Sashe 51
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanda Innti taga Iftihal bata san lokacin ta saki wani irin kuka ba, ta riƙe Babban yaya jikinta na wani irin rawa da kakkarwa kamar mazari. "Na shiga uku Yaya, me na aikata wa Iftihal? Me yake damuna ne, me ya sa nake biyewa Daada wajan saɓon Ubangiji? Ba haka na yi niyya ba, abin da nake niyyar yi daban abin da nake aikatawa daban, ina jin kamar narasa kaina yaya. Na yi asara a matsayina na uwa, na yi saɓon Ubangiji"
Wani irin kuka take yi har da shassheƙa, idanunta kamar za su fito waje. "Na rusa rayuwar yarana, wani ciwo nake ji a ƙirjina Yaya" gam yaya ya rungume Innti a jikinsa idanunsa sun yi jajur wani irin ruwa ya taro a cikinsu ya kasa cewa komai. Ana ƙuri haka ta zubawa Iftihal ido, zuciyarta na buɗewa haka ƙirjinta, idanunta na soyewa na rashin sanin dalili ko hawaye ya kasa fita daga cikinta. Wanka Innti ta yi wa Iftihal ta gasa mata jikinta, data duban jikin yarinyar bata san sanda ta sake sakin wani ihun ba tana rungume Iftihal. Ta bata magani ta kwantar da ita bacci ya ɗauke ta.
Cikin dare Iftihal ta riƙe Ana saboda a jikin Ana ɗin take, ta shiga bata labarin abin da Baita ya yi mata, ta ɗauki wani abu ta damƙawa Ana a hannunta. Ana ko tari bata yi sai ƙanƙame Iftihal kawai ta yi a jikinta.
Wajejen ƙarfe uku na dare ya banko ƙofar ya shigo, hannunsa riƙe da kwalbar giya yana layi da tangaɗi, kamar yadda ya saba yau ma ɗin tsirara ya shigo, yana shigowa gaban Innti ya yi mummunan faɗuwa. Tana zaune akan ladduma tana istigifari, jin shiru ya saka Innti juya wa dam! Ƙirjinta ya buga jikinta na wani irin rawa da ɓari ta miƙe tsaye, ganin Daada ya gurfana a gaban Ana ya yaye rigarta yana ƙarewa ƙirjin yarinyar idanu, maganganun da sukai da Alhaji Baita yake tunawa, ya faɗa masa hanyoyin da zai bi idan yana so ya yi kuɗi ya shahara ya nemi duniya, dole sai ya kasance da Ana.
"Daada!" Ta kira sunansa da ƙarfi. "Innalillahi raji'un mene haka?"
Kafin ta ƙarasa ya saka hannu ya damƙo ƙirjin Ana da suke tubarakallah, bata saka rigar mama saboda ciwon ƙirji take yi.
Duk abin da yake faruwa akan idanun Iftihal data farka ta yi sallah ta dinga yi wa Daada addu'a domin har zuciyarta tana ƙaunarsa.
"Innti ina son na kasance da Ana" ya sake faɗin "Zan kasance da Ana a wannan daren ina kwaɗayinta, zan yi arziƙi idan na kasance ta"
Kau! Kau! Kau! Kau! Innti ta jerawa Daada maruka huɗu a fuskarsa lokaci guda, tana wani irin huci ta ce "Wannan ya zama na ƙarshe, hatta Iftihal ba zata koma inda ta fito ba, idan ka shirya na shirya shege kafasa" ya ji zafin marin har wuta ya gani.
"Muddin ina raye sai na kusanci Ana!"
A firgice Iftihal ta fito daga É—auki ta yi wa Daada wani irin kallo, hijabi ne a jikinta wanda ta yi sallah, duk irin masifar da ake Ana bacci take sosai. Ga wani duhu a tsakar gidan babu nepa, "Sai na kusanci Ana!" Shine ya dinga yawo a zuciyar Iftihal.
