Sashe 14
Hiyaam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta sulale a wajan tana dafe kanta, daidai nan messenger ya shigo da sauri yana faɗin "Golden voice kin yi baƙuwa a reception" bayan messenger tabi tana zuwa ta hango matar, wacce kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci Bafullatana ce, da kuma ɗanyen jikin dake tattare da ita na haihuwa.
Tana ganin Ahlam ta zabura tana durƙushewa ta ce "Ki taimaka mini kar ki saka abin nan a iska yabi duniya, ki taimaki igiyar aurena kar a sake ni, idan ya rabu dani wallahi yanka ni za'a yi a gida, ki tausaya wa rashin gatana nasan ke macace, ba za ki so na wulaƙanta ko aurena ya mutu ba, na haƙura na bar komai a wajan Ubangiji don Allah kar ki saka na roƙeƙi" baya da baya Ahlam ta fara ja, jikinta na rawa da kakkarwa ta juya a guje zuwa studio wanda aka rufe ko'ina gudun kar iska ta shiga, tuni Yussy ta shirya komai gabatarwa kawai ya rage, tana ƙoƙarin buɗe ƙofa ta ji an buga mata uwar tsawa a firgice ta juya idanunta ya sauka akan Md ɗin.
***
Ƙafarsa ta ɗora ɗaya kan ɗaya idanunsa zube cikin farin glasses da kaya na shan iska a jikinsa, ƙasaita kamala da ilimin zamani da gogewa ta shiga cikin manyan mutane ya gama zama a jikinsa. Labarai yake kallo a Aljazira girman parlourn kaɗai abin kallo ne. Wayarsa ce ta fara ƙara alamar shigowar kira ya juya kaɗan, sai ya miƙa hannunsa me ɗauke da gargasa zuwa kunnensa ya gyara zaman Bluetooth.
"Indabawa ya ake ciki?" Ya furta a tausashe yana sake lumshe idanunsa.
"Abin da kake jira ne, Government house ta fitar da sabbin forms na É—aukan matasan da suka kammala University babu aikin yi, an fitowa da tsarin Allowance for the other students da basu samu Form na aikin ba da za'a dinga musu shi monthly" ya yi jim.
Indabawa ya ce "Kana jina?"
"Wane ya akai wannan buƙar ga Shugaba? Wa aka bawa damar rabawa local government forms ɗin da Reps?"
"Actually ban sani ba, amma kai aka bawa duka forms ɗin ta hannunka za su fita" sai a lokacin ya saki ajjiyar zuciya ta samu nutsuwa ya ce "Ina ga abin da za'ayi, zan ɗan rabawa rukuni sai ku bawa familys naku, za'a sanar a Internet dama ga masu son aiki su je Government house a tantance aiki ne kyau ga wanda suka kammala University suka fita da first class, sauran aikin zan sanarwa da Kalido yadda za'a tsara, ba za'a raba ko ɗaya ba, duk me buƙata siyar masa za'ayi, idan mata ne a tura su office ɗin P.A na, idan sun ji jarrabawar da ya yi musu sai a basu"
"Yadda ka ce haka za'ayi, Allah Ya taimake ka, na hannun daman Shugaba ƙasar taku gwamnati taku" ɗan murmusawa kawai ya yi kafin ya kashe kiran.
***
Iftifal ce ke tafiya daga aiken da Innti ta yi mata na karɓo kuɗin adashi, tun daga nesa ta hango majalisar dasu Daada suke zama, kamar koyaushe yana zaune suna karta sai busa sigari Daada yake yi yana fesarwa tazo dab dasu ta durƙusa har ƙasa tana wasa da yatsun hannunta da suke farare tas abinsu.
"Ina yininku?"
Ta ce a sanyaye da murya me laushi.
Alhaji Baita ji ya yi wani abu ya yi masa zillo ya tsarga masa, kamar tsohon maye haka ya shiga suɗe bakinsa yana washe haƙoransa masu jan goro, nan da nan ya rasa nutsuwarsa sai riƙe wando yake yi.
