← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 166

Sashe 4

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

sannan suka katse wayan, tashi tayi ta jona wayan a caji ta juya ta fito daga dakin, har ta karaso kasa, ta sauka daga benen ta jiyo muryoyin yan gidan a dinning suna cin abinci, karasowa tayi wajensu, Mahir na ganinta yace Yaa Batuul kinyi kyau, Hafix ma yabishi yace kinyi kyau, tayi murmushi tace musu nagode, kuyi shiru ku gama cin abinci,

kujera itama taja ta zauna a gefen Baba daga hagu, Baba ne ya ce mata

"kinga kayan nan yayi miki kyau amma ba kiyi ta saka baqin kaya ba a kowane occasion",

Aunty ce tace ai Y'ar kauye ce,"

ta juyo ta dubi Baba tai raurau da ido, yana ganin haka ya yace

"脌 ah Mamana ba y'ar kauye bace, ai kayan nayi mata kyau" ko ? ya tambayeta ,murmushi tayi sannan ta dauki plate, ta janyo wani babban tray da aka rufe da foil paper ta bude,Danderu ne na kaza yana ta tiriri da kanshin kayan yaji, kadan ta saka 脿 plate din sannan ta sake janyo wani food flask din ta dauki masa daya a ciki tare da miyar masa, a hankali ta riqa ci ba tare da cewa komai ba har suka gama

Sun gama cin abincin ne suka tashi suka koma palo, Fa'iza da Janet ne suka zo suka gyara dinning din tare da kara turaren wuta 脿 duka electric burners din gidan

Sai da kowa ya zauna ya nutsu sannan ta dubi Baba tace

"Baa inason inje wajen Farida tunda gobe da jibi we Will ne busy,

"Okay what time zakije ?

Cewa tayi "ko yanxu tunda naga its already after 12"

" Tunda su Baa Liman(Driver)suna hutu sai Ahmad ya kaiki dan ya fiki iya driving kuma bana Son kina driving ke kadai especially a Maiduguri da ba a bin r茅gulations din driving "

"Okay Baa nagode, " Aunty dai bata ce komai tunda Baba ya yadda shikenan. Tashi tayi ta k'ara haurawa sama ta dauko jakarta ta channel purple shima irin kayan da karamin gyale shima purple amma light, ta kara duba fuskanta a mirror sannan ta sauko

Tana saukowa taga Ahmad riqe da key din mota a hannunshi yana jiranta, karasowa tayi ta ce wa su Baba zasu tafi, "

yayi musu sai sun dawo sannan yace mata idan ta gama sai ta kira a zo a dauketa, tace toh",

Tacewa Aunty sai Sun dawo, Aunty tace mata ki gaishe da Ammah kice mata nima zanzo ko bayan mun koma Abuja ne, Toh tace sannan suka fita suka nufi inda akayi parking motocin gidan suka shiga wata Audi fara sol, Ahmad ne ya tambayeta anguwan da zasu bayan yayiwa mai gadi horn kamin yazo ya bude mishi kofan, ce mishi tayi Old GRA ne in munje zan nuna maka hanya, Ya juyo yace mata

"Yaa Batuul Allah kwatancanki akwai wahala yanxu sai mu kai two hours muna neman wajen da baifi muje a 20 mins ba "

"Tace toh ka bani inyi driving"

baice mata komai ba yaja motan suka bar gidan bayan mai gadin yayi musu a dawo lafiya

Tafiyan minti goma sha biyar suka isa gidansu Farida a old GRA ,Horn yayi aka bude musu gate suka shiga, suna shiga gidan bugun zuciyanta ya karu, ambaton Allah ta riqa yi har sai da taji ya dan ragu sannan ta bude motan ta fito daga ciki tare da yiwa Ahmad sai anjima akan in ta gama zata kirashi

Farida na Jin tsayuwar mota ta fito daga cikin gida a guje tazo ta rungume Batuul ta na ihun i missed you so much babe,

"Batuul ce tace mata sakeni kar ki ballani Baba ya hanani zuwa nan gaba"

Dariya tayi sannan tace nasan Baba bazai hanaki zuwa sai dai in ke zaki min halin naki ki qi zuwa, Batuul batace komai ba har suka karasa ciki ,tacewa Farida Ammah da Abui da Sadiq fa ?

