← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 64

Sashe 46

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin kallo ya cillawa Liya sai ya je ya ɗakko tsinke ya miƙa mata ya ce "Cire abin da yake miki kama dana namiji a jikina da kike kirana da Bala ba kunya da tsoron Allah" girgiza kai kawai ta yi tai dariya. Juyawa Innti ta yi zata fita ya yi saurin miƙa hannu zai riƙe ta, ta yi saurin ɗaga hannunta ta kwaɗa masa mari ta ce "Mara ta ido fitsararre kawai....," bata ƙarasa maganar ba Hanna ta ɗauke Innti da mari.

*

A nutse ya duba agogon dake maƙale a tsintsiyar hannunsa, yaga lokaci yaja yamma ta kawo kai tun yaushe suke wajan nan? Gashi ko mutum ɗaya ba'a yi wa Interview ba, sai dai a dinga kiran mutanen da aka ga dama. Ya saki siririn tsaki tare da miƙewa ya ƙarasa wajan mutumin ya ce.

"Wai What's going on here? Tun safe muna wajan nan, kune kuka kira mu bawai mu ne muka kawo kan mu ba. Idan yaudara ce abin ai gwara mu sani mu cire rai" wanda yake zaune akan kujera ya juya ya kalli Yaa Sam

"Shine zaka zo kana mana ihu a saman kai saboda rashin kunya? Shi talaka duk inda yake sai ya nuna halinsa ne?" Yaa Sam ya tattare baƙar ƙirarsa ya cure waje guda yana fito da idanunsa waje ya kalli mutumin sosai cikin turanci ya ce "Kuma wannan talakan yasan limit ɗinsa ya kuma iya talaucinsa, yana da zuciyar nema. Gwamnati ta neme mu, ita kuma Gwamnati ta kowa ce, haƙƙinta ne yin abin da take yi, tunda mune muka kafa gwamnatin. Kuma wallahi a shirye nake da shiga rediyo na faɗi irin wulaƙancin da kukai mana. Ai na haddace sunanka tsaf a kaina"

Jin furucin Yaa Sam ya saka mutum miƙa hannunsa ya ce "Have a seat, muga ducoment ɗin naka?" Ya miƙa masa ya shiga dubawa, a hankali ya ɗago kai ya kalli Yaa Sam ganin tun daga kan primary school har University result ɗinsa masu kyau ne, irin wanda ake buƙata. "Ina zuwa"

Ya ce yana miƙewa gefe ya koma ya kira waya yana ɗagawa ya ce "Sir an samu exlty irin ducoment ɗin da kuke so, har bangaren karatun na Accounting. Ka faɗawa wanda ya ce sai siya ya bada 3 millions a cire sunan Haysaam a ɗora na yaronsa, ko kuma ya tafi akan sunan na Haysaam" ya yi jim.

Can ya ce "Sure sir, ok I'll in sha Allah"

Few minutes ya dawo ya kalli Haysaam ya ce "Malam Haysaam, zuwa gobe ka dawo da za'a yi maka takadda na offer later congratulations"

Sak Haysaam ya yi yana kallon mutumin, wani irin hamadala yake yi a zuciyarsa, ashe yana da rabon cin muriyar karatunsa? Ashe iyayensa za su ji daɗi tun suna raye? Ashe zai samu kuɗin da zai kula da Ana? Sai samu kuɗin da zai auri yarinyar da yake mutuwar so da ƙauna kamar numfashin shaƙarsa. Ya zame ya yi sujudur shukràn kana ya tafi yana hamdala.

