Sashe 42
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Anwar na daidaita tsayuwarsa ya ce "Kana nufin ba kai ne ka tura ɗan'daban Bright fm ba?" Cikin kiɗima da gigita baba ya ce "Wallahi bani bane, ni bani da yaro namiji ma, balle na samu saurayin ɗa ka tambayi maƙota ka ji. Wallahi ban san an yi ba, ban aika kowa ba, na san har zuciyata ban ji daɗin abin da yarinyar ta yi ba saboda ɓata mini suna zai yi kuma wataƙila azo har gida aka me mini matata. Amma ban tura kowa yin wannan ɗanyen aikin ba ka yarda dani" Anwar ya hura iska kaɗan daga cikin bakinsa yana karkaɗa ƙafa ya numfasa ya ce "Baba ka yi haƙuri kana under suspect ne, ba zaka iya cire zarginmu akan ka ba. Ka yi haƙuri za mu tafi dakai domin yin bincike, idan gaskiya ta wanke ka shikenan" jikin Baba duka rawa da ɓari yake saboda tsoro
"Na shiga uku ku yi mini yawan rai, bana son abin da zai kai ni wajan Æ´an sanda"
Ya haɗe hannu bibbiyu yana bawa Anwar haƙuri, Anwar ya nuna Md ya ce "Wannan zaka bawa haƙuri bani ba, case ɗinsa ne" Tun kafin Baba ya yi magana Md ya buɗe mota ya shige ciki, kafin kace wane aiki jama'a sun taro a wajan ana yamaɗiɗin an kama Malam Sani saboda abin da suka yi wa amaryarsa na rashin kyautawa shi da uwar gidansa, da uwargidan ta ƙonewa amaryar jariri saboda ta haifi ɗa namiji ita kuma tana baƙinciki bata taɓa haifar namiji ba, mutane sunga rashin kyautawar hakan. Gashi amaryar me haƙuri da nutsuwa da biyayya. Zance ya isa har kunnen Talatuwa uwar gidan Alhji Sani ta dinga danna ashar wai ƴan unguwar sun zama munafukai sun wa mijinta shunan ƴan sanda a kama shi.
*
Ahlam ta jima zaune a reception na Hisba amma babu wanda yabi ta kanta miƙewa ta yi ta nufi wajan wani da yake sanye da uniform ta ce "Sannu da aiki ya ƙoƙari" Ya ɗan dube ta kaɗan ya ce
"Aiki Alhamdlh"
"Sunana Ahlam Abdallah Kurmi matashiyar ƴar jarida a Bright Fm" ta ƙare maganar tana nuna masa ID card ɗinta. "Alfarma nake nema idan zan samu, kusan na ce taimako ma ɗan'uwa idan zan samu" Ya ce
"Daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaƙi? Har na zama ɗan'uwa. 3 minutes da suka shige a ban sanki ba kike" murmushi ta yi masa ta ce
"Mu Æ´an jarida kowa namu ne" ya jinjina kai
"Ok me kike buƙata yanzu?"
"Appointment, na interview da Sayyadi Baffa" wani irin buɗe idanunsa ya yi da mamaki ya zuba mata ido daga sama zuwa ƙasa.. ya kasa cewa komai.
"Ko baka ji ba?"
"Na ji. Kin zo da abin da ba za ki taɓa samu ba yarinya. Ki yi haƙuri ki nemi wani" girgiza kai ta yi Idanunta na ciccikowa da hawaye ta ce "ka taimaka mini, wallahi interview dashi shine kaɗai hope ɗina. Ko numbersa ce a ka bani zan yi magana dashi, idan kuma yana nan ka yi mini iso a wajansa"
Mukhtar ya ce "Hajiya ko mu da muke tare dashi numbersa bai taɓa shiga wayarmu ba, balle wasu. Ki yi haƙuri ki koma, ko kuma ki yi Interview ɗin dani kawai" a sheƙe ta kalle shi da kyau. "Yaushe zan gashi?"
