← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 166

Sashe 97

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kuka Batuul ta dinga yi tana sauk'e ajiyar zuciya jikinsa, ya kasa cewa komae don har cikin ranshi yake jin kukan nata, dad'a rungumeta yayi sosae ya daura kanta a kirjinsa, a haka har ya samu tayi baccin amma har lokacin tana sauk'e ajiyar zuciya, shi kam sam ya kasa rintsawa gashi yana son yayi wanka amma ya kasa dauketa daga jikinsa, sai wajen k'arfe biyu ya samu bacci ya dauke sa shi ma, da asuba ya dad'e da tashi har lkcn tana jikinsa ya kasa kwantar da ita jin yanda jikinta ya dau xafi, kallonta yake yana kwantar mata da dogon gashinta da ya barbaje a hankali, kamar ya maidata ciki haka ya dinga ji, wani irin feeling yake ji a tattare dashi da ya kasa gane ko wane iri ne, a hankali ya lumshe ido yayi kissing lips d'inta ya kwantar da ita ya shiga toilet, da k'yar ta iya bud'e idanuwanta da suka kumbura sukayi ja jin ya shige toilet don tuni ita ma ta tashi sai dai bata nuna masa idonta biyu ba, tayi yunk'urin tashi taji wani azababben ciwo, bakinta ta toshe dan kar tayi k'ara ya jiyota, da k'yar ta samu ta miqe daga gadon tana d'ingishi ta fice daga d'akin, babu abinda takeyi sai hawaye, tana shiga d'akinta xani kawae ta iya daurawa ta fad'a kan gado ta fashe da kuka abin tausayi, sunan Aunty da Baba ta dinga k'ira, ita kadai tasan abinda take ji a lokacin, wani baccin wahala ne yayi gaba da ita, Abuturrab na fitowa daga toilet yaga bata dakin, murmushi yayi, yayi hanyan kofa zai fita yaji wayarshi na ringing, komawa yayi ya d'au wayan, da mamaki yake kallon screen d'in ganin mai kiranshi, yana d'auka yaji tace "Hello bae na dawo fah, yanxu na baro airport ina hanya, na ma kusa" girarshi d'aya ya d'age kamar tana wajen a daburce yace "ke hankalin ki d'aya kuwa? bakice min zaki dawo ba kika d'auko hanya kika taho" da mamaki tace "Haba babe, sai nace maka xan dawo, beside kwananmu nawa bamu had'u ba, ko d'okin ganina ma bakayi" ya sauke ajiyar xuciya a hankali yace "ohk then, Fine naji" da haka ya katse k'iran ya jefar da wayar kan gado, hannu yasa ya baje gashin kanshi ya lumshe ido, duk ya rasa abun yi, he is just confused, idonshine ya fad'a kan bedsheet d'in da yayi staining, d'an tsaki yaja ya yaye bedsheet d'in yayi toilet dashi ya jefa cikin washing machine, fitowa yayi ya canja wani, ya juya kenan zai koma toilet Ajiddeh ta turo kofan dakin ta shigo wani iska mai d'umi ya furzar daga bakinshi, a guje ta k'araso ta rungumeshi cike da farin ciki, murmushi ya kirkira yana kallonta kawae, tace "Babe jikin Mummy Alhmdllh, duk ita ce ta takura sae na dawo Wai ta ji sauki, taki bari na inje gidan 'yan uwa mu gaisa, kai babe kaga yanda nayi missing dinka kuwa" kallonta kawae yake sai dai gaba d'aya hankalinshi baya kanta, kallon gadon tayi tace "A'ah Baby kai ka canja bedsheet d'in?" kai kawai ya iya gyad'a mata da sauri, d'agowa tayi tana kallon fuskanshi tace "Baby toh mesa ka canja? Me ya same shi, ae sabo ne na shimfida" murmushi ya k'ak'aro yana kkrin controlling kansa kar ta gano sa yace "Yeah, yea coffee ne ya zube jiki, and I changed it just now" bata bari ya gama ta had'a bakinshi da nata, janye jikinshi yayi daga nata ya zaunar da ita kan gado yana murmushi yace "Am, am coming babe" toilet ya shige, yyi saurin tarawa bedsheet din cikin machine ruwa dan yasan halinta zata iya zuwa ta duba, da kanshi ya dirje sannan ya maida cikin washing machine din, fitowa yayi ya sameta zaune inda ya barta, kissing d'inshi ta shiga yi passionately, amma gaba d'aya hankalinshi na gun Batuul, so yake yaga halin da take ciki, da k'yar ya samu ya lallab'ata har tayi bacci wajen k'arfe takwas, tana fara bacci ya sauk'e ajiyar zuciya ya janye jikinsa daga nata ya dauki makullin mota ya fice daga d'akin, kai tsaye d'akin Batuul ya nufa, tana kwance kan gadon har lkcn