya ta kalli Daada da yake tamboɗe ta nuna shi da yatsa ta ce "Shi ɗin wanne hakƙi naki ya sauke, mene abu ɗaya da ya yi miki wanda kike jin ya cancanci amsa sunan miji da uba?" Innti ta juya ta kalli yaran nata gabaɗayansu ta ce
"Ta ce wai na bata amsa?"
Duk suka zubawa Innti ido ban da Ana. "Me ya sa ba zan so wanda ta silarsa na samu alarbarkatattun yara irinku ba?" Wani irin murmushin takaici Ana ta yi tana sake watsa idanunta akan Innti kafin ta girgizar kai ta yi baya tana ƙoƙarin zubewa a wajan saboda ciwon da kanta ke yi mata. "Uhm... Uhm haka ne"
Sai ta ce "Mashayi, ɗan giya, me fifita karuwarsa akan ki, me aibata yaranki, me yi mana fatan mu farraƙa, ɗan caca irin shi kike so, kike ƙauna har haka a ranki?"
"Innalillahi! Aysha;....
"Ki so mijinki Innti, ni kinga ubana nan" Ta nuna Babban yaya dake tsaye ya rungume hannunsa a ƙirji idanunsa sun yi jajur ilahirin jijiyoyin kan shi sun fito sosai a saman goshinsa dukkan wata gargasa da Ubangiji Ya halitta a jikin Babban yaya sai data mimmiƙe daga fatar jikinsa, ya dunƙule hannayensa hagu da dama har wata power ta tashi a damtsen hannunsa buɗaɗɗan jikinsa me ɗauke da gaɓoɓi suka gama bayyana. Wani abu ya tsarga masa lokacin da Ana ta kira shi da sunan uba, mahaifi wani irin responsibility ta ɗora masa na kulawa da ita, bai mata alƙawari ba, amma yana da tabbacin zai amsa mata, zai bata dukkan wata kulawa da uba yake bawa ƴarsa. Ji ya yi zuciyarsa tana rarrabewa wani abu yana shiga cikinta.
"Daga yau Babban yaya shine Abbaana, shine ubana, da sunansa zan dinga amfani har abada idan ya zama dole na yi amfani da sunan namiji a jikin sunana kenan"
Sai a lokacin ta ji kamar numfashinta na season a ƙirjinta yana kakkatse mata. "Ki so mijinki Innti, ina fatan soyayyar da kike masa ba zata ja rauninki zuwa ga tsine mana ba kamar yadda mijinki ya yi....," a hankali ta ce "You're my world Innti"
BuÉ—e baki Innti ta yi zata hau kan Ana da faÉ—a sai ta yi saurin sauya harshe daga faÉ—an zuwa addu'a a zuciyarta ta shiga yi;
"اللَّهÙمَّ Ø§Ù‡Ù’Ø¯Ù Ù‚ÙŽÙ„Ù’Ø¨ÙŽÙ‡ÙØŒ ÙˆÙŽØ£ÙŽØµÙ’Ù„ÙØÙ’ ØÙŽØ§Ù„ÙŽÙ‡ÙØŒ وَاجْعَلْه٠مÙÙ†ÙŽ الْبَارّÙينَ بÙÙŠØŒ وَاغْÙÙØ±Ù’ لَه٠وَارْØÙŽÙ…ْهÙ. Ma'ana. (Ya Allah ka shiryar da zuciyarta, ka gyara halinta, ka sanya ta cikin masu biyayya gare ni, ka gafarta mata ka yi mata rahama).
Juyawa Ana ta yi itama da niyyar barin wajan. Sai ta yanke jiki ta faɗi a wajan. Yunwar da ta ci ƙarfinta da ciwon da gefen kanta ke yi mata ne ya haddasa mata hakan. Kafin ta miƙe zaune Daada ya saka ƙafa ya taka mata ruwan cikinta, tsananin zafi da azaba sai gani sukai fitsari yana bin ƙafafuwanta a hankali ta zubawa Daada ido, kallon da yake nuna tsoro da mamakin kiran shi da Uba. Kafin numfashinta ya ɗauke ta miƙa hannunta da ƙyar zuwa ga Babban yaya ta ce "Zan mutu Abbaa ka ɗauke ni"
"Cikina Abbaa....
Bata iya ƙarasa faɗa ba saboda wani duka da Daada ya kai ruwan cikin Ana a karo na biyu daidai lokacin da numfashinta ya tsaya. Da wani irin fitar hayyaci Babban yaya ya saka haƙora wajan datse harshensa jikinsa na tsuma da kakkarwa ya yi kan Daada ya saka hannunsa guda ɗaya ya damƙo wuyan Daada ya ɗage shi sama, ƙafafuwan Daada suka fara lilo a ƙasa, wata sabuwar kururuwa Innti ta yi saboda abin da bata taɓa zato bane ya faru. "Yaya mene haka, ubanka ne mahaifi ka sake shi, muddin nina ɗauki cikinka wata tara, na shayar da kai nono wallahi idan baka sake shi ba ban yafe maka ba, ya zama na ƙarshe a rayuwa da za ka yi tunanin taɓa jikin mahaifinka"
Babban yaya bai ko kalli Innti ba jikinsa kamar an jona masa wutar lantarki haka yake tsuma, ya manne Daada da jikin bango wanda ya fara hango kabari kafin ya yi cilli dashi zuwa gefe guda.
