← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 64

Sashe 63

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ta ji daren na yi mata nisa, tuna cewa Alhaji Baita ya bawa shekaru Sittin baya. Kaddarar wasu mutanen na zuwa cif da cif kamar sune suka zanawa kansu taswirar rayuwar, tun daga farko har ƙarshe fari tas take, kamar yadda rayuwar Nadiyaah ta kasance, komai na rayuwarta kamar ita ce da kanta ta zaɓawa kanta yadda za ta wakana. Wasu kuma raba dai-dai suke yi, daga farko farinciki irin mai mantar da mutum wani abu kan iya faruwa dashi na ƙaddara, sai daga baya reshe ya juye zuwa mujiya, kwatankwacin rayuwar Ahlam Abdallah Kurmi. Wasu mutanen kamar dare biyu haka rayuwarsu take ciki saboda ƙaddarar da ta yi musu ƙulli, babu farinciki ko kaɗan kamar yadda ta kasance a rayuwar; ANA. Wasu mutanen kuma gabaɗaya ƙaddararsu a baibai ba su fahimci kansu ba, balle su fahimci ƙaddararsu har su yi maganinta. A ɓangaren Batty hakan lissafin yake a rigar Biya gidan Dikko.

Ta ɗaga jajayen idanunta cikin ƙunci da raɗaɗin zuciya ta ce "Allah Ya nuna mana gobe, ko gawata ko ta Babana..," Sai ta yi shiru. "Ko ta Alhaji Baita"

GabaÉ—aya suka kalle ta banda Yaya.

Bayan sun koma bacci, wannan sanyin da yake ratsa jikin Yaya shine ya fara, ya yi iya ƙoƙarinsa wajan hana hakan faruwa amma ya kasa. Sannu a hankali sanyin ruwan kogin ke ratsa jikinsa alamar baya tare da Ana a yanzu ɗin.

Itama data farka bata ganshi ba, babu kowa sai ita, fresh tunaninta ya dawo ta ƙwala kiran sunan Innti da Iftihal a gigice, ta dinga kuka da ihu ta bigirma ta rarrashi kanta. Hijab ta ɗauka ba ta ganin ko gabanta ta shiga Napep ta ce Hisba Headguater.

Tana zuwa ta kalli wani mutum ta ce

"Shugaban Æ´an Hisba nake son gani"

Ya kalle ta sosai, yarinya ce bata fi 17 years ba. Ya ce "Baya nan ki bada bayanin abin da kike so za a sanar dashi ko?" Ana ta girgiza kai ta ce "Matsalata ai bata ƙananun ma'aikata bace, shugaban Hisba ɗin nake son gani da kan shi, akwai abin da zan faɗa masa wanda sirrina ne, kuma na yi masa wasu tambayoyi" ya dinga kallon ta da mamaki yace "Ikon Allah, ƴar ke ɗin nan ce kike da matsala, ko auren dole za a yi miki?"

Wani irin jirkitaccen kallo Ana ta yi masa.

"Malam ba wasa na zo ba, keep a joke aside please. Ina shugaban Hisba É—inku yake?"

Ya ce "Me kike buƙata a wajansa?"

"Ƙarar mahaifina na kawo. Ina so ya kawowa rayuwata ɗauki, kamar yadda ka ce haka ɗinne, auren dole za a yi mini kuma bana so, domin ni ba matar tsoho bace, ina so ya shiga tsakanina da mahaifina. Ni na yarda zan yi aure idan ana buƙatar hakan, amma idan shugaban Hisba ɗin naku ya amince zai aure ni. Auren rufin asiri kafin na samu wanda nake so" ta yi shiru tana sauke ajjiyar zuciya har ta juya ta dawo tace

"Oops, ka faɗawa shugaban Hisbar taku, na kawo ƙara idan bai ɗauki mataki ba, dukkan abin da ya samu da faru da rayuwata shine sila kuma shine sanadi, ga number wayata"

Ta bada number Yaa Jaheed.

Tana fita ya saki dariya kawai ya cilla number a bakinsa ya taune tas.