Mukhtar ya ce "Babu rana"
"Me ya sa babu rana a ganinsa? Help me"
"Muma ba ganinsa muke ba, bata wannan ƙofar yake shigowa ba, ba kuma tanan yake fita ba. Za mu iya yin fiye da watanni 8 bai saka mu a idanunsa ba, muma haka. Maganar da nake yi miki baya gari yaje da'awa ne" Ahlam ta riƙe kai tana sakin numfashi. Kamar ta zunduma ihu haka take ji a ranta murya a karye ta ce "Na gode" tana ƙoƙarin fita daga headquarter ɗinne daga jerin motoci wajan huɗu sun shigo ciki, motoci na alfarma da tsari wani irin sanyi ta ji yana saukar mata a zuciya da farinciki gani take buƙatarta ce zata biya, har ranta ta ji cewa Sayyadi Baffa ne ya dawo. Bayan sun yi parking wani da jikinsa yake a buɗe yaje da sauri ya buɗe bayan motar dake tsakiya, hakan ya saka Ahlam buɗe ido, madadin taga ƙafar namiji sai taga farar ƙafa ta fito sanye da takalmi me tsini wanda yake da igiya, a hankali kuma wacce take cikin motar ta fito tana sanye da abaya me kyau ta yi rolling kanta shigar Larabawar ya amshi fatar jikinta da kyau ta shagala da kallonta da yadda aka mara mata baya, har bata san ta shige ba, sai data dawo tunaninta taga babu kowa a wajan, idanunta ya sauka akan ɗan card ɗin daya faɗo ta ɗauki card ɗin ta saka a jaka duk da bata san na mene ba ta yi gaba.
Bright FM ta yi zuciyarta a cunkushe da damuwa, tana tunanin shi kenan babu wani award da za'a iya bata a wannan taron.
*
A can Kankarofi Yaa Jaheed ne ya fara shigowa shine kuma ya fara ganin halin da Yaa Jadid yake ciki, a gigice ya ɗauki ruwa ya dinga shafa masa, fuskarsa ta kumbura sosai da hannunsa da ƙafa cikin ikon Allah ya farfaɗo, sai ya farfaɗo da wani irin masifaffan ciwon kai da zazzaɓi ya shiga yin amai mara kyan gani. Yaa Jaheed ya buɗe Innti ganin halin da Jadid yake ciki ta fara salati Idanunta cike da hawaye, duk wani abu da take tunanin tana dashi ya ƙare bata da komai ta rasa tunanin da za ta yi. Yaa Jadid ya riƙeta
"Innti mutuwa zan yi ki yafe mini"
"Yaa Jadid ba zaka mutu ba, zaka samu lafiya in sha Allah zanga aurenka da yaranka da izinin Allah za ka ji daɗin rayuwa kaima" ta faɗa tana rungume shi zuwa jikinta. Jaheed ma ya durƙusa wajan riƙo hannun abokin haihuwar tasa. Suna zaune Babban yaya ya shigo idanunsa wasai wannan karan kamar kuzarin jikinsa ba irin na baya bane.
"Kada ka buÉ—e É—akin nan Babban yaya"
Innti ta faɗa ganin ya nufi ɗakin da Daada ya rufe Ana a ciki, baya son musu da Innti kamar yadda baya buƙatar barin ƴarsa a ciki. "Ban san wanne kunne gare ku ba, ba zaku taɓa barin bakina ya zauna lafiya ba, na yi yaƙi da kai Yaya na yi da ƙannenka? Na faɗa muku maganar Daada da abin da ya yi dole ku yi biyayya akai muddin kuna son na zauna lafiya daku. Ba zan taɓa yafe muku ba idan kuka bijire masa wallahi" wani abu Babban yaya ya ji ya sauka a ƙirjinsa, ya haddasa masa wani irin ciwon kan daya fara gani dishi-dishi. Damuwa da takaicin rayuwarsu da bai taɓa yi ba shine yake yi a yanzu. "Innti haka za mu yi rayuwa?" Cewar Yaa Jaheed
"Allah yana sane da komai, zai shiga cikin lamuranmu ya kawo mana tallafi in sha Allah" Yaa Jaheed ya ce
"A samu abu a bawa Jadid"
Ta kalli Jaheed É—in tana shafa kan Jadid ta ce "Bani da komai sai hukuncin Ubangiji Yaa Jaheed"
Gently ya shigo cikin gidan yana takawa a hankali da nutsuwa da kamala sai ƙamshi yake yi irin ƙamshin turaren marasa shi ɗin nan, excuse ya ɗauka a wajan wanda yake bi layi akan zai dawo gida yaga ƙanwarsa bata jin daɗi.