A gigice kuma cikin wani slow ya yi kan Ana da yana durƙushewa akan ƙafafuwansa ya yi zaman raƙuma ƙoƙarin magana yake yi ya kasa sai laɓɓansa da suke rawa da wani sounds dake fita ta cikin gurnaninsa. Rabon da su ji sautin muryarsa ta fita har haka sun mata, yadda yake ƙoƙarin kiran sunan Ana kamar yadda ya sama idan yaso ya saka Innti saurin yin baya tana dafe ƙirjinta. Tashin hankali da tunanin Iftihal zata rasa Ana ya kasa ɗaukan zuciyarta ta yanke jiki ta faɗi cikin sauri Jaheed ya taro ta jikinsa yana kiranta.
Kakkar haka laɓɓansa da harshensa suke masa rawa ya zubawa fuskar Ana ido a cikin saman kan shi ya ji ya kira sunanta da ƙarfin gaske.
"Shettyyy...
Da wani irin slow Babban yaya ya rungumota jikinsa gabaÉ—aya yana bubbuga fuskarta yadda Jaheed ya wanzu yana kiran sunan Iftihal. "Jini... Jini a jikin Ana"
Jadid ya ce a firgice shima zuciyarsa na ƙoƙarin tsayawa da aiki jikinsa na wani irin rawa da kakkarwa idanunsa na ƙaƙƙafewa.
"Na rasa yarana na rasa aminai na" Gabaɗaya neman ficewa daga hayyacinta Innti take shirin yi saboda tashin hankali. Tsam kuma Babban yaya ya rungume Ana a jikinsa, gashi jikin nasa sanyi sosai kamar na maciji idanunsa suka rikiɗe tare da yin blue sosai wani haske na fita daga cikinsu sai girgiza kai yake yi. Ya rasa abin yi a nutse ya saka tafukan hannunsa wajan riƙo fuskarta yaga babu alamar numfashi a tattare da ita babu alamar tana jin shi, babu alamar akwai rai a jikinta. Da wani irin rawar jiki data zuciya ya manna bakinsa a goshinta ya sumbace ta.
Daidai lokacin Haysaam dake ta sallama ba'a amsa masa ba ya faɗo cikin gidan, Jallabiya ce a jikinsa ash wacce tabi farar fatarsa jikinsa ta kwanta bai iya tsayawa tambayar mene ya same ta ba ya kalli Jaheed ya ce "Jeka ka tashi Mas'ud ya ɗakko napep ɗinsa yanzu" yana faɗin hakan ya sunkuya ya sunkuci Ana a jikinsa ya yi waje da ita. Daidai nan Iftihal ta farka tana fasa wani irin gigitaccen ihu da kiran sunan Ana. Daada da yake numfashi da ƙyar yana riƙe wuyansa da yake jin kamar ya kumbura ya yi baya yana faɗin "Allah Ya sa ta mutu na huta, daman sun yi mini yawa ai ba zata taɓa albarka ba, Innti duka yaranki ba za su taɓa yin albarka ba, tsinannu ne" Babban yaya ne ya miƙe yana tattare hannunsa ya nufi hanyar ficewa daga cikin gidan. “MURAAD†cak ya tsaya bai juya ba saboda baya son taga sauyin da ya yi
"Muraad ka dawo mini da Shalele da ƙafafuwanta, Muraad ka dawo da ƴarka"
"Itama ta bashi Shetty kenan? Ta yarda shine uba kuma mahaifin Anarta?"
Ya yi jim.
"Muraad"
"In sha Allah" ya ce a taƙaice a karo na biyu bayan kiran sunan Ana da ya yi. Yana faɗin hakan ya saka kai ya fice yana ɗan ranƙwafar da kan shi abinka da dogo
Yana fita ya tarar har an fito da Napep É—in, Mas'ud ba zai iya kai su ba, don haka Yaa Sam ne ya shiga gaba Babban yaya ya zauna a baya rungume da Ana suka tafi asibiti mafi kusa. Jaheed ya koma gida. Emergency aka amshi Ana babu ko biyar a hannun Babban yaya, kuÉ—in da Haysaam ya tanada domin tafiya Lagos dasu a gobe sune ya fito dasu ya bayar aka siyo kayan aiki dasu, suka jira a reception su kuma.
***
KANO/ MAITAMA SULE GRA
BAFFAS ESTATE.
An sanya sunan unguwar MAITAMA SULE ne domin girmama fitaccen ɗan siyasar Kano, Yusuf Maitama Sule wanda aka fi sani da Dan Masanin Kano. Ya kasance babban ɗan siyasa, jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma mutum mai daraja a tarihin ƙasar. Saboda irin gudummawar da ya bayar, aka sanya masa wannan yanki mai daraja. Maitama Sule GRA yana cikin sabbin yankunan birnin Kano. Yana kusa da manyan hanyoyi da wuraren gwamnati Tsarinsa na “GRA†(Government Reserved Area) yana nufin an tsara shi ne musamman domin manyan mutane da attajirai tare da masu faɗa a ji na faɗin Jihar Kano. Gidajen MAITAMA SULE GRA mafi yawansu manyan mansions masu tsada ne wanda aka yi su da arziƙi bada kuɗi ba. Duplex da gidajen zamani Filayen suna da girma sosai (ba kamar tsofaffin unguwanni ba) Yawancin gidaje suna da: CCTV tsaro na sirri,lambuna (gardens) a matsayin arziƙi ana ɗaukanta matsayin unguwar masu kuɗi sosai (elite area) Mazauna sun haɗa da: ƴan kasuwa masu arziƙi ƴan siyasa manyan ma’aikatan gwamnati. Farashin gida ko haya a nan ya fi yawancin unguwanni tsada.