***
BIYA.

Yana kwance bakin ruwan yana rawar ɗari hannunsa dafe da ciki da kan shi, idanunsa rufe ruf dasu. Gabaɗaya hankalinsa yana kan Ana da tunanin halin da take ciki, ko yatsarsa ya kasa motsawa. Ya yi namijin ƙoƙarin ɗago hannunsa ya ware takaddar da Innti ta rubuta kafin ta rasu, kyakkyawan rubutunta ne ta ce "Yaya ban sani ba ko za ku dawo ku same ni, zuciyata ta yi mini nauyin dana kasa tantance abin da yake damuna, idan na tuna na yi saɓon Allah wajan yin biyayya ga Daada sai na ji kamar zuciyata za ta fashe. Na sani babu biyayya ga mutum wajan saɓa wa Ubangiji, amma na biyewa Daada mun aikata son rai. A jiya na sake jin wa'azi,"Lā ṭā‘ata li makhlūqin fī ma‘aṣiyatil Khāliq." Ma'ana: "Babu biyayya ga wani halitta idan biyayyar za ta jawo saɓa wa Mahalicci." Yaya ya zan yi da hakƙin Iftihal, na yi lafila na roƙi zaɓin Ubangiji, ina da yaƙinin ya amsa kuma ya gafarta mini. A yau da safe na fahimci ina yi wa Daada biyayya ne saboda ban san wacece ni ba, bani da alaƙa dashi ta kusa ko ta nesa balle ta jini, ina tunanin tsoron gaskiya ta bayyana ku tambayi wacece ni ko asalina, ban sani ba, kuma zai iya korata ya ƙwace mini ku"

Sai ta yi sakin layi ta ce "One day I may die without saying goodbye to you but I'll never forget to say thank you, because you hold most lovely part of my life. Ina rubutu wannan a lokacin da tunanina ya dawo na san wacece ni, ina tsoron na sake mancewa, zan tafi da raɗaɗin sabon Ubangiji da na yi, Yaya an ce; Ana biyayya ga mutane ne a cikin abin da ya dace da shari'ar Allah. Idan umarninsu ya saɓa wa umarnin Allah, to a ƙi bin umarnin cikin ladabi da hikima, domin biyayyar Allah ita ce tafi kowace biyayya. Muddin ina raye kuma na cigaba da mance kaina zan ta aikata saɓon Ubangiji wajan yi wa Daada biyayya, na riƙo zaɓin Ubangiji"

Ta sakin layi.

"Na bar maka Ana duniya da lahira, ta amsa sunanta da naka, Aysha Muraad Ana. Ka kula mini da ita don girman Allah Abbaa, asalina ba musulma bace, daga baya na musulunta. Sunana.... Sunana.... Sunana"

Ta rubuta sunana sau wajan biyar kafin tace

"Sunana ANUM"

"Laaa kaÉ—o, ka dawo kai ne?"

Muryarta Batty ta sauka a cikin kan shi, ya yi saurin rufe idanu yana damƙe hannunsa.

"Ina ta nemanka shine ka gudu ka barni, ko kana tsoran na cinye ka ne? Ni fa mayya ce"

Babban Yaya ya yi wa Batty shiru.

Ta washe bakinta ta ce "Kyakkywa ne kai, kalli gashin fuskarka me kyau, kuma kana wanka kullum kana ta ƙamshin abinka ko?"

Ta miƙa hannu ta shafin kwantaccen sajen gefen fuskarsa "Innalillahi, laushi" ta faɗa tana yin saurin ɗauke hannunta ta ce "Kai"

Ta zungure shi, ko motsi bai ba, "baka magana?" Ta zabga uban tagumi

"Allah sarki kurma ne, sunana Batty"

Ya yi mata burus sai ta sunkuya dai-dai fuskarsa ta zaro harshe ta ce "In cinyeka na lashe ka" harshenta ta taɓa tsinin hancinsa.

