Sashe 58
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Wajen sha 膹aya Ammah ta shigo ta gansu a 膹akin Faridah suna kwance kan gadon Farida suna kallon wani abu a system sai dariya sukeyi, ta da膹e tsaye tana kallon yadda Batuul ta sake, sosai hakan yayi mata da膹i, basu lura da tana 膹akin ba sai da sukaji ta k'ira sunan Farida, da sauri Batuul ta mik'e tana gyara 膹ankwalin kanta kamar ita aka k'ira, murmushi Ammah tayi tacewa Farida "Ki shirya kije Baa Liman na jiranki zakije gidan Yaa Mera ku kai mata sak'o", kai ta gya膹a tace "Toh Ammah", ta juya ta kalli Batuul da tayi shiru tace "Ki shirya mu tafi", Ammah da har ta juya zata tafi ta juyo tace "A ah, ke nace kije, bance zaki tafi da ita ba, banda ita a yawo yanxu, duk fitan da zatayi yanxu sai da sanin mijinta", da sauri Batuul ta 膹ago idanunta da suka fara kawo ruwa jin abinda Ammah tace, taci gaba da cewa "Bitti tashi muje kamin ta dawo, muje in k'arasa harha膹a miki abubuwan da nasan zaki buk'ata kamin anjima ku tashi tafiya kuma babu time", zuciyantane ya shiga bugawa jin abunda Ammah tace, yau kuma zasu tafi, ina 膹in wai zasu tafi da har za ayi mata shirin abinda zata buk'ata, gaba 膹aya kanta ya gama 膹aurewa, gabanta ya shiga faduwa, Allah yasa ba can kasar Ammah ke nufi ba, jiki a sanyaye ta tashi tabi bayan Ammah sukayi waje Farida kuma ta sa mayafinta tayi waje, har suka isa 膹akin Ammah Batuul sak'e sak'e takeyi a ranta, sai da Ammah tace mata ta zauna tukunna ta samu guri ta zauna k'asan carpet 膹in, 膹agota Ammah tayi ta zaunar kan gadon, sai sissinne kai take wai ita kunya, wasu manyan kwalaye Ammah ta nufa tacewa Batuul "Bitti kinga wannan ma nakine, 膹azu Aunty tasa aka kawo miki shi, turarrukan wutanki ne da na shafawa, in kinje kullum ki riqa amfani dasu, ya zama kullum 膹akinki akwai shi, kinga dai yadda Mamanki takeyi ko, ko gidanku aka shiga sai an fito ana k'anshi, toh haka zaki rik'ayi kema kin ji, zakije inda bakisan kowa ba Bitti, ki dage da addu'a, duk abinda Abu zai yi miki kar kice zaki fa膹awa su Aunty, nima matsayin Aunty nake in har yayi miki abunda ba da膹i kar kiji komai ki k'irani ki fa膹amin, ni da kaina zan sab'a mishi", take idon Batuul ya fara zubda hawaye hankalinta ya tashi ba kadan ba, Ammah taci gaba "Kinga in kun koma bake ka膹ai bace, ki bata girmanta a matsayinta na wacce ta girmeki, babu ruwanki da shiga harkarta, babu ruwanki da duk wani abu da zakiga tanayi indai ba ta ha膹a dake bane, ki zauna da ita tsakani da Allah, kinga zaman aure ne yasaki barin gaban iyayenki har wata k'asa, kiyi hak'uri ki zauna sannan ki kula da ibadunki, ki kula da kanki sosai kinji, Allah yayi miki albarka" sosai Batuul ta shiga kuka kamar anyi mata wani abun, da k'yar Ammah ta rarrasheta ta bata baki tayi shiru, Ammah dake cicciro kwalaban turaren cikin kwali tana yiwa Batuul bayanin duk yadda suke, ta dubi Batuul tace "Bitti tashi je ki k'iramin Yayanku yazo ayi packaging kwalayen nan", jiki a sanyaye take kallon Ammah tace "Ammah bansan ina yake ba", Ammah tace ai bazai wuce 膹akinshi ba, kije can yana 膹akin kice yazo ina nemanshi yanxu", kamar bata son mik'ewa a hankali ta tashi jiki ba kwari ta dauki mayafinta, har ta fara tafiya ta juyo tace "Ammah inane 膹akin nashi yake?", Ammah tace "膹akin k'arshe