Sashe 17
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaa Sam ya jinjina kai. A hankali ya juya tare da bin bayan Ana ganin ta yi gaba ya ce "Madam, takalmin fa?" Sak ta yi sai kuma ta juyo a nutse bata yarda ta kalle shi ba, ta fito da kuɗin hannunta ta miƙa masa. Yatsun hannun Sam ya bi da kallo ganin wasu kwantatun gargasa kwance a kowacce gaɓa ta yatsun hannunta, sun yi kyau sosai gwanin sha'awa. Ya san nufinta da baƙar zuciya saboda ya ce ta tsallaka yaron shi ne ya gogawa kan shi laifi. "bata son kuɗin ta fasa siyan takalmin kuma" haka yanayinta ya nuna. Sai ya tattara ya yi watsi da ita tare da yin gaba duk yadda yaso ya yi magana da ita. Ita ma gida ta nufa zuciya ba daɗi. Ana bata san abin da take ji a zuciyarta ya yi ƙarfin da zai saka ta rasa sukunin zuciya ba, sai da ta ji kamar damshin hawaye a saman fuskarta, a hankali ta miƙa hannunta zuwa ga zagayayyiyar fuskar tata, ba hawayen bane domin ƙarfin abin bai kai girman da zai saka ta zubar da hawaye a banza ba. Amma me ya sa yake cin zuciyarta har haka? Bata sani ba, amma hakan baya rasa nasaba da yadda aka aibata mata uba a gabanta.
"Me ya sa zan ji zafi har haka? Me ya sa zan ɗauki lamuran Daada na ƙwarzafi raina da shi na hana zuciyata sukuni?" Ita da zuciyarta suke wannan taɗin, tana cilla ƙafafuwanta ba tare data san inda suke samun masauki ba, ta ji zafi tabbas.
Ta kuma ji raÉ—aÉ—i tabbas.
Bata san ta ƙarasu ƙofar gidansu ba, sai data na ƙoƙarin shigewa ta yi gaba ba tare data sani ba ta ji an yi saurin riƙo hannunta. Bata firgita ba, saboda dakkakiyar zuciyarta sometimes, rigima kuma a jininta kawai take.
"Daga ina? Yaushe kika fara haka?"
Idanunta ta watsa a saman fuskar Jadid ta dube shi na wani lokaci kafin ta tabbatar a ƙofar gida take ta raɓa ta gefensa ta shige. Wani abu na musamman dake sanyaya zuriyar Ana ganin abin data fi so a rayuwa.
Yanzu ma tana ɗora idanunta akan Innti da Iftihal ta ji ta nemi dukkan damuwar data cushe mata a tsakiyar ƙirji ta rasa. Iftihal ce ta kalle ta kafin ta ce "Mahaɗita ko dai mu tattara ki kawai ki koma gidansu Yaa Sam?"
"Da kin duba mini, ko babu komai zan huta da cin arne da kwat. Ya kike MahaÉ—ita?"
Iftihal ta ce "Ba lafiya ba, bani da lafiya"
A ɗan rikice Ana ta dafe ƙirjinta saboda wani azababben bugawa da ya yi mata, wani tsoro ya lulluɓe ilahirin ƙofofin zuciyarta, idan ba ta yi ƙarya ba, har wani zazzaɓi ta ji ya fara saukar mata. "Mene ya same ki? Me kike so? Ina ke miki ciwo, mene damuwar?"
Yadda ta rikice kawai Iftihal ke kallo tana jin wata sabuwar soyayyar abokiyar haihuwar tata yana sake samun gurbi na musamman a zuciyarta. Idanunta ya kawo ruwan hawaye ta sake tabbatar idan bata raye Ana zata samun bugawar zuciya, yanzu ma idanunta ya zama kamar ba nata ba, jikinta sai faman rawa da kakkarwa yake yi.
"Ayshatul-Haleeym!"
Innti ta kira sunanta da ƙarfi tana jijjigata, amma tuni ta fara rasa nutsuwarta daidai lokacin Babban yaya ya shigo cikin gidan shi da Jadeed tsayawa suka yi, Jaheed ya dubi Ifti, Babban yaya kuma Ana da ake jijjigawa ya zubawa kasalallun idanunsa masu kyau.
