← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 64

Sashe 28

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan da nan Hunter ya haɗe fuska kamar bashi ya gama waƙa ba, a wannan lokacin duk wanda ya kalli fuskarsa sai ya girgiza ya ji gabansa ya faɗi ya ji kuma kamar ya saki fitsari a wando. Ya durƙusa gaban matar, ya zuba mata fararan manyan idanunsa kafin ya zaro wata kaifaffar wuƙa a ƙugunsa me kama da zarto, ganin hakan ya saka mutanen da suke ɗaure suka fasa gigitaccen ihu, suna rungume na kusa dasu, ƙafa ɗaya Hunter ya saka ya danne kan matar ya saita wuyanta daidai maƙogaranta ya shiga yanka wuyanta, zillo take jini na feshi ta wuyanta, bata gushe ba tana ambaton Allah da kalmar shahada tare da yin kaffa tare da shure-shure har rai ya yi halinsa.

Yau sun kashe mutane wajan goma akan ƙin fita daga Musulunci, da yawansu kuma waɗanda aka kashe Fulani su gaba da baya. Jago ya ce

"Ga wata fara kyakkyawa can, ko za'a kiwatawa Triplets-T ne ita?"

Hunter ya juya ya kalli yarinyar wacce ta ƙurawa gawar mahafiyarta idanu sai ya girgiza kai ya ce "No need, ba layinsa bane, ya dai bada umarnin duk matan da suke wajan ko ba'a kashe su ba, a tabbatar sun san namijin a gun nan so idan kana ra'ayinta go ahead" Jago ya ce

"Kai baka da ra'ayi ne ?" Hunter ya tattare girarsa biyu ya É—age zuwa sama kafin ya ce "Tawa tana can duk runtsi zam koma gare ta, Ayshatuna matar Hunter yaron T.T.T. na hannun damar Triplets-T" yana faÉ—in hakan ya koma cikin rumfar daya fito.

***
TAJMAHAR PALACE.

Shirun da masarautar ta ɗauka na yau na musamman nan, ba sai an yi shela an faɗawa mutum wani abu na musamman yana faruwa ba, duba da yanayinsu manyan jami'an masarautar da suke tsaye tun daga gate na farko har zuwa na huɗu. Masarautar Tajmahar ba kawai masarauta ce ba, duniya ce gudu ta musamman, masarautar da take da iko da zartarwa, masarauta ta zamani da kayan ƙawa. Ginin golden ne da ita me haske da ɗaukan idanu tun daga sama an rubuta TAJMAHAR PALACE. Doka ce aka saka tun satin daya shige, an rufe shiga da fitar mutane, idan kana cikin Tajmahar kar ka fara yunƙurin fita, idan kana waje kar ka yi tunanin shigowa ciki, wannan umarni ba iya na jama'ar garin bane, hatta hadimai, bayi, barori, da ƴan majalisa na fada umarnin ya hau kan su, ba iya su ba, hatta jinin Tajmahar wannan ƙararrawar umarnin ta hau kan shi. Tor Tiv ne kawai me yin yadda yasu a daidai wannan lokacin.

Sannu a hankali ya fito daga ɓangarensa, yana taka ƙafafuwansa kamar baya son taka su, duk inda ya ɗora ƙafarsa ɗaya sai ya ɗan jira, da yawan lokaci wannan izzar da gadara bata biya damunsa ba, sai ya sako ƙafarsa zuwa Tajmahar, jinin Tajmahar ya ƙara sanar dashi waye shi, matsayinsa da abin da yake jira. Farar fatarsa me ɗaukan ido sai sheƙi take yi ta dalilin wuyan da yake sakkowa daga gashin wuyansa yana sauka a fatar wuyansa tare da sakkowa jikinsa. Garden za shi, har ta gilma ya ɗan ja ya tsaya, ya ɗauki lokaci yana kallon waje guda kafin ya juya zuwa inda ya ganta zaune ɗaure da sarƙa a jikinta.

