← Book details Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 64

Sashe 5

Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bashi da masaniyyar yadda rayuwar Ifti zata kasance idan tsohon ya mallake ta a caca, domin mutum ne me shekaru 62 a duniya, kaso ɗaya daga cikin haƙoransa duk a cinye suke, sauran kuma goro ya yi musu ado da lalle, sun yi jawur ko magana ya yi warin goro ke fita, ƙoƙofin gidansa, kulle suke da mata huɗu cif, yaransa, da jikokinsa kamar gyaɗa saboda azabar yawan da suke dashi.

Haka gidansa yake, kamar rayuwar bariki.

"Ka saka Iftihal a cacar nan da Alhaji Baita ya yi maka ta yi, kana kallon yadda ka haɗa zumunci da talauci dai" cewar Ɗahe yana cilla kartar a ƙasa da murmushin ƙeta

Ƙwarai da gaske, Daada da talauci kamar tagwaye ne, suka fito daga mahaifa guda, ko dai yaga bayan talaucin nan, ko kuma shi talaucin yaga bayan Daada ya kai shi zuwa inda ba'a dawowa idan anje.

Ganin Daada ya yi shiru, yana ta jan sigarin hannunsa, ya ajjiye kartar da suke bugawa, ya saka Malam Ɗahe miƙa hannunsa zuwa kafaɗar Daada ya jijjigata, alamar tabbaci akan shawarar da yake basa, wacce babu zamba cikin aminci a tattare da ita ya ɗora

Da "Ka saka a ranka, É—iyarka ce jarinka"

"Amfaninta kenan" Ya nanata yana jinjina kai, alamar tabbacin maganarsa ga Daada.

"Su yara mata dukiya ne, kadarar rufawa kai asiri, ka amince ka saka Ifti a cikin cacar nan, sai ka ga ta ciwo maka maƙudan kuɗaɗe kuma yanke talauci wlh"

Garba ya riƙe zancen daga wajan Malam Ɗahe, yana sake yi wa Dadaa ingiza me kantu ruwa wajan sanya ɗiyarsa mai hankali da nutsuwa da kamala, kyau da tsarin halitta. Dadaa ya yi shiru yana tunani, idan abin da yake buƙata ne a zuciyarsa, bai shige kuɗi masu ɗumbin yawan da zai iya sake dulmiya su a cikin cacar ya sake cin ninkin su ba, yana son kuɗi fiye da duk wani abu da yake cikin wannan duniyar, ƙamshin jaka guda kaɗai dagula masa lissafi yake yi balle yaga fara ƴar shehu, mulmulalliyar dubu ɗaya, ko notikan kansa basu kunce ba, da ƙyar yake iya hattama nutsuwarsa ya daidaita zuciyarsa gudun murna da zumuɗi kar su yi masa illar da zai gaza ganin bayan dubu ɗayan. Ya dube su, yana nazari.

Yana buƙatar lokaci,lokacin da zai tantance mene yafi muhimmaci a gare shi, a tsakanin ɗiyarsa Iftihal da dukiyar da ake magana akan ta, sai ya nutsu, yadda zai tantance

Me ake nufi da zuri'a ta Æ´aÆ´a mata,
Me ake nufi da arziƙi masu rufin asiri.

"Ina buƙatar lokaci"

Ya furta yana miƙewa tsaye.

"Wanne lokaci kuma kake buƙata, ƴa dai taka ce, kana da iko da rayuwarta, kamar yadda miliyan ashirin ɗin nan suke jiranka"

"Malam ÆŠahe, a bani lokaci, bari zan je na dawo sai mun haÉ—u zuwa tsakiyar dare ko safiya ko kuma war haka yammacin nan"

Wani irin maƙetacin murmushi Alhaji Baita yake wanzar dashi a fuskarsa, murmushin da indai a kaga ya yi a cikin abu biyu ne za'a samu guda, wanda ya zama zakarar gwajin dafi. Ko dai budurwar zuciyarsa ta hango masa kyakkyawar matashiya wacce zai huta ya more tsofansa a jikinta, ko kuma an yi masa batun caca, me kawo ruwan kuɗi.