*

A can rugar Biya a gidan Moddibo, Mado ne kwance jikinsa ya rikice babu yadda yake jikin ya ɗauki zafi rau kamar gaushin wuta saboda zafi, sai sambatu yake yi yana faɗin "Ga kura nan ga doki nan, za su kama ni ga wuta nan tana bini gata nan zata cinye ni" Malamin da aka kira ya girgiza kai yana zubawa Mado dake kwance idanunsa rufe ido, kaya ne a jikinsa irin yadin nan me kyau da aka goge masa jikinsa aka saka masa. Moddibo ya nisa ya ce "Ka gani Malam Horo, ɗazo jikin gwanin sha'awa sanyi ƙalau har aka bashi kindirmo ya ɗan sha amma duba ka gani yadda ya rikice lokaci guda"

Malam Horo ya ce "Sannu Mado, sannu ka ji. Allah yo jam tan" ya faɗa yana taɓa Mado “Malam Hooro, too aljannu’en ngari natti dow ɓandu Mado naa?” Horo ya yi shiru yana kallon Mado da nazari ya kalli yadda yake zabura da surutai marasa ma'ana.

"Sune, abubuwan da yake yi duk sharrin Aljanun ne, za'ayi masa Ruƙiyya idan Allah Ya so za su bar jikinsa. Sannu Mado, Allah yo jam tan" jakar kayansa ya buɗe ya ɗakko wata kwalba me ɗauke da maganin zafi ya ajjiye a gefe, sai dogon carbi irin me guda dubu ɗin nan ya ce "ku riƙe shi da kyau, babu mamaki shaiɗanun jinnu ne ke addabar shi da bibiyar rayuwarsa" Mado ya ƙurawa Malam Horo ido kamar ya buɗe baki ya sace masa bashi da wata iska kar ya yi masa ruƙiyya amma babu bakin magana, suka riƙe shi Malam Horo ya shaƙa masa man zafin cak numfashin Mado ya tsaya na wani lokaci, saboda yadda maganin ya ratsa ƙwaƙwalwarsa ya gigita mata lissafi, jikin ya ƙara birkicewa ya fara fusge fusge da wani irin numfashi yana samƙamewa. Moddibo ya riƙe shi gam ya ce "Sai kun tafi inda kuka fito, ku bar jikin bawan Allah ina faɗe muku tun tuni amma kun manshe ni ɗanbaza ko? Ga Malam Horo nan gare ku ai" tsananin azaba ta saka Mado riƙo hannun Moddibo da kyau yana fidda wani irin numfarfashi, Malam Horo ya saka hannunsa a goshin Mado ya danne ya fara addu'a yana tofa masa, ba'ayi minti biyu da danne goshin ba, Mado ya yi wata fusga da salati da ƙarfi jikinsa ya saki alamar rai ya yi halinsa.

Malam Horo ya ce "Allahamdulilah bacci ya É—auke shi kar a tashe shi sai ya farka da kan shi, idan ba haka ba za'a samu matsala"

"A'a Malam Horo idan Allah Ya so babu me tashin shi. Mun gode miyyeti masin" sallama ya yi musu ya fita, Moddibo kuma ya fito daga bukkar Mado ya saki assabari ba tare daya san gawa ya rufe ba.

*

Tunda ya shigo gidan yake surfa masifa kala-kala. Girgiza kai kawai ta yi kafin ta ce "Yanzu shi ya ce maka aurenta zai yi ko me? Me yake dashi da zai É—akko wa kan shi maganar aure? Ji nake a can Lagos É—in ba wani aikin kirki yake ba Masinja ne shi a bankin" Ya ka da baki wajan faÉ—in "Ai na ga take takensa, ko yana da halin yin ban lamunce masa auren Æ´ar mashayin mutumin nan ba, mara kunya fitinannen mutum. Haka jiya akan idanuna ya shige da wata shiryayyiya. Ba zan iya haÉ—a iri dashi ba" ita dai abin da take yi ya cigaba da yi.

Dai-dai nan ya sako kan shi cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, gogaggen yadi ne a jikinsa daya sake fito da kwarjininsa, sai ƙamshi yake fitarwa dawowarsa kenan daga Interview ya shiga ya yi wanka. Baba ya ce "ka shigo a dai-dai"

Kallon mahaifin nasa ya yi ba tare da ya ce komai ba. "Yaushe zaka koma can Lagos É—in?" Haysaam ya kalli Baba sai ya yi shiru

"Magana nake ka tsare ni da ido?"