***

Suna zaune da yawa. Ɗaya daga ciki ya ce "Idan mu ka yi wasa Sayyadi Baffa zai ɓata mana sabuwar gwamnatin da muka kafa, ya zama dole mu ɗauki mataki akan shi, kamar yadda muka ɗauka akan Hafizz Hafizz Baffa, a shekarun baya shi da ƴarsa Diyanaah Hafiz Hafiz Baffa, ba za mu zuba idanu ya rusa mu ba, kuma dole adadin musulmai a ƙasar nan ya yi ƙasa, kun san ba za su taɓa zaɓar Jonathan ba, suna da kishin musulunci" a hankali ya numfasa kafin ya ce

"Ba iya Baffa ba, hatta Major sai mun É—auki matakin gaske a kan shi, za su iya zame mana matsalar gaske a tattare da tafiyar nan?" A hankali ya jinjina kai kafin ya ce

"Ya batun wannan maganar da aka yi?"

Madubi ya ce "Tana nan, an gama jadawalin su É—ari ne cif Yaranka ya daÉ—e" ya yi shiru.

"A faÉ—awa Baita ya rufe bakin jama'a daga abin da yake shirin faruwa a garin nan"

Madubi ya ce "An gama"

***
Al'amarin ya yi wa Ana zafi, ga rashin Abbaa, su Jaheed kuma idan sun fita nema sai dare suke dawowa gida. Ta ɗauki ciki takadda ta rubuta tarihin rayuwarta tas, komai da komai har batun Iftihal da Innti. Ta ɗora da "Wannan saƙon naka ne shugaban Hisba, na zo baka nan wannan takaddar ta zama shaida, rayuwata idan ta lalace akwai saka hannunka, kuma kai ne sila, ka zo ka aure ni kafin mahaifina ya rusa rayuwata, babu isasshen lokaci, duk wanda ka cewa gidan Daada a unguwar Kankarofi ya sani ga number wayar Yaya nan" ta ninke takaddar ta sake komawa Hisb Headquarter, cikin sa'a ta samu Ansar ya bata haƙurin Shugaban baya nan, amma zai bashi in sha Allah"

Cikin rashin sa'a da saurin da Ansar yake yi, sai ya saka takaddar cikin jerin wasiƙun da aka riga aka karanta su a ofishin Baffa.

Sanda ta dawo gida dare ya yi kuma kai tsaye ɗakin Yaa Sam ta shiga ta same shi yana ta tattare kayan da zai tafi interview da su, ta durƙushe a wajan ta fashe masa da kuka kamar ranta zai fita ta ce "Yaa Sam ina Abbaa, ban ga Abbaa ɗina ba. Daada ya ce zai kai ni gidan Alhaji Baita ba zan jure ba"

"Nanaah, za ki iya aurena?"

Yaa Sam ya yi furucin lokacin da take durƙushe a cikin shagon nasa a tsakiyar daren. Kasa magana ta yi, ba ta da zaɓi face abin da ya zaɓa mata. "Nanaah...........

Ya kira sunanta da ƙyar ganin ta ƙi tashi ya saka hannunsa wajan ɗagota tsaye, ƙafafuwanta rawa suke sosai tana ƙoƙarin sake zubewa a wajan, sai ya taro ta ya jinginata da jikinsa ya tallafo haɓarta yana kallonta da nasa rinannun idanun wanda suke raba pain ɗin a tare ya ce. "Tun da ba ki da wani saurayi give me a chance, ki bani dama na zama mijinki Nanaah, ki bani dama" a hankali take kallon shi ta kasa cewa komai, ta rasa kalma ko ɗaya a bakinta.

Ya cure girarsa ya ɗage ɗaya ya ce "Na sani, na sani kalma ta soyayya ba ta taɓa kilmawa a tsakaninmu ba, amma ina jin soayyarki a zuciyata bani da ƙwarin gwiwar faɗa miki tunda na san mene burinki. Ki bani haɗin kai wajan tallafar rayuwarki na aure ki, ko zuwa gaba idan kin samu wanda kike so sai na sawwaƙe ko?" Ta yi masa ƙuri da idanunsa.

"Amma kai abokina ne, Yayana kuma"

A nutse da kamewa ya ce "Kuma mijinki zuwa gobe da yamma, ki amince mini"

"Amma ni bana sonka da aure fa"
Chapter 63 · 0% Book details