Musamman da idan ya rufe idanunsa yake hasaso tsanain kyawun fuska irin na Iftihal

Da faffaɗan ƙugunta,wannan mazaunan daya zauna das, ta cikin hijabin daya kwanta a bayanta ya hango hakan. Yabi Daada daya shige ya bar wajan da kallo, tare yin kwana ya ɗauke idanunsa yana kallon Garba ya ce

"Garbati"

Cikin rawar jiki Garba ya amsawa Alhaji Baita da murmushi a fuskarsa

"Ni kaÉ—ai na ga yarinyar nan Æ´ar wajan Daada, ko kaima ka ganta don Allah?"

"Alhaji wai Iftihal kake nufi? Daman baka da labarin tagwayen yaransa, Ana da Iftihal? Ai kaf unguwarsu babu yara masu kyawun É—iyoyin Daada" Garbati ya shiga labartawa Alhaji Baita bayani akan su Ana da Iftihal "Ita wacce ta shige ita ce Iftihal ana ce mata Ifti, É—ayar ta gida kuma sunanta Haleeym ana ce mata Ana, kyawawa dasu"

Wani yawo ne ya taro a ƙasan maƙoshin Baita cike da zalama ya ce "Kasan da yarinyar nan baka taɓa bani labarinta ba?"

"Alhaji tuba nake, na gansu ƙanana ne yanzu fa suke aji uku na Sakandire"

"Irin waɗannan sabbin ƙinƙisar nake so, a ganin farko yarinyar nan ta dagula mini lissafi sai tsiyaya nake ta yi ta ciki"

Garbati ya shanye mamakinsa, wajan yin amfani da tafin hannunsa zuwa bakinsa ya rufe, ya sauke muryarsa a ƙasa kamar wanda wani zai ji me zai faɗawa Alhaji Baita ya ce "Ko zaka ƙara miliyan goma akan ashirin ɗin nan, yadda za mu samu damar shawo kan Daada ya afka cikin cacar, ina da yaƙini kai zaka lashe tunda ka fisa iya yin wasan nan nesa ba kusa ba, idan ka cinye sai ka yi gaba da ƴarsa ka more abinka, amma wani hanzari ba gudu ba, ka rufe ƙofofin gidanka, kar wankin hula ya kai mu zuwa dare, babu abin da ya rage maka na jerin ɗakuna huɗun nan sai dai ka haƙura" da wani irin yanayin da yake nuna Alhaji Baita yaje ƙarshe, irin wa'adin da ba zai iya tausasa zuciyarsa har ya gamsar da ita akan ta yi haƙuri da Ifti ba, ya ce

"Sai na buɗe ƙofa ɗaya, ka ga an samu sarari zaman Iftihal a ciki ko?'

Ya yi furucin yana kallon Garbati.

Caraf Garbati ya ce "Wannan ma ya yi"

***

Duk yadda Ifti ke sauri kar Babban yaya ya rigata cimma isa gida kamar yadda idanunsa ya nuna gargaɗi a gare ta, tafiya take yi cikin ɗan karsashin da ya yi mata saura a matsagaicin jikin nata, ta na yi tana juyawa ko Daada ya biyo bayanta, sai taga babu komai dake biye da ita sai ƙurar iskar bazarar dake tashi, a haka ta dinga bin jigin bango tana gujewa kwatocin lungun data shigo cike da taka tsantsan, kamar bangon da take bi zai tsake ta shige ciki, tana karyawa lungun da zai kai ta gida, tun a bakin hanyar ɗaya lungun wanda ya kasance yana da mahaɗa biyu ta hango shi yana tafiya, kamar baya son takawa, idan ya cire ƙafa ɗaya sai ya mayar da ɗaya, hannunsa duka biyun ya adana su cikin aljihun wandonsa, hular tsakin daya saka ya ɗan karkatar da ita zuwa gefe guda a kan.

Buɗewar farar manyan idanunsa, da yadda ƙwayar idanun ta juya a cikin gurbinta, ya bawa Ifti tabbaci yake bata akan zai ci ubanta idan ya rigata ƙarasawa cikin gidan.

Sai ta ƙarawa tafiyarta sauri, wuf kamar iska ta ƙarasa shigewa da gudunta tana haƙi.

"Ass... Assalamu alaikum"

"Wannan gudun ke kuma na mene? Gudu kina ɗiya mace haba ƴar albarka irin arziƙi a bari don Allah"

Innti ta faÉ—a bayan ta amsa sallamarta.