by your left", jiki a sanyaye ta juya ta fita daga dakin, tafi minti biyar bakin k'ofar 膹akin tukunna ta shiga knocking a hankali kamar bata so aji gabanta na faduwa, bayan 'yan mintuna taji ya murda kofar ta koma baya da sauri, shi kam tsayawa kallonta yyi da mamaki don yyi tunanin farida ce hkn yasa ya taso ya ji dalilin knocking maimakon sallama, hade rai yyi ya juya ya koma cikin dakin, a hnkli ta bi bayansa ta shiga dakin ta tsaya daga bakin kofar kanta a kasa tace " Ammah na kiran ka" mikewa taga yyi, tana ganin hka ta juya da sauri xata fita daga dakin yyi hanxarin rikota ya juyar da ita yana mata wani irin kallo, kin bari su hada ido tayi, yyi wani murmushin yace "Tunda kika yrda aka hada mu dama akwae sharadodin da xan lissafo maki kafin mu bar kasar nn, nd yhu have to abide to them ol idan kina son kwanciyar hankalin ki da xaman lfyan ki, it's vry well knwn to yhu dat ni bana son ki, yea bana sonki sure, we 2 were neva on gud terms ryt frm d start! Duk da hkn baki yi making any effort ba wajen preventing parent dinmu frm hooking us up, rather yhu encouraged them ta hanyar amince masu dari bisa dari, So...." Wani matsanancin kuka ta fashe da ta durkushe wajen ta shiga rerawa, komawa baya yyi yana kallonta, lkci daya hankalinsa ya tashi, kofan da ke bude ya kalla ya karasa da sauri ya rufe, snn ta dawo ya durkushe gabanta shi ma yana kallonta yace "Na maki wani abun ne?" Kuka take ssae, kukan bakin ciki da kukan tausayin kanta, ji take kmr Allah ya dauki ranta ta huta kawae, ko bae fada ba tasan karshen farin cikinta ne a duniya ya xo, a dan rikice yace "Talk to me mana, me na maki kike kuka, why kike son hada ni da mahaifiyata ne wae, daga magana sae kuka," kin dagowa tayi bare yasa ran amsa, sae kukan da take har da sheshsheka, ji yyi an bude kofar dakin Ammah, ae bae san lkcin da ya jawota jikinsa ya rungumeta ba, wani dad'da'dan sanyin kamshin da ya bugi hancinsa ya sa shi runtse ido da sauri, ita kanta sae da ta tsorata ta kasa ci gaba da kukan da take gabanta na faduwa, sun kusa minti biyar a hka, cikin sanyin murya idonsa lumshe har lkcn kmr me rada yace "Am... am.. I mean am srry!" A hnkli ya kuma cewa "Am srry" sae kuma ya bude idanuwansa ya daura kan gashin kanta dake fitar da wani fitinannen kamshi don gyalenta ya xame, d'ago kai tayi suna hada ido ya saketa ya mike da sauri, da kyar ita ma ta mike kanta a kasa xata fita ya fixgota ya wani hade rae kmr ba shi ba yace "clean those tearz" sunkuyar da kai tayi, ya ciro handki a aljihunsa ya dago kanta ya shiga goge hawayen fuskarta, yana mayar da handki din aljihunsa ta juya ta fice ya bi bayanta, ko da suka koma dakin Ammah bata ciki, Batuul taje can karshen gado ta xauna bayan ta daura mayafinta a kai, stool ya ja ya xauna shi ma ya fiddo wayarsa yana dannawa, lkci lkci yake satan kallonta ita ma hka, da sun hada ido kuma ya jefa mata harara, a hka Ammah ta shigo ta samesu, xama Ammah tayi yace "Gani Ammah" Ammah tace "Eh dama wa en can kwalayen xa ayi packaging kadda lkci ya kure ko ya kaga" kansa a kasa yace "Toh Ammah bari in kira sadiq," ya mike ya fita daga dakin, Ammah ta juya ta kalli Batuul, da sauri ta sunkuyar da kai cike da kunya don gani take kmr Ammah xata ji kamshin turarensa a jikinta.