← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 64

Sashe 54

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shifa ko motsi yaya kamar an yi masa dolen yi ni ne, da ƙyar ya iya matsawa kusa da Ana sosai ya ɗora bakinsa a kunnenta yana dafa kanta ya ce "Shetty" a hankali ta ce

"Abbaa"

"Pray for her" ya ce silently.

"To Abbaa" ta kalli Iftihal sai ta ce

"To me zan ce? Mece addu'ar? Ya ake yi?"

Yaa Sam ya ce "Anything, ki yi mata"

Bata kalli Yaa Sam ba idanunta akan fuskar Abbaa gabaɗaya ya ɗora goshinsa a saman nata ya riƙe kanta.

"Ni ban iya ba"

Da ƙarfi kuma ta ce "Allah Ya ji ƙan ki Mahaɗita, Allah Ya yi miki gafara, Ubangiji Ya saka miki tun a nan duniya, Ubangiji Ya duba kawaici da haƙurinki, yadda kika so mijin Innti ina addu'ar Ubangiji Ya hana shi sukuni da soyayyarki bayan bakya duniya" a hankali ta miƙe tsaye tana murmushi Babban yaya ya miƙe ta yi saurin riƙe hannunsa ta ce "Abbaa ina jin tsoro sosai"

Gam ya riƙe hannunta sai ta fara gani dishi-dishi ta miƙa hannunta ta shafo fuskar Babban yaya da take ganinta a wata suffa ta daban a hankali ta ce "Waye kai? Ina Abbaa?" Ta runtse idanunta, Babban yaya da yake riƙe da ita ya shafi fuskarsa sai ya ji suffar da baya so a san da ita, ita ce ta bayyana a idanun Ana. Ana ƙoƙarin sake buɗe idanu take ta kalli mutumin amma ta kasa. "Abbaa kana ina, bana gani, nima mutuwa zan yi zan bi mahaɗita Abbaa" faɗawa jikin Babban yaya ta yi dai-dai lokacin da numfashinta yake tsayawa a ƙirji, tana faɗowa jikinsa ya haɗe hannunsa biyu ya rungumeta ya ɗora fuskarsa a wuyanta domin baya son kowa yaga yanayinsa.

Da wata kamilalliyar murya ya ce

"I'm sorry Mamaaa...

Daidai nan Jaheed ya yake jiki shima ya faÉ—i babu numfashi zuciyarsa ta kasa É—aukan mutuwar masoyiyarsa.

***
BIYA.

Taron jama'a ne masu ɗauke da jajayen kaya sama da mutane ashirin a ƙarƙashin bishiya cikin tsakiyar daren, layi bayan layi ake binsu da jini ana basu umarnin sha, ko da aka zo kanta ta zubawa jinin idanu ta yi kamar ba zata amsa ba. Sai kuma ta amsa ta shanye, suna gama sha suka hau kan wata dabba kamar jirgi ta tashi dasu zuwa sama. A firgice ta farka daga madadin da take yi, lokacin ana ta kiran sallar Asuba ne.

Hindatu ta yi shiru tana zabga uban tagumi da tuna mafarkin, wannan shine karo na uku tana mafarki, na farko ta yi mafarki an bata É—anyen nama kyauta aka ce ta ci, kuma ta cinye, na biyu ta yi mafarki tana É—aure rago da akuya. Yau kuma mafarkin shan jini ta yi. Abin duniya ya addabi Hindatu ta rasa wa zata faÉ—awa, da Gana kawai suke kirki a unguwar. Har gari ya yi haske tana zaune.

"Hinde, yau an É—auke miki sallah ne?"

Da raunin murya ta ce "A'a malam"

"Sai ki fito kar mukutarinta ya shige ko?" Ta miƙe tana saka hijabi ta fito, wani ihu ta kurma sanda ta yi arba da kayan cikin Malam a sarari, da jinin da yake gudana a jikinsa. Ta dafe ƙirji tare da rarraba idanu.

Malam ya ce "Lafiya kike wannan ihun?"

Hindatu ta kasa magana kamar zata zauce ganin yadda kayan cikin Malam ke ta motsi, a guje ta juya zuwa É—aki tana rufe idanunta.