Jikinta duk ya farfashe jini na zuba a jikinta, gashin kan nan nata a diddige, wannan shine karo na uku yana ganinta, dukkan bayin Tajmahar ai ba'a nan suke ba, me ya sa aka fito da wannan waje ne? Miƙewa ta yi a hankali ta fara tafiya duk inda ta taga jini take bari shaida. Har zai shige sai ya dubi wani badakare, cikin sauri badakaren ya yi ƙasa da kan shi sai kuma ya ce "Umarninka biyayya ne Madaki"

Wanda aka kira da Madakin ya juya ya cigaba da tafiya yana jin bugun zuciyarsa na ƙaruwa. Tun kafin ya kai waje ake yin ƙasa da kai tare da rusunawa har ƙasa, a haka ya shige hadaɗɗan garden ɗin yana shiga ya ƙarasa kan wata kujera wacce take a kwance ya bi kan kujerar ya kwanta idanunsa na kallon saman masarautar Tajmahar ɗin.

***
Duk da sanyin safiya ne wajejen 11:30 bai hana su jeruwa a majalisar da suke zama koyaushe suna sana'ar tasu ta karta ba. Su wajan biyar ne yanzu ma, Alhaji Baita, Daada, Ɗahe sai Garbati na ƙarshen kuma Sadisu. Tsofaffi ne masu iyalai da kuma shekaru sai dai sun lalata tsofan su wajan son abin duniya da kuma aikata saɓo. Daada ne rangwamen shekaru a cikin su. "Daada ko dai kana jin tsoro ne?" Garbati ya yi furucin yana daidaita zaman shi tare da kallon katin kartar dake hannun Daada. Yau ne suke yin cacar da Daada ya saka Iftihal a ciki, don haka wasai Daada yake jin zuciyarsa yana hasaso kan shi nan da mintina biyar ko goma ya zama mamallakin Naira biliyan Ashirin cif. Sai murza raguwar katin daya rage a hannunsa yake me alamar Square 2 sai ya jinjina kai

Ya ce "Garbati me kake ci na baka na zuba?"

Cikin sauri Garbati ya ce "ÆŠoki da zumuÉ—i mana"

"Muje zuwa" Alhaji Baita ya furta yana cilla Square 1. Bayan ya saka ya dubi Daada ya ce. "Zagayenka ne abokina" ganin alamar nasara a tattare da Daada sai ya yi murmushin daÉ—i da farinciki

Ya ce "Nasara tawa ce"

"Ina maka fatan samun ta" In ji Alhji Baita ya yi masa raddi

Daada ya cilla Triangle 1 . Sai ya rasa juyinsa don haka ya yi hold on. A tunaninsa Alhaji Baita bashi da sauran katuna ya yi murmushin jin daɗi ya ce "Na rasa katina, na yi nasara" ya fara miƙewa tsaye da shirin ɗaukan jakar.

"Last card!" Alhaji Baita ya faɗa yana ajjiye katin hannunsa, Daada babu yadda zai yi yana ji yana gani Alhaji Baita ya saka katin kuma ya yi nasara. Zufa ta shiga yankowa Daada a kowanne ƙofa na gargasar jikinsa. Ba wai murnar kuɓutar da ƴarsa yake yi ba, baƙincikin rashin samun miliyan ashirin ɗin ita take ƙoƙarin ganin bayansa a yanzu. "Kuɗina ya dawo, kuma na ci yarinyarka a caca Daada, ba tare da kowa ya ji ya gani ba, ka shirya ƴarka ka kawo mini ita gidana a matsayin yarinyar da na ci a caca finally" ya faɗa da murna yana tattara kayan.

Daada ya kalli Alhaji Baita da jajayen idanunsa na makakku ya ce "Kutumar, kana nufin ka tafi da miliyan ashirin ɗin kuma na baka yarinyar da nake kallo matsayin jari? Ai da na baka Iftihal gwara na kama mata hayar shago a sabon gari ta dinga samar mini kuɗi, daman na jima da wannan burin" "Ka yi ƙarya, ka kuma kwana da yunwa Daada" Alhaji Baita ya miƙe tsaye yana kallon Garbati ya ce "Ɗakko mini yarjejeniyar nan Garba" cikin sauri ya fito da ita, Alhaji Baita ya amsa ya nunawa Daada.

