Sashe 117
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Washegari kamar kullum da ya tashi sllh saida ya tashi Ajiddeh amma bata tashi ba, shi kam daga masallaci d'ayan gidan ya wuce, a kitchen ya taddasu su biyun duka Farida har ta shirya, k'arasowa yayi cikin kitchen d'in yana amsa gaisuwan Farida ya isa inda Batuul ke jingine jinkin Fridge, yana zuwa ya jawota jikinshi ya d'aura hannunshi kan mararta a hankali, da sauri ta d'aga ido taga ko Farida na kallonsu, ai kuwa ido hud'u sukayi da Faridan, maza tayi ta d'auke idonta cike da kunya snn ta riqe mishi hannu, rankwafowa yayi daidai wuyanta da muryan shagwab'a da ya sauqe mata kasala gaba d'aya yace "Ina duba Baby na", cike da jin kunya a hankali tace "Yaa Abu Farida fa na nan" kallon Faridan yayi, suna had'a ido ya sakar mata wani irin kallo, babu shiri ta bar abinda takeyi ta rage wutan stove d'in tayi waje da sauri, tana fita ya juyo da Batuul d'in, y'ar rigar dake jikinta ya d'age ya shiga making circles a flat tummy d'inta da yasata jin wani sabon feeling na daban na ratsata, a hankali yace mata "Meh zaki bawa Farida?", sai lokacin abin ya fad'o mata d'ago kai tace "Nima ban sani bafa, kawai zan bata kosu bracelets d'ina ko?", ta tambayeshi, murmushi yayi ya janye hannunshi cikin rigan nata ya kamota yace "muje ki gani sai ki duba ki ga In yayi a bata", babu musu ta bishi a baya suka fita waje, Farida na ganin fitansu ta koma kitchen taci gaba da abinda takeyi tana murmushi cike da jin dadin irin xaman Bestyn nata da yayanta, suna shigowa daidai nan Faridan ma ta fito riqe da bowl d'in oat a hannuta tana jujjuyashi, a nan ya bar Batuul ya haura sama, ba a jima ba ya sauko yace su wuce, cikin y'an minutes suka isa airport, sai lokacin Batuul ta dad'a tabbatar da tafiyan Farida, kamar kar su rabu harda k'wallanta, k'ok'arin fitowa ta shigayi daga motan zata raka Farida yayi maza ya rik'ota yana kallonta yace "Ina zakije haka?" , zumb'uro mishi baki tayi cike da shagwab'a tace "zan rakata mana", kai ya girgiza yace "kinada hankali zaki fita a haka ko mayafi babu?, dubi kayan dake jikinki?", kallon kanta tayi taga koh kayanta are, wandone jikinta sai jacket iya gwiwa da hood amma yake fad'a mata wai kada ta fita a haka, rai b'ace ta koma ta kwanta sai Faridan ce ta zagayo tayi hugging d'inta, dan takaici kasa magana tayi sai hawaye da ta dinga yi, shi ya d'auki jakan tsaraban ya rakata dashi yace mata inji Batuul, ya k'ara mata da kud'i masu yawa, har saida yaga ta shiga jirgi sannan ya juyo, a mota ya tadda Batuul har tayi kukanta ta gode Allah, ko sau d'aya bata kalleshi ba bayan ya dawo, haka ya k'arashi surutunshi suka isa gida, yana parking ta bud'e mota ta fita a guje, a gujen shima ya bita dan har ranshi yakejin gudun nata snn gashi ba lafiyane da ita isasshe ba, daidai takai k'afanta kan 5th stair case ya cimmata, wani razanannen k'ara ta saki da yasata durk'ushewa k'asa, binta yayi ya kamota jikinshi yana mata wani irin kallo yace "Fatima ban hanaki tsalle ba?, bakida hankali koh?, next time you try this shit I will slap you", gaba d'aya bata sanma mey yake fad'i ba sai yarfe hannu da takeyi, kuka sosai ta shiga yi tana k'iran sunan Auny tana riqe da cikinta, rud'ewa yayi ganin da gaske take ya d'agota yace "Batuul talk to me, cikin ne?", a hankali ta shiga gyad'a mishi kai a wahalce, duk ya rasa mey ma zaiyi dan duk ya rud'e, cak ya d'auketa sukayi asibiti, ikon Allah ne kawai ya kaisu lafiya dan baisan irin driving d'in da yayi ba, likitocin this time ma cikin gaggawa suka amsheta, sai kukan wahala take tana k'iran sunan Aunty, har dare likitocin na kan Batuul sun kasa gano Ina matsalar take gashi duk wani taimako da zasuyi sun mata shi amma babu wani ci gaba, Abu kam tsayawa kawai yayi yana kallonsu ya kasa cewa komai, kamar shi ke ciwon har fad'awa yayi daga yini d'aya. Sai karfe takwas da wani abu na daren bacci ya dauketa shi ma sai juye juye take, Abuturrab dake xaune gefenta ya tsura mata ido cike da tausayinta ganin yanda ta wani rame daga safen xuwa dare, mikewa yayi da kyar ya nufi office din likita, nan ya shaida ma likitan in dai cikin xai bada matsala kawai a cire sa, ficewa yayi daga office din ya nufi gida kafin ta tashi don dauko wayarsa, Ajiddeh na xaune parlor kamar ko da yaushe, yau dai sai ya gaya mata ma'anar fitar da yake da asuba ko sallama babu baxa kuma ta kara ganinsa ba sai dare, bin sa da kallo tayi ganin ko kallonta bai yi ba ya haura sama, mikewa tayi ta bi bayansa, xaune ta samesa gefen gado, da ganinsa kasan akwai matsala, ta karaso da sauri ta xauna gefensa tace "Me ya faru babe? What's wrong?" Rike kansa yayi bai ce komai ba, ta dago kansa tace "Talk to me mana, me ya faru" Da kyar ya iya bude baki yace "Batuul!" Ji tayi kamar ya soka mata mashi, lokaci daya xuciyarta ya shiga tafarfasa, ta dake tace "What about her?" Cike da confusion yace "I just don't know, tana asibiti" wani farin ciki ya lullube Ajiddeh, sai dai cike da damuwa kamar gaske tace "Ayya, Allah ya bata lafiya" mikewa yayi da kyar ya dau wayarsa xai fita, tace "plss xan bi ka muje in dubata babe" bai tanka ta ba ya fita, ta mike cike da murna ta dau hijab ta sa ta bi bayansa da sauri, har ta shiga motar bai ce mata komai ba ya tada suka kama hanyar asibitin, ba karamin tashi hankalinsa ya kuma yi ba ganin likitoci a kanta, su Ajiddeh kamar na kirki ta dinga kwantar masa da hankali wai she will be fine. Likitocin na fita ya shiga Ajiddeh na biye da shi a baya, rungumeta yayi ta kankamesa tana kiran sunansa cikin kuka, a rikice yace "Don't worry Fatima xa a cire babyn ki huta kin ji" girgixa masa kai kawai take tana kuka sosai, Ajiddeh ta xauna gefenta tana mata sannu, rike hannunta Batuul tayi ta fada kanta tace "Wayyo Mutuwa xan yi Anty ki taimake ni cikina" shiru Ajiddeh tayi tana kallonta lokaci daya jikinta yayi sanyi jin ta ambaci mutuwa.
[12/1, 15:42] 80k: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐
78
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
[12/1, 15:42] 80k: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐
78
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*