Da murmushi ta ce
"Haysaam?"
"Na'am" ya amsa yana kallon Jadid dake cinya, kafin ya ɗauke idanunsa ya durƙusa ya gaishe shi ya ce "Jikin nasa ne kuma?"
"Shine Haysaam amma da sauƙi Allahamdulilah"
Ya jinjina kai a gajarce ya ce "Allahu ya bashi lfy" suka amsa da amin. Jaheed ya gaisar da Haysaam shi kuma Yaa Sam sukai musabaha da Babban yaya, sanyin hannun Babban yaya ya bawa Yaa Sam mamaki sosai. "Mutuniyar tana cikin É—akin can tun jiya Daada ya rufe ta"
Bai magana ba ya miƙe ya nufi ɗakin zuciyarsa na tafasa da ace Daada bashi da alaƙa da Ana wallahi da yau babu me ƙwatar shi a duniya sai Allah. Wanne irin uba ne shi wai? Ƙafa ya saka ya daki ƙofar ta buɗe. Tana kwance tsananin azaba ya saka ta yi fitsari a wajan idanunsa ya fara kawar wa gefe saboda rigar jikinta da take yaye, babu ko halfvest a jikinta balle rigar Mama.
Ya saka yatsu biyu ya rufe mata jiki ya zubawa fuskarta idanu yana jin wani abu na buɗewa a ƙirjinsa tare da harba masa fiye da adadin tafiyar lokaci, ta yi masa kyau a yanayin baccinta ko suman, a karo na farko ya rusketa a yanayin da bai taɓa ganin wata ƴa mace a duniya ba.
"I'm very sorry Jerry"
Ya san zata ji haushinsa idan ya bata labarin yadda ya ganta, amma zai adana wannan maganar har zuwa lokacin daya dace ya faÉ—a.
"Nanaah"
Ya furta silently yana É—an bubbuga gefenta bata motsa ba, ya kai fuskarsa dab da datata ya buÉ—e bakinsa ya shiga hura mata iska a fuska ya yi using yatsu biyu wajan goge mata zufar fuskarta.
"Yaa Sam....
"Yaa Sam ka tafi dani, zan bika zani"
Shine abin da ya ji tana faÉ—a cikin mawuyaci hali. "Zani dake in sha Allah, ba zan koma Lagos ba sai dake Nanaah, open ur eyes"
Ta buɗe Idanunta suka kalli juna, ta ɗauka mafarki take yi miƙe a gigice ta riƙo hannunsa ta shiga tattaɓa shi ta koma kan fuskarsa ta shafa. Ya yi saurin riƙe hannun nata ya ce "Stop, Haysaam ne ba Aljani ba"
Yana furta hakan Babban yaya ya sako kai cikin ɗakin da sauri Ana ta miƙa masa hannunta ta ce "Abbaa"
Ya riƙo hannunta cikin nasa ta miƙe tsaye jikinta duka rawa yake yi da ɓari ganin haka ya ɗan jata gefensa ya rungume yana shafa kanta. "Bari na je, kizo gida ki saman" Haysaam ya furta yana juyawa, yana jin kamar ya ɗauki Ana ya tafi da ita gabaɗaya.