***
BAFFAS ESTATE.
9:00 na safe.

Baffas estate ya yi shiru baka jin motsin komai da kowa, tun bayan dawowar Sayyadi Baffa, tun daga kan ma'aikatan gidan zuwa jami'an tsaro, da jama'ar gidan kowa cikin taka tsantsan yake yi, sun jaddada komai na abin da zai iya zamewar su matsala a gidan.

Hidaya ce ta kalli Diynaah wacce take sakawa Nadiyaah maganin ciwon idanu ta ce "Mamy ta ce an saka ranar auren Ukhty Azizah da Baffa, wai za'ayi musu aure tare"

Cak Diyanaah ta tsaya daga abin da take yi, Nadiyaah ma Idanunta da ya yi jaa ta watsa akan Hidaya kafin ta ce "Waya ya tsara haka?" Hidaya ta ce "Mamy tace Abba Malami ne, wai dole Baffa ya yi aure wai kuma ya auri Azizah"

"Ya Rabbi!" Cewar Diyanaah.

Nadiyaah ta yi ƙasa da kanta hawaye ya cika idanunta jikinta ya shiga rawa ta kalli Diyanaah ta ce "Baffaa am zai yi aure?"

"Shikenan Baffa zai yi aure mu dinga jin kunya a cikin abokanmu a dinga cewa Baffa ya yi aure? Kuma sai a haifa mana ɗan ƙani?" Diyanaah itama fashewa ta yi da kuka sosai suka haɗu waje guda suka dinga kuka, nan da nan jikin Nadiyaah ya ɗauki wani irin zafin zazzaɓi daman kwana biyu ba lafiya ce da ita ba, da sauri Diynaah ta ɗauki wayarta ta nemo number Baffa data saka masa Baffa am. Ta dinga kira baya ɗauka a kira na uku ta ji ya ɗauka ya yi shiru na ce wani lokaci. "Baffa am" ta kira sunansa da soyayya me ƙarfi dake huda zuciyarta ta ce

"Nadiyaah babu lafiya Baffa..," Ƙit ya kashe wayar bai bari ta ƙarasa faɗa ba. Ta kwantar da Nadiyaah. Ta ce "Ukhty ki narke sosai, ki ce wa Baffa bakya son auren za ki mutu muddin ya ce zai yi aure kin ji"

Diyanaah ta fi Nadiyaah wayo sosai, kamar yadda Diyanaah ta ɗakko sunan mahafiyarta, haka Nadiyaah ta ɗakko sanyin halin mahafiyarta, kamar yaran ɗaya sak. Tun kafin ya shigo suka ji alamar zuwan nasa ta ƙamshin da yake sanar dasu, jin hakan ya saka Nadiyaah rufe idanunta, ta ƙofar daya saka aka yi tsakanin shashinsa dana yaran nasa ya shigo, kyakkywar farar Jallabiya ce a jikinsa, fara sol da ita babu zanen komai a jikinta, sai wani sassanyan ƙamshi na musamman daya cika ɗakin tun sako ƙafarsa da ya yi zuwa ciki, jerarrun yatsun ƙafarsa Diynaah ta fara sauke idanunta akai, taja numfashi ta sauke, zata buɗe murya a ko'ina ta nuna wannan bawan Allan ta ce shi ne mahafinta farincikinta, irin uban da ake taƙama dashi da kuma tutiya. Asalin fatar Baffa ba zaka iya tantance ta turawa ce ko Larabawa ba, jin Nadiyaah babu lafiya ya saka ko rawanin da yake sakawa a kan shi bai samu dama ba, kan shi babu komai ya shigo cikin bedroom ɗin bayan ya samu izinin shigowa daga bakin Diyanaah.

Sumar ƙan shi baƙa ce sosai, a cuccure take ta yi gado gado ta murmuɗe ta saka har ƙasan wuyansa, wata tayo gaban goshinsa, akwai ratsin jaa a sumar gaban goshinta.