Yadda ta kasance me shegen tsoran duhun dare da abin da yake cikinsa, hakan bai hanata fitowa tsakiyar tsakar gidansu ba, ta dubi gabas da yamma, kudu da arewa tana jan wani irin ƙarfaffan numfashi daga baki ya sauka a ƙirjinta, jiki na rawa ta zube a ƙasa bayan ta kalli gabas ta yi Sujjada ta ɗago, hannunta ta miƙa zuwa sama idanunta na kallan sararin samaniya gangar jikinta na fuskantar Alƙibila cikin sarƙewar harshe ta fara magana. "Allah Ya tsinewa babana, Allah ka yi sanadin mutuwarsa yau, Ubangiji ka haɗa shi da ajalinsa a cikin daren nan, idan ya yi tsayin rai, Allah ka hana babana jin daɗin rayuwa, ka yi masa farraƙu da farincikinsa, Allah ka sanya babbar mota tirela ta yi awon gaba dashi yadda ko ƙashinsa ba za'a gane ba, Allah ka sanya bilo inci goma ya faɗuwa babana a kan shi idan yana bacci, Allah ka haɗa babana da ƴan daban da za su sassara naman jikinsa, Allah ka ɗorawa babana ciwon zuciyar da zai ajalinsa, Allah ka hana babana shiga Aljanna, ka yi masa iyaka da walwala, farinciki, da jin daɗin rayuwa...," bata ƙarasa faɗa ba, Daada ya sunkuci Iftihal baya ganin ko gabansa bai zarce ko'ina ba sai cikin rijiya, cumdum haka ya cilla Iftihal a cikin rijiyar.....
*H I Y A A M*
Page 14: The Visitors
Bright pens
Yota/001
I Dedicated this book to you Pixie.
Kasa motsi Innti ta yi saboda wani abu daya tsaya mata a ƙirji, ya daki zuciyarta ta kasa ko jan numfashi saboda tashin hankalin ganin yadda Daada ya cila Iftihal a cikin rijiya. Numfashinta ya shiga kakkatsewa jikinta ya ɗauki rawa idanunta rufe ta fasa wata iriyar ƙarar data farkar da Ana daga bacci ɓarawo daya ɗauke ta. Da ƙyar ta buɗe idanunta, ta miƙa hannunta zata taɓo Iftihal saboda numfashinta data daina ji yana sauka a fuskarta, wayam babu Iftihal.
Ta juya domin ganin ina ta Iftihal take, sai taga ashe a tsakar gida bacci ya É—auke ta, bayan ta samu ta yi bacci, ita kuma Innti ta kira ta, kiran daya saka bata koma É—akin ba. "MahaÉ—ita....
Ta kira sunanta da muryarta me sanyi, sai ta yunƙura ta miƙe tsaye, ita da fari ihun Innti a mafarki ta ji shi, sai ta ɗauka ko Anum ce? Tana ƙoƙarin shiga ɗakin Innti ta sake sakin wani ihun tana faɗin "Ka cilla mini yarinya a rijiya Daada, shikenan ka kashe mini Iftihal"
Dam! Ƙirjin Ana ya buga da matsanancin ƙarfi, sai Idanunta ya fara dishi-dishi tun kafin ta tabbatar da abin da kunnuwanta suka ji, da wani irin sauri ta juya taga Innti a tsakar gidan wajan bakin rijiyarsu. Ta juya ta kalli Daada da ya yi baya yana sake tangaɗi ya ce "Au duk gargaɗin da na yi mata bata jiba shine ta dawo mini gida? Ni zata jawa jarfar Alhaji Baita? To ga sakamakonta nan" Ya yi shaƙuwa yana fashewa da dariya.
"Innti ai tunda kika haifi yara ba za ki taɓa jin daɗi a wajena ba, tun a cikin Muraad na faɗa miki ki tsayar da haihuwa kikai burus dani, kullum sai dai ki dinga haihuwa kamar akuya? Bani da ra'ayi ƴaƴa bani da burinsu"
Innti bata da lokacin tsayawa ta ji surutan Daada sai ta juya da sauri zuwa É—akin yaran
"Yaya, Jaheed ku fito.....