"Lafiya lumi Iftihal, unguwa za'a ne?" Garbati ya amsa mata yana zungurin Alhaji Baita. Jinjina kai kawai ta yi, shi kuma Alhaji Baita ya karkace yana zaro kuÉ—i sabbin Æ´an dubu dubu har dubu biyar ya É—auka ya bawa Ifti. "A'a Baba, na gode"
"Ke Iftihal amshi, don ubanki"
Ta ji muryar Daada.
"Daada Innti ta hana mu amsar kuÉ—i wajan wanda bamu sani ba, babu kyau ta ce" Alhaji Baita ya ce
"Ayya ayyya, ban ji daÉ—i ba nine ba ki sani ba Alhaji Baita? Abokin mahaifinki ne ni Æ´ar nan"
"Wallahi ban sanka ba"
Ta faɗa a tsorace, tsawar da Daada ya yi mata ita ce ta saka ta amshi kuɗin tana yin godiya kana ta miƙe ta tafi. Bayan ta shige Garbati ya ce "Daada kaga irin arziƙin da yake tattare da yara mata? Wallahi ko sabon gari ka kai su, ka kama musu shago kaga yadda za'ayi taruruwar tayin su, kamar nama a miya haka Ana da Iftihal za su zama, ka amince da wannan cacar Dada"
Daada ya numfasa yana kallon Alhaji Baita, kafin ya ce "Baita ka tabbatar Miliyan ashirin zaka saka a wannan cacar? Ka tabbata ko?"
"Haba Daada, ba ƙaramin mutum bane ni, kaf unguwar nan waye kullum ake miya da nama a gidansa idan ba ni ba? 20 Millions ne cash" Daada ya shiga lissafin dokin Rano, rayayye da matacce, hango kan shi cikin daula da arziƙi yake, hango yadda zai gina tangameman gida, ya siya mota da abubuwan mure rayuwa, yadda zai ƙara aure ya ajjiye mata har huɗu, ga Tani a gefe biyar cif kenan. "Na amince, na amince"
"Na amince wallahi, da gaske na amince"
"Ka amince dame?"
"Na amince da saka Ayshatul-Iftihal, Ifti a cikin cacar, ina da yaƙinin ni zanci" wani irin shu'umin murmushi Garbati ya yi ya juya ya kalli Alhaji Baita kafin ya ce
"Sai a yi komai a rubuce ai"
Suka É—akko takadda kowa ya yi rubutu.
"Ni Alhaji Baita na saka Naira miliyan ashirin a wannan cacar, idan Daada ya ci, zan bashi kuÉ—in, kamar yadda sharuÉ—an cacar yake"
Shima Daada ya rubuta.
"Ni Daada, na amince da saka Æ´ata Ayshatul-Iftihal Ifti, a cikin wannan cacar, idan Alhaji Baita ya ci, zan mallaka masa Æ´ata Iftihal da hannuna"
Aka saka kwanan wata, da saka hannun kowa dana shaidu suka tsayar da ranar da za'ayi wasan kamar yadda aka tsara.
Da saurin daya rage a jikinta ta nufi gidan nasu, kanta a ƙasa tun kafin ta ƙarasa ta hango shi tsaye ya harɗe hannunsa a ƙirji, milk ɗin shadda ce a jikinsa ta haska farar fatarsa ya ɗora zanna bukar a kan shi, sajen gefe da gefen fuskarsa sun yi kwance yana da tsayi da buɗewar ƙirji babu alamar wasa a tattare dashi. Ta durƙusa har ƙasa ta ce
"Yaa Sam, ina yini"
Daga sama har ƙasa yake kallon ta ya yi shiru har sai data sake maimaita kanta. A hankali ya ce
"Lafiya" ya faɗa da ƙyar.
"Bari na faɗawa Ana ka dawo, ƙila bata sani ba....," bata ƙarasa faɗa ba, ta hangu su, su huɗu jere sanye da Jallabiya a jikinsu suna tafe suna rangaji da yarfe hannu zuwa gefe, sai karairaya suke yi kamar babu ƙashi a jikinsu, babban cikinsu ya saka ɗankwalin atamfa wajan ɗaure ƙugunsa dashi ya rataya baƙar jaka a kafaɗa, suna tafe suna hira sai su yi shewa su tafa. Ganin haka ya saka ta yi saurin cewa "Yaa Sam bari na shiga na kira maka ita yanzu yanzu" ta yi saurin shigewa ciki gudun kar su same ta.