"Shalelen Innti... Ana.... Ayshatu....."
Innti ta faÉ—a a gigice.
"Babban yaya duba mini ita, Yaa Jadid É—ebo mini ruwa me sanyi a randa ka ji"
A kiɗime Jadid ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Ko dai aljanu ne suka shaƙe mata wuya, ko ta yi faɗa da wasu ne?"
Bata iya bashi amsa ba, gabaɗaya ta rungumeta a jikinta bata taɓa ganin girman yaranta, Iftifal fashewa da kuka ta yi tare da durƙushewa a wajan ta riƙe hannun Ana gam a cikin nata, cikin kuka take faɗin "Ki yafe mini mahaɗita, ba zan sake ba, ba zan kuma yi miki irin wannan wasan da zuciyarki zata kasa ɗauka ba, ki yi haƙuri" sai a lokacin Babban yaya ya fahimci abin da yake faruwa da kuma dalilin shigar Ana halin da take ciki, wato a kowacce haihuwar tagwaye akan samu mugu ɗaya da zai dinga gallazawa ɗayan, Iftihal ba mugunta take wa Ana ba, amma tana raunata zuciyar yarinyar da soyayyarta, jin cewa Ifti babu lafiya ya saka Ana fita daga hayyacinta.
A hankali ya durƙusa dab da fuskar Ana ya miƙa yatsun hannunsa guda biyu na tsakiyar ya shafi fuskarta kaɗan kafin a hankali ya sauke a gefen ƙirjinta ya danna a nutse. Ajjiyar zuciya ta sauke me nauyi jikinta ya saki a jikin Innti bata motsa ba, bacci ya ɗauke ta a nan jikin mahafiyarsu.
Innti ta dubi Iftihal ta ce "Iftihal....
"Na'am, Innti"
"Shin ba ki aminta da son da Ana ke miki bane? Ba ki yarda cewa zata iya rasa ranta idan bakya duniya ba? Ba ki yarda ba ko?"
"Na yarda Innti, wasa nake mata"
Innti ta ce "Wasa? Wasa da rayuwarta ko zuciyarta? Bari na faÉ—a miki za ki iya yi mata wannan wasan, wasan da har abada zai iya rabaki da ita, kar ki kuma na faÉ—a miki"
Cikin kuka da murya a raunace har ta fara dashewa ta ce "Na tuna Innti, ki yafe mini don Allah ba zan kuma ba in sha Allah"
"Shikenan, Allah Ya yi muku albarka gabaÉ—aya, Ubangiji Ya duba gabanku da bayanku ya tsare kima da mutuncinku"
"Amin" Iftihal da Jadid suka amsa.
Babban yaya ɗaki ya shige abin shi ba tare da ya ce komai ba, Jadid ya yi shiru ya zubawa Innti idanunsa kamar me buƙatar wani abu. Suna ta zaune har Ana ta farka, ko data farko ta manta da abin da ya faru ta ce "Gaskiya daga yau kullum a cinyarki zan dinga bacci uwata, kin ji laushi? Ubangiji Ya yi mini arziƙin da zan saka ki ji daɗi ki huta ki daina jin tuwo kwata-kwata, ki ce amin" Girgiza kai kawai Innti ta yi tana amsawa da "Amin" a zuciyarta. A hankali ta ja idanunta ta lumshe tana jin fresh air ɗin wajan na sake saukar mata da nutsuwa, abubuwa da yawa take son yin tunani akan su, na farko yadda zata rayu har abada ita da Innti da Iftihal, na biyu tunanin rayuwar mutanen da take gani a cikin baccinta, ta rasa dalilin da ya sa take mafarki dasu, ta rasa su waye, bata kuma iya hango haɗinta dasu ba. “MAMAA? UW?†ta furta a sanyaye domin sai a lokacin ma sunayen ya faɗo mata. Abu na uku alaƙarta da Daada ta rasa tudun dafawa domin har yanzu ta kasa gasgata cewa, shi ɗin mahafinsu ne, bai dace da uba ba sam.