"Sai na haÉ—a kuÉ—in mota in sha Allah" Baba ya dube shi ya ce

"Nawa ne zuwa Lagos É—in?"

A ɗan taƙaice ya ce "Ya danganta"

"To Allah Ya taimaka ya yi muku albarka. Bance kar ka taimaki yarinyar ba, amma rai na baya mini daÉ—i ganinka da ita, yanzu É—an mutum ake kiwo ba dabba ba, ka lura" Yaa Sam ya yi kamar bai fahimta ba da kamala a tattare dashi ya ce "Wacece?"

"Ladidi yama sunan yarinyar?"

Caraf Walid ya ce "Ana sunanta Baba" Yaa Sam ya juya ya kalli Walid sai yaron ya yi saurin yin ƙasa da kai. "Ka kawo mini abinci shago" yana faɗin hakan ya fice zuciyarsa babu daɗi. Shagon nasa da yake jikin ɗakinsu ya nufa, yana jin baba yana faɗin shi sam bai ga amfanin karatun Haysaam ba, an ƙare karatu babu aiki, ganin takaddar ƙosai yafi faranta masa akan takardun Sam.

Kwanciya ya yi a katifar ɗakin ya lumshe idanunsa ya rufe fuskarsa da hula yana jin Walid ya shigo shagon ya ajjiye masa abinci. Yaron ya dinga kallon ledar dake ajjiye kamar ya ɗakko sai ya fasa. Yana ta kwance tunani ya yi masa yawa a zuciya ya ji alamar an buɗe ƙofar an shigo, bai motsa ba kuma bai buɗe idanunsa ba, har ta ƙarasu gefen wajan ta durƙusa kanta a ƙasa yana jiran ya ji ta yi masa magana amma shiru. A hankali ya cire hular ya buɗe gargasar idanunsa tare da kallon inda take daf dashi, tun kafin ya yi magana ta rushe masa kuka, ya san yadda take ƙoƙarin danne rauninta bata bari aga gazawarta kukanta sai ya riƙe ta shi

"Nanah.......

Ta kasa amsawa sai ta kifa kanta a cinyarsa ta sakar masa wani irin kuka me raunata zuciya, yaja idanunsa ya lumshe su yana jin zuciyarsa na buÉ—ewa. Bai sake magana ba sai É—ora hannunsa da ya yi a saman kanta.

Ganin kukan zai iya haddasa mata ciwo a hankali ya ce "Enough, daina kukan hakan" "Yaa Sam...,"

"Shhhh" ya katse ta wajan ɗora yatsarsa a bakinta ya zaunar da ita kusa dashi ya janyo kwanon abincin ya buɗe, banɗashen gurasa ne ya ji mai da ƙuli an yayyanka masa ita. "Muga hannunki?" Ta nuna masa bai gamsu da tafin hannun ba ya tanƙwashe ƙafarsa tare da saka kwanon a tsakiya ya shiga ɗakko gurasar yana bata a baki shima yana ci, idan ya bata sai ya saka a nasa bakin. Ya sake ɗakko ya miƙa mata har ta saka a bakinta ta turo ta faɗo hannunsa ta ce masa

"I'm full" ya É—an kalle ta anutse.

"Kuma kika fara sata a bakinki?"

Ta É—auke kai "To ba sai ka cinye ba kar a yi asarar abincin" ya kalli gurasar duk yawon bakinta kamar ba zai magana ba sai kuma

Ya ce "Abin baka zan ci jaririyar Innti?"

"Yap. Ai ni na ci fa"

"And.......?"

Ya É—ora da "I mean who are you to me?"

"Uhm mmm ba budurwa ba, ba mata ba, hmm ƙawarka ce ni, I'm your friend" girgiza kai kawai ya yi yarinyar da a haihuwar awaki ya yi jika da ita maybe. "Miƙo mini ledar can" tana juya ya cillar gurasar a bakinsa ya cinye tas. Ledar ta ɗakko Apple ne guda ɗaya a ciki sai Yougurt da Biscuits biyu.
Chapter 46 · 0% Book details