"Ammah da Sadiq basu dawo ba inaga Sun tsaya wajen Ayyi, Abui yana Shehuri, Nida Yaa Abu ne a gida kawai shima yana sama,

Batuul tace "okay",

sama suka haura suka isa dakin Faridan, suna shiga ta cire gyalenta ta ajiye a akan gadon ta juya inda fridge din dakin yake zata dauki Fanta, tana budewa taga babu Fanta 脿 fridge din, "kinsan zanzo shine baki saka Fanta a Fridge dinki bako, sai tarin bakaken drinks da kika ajiyewa mutane(coke),ni na sauka fridge din kasa in dauko, batajira jin abinda Farida zata ce mata ba ta sauka ta isa dinning area ta bude standing fridge din zata dauki Fanta taji wata Murya cikin sanyi an Ce "Farida kawomin bottle water daya", bugun zuciyantane ya k'ara tsananta, Bata juyo ba kuma batayi magana ba har sai da ya k'ara maimaita maganar amma yaji shiru, ransa ne ya b'aci ya taso yaga abinda takeyi da har ya hanata amsa mishi, yana zuwa ya fizgota da k'arfi da har saida ta fada kirjinshi kamin yayi sauri ya janyeta
[8/22, 1:35 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

6

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

tsayawa yayi ya na kallonta ita kuma kanta 脿 kasa, ba a Jin komai sai bugun zuciyanta da ya kara tsananta, riqon da yayi mata ne da kuma bugun zuciyanta yasa hawaye taruwa 脿 idonta, kiciniyar kwace kanta ta fara yi daga wajenshi amma yaki saketa, Dumi yaji a hannunshi ya juya yabi hannun nashi da kallo, hawayen da ya gani ne yasa shi sakinta a hankali ya juya mata baya, juyowa ya sakeyi zai yi mata magana yaga bata wajen,

Parlour ya koma zauna yabi stairs din da ta hau da kallo, lokaci daya ya shiga kwada ma Farida qira, A bakin kofa ta kusa cin karo da Farida, Farida tace "kinga abinda nake gaya maki, I Wonder why he is calling me yanxu" bata karashe maganan ba ta ta riqe Baatul tana tambayarta "Why are you sore ? Mey ya sameki kuma idonki ya canja , kamin ta bata answer ta sukaji ya sake kwada ma Farida kira, bata jira cewan Batuul ba ta sauka kasa tace "Gani Yaa Abu" a nutse yace "Who is she ? I mean that lady, doesnt she talk ko kuma gaisuwa ne bata iya ba ? A zuciyanta cewa tayi "Innalillahi wa inna illaihi rajiun, Yaa Abun nan komai ba a yi mishi daidai, in nayi magana yace na cika surutu, yanxu kuma Batuul bata yi magana ba zaiyi fada" Tana cikin tunanin taji yace "am i not asking you ?"
"No Yaa Abu bata jin dadi ne shiyasa bata gaisheka ba, Ce mata ya sakeyi "daga ina take"? "Batuul cefa kawata tun muna Centagon wacce ka kaini gidansu a Maitama last year da ka dawo har kace bazan kwana ba",

Hannu ya daga mata alaman ya isa,

"ki miqomin ruwa a fridge", a kan center Table din gabanshi ta ajiye ta juya ta bar falon

D'aki ta nufa, tana shiga ta tarar da Batuul 脿 tsaye tana riqe da jaka da gyalenta a hannu, "Zan tafi gida"

"Ban gane zaki tafi ba saboda mey" Farida ta tambaya , Yaa Abu yayi miki fada ne dan nasanshi da yiwa mutane fada, "Ni baiyi min komai ba kawai zan tafi ne"

"In kinje toh mey zaki cewa Aunty ya dawo dake bayan kince har dare zaki kai " kuma in Ammah ta dawo mey zan fada mata ? That kinzo har kin koma ? If Yaa Abune baza mu sake bin hanyan da yake ba nima haka yake min

"Toh naji bazan tafi ba amma baza muje inda yake ba " Farida ta kyalkyale da dariya tace,

"Keh da kika ce zaki fada mishi ina gulman shi yanxu kuma ke da kanki zaki qi bin hanyan da yake "

"Ni ki rabu dani, kuma ai ni babu abinda yayi min kuma zan fada mishi din ai", haka suka ci gaba da hira har Batuul ta manta da Abutturab na gidan

Yana zaune a palo bayan ya kurbi ruwan da Farida ta miqo mishi, tunani yayi na lokacin da Baatul ta bigeshi a masallaci da yadda tace mishi sorry har yanxu da ta zo gidansu yaga hawaye a idonta, hawayen da ya tuna ne ya sashi ajiye ruwan yana fadin "Damn it" 脿 hankali, "does shi always cry"? Yana cikin tunanin yaji an bude kofan palon , Ammah ce tare da Sadiq a bayanta suka shigo suna hira, ciki suka karaso suka zauna a palon, Abu ne yayi musu sannu da zuwa, Ammah ce tace "baku tsaya anyi hawa bane da ku "? "Ehh naso mu zauna sai kuma na fasa amma Abui yana can" , "Muma munje mun duba Ayyi ne, sannan ta kwalawa Fanne kira,cikin hanzari Fanne ta karaso tacewa Ammah "sannu da zuwa,Gani"
"kije ki duba min Farida kice mata mun dawo, sama Fanne ta haura ta fadawa Farida sakon da aka bata sannan ta fita, Farida tacewa Batuul "muje ki gaida Ammah nasan baza ta hawo palon sama ba shiyasa ta sa a fadamin"
Chapter 4 · 0% Book details