Baffa a tsaye yake sosai a saman ƙafafuwansa, cike da kuzari, izza, mazantaka taƙama da ilimin addinin da yake dashi, uwa uba kwarjini, haiba da salon nasa ra'ayin, har wani yellow yellow fuskarta take yi tsabar haske kyau wajan Sayyadi Baffa ba'a magana, duk kyan da yaransa suke dashi ko kwatan nasa basu ɗauka ba. Ya yi tsaye hannunsa ɗaya riƙe da ƙaramin carbi, ɗaya hannunsa yana zagaye a bayansa ya zubawa Nadiyaah idanunsa.

"Barka da shigowa Yaa Baffa"

Cewar Diyanaah tana yin ƙasa da kanta.

Ya juya launin ƙwayar idanunsa a kanta da wata kalar nutsuwa da yanayin da yake nuna magana kai tsaye yake mata da "Kar ki sake ɗora photo a Social media Diyanaah Sayyadi Baffa" cikin sauri ta ce "In sha Allah Baffa"

A jikinsa ya ji zai wahala ciwon idanun Nadiyaah idan ba Kambun baka bane. Ya ƙarasa ya zaune kusa da ita, jikinta zafi sosai don haka ya shiga yi mata addu'a yana tofa mata. Nadiyaah ta girgiza kai ta ce "Baffa am, don Allah Baffa kar ka yi aure, idan ka yi aure zan iya mutuwa, za'ayi mana dariya ace mahafinmu ya yi aure, kuma har a yi mana ƙani" jin abin da ta ce ya saka su waro idanu sai kuma yaja idanuna ya lumshe, kishin mahaifiyarsu suke yi wacce bata raye ma.

Diyanaah ta ce "E, Baffa. We're 17 years fa, ai tun muna ƙanana za ka yi aure ba yanzu ba, kuma duk wacce ka aura zata rabamu da kai. Muna son ka Baffa don kar ka yi aure"

Ta zame zuwa ƙasa cikin sauri ma Nadiyaah ta sakko suka jeru a gaban Sayyadi Baffa.

Da wani irin kuka me narkar da zuciyarsa suka ce "Kuma muma idan mukai aure, matarka tana haihuwa mu muna yi? Ka tausaya mana Baffa,bama som ka auri kowa" Diyanaah ta ce "Ukhty ba kin ce ana aure a aljanna ba, kinga sai Baffa ya yi aure da Ammie a can aljanna ko? Please Baffa"

Kuka suke yi sosai, gani suke babban tozarci ne ace mahafinsu ya yi aure a age ɗinsa, Shugaban Hisba da kan shi, shi da yake gujewa mu'amala da mata baya saka so a tsarin rayuwarsa, duk wata mace Garzali ce a idanunsa. Ya dubi yadda suke kukan kamar za su rasa rai. Ya miƙe a nutse ya riƙo hannayensu, a hankali ya sumbaci kumatun kowacce kafin ya juya ya bar ɗakin nasu. Sanda ya fito direct babban parlornsa ya nufa saboda tun jiya yake ganin shigowar saƙon Mu'allim, sai ya bashi izinin zuwa, yana shiga yaga Mu'allim tare da Liman zaune, jin zuwan Sayyadi Baffa ya saka su miƙewa tsaye kan su a ƙasa? "Barka da zuwa" Suka ce a tare, ba tare daya kalle su ba ya nemi waje ya zauna. Shiru shiru babu wanda ya yi magana, a hankali ya ɗaga kai ya kalle su, ya juya ya kalli Liman a nutse

Gaban Mu'allim sai faÉ—uwa yake yi, ya É—an zunguro Liman

"Liman Please, ka faÉ—a masa"

Liman ya kalli Mu'allim sai bai ce komai ba.

Baffa ya harɗe ƙafa idan ya kalli wannan sai ya kalli wannan. A nutse ya miƙe zai fice. Mu'allim ya ce

"Na samu matar aure ne Baffa, a unguwar Kankarofi, sunanta Aysha......," ya É—auke labarin komai har abin da Babban yaya ya ce ya faÉ—awa Baffa ya É—ora da "Baffa Please, ko dan ciro yarinyar daga faÉ—awa wani hali ka amince na aure ta, wallahi ina son ta da gaske. Amma idan ka ce a'a shikenan"

Baffa ya yi shiru bai ce komai.

Liman ya ce "Ka taimaka Baffa"
Chapter 54 · 0% Book details