Tattara maganar ta yi waje guda ta watsar. Ta juya ta kalli Innti ta kalli Iftihal sai ta ce
"Ni dai ku dinga saka ni a addu'a, Allah Ya bani miji kyakkyawa ko da maye ne shi" Ta yi maganar hankalinta kwance.
Iftihal murmushi kawai ta yi.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Innti ta zabga uban salati tana riƙe haɓa. Kafin ta ce "Ubangiji Ya miki zaɓi da mafi alheri a rayuwarki daku duka gabaɗaya ya nisanta ku daga abin ƙi, Allah Ya rabaku da auren maye. Maita babu daɗi" Ana ta yi shiru saboda tuna dramar ɗazo da aka yi da aka ce mata mayya.
Jadid ya ce "Daman gata nan kamar kazar mayu saboda rashin kuzari, tatsa É—aya zai mata ya suÉ—e abin shi, ji jaraba wai maye?"
Idanunta a lumshe ta ce "Allah idan na auri mummunan miji zan iya haɗiyar zuciya, ina son abu me kyau, ina son kyakkyawan miji ko Aljani ne...," bata ƙarasa faɗa ba Babban yaya ya fito yana kallon ta, itama kallon shi ta yi ƙwayar idanunsu suka shiga cikin na juna ya ɗauke kai yana yin waje abin shi.
"Innti kin gama É—inkin atamfar nan?"
"Wanne É—inki? Abin duniya duk ya daman bayan kin ce ya yi kyau kin fita daga nan na rasa meke faruwa dani, komai ya lalace gashi yanzu atamfar jama'a ta yi kaca-kaca"
Miƙewa ta yi ta nufi inda taga atamfar tana ɗauka ta tuntsire da dariya ta ce "Daman abu ya fiya kyau masifa ne, Allah ya kyauta"
***
Bayan ya kammala gyarawa wani wayarsa da ta ci screen ya ajjiye sannu a hankali ya zubawa gefe guda idanu, ya ɗan girgiza kai sai asalin kamannin da yake dashi na zubi da labarabawa suka fara bayyana, yana tsoron wannan sauyin yanayin a cikin jama'a kar su dinga gudunsa, shi kan shi bai san meke faruwa da rayuwarsa ba, tsakanin baƙar fatar da farar fatarsa me sheƙi da ɗaukan idanu wacece asalin halittarsa? Ya miƙe a hankali ya shiga takawa ya ƙarasa jigin bango madubin dake maƙale ya kalla, daya kalli fuskarsa shi da kan shi ya ji tsoron ace shine wannan domin kyawun fuskar ya yi masa yawa, kyawun da zai zame masa bala'i ne. Waye shi idan ya ɗauke cewa shi Babban yaya ne? Ya tattara maganar ya watsar yaje ya zauna saboda gajiya da yunwa tunda uban gidan nasa ko kwabo har yanzu bai bashi ba. Bacci ne ya ɗauke shi a wajan.
Babu jimawa ya ji iska na kaɗa shi, sanyin ruwa na ratsa jikinsa ga ƙarar tsuntsaye na tashi alamar yana cikin daji ne. Ya buɗe idanun, bai san alaƙar da yake da ita a wannan wajan ba, bai san me ya sa yake zuwa nan ɗin ba. Numfashi ya ji yana sauka a fuskarsa kafin ya gama buɗe idanunsa ya ji siriyar murya ta shiga kunnensa an ce.
"KaÉ—o....
Ya yi saurin janye fuskarsa, sai ta kuma matso da tata har goshinta na sauka a nasa, ta washe fararan haƙoranta masu kyau ta ce "Kai kaɗo ne ko? Kai kyakkywa ne zaka zo a yi mana aure irin wanda ake yi?" Nan ma bai magana ba sai kallon ta kawai da yake yi, ya zame kaɗan ya yunƙura ya tashi sai a lokacin yaga ɗanyen barkonon data yatsar a wajan.
"Wayyo Allah, kana da kyau kai kyakkywa ne, amma baka da lafiya shi ya sa baka da kuzari"
Ya yi mata shiru.