Ya ce "Wasan WHOT wasa ne na haramci wanda idan jami'ai suka ji za su kama mu, kaina talaka kai zaka dauwama a wajansu bani da asara ni kam. Ina baka shawara bakinka a laikum ka je ka fito mini da ita"

"Na baka Iftihal a matsayin me?" Cikin isa da izza Alhaji Baita yana dariya ya ce

"A matsayin yarinyar da na ci a caca" Dadda ya haɗiye wani abu me ɗaci a maƙoshi yana ayyana yau har Innti ta shiga uku a wajansa. "Na ji, ina nufin aurenta za ka yi ko me? A matsayin me za'a kaita"

"Ko a matsayin mene baka da ruwa da tsaki, zan dinga hutawa ne a jikinta ba wani abu ba" Kallon Alhaji Baita kawai Daada ya yi kafin ya juya ya bar wajan. "Kar ka manta" Cewar Alhaji Baita "A daren nan za'a kawo ta bani da haƙurin jira na gama kaiwa geji"

WHOT wasa ne na katuna da ake yi domin nishaɗi ko gasa, inda mutane ke ƙoƙarin ƙare katunansu kafin sauran ƴan wasa, wasu na ce mata wasan karta wasu caca suke kiranta dashi a turance kuma ana kiranta da WHOT. Wasu na yi domin nishaɗi wasu kuma suna saka kadararsu na abin da suka mallaka a ciki. Idan ka yi nasara ka ciyo abin da ba ka yi tunani ba, idan ka yi rashin sa'a za'a cinye abin da ka saka. Kamar yadda Daada ya saka ɗiyar cikinsa a cacar kuma aka yi nasarar cinta. Hukuncinta a shari'a ya bambanta, Idan ana yin Whot da kuɗi (caca)Wannan yana shiga cikin abin da ake kira Maysir. A Musulunci, an haramta caca a fili haramun ce ta kowacce siga kamar yadda dalilai suka zo a cikin Alkur'ani mai girma, caca tana haddasa rikici da rigimar da zata iya yin wa'adin ran wani, tana hana ibada akan lokaci wasu basa yi, tana cin dukiyar mutane ba bisa ƙa'ida ba. Duk kuɗin da mutum ya samu a Whot ko ya mallaki wani abu, ba zai taɓa zama halak ba, waɗannan abubuwan sun zama haram a gare shi. Wasu kuma Malaman suka ce, Whot idan ana yi da sigar nishaɗi suka ce babu haramcin muddin bata hana mutum ibada ba, wasu kuma suka ce makruh ne (ba a so), saboda tana iya kai wa ga yin cacar yana iya ɓata lokaci.

Kamar zai tashi sama haka Daada ya nufi hanyar gidansa sai surfa bala'i yake kamar zai ciro bakinsa ya ajjiye a ƙasa. Bugo ƙofar da ya yi ya saka zuciyar Innti bugawa da ƙarfi, salati ta saki saboda tsabar yadda take tsoron ganinsa ko shigowarsa cikin gidan. Yana shigowa Iftihal na fitowa daga cikin ɗaki sanye da uniform zata tafi makaranta. Jikinta na rawa ta durƙusa ta ce "Ina...,"

Bata ƙarasa ba ya sakar mata wata uwar tsawa da faɗin "Gidan ubawa za ki da safiyar nan?" Kanta a ƙasa dukkan jikinta rawa da ɓari yake yi saboda tsananin tsoron daya gama ratsa mata zuciya bata taɓa jin tsoron wata halitta a duniya sama da halittar dake tsaye a gabanta ba, bata taɓa jin tsoron wani ba kamar yadda take tsoron mahaifinta Daada. Maganarsa faɗuwar gaba take haddasa mata, ko tari ya yi sai ta saka hannu ta dafe ƙirjinta domin ji take kamar zuciyarta ce zata faɗo ƙasa ta cikin ƙirjinta ba tare data shirya hakan ba.
Chapter 28 · 0% Book details