"Muraad kana ina?"
Jikinta duk rawa yake yi.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Ta ce tana dafe ƙirjinta tana jin kamar zuciyarta ce zata faso ƙirjinta saboda nauyin da ta yi a ƙirjinta da kuma yadda take buga mata tare da yi mata motsi tana fitar da wani irin numfashi.
"Innti....,
Ta kasa maganar tana ƙanƙame jikinta da tsoran yin tambayar da tsoran abin da za ta ji. Idanunta kamar za su faɗo saboda wani irin girma da suka yi suka zazzago Ana ta ce "Ina mahaɗita? Ina take? Akwai abubuwan da take faɗa mini wanda bata kammala ba ta yi bacci, Innti ki nuna mini mahaɗita tana ina?" Innti ta kasa amsa Ana, sai kurma ihun sunan Babban yaya take yi da Jaheed. A firgice Jaheed ya fito sanye da Jallabiya, ya bar Jadid a cikin ɗaki. Jaheed ya kalli Innti.
Ya ce "Innti lafiya? Wani abu ne ya faru?" Ya ce a tsorace
"Ya cilla Iftihal a cikin rijiya...
"Ya saka mini yarinya a rijiya"
Ta fusgo Jaheed zuwa gabanta ta ce "Jaheed na shiga uku, na shiga uku, na kashe ƴata da hannuna na rasa Iftihal, na rasa yarinya me haƙuri da biyayya" ta matse kafaɗunsa ta ce "Ina Yaya? Ina Muraad yake Jaheed" He can't believe it, ya ji me Innti ta ce tabbas, ya kuma san bata ƙarya, ya rasa dalilin da hujja na rashin yadda cewa Daada ya cilla masoyiya a rijiya, Iftihal ɗinsa? Abokiyar wasan shi. Ya yi cak ya kasa motsi, ya ƙurawa Innti idanunsa da sukai wani irin juyawa a karo na farko. Ganin shima kamar ya rasa kan shi ya saka Innti matse kafaɗunsa ta ce "Jaheed ina Yaya? Iftihal a rijiya, kar na rasa Ayshatuna"
"Babban yaya baya É—aki"
"Innalillahi!" Tana dafe kanta.
Jaheed ya nufi rijiyar ta yi saurin riƙe shi tana girgiza kai. "Kar ka shiga Yaa Jaheed, ba zaka iya ba, rijiyar akwai zurfi, kar na rasa ku gabaɗaya" ta furta tana haɗiyar zuciya. Jaheed ya ce "Innti jinkirin zai saka wani abu ya faru, sai yaushe za mu jira?"
"Mu jira hukuncin ubangiji"
Ana tunda ta ƙurawa rijiyar idanu bata ko ƙiftawa, ko numfashi ta gagara ja da saukewa. Da wani irin yanayin tashin hankali idanunta rufe ta nufi rijiyar tana ambaton sunan Iftihal, ganin Ana na shirin faɗawa rijiyar ya saka Innti riƙota ta matse ta a jikinta. "Wallahi mutuwa zan yi idan na rasa mahaɗita, ki bari na shiga zan ceto ta, na miki alƙawarin babu abin da zai same ni, ki yarda dani Innti. Zan iya kamar yadda Abbaa zai iya" wani surutai take babu kan gado a ciki, idanunta rufe jikinta ya ɗauki rawa. Innti ta girgiza kai tana sake riƙe ta.
"Yaya ina ka shiga? Kana ina Muraad" Innti ta ce da nauyin zuciya, duk irin kukan da Innti take yi babu maƙocin daya shigo, hatta Yaa Sam da yake kodayaushe idanu biyu Allah bai nufe shi da jin abin da yake faruwa a gidansu Ana ɗin ba, Salati kawai Innti ke yi ta ƙanƙame Ana ta shiga kokawa da ita ganin yarinyar na shirin ƙwacewa, daga cikin ɗakima jikin Yaa Jadid ya rikice.
***
TAJMAHAR PALACE.