"Wallahi Babban yaya na gani"

Ta ce da ƙyar tana juya idanunta, sai kuma ta zare hijabin jikinta ta rataye saman igiya tare da ƙarasawa kusa da Innti dake bakin murhu tana tuƙa towon masara. "Barka da gida Innti, kawo na ƙarasa miki aikin ki wuta kin ji uwata?" Innti ta girgiza kai ta ce

"Jeki abinki ki huta ƙasan bishiya kafin a kira sallar magariba ku tafi makarantar dare ko"

"Allah sarki uwata, Ubangiji Ya yi mini arziƙin da za ki huta, Allah Ya kula mini dake Sahibata" murmushi kawai Innti ke yi.

"Mutuniyar abin Æ´ar haka ne? Innti kawai kika gani a taskar gidan ashe?" Cewar Jadid

"Tuba nake Yaa Jadid"

Ta ce tana ƙarasawa ƙasan bishiyar da yake zaune saman tabarmar da Ana ta yi bacci akai, labari sosai Ifti ta shiga bawa Jadid suna tafawa kamar ba yayanta ba.

"Sannu da dawowa yaya"

Suka haɗa baki ita da Jadid wajan faɗa suna daidaita nutsuwarsu, jinjina masu kai kawai ya yi sanda ya shigo ɗin, a hankali kuma ya durƙusa daidai inda Innti take yin aiki yana ɗan lumshe idanunsa saboda hayaƙi, ta juyo ta kalle shi, shima ya ɗan kalle ta, da body language ya yi mata magana sai ta ce "Sannu da hanya yaya, kaga ka riga Jaheed shigowa yau, shima na san yana hanya duk inda yake, wataƙila bai kammala sallamar mutane ba, tunda uban gidan nasa ya ce kamar ya yi tafiya shi kaɗai ne a katin yau"

Shiru Babban yaya ya yi.

Da nutsuwa kuma ya miƙe ya shige cikin ɗakinsu, wanda suke kwana su uku a ciki.

"Innti wai ina MahaÉ—ita ne?"

"Wai Shalelen Innti?"

Maganar Jaheed ta riga shi shigowa cikin gidan, ya ƙarasa maganar sanda yake durƙusawa a kusa da Innti cike da ladabi ya ce "Sannu da aiki Innti" cikin kulawa ta amsa masa "Yanzu nake maganarka yaron kirki"

"Sai gani ɗan halak yaƙi ambato"

"Ma sha Allah, Allah Ya yi muku albarka ya kare ku daga dukkan sharri da abin ƙi"

"Amin"

Da ita suka amsa.

"Innti wai ina MahaÉ—ita?"

"Sannu kashin awakai, tana cikin ɗaki kin san yau da miskilanci ta tashi, gashi ana abokin gaban nata, ƙato da kwat" inji Jadid.

Dariya sosai Jaheed ya yi kafin ya ce

"Tuwo da miyar kuka"

Duk kiran da Ifti ke yi wa Ana ƙin fitowa ta yi, sai da aka kira sallar magariba sannan ta fito tana kame fuska taƙi yi wa kowa magana, tana shirin ɗaukan buta ta ji an zabga mata ranƙwashi a kanta, zafi da raɗaɗin da ta ji ya sauka har tsakiyar ƙwaƙwalwarta, yatsun ƙafafuwanta suka shiga rawa da kakkarwa, jikinta ya dinga tsuma kamar ya watsa mata ruwan sanyi, da wani irin rawar jiki ta ɗago har wani ruwa ne yake kwanciya a cikin manyan idanunta wanda suka samu surki da wata zaiba, blue- blue haka cikin idanun Ana suke, kodayaushe kamar an yi mata ado da kwalli haka suke nuna wa, saboda wani ɓaki siriri daya zagaye ƙasan idanunta da saman idanun wanda ya ƙarawa ƙwayar girma wai da aniyya, girmansu ya yi daidai da tsarin zagayyiyar fuskarta. Ganin Babban yaya tsaye da buta a hannunsa ya saka ta yi sak.Curarriyar girarta ta tattare waje guda.

Ta kafe shi da idanun da lokaci É—aya suka fara surkawa, gefenta ya bi ya shiga banÉ—aki abinsa ba tare daya sake bi ta kanta ba, Ana tabi hanyar da yabi da kallo.
Chapter 5 · 0% Book details