bacci take, amma kana gani kasan a wahalce take, wani tausayinta ne yaji ya ratsa shi, dab bakin gadon ya tsaya ya d'auketa cak, kara ta saki a tsorace, yyi saurin rungumota jikinsa, har cikin ranshi ya dinga jinta" k'asa ya sauk'o da ita ya bud'e mota ya sakata ciki snn shima ya zagaya ya shiga ya tada motar suka bar compound din, hade kai tayi da gwiwa tana rera kuka a hankali, duk ya ma rasa me xai ce mata har suka isa daya gidansa, yana gama parking ya bude motar ya fito ya xagaya ta inda take ya bude, daukarta yayi kamar daxu suka shiga cikin gidan, bai direta a ko ina ba sai kan gado, ya xauna kusa da ita ya rungumota cikin sanyin murya yace "I said am sorry, kiyi hakuri plss" kuka take har da shessheka, a hankali yace "Its painful ko? forgive me plss" bata ce komai ba, ya lumshe ido yana shafa bayanta a hankali, kwantar da ita yayi jin tayi shiru sai ajiyar xuciya da take saukewa ya mike ya shiga toilet, very warm water ya hada a bathtub ya fito ya dauketa, sai da suka shiga toilet din ya fara cire mata xanin jikinta, ta rike da sauri hawaye na xubo mata tace "A'a ka bar ni xan yi da kai na" yace "But you are in pain ki bari in taimaka maki" ta fashe da kuka tace "No plss" bai kara bi ta kanta ba ya cire xanin ya saka ta cikin ruwan dumin, ihu ta kwala jin wani sabon axaban, ta dinga kiran Anty tana yarfe hannu idonta rufe don baxata iya kallonsa ba, sosai yaji tausayinta, yasan bai kyauta mata ba, tunda ba haka yayi ma Ajiddeh ba, ko da yake ita wannan bbu gardama ta bashi kanta kamar jira take, sau uku yana canxa ruwan sannan ya taimaka mata tayi wankan tsarki, tayi wanka ta wanke baki, ta dauro alwala ya dauketa suka fito, rufeta da bargo yayi ganin yanda take rawan sanyi, ya sauka downstairs don hado mata tea, da kyar ya lallabata ta sha tea ta koma ta kwanta, makullin mota ya dauka ya fita xuwa phamarcy don siyo mata pain reliever jin yanda jikinta yayi xafi sosai, ko kan ya dawo har tayi bacci, ajiye ledan drugs din yayi ya xauna gefenta yana kallonta, sai lokacin ya tuna ashe fa bai yi sallah ba, mikewa yayi da sauri ya nufi bayi ya dauro alwala ya fito ya shimfida darduma yayi sllhn. Yana xaune kan darduma har lkcn wayarsa ya fara ringing, ya mike ya dauka yaga Ajiddeh ce, d'agawa yayi daga daya bangaren tace "Babe ina ka tafi haka har yanxu?" A takaice yace "Aiki, I saw yhu were sleeping shiyasa ban tashe ki ba kawae na wuce" a d'an shagwabe tace "Toh come back early plss," yace "Ayt!" Tace "Babe ban ga yarinyar nan ba fa tun da na dawo" ya lumshe ido yace "Yea bata nan, tana gidansu wata kawarta wai, tun da kika tafi" Ajiddeh ta tabe baki a xuciyarta tace Allah sa ma tai ta tsayawa gidan kawar tata, a fili kuwa ca tayi "Eyya, ashe tasan mutane a nan" kallon Batuul dake motsi yayi, da sauri yace "look babe, We'll tok later, am busy yanxu" daga haka ya katse wayar ya nufi Batuul da sauri. 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

67

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Kan gadon ya koma bayan ya ajiye wayan hannunshi, kallon Batuul dake bacci kawai yakeyi yana lumshe ido tare da bud'esu, ya dad'e sai kallonta yakeyi, tausayinta yakeji har cikin ran shi, bai san lokacin da wani murmushi yayi escaping lips d'inshi ba tunawa da yayi da ranan da ya fara had'uwa da Batuul har kawo jiya da daddare, murmushi kawae yake yana girgixa kansa ya kwanta gefenta ya jawota jikinshi ya rungumeta, a tsorace ta saka y'ar k'ara tana k'ok'arin tashi, rungumota ya dad'ayi jikinshi kamar wacce za a k'waceta a hannunshi, a kunne ya rad'a mata "shhhh sleep, babu abinda zan miki", maida kanta tayi kan faffad'an k'irjinshi a sanyaye tana maida ajiyan zuciya, har lokacin heart beat d'inta bai koma normal ba dan gani take zai mata wani abin, ta dad'e idonta biyu har sai da taga ya jima bai yi mata komai ba ta samu bacci ya d'auketa.
Chapter 97 · 0% Book details