Yana ganin sun ƙarasu ya shige gidan dake kusa da gidansu Ana abinsa.
Ana na zaune tana duba É—inkin da Innti ta yi tana mai yaba rigar wajan faÉ—in
"Gaskiya ɗinkin nan ya yi kyau Innti, irin shi za ki yi mini da ƙaramar sallah kin ji uwata"
"Allah Ya nuna mana Indo, yasa muna raye"
"Innti ga Baba Bala nan"
Iftifal data shigo ta faɗa a ruɗe, kamar walƙiya haka Babban yaya ya shige ɗakinsu.
"Gafaranku dai"
Suka furta a tare suna shigowa cikin gidan, Ana da Iftihal suka yi saurin komawa waje guda, Innti ta amsa da "Allah yai mana"
Suna shigowa tsakiyar tsakar gida, suka yi shewa "Ahayye... Riiiii" suka game kwankwaso waje guda ana karya kai gefe guda. Hakan ya faru bayan ido biyu da sukai da rigar Maman Innti dake shanye a igiya.
"Yaya ga abar fa"
Ƴar Beauty ya ce yana saka dariya
Ya maƙale hannu a kafaɗa kamar mai shan inna yana tauna cimgam ƙas ƙas. "Sai dana fito naga wannan na tuna ashe tsirara na fito" wanda aka kira da yaya ya faɗi hakan
"Kai Yaya, haka maza suka ƙare miki kallo a hanya ashe?" Cewar Abar ƙauna.
Sukunbiya ya rangwaɗar da kai. "Bari kawai, shi ya sa na jini tantsan tantsan, ba tsiya ba arziƙi ki ce a ɗaiɗaice na fito" ƙas ya faɗa yana bada sauti.
Tiƙa-tiƙan maza ne, wanda akewa laƙabi da ƴan daudu suke maganar a tsakaninsu.
Ita dai Innti É—inkinta kawai take yi.
Ƴar Beauty ya kalli Sukunbiya ya ce. "Yaushe duniya ta yi tunbuɗi na fitar da sabbin ƙinƙisa a gidan nan Yaya?"
Sukunbiya ya ce
"Ke uwar gane gane, Æ´aÆ´ana ne su fa, É—an yayanka ai É—anka ne bana son haka"
"Baba Bala ina yini"
"Kinga yini akan ki Ana, ni za ki kalla ki kira da Bala, ina mace Æ´ar'uwarki ta ina na yi miki suffa da namiji, shi yasa bana son shigowa cikin gidan nan wallahi aikin kawai"
Ana ta tura baki gaba ta ce
"Ai shi ya sa naga nono a ƙirjinka, wallahi mugun duka ne baka ci ba, da sauri zaka dawo asalin namiji ina faɗa maka"
Iftihal ta buÉ—e baki da mamakin Ana. Innti ta ce "Ana, wacce magana ce haka?"
"Innti ki bari na faɗa masa gaskiya, sai ya dinga yawo yana zubar mana da rigar mutumci, waye zai aure mu idan yaga ƙanin babanmu ɗan daudu ne, ni da nake burin auren kyakkywan miji, kuma kin san kyakkywan maza yawanci masu kuɗi ne"
Innti ta kasa magana.
Ana ta murguÉ—a baki ta ce
"Wallahi walakiri ba zai maka da kyau ba idan ka mutu a haka, jibgarka za'ayi kamar jaki, ai sai ka auri namiji ƙarshen daudu kenan"
Bala Sukunbiya ya ce "Ni kike faÉ—awa haka? Kamar a bakin Daada wallahi, sai na ja miki masifa za ki san kin yi da watsastse"
Caraf Ana ta ce "Kaga watsewa a kan ka, da kai da Daada duk ku kaga duhu, wlh sai na yi addu'a in sha Allah nono ya fito maka har ciki, wai Sukunbiya?" Sai ta sheƙe da dariya
"MahaÉ—ita yau miyarmu da Sukunbiya za'ayi" takaici ya kama Sukunbiya.