Sashe 144
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
聽 聽 聽 Wanka tayi ta zauna bakin gadon daga ita sai d'an towel, shima lokacin ya fito daga toilet d'in yace "Bata kawo kayan ba har yanzu?", kallonshi tayi ta zumb'uro mishi d'an k'aramin bakinta tace "Nace fa zanje In d'auko ka hana, nasan bacci takeyi ka tada ta", bai kulata ba ya d'auko wayarshi ya k'ira Farida a waya, yana bugawa ta d'aga yace "Har kin kawo kayan kenan ko?", kamar tana gabanshi ta girgiza kai tace "Yanzu nakeson in k'irata ta fad'amin wanda zata saka fa",聽 yace "Get the whole box here", ido ta wara kaman yana gabanta tace "Kai Yaaa Abu, da nauyi fa", bai jira mey zatace ba ya katse wayan", kayanshi dake ajiye kan gadon ya d'auka ya sanya, kinkiman akwatin ta shiga yi a ranta tana mitar tada da yayi daga bacci, gefen Batuul ya zauna ya shafi gefen fuskarta tareda juyota ta fuskanceshi yace "Fushin meye ne wai har yanzu haka?", ya fad'a yana shagwab'e mata fuska, d'auke kai tayi tace "Ni fa sanyi nakeji ka hana kuma inje in d'auko kayana", kallonta yayi cikin ido da ya sata tayi saurin sadda kai k'asa yace "bana son kina stressing kanki, am there all the time", ya kamo hannunta ya damtse cikin nashi, daidai lokacin Farida tayi knocking tareda turo k'ofan ta shigo da akwatin tana haki,Batuul na jin k'arar tab'a k'ofa dama ta janyo hijab d'inta ta saka, jan akwatin tayi har cikin d'akin ta snn ta dubi Abu tace "Ina kwana", daga gani daga bacci ta tashi yace "Baki iya jiran izini ba kawai you barged into d'akin mutane ko?", zumb'uro mishi baki tayi a ranta tace "Hmmmm ai saidai idan ba Yaa Abu ba", a fili kuwa cewa tayi "yayi nauyi ne shinefa na shigo kuma saida nayi knocking", idonta ne ya fad'a kan Batuul dake zaune daga ita sai d'an towel da hijab, duk ta shagwab'e fuska kamar zatayi kuka, batasan lokacin da dariya ta kubce mata ba, dariya takeyi harda hawaye snn ta tsagaita dariyar tayi pointing Batuul tace "Ya Allah, you have started gaining weight, Affan have to hear of this, kin ganki kuwa?" Abu da ya tsaya kallonta da mamaki ya daka mata tsawa yace "kina da hankali kuwa?, c'mon get out kamin in tashi in sameki", kallon Batuul da tayi raurau da ido yayi, yasan kuka take shirin mishi, Farida da ke tsaye wayarta ta ciro cikin aljihun rigan baccinta zata k'ira Affan, tsawa ya sake daka mata yace "Na fara wasa dake ko Farida?", kamin tace wani Abu ya tashi ya fizgota ya karb'e wayan ya turata waje, dawowa yayi bakin gadon yana kallon Batuul dake jiran k'iris ta fashe da kuka baki a tab'e, a hankali tace "Dagaskene av gained weight?", in banda iskanci irin na Farida babu ta inda yaga Batuul ta k'ara jiki, dalilin da yasa ma kenan bayason kaita gida sbd yadda duk ta rame, ya d'aura hannu kan wuyanta yana tab'a collar bone d'inta yace "I want you to, kin rame dayawa kuma banaso ni", tasan bazai fad'a mata ba, cire hannushi tayi ta mik'e ta isa gaban human size mirror dake d'akin tana kallon kanta, itama d'in babu ta inda taga ta k'ara k'iba, tasowa yayi ya biyota gaban mirror ya rungumota ta baya tareda tareda sauk'e ajiyar zuciya yana shak'an k'anshinta masu dad'i, ido ya lumshe ya bud'e dai dai nan hawayen da take ta rik'ewa suka gangaro, da sauri ya juyo da ita yana girgiza kai yace "Glitter noo, kar kiyi kuka plss", muje kisa kaya yau sai Farida ta fad'amin yadda akayi kikayi gaining weight" ya聽 fad'a tareda kamo mata hannu, d'ayan hannunta ta saka kan nashi, juyowa yayi ya dubi fuskanta yaga duk sai glittering d'in hawaye suke, rungumota yayi, bai tab'a ganin mutumin da hawaye bai mishi wuyar zuba kamar Batuul ba, jawota yayi suka koma bakin gadon, a hankali tace "Nasan ban k'ara jiki ba but nan gaba in nayi fa?, you will stop loving me ko?", yanzu ya sake tabbatar da harda yarinta cikin lamarin Batuul, dan kawai tayi jiki sai ya dena sonta?, he love her for whatever she is and whatever she will become of, wani light peck yayi mata a goshi ya rik'o hannuta cikin nashi yace "Hey look at me", kasa d'agowa tayi ta kalleshi saida taji yace "Glitter look at me", d'azu ma taji word d'innan daga bakinshi sai yanzu ta san da ita yake, sunaye biyu kenan ya saka mata yanzu, Haya da Glitter, har cikin ranta takejin sunan, a hankali ta d'ago ta dubeshi, Hannu yasa ya share hawayen dake shirin zubo mata yace "what will make you change the way you feel about me?", shiru tayi ta kasa cewa komai saida yace "Uhmm ina jinki", jiki a sanyaye ta girgixa mishi kai, yace "Ki bud'e baki kiyi min magana a hankali tace "Babu", yace "mesa kike tunanin gaining weight zaisa in dena sonki, wa yace miki jikinki nakeso Haya, wa yace miki structure d'inki nakeso?, Ina sonki for who you are da kuma what you are yet to be, banason sake jin kin sake fad'an haka, zamuyi fad'a kinji ko?", kai ta gyada mishi yace "Good" yana sa hannu cikin gashinta da bai bushe ba yace "zakiyi mura fa kina barin gashinki da ruwa", tace "yanzu fa zansa kaya inyi drying d'inshi", ta fad'a tana k'ok'arin tashi ya rik'ota yace "No ki bari in mun sake jik'ashi sai kiji dad'in drying da kyau", sarai tasan abinda yake nufi da hanzari ta mik'e tana dariya tace "A ah nikam, I can dry it haka nanma", dariyan yayi shima ya kamata ya zaunar kan stool ya shiga drying mata dogon gashin kanta mai santsi da shek'i, sai da ya gama snn ya taimaka mata ta shirya cikin navy blue lace mara nauyi mai k'ananan jan patterns yace su sauk'a ya fara jin yunwa, ya rik'o hannunta suka sauk'o dinning area, suna k'arasowa tayi maza ta janye hannunta cikin nashi, kallonta kawai yayi baice komai ba har ta zauna snn ya zauna, daga kitchen Ammah da Sadiq suka fito, da alama daga exercise yake saboda kayan jikinshi, yana riqe da apple yana taunawa biye da Ammah yana mata magiya, juyawa tayi ta dubi Sadiq tace "Kana jina fa Sadiq nace bansan zancen ba, ka samu Abui kuyi maganan dashi", ta k'arasa dinning d'in, Da sauri Batuul ta tashi ta karb'i pan d'in dake hannun Ammah tace " *Ammah Nda wattu* Ina kwana Ammah", "Ammah da murmushi fuskanta tana goge hannunta tace " *Bitti k3lewa selai, k3lewan fanema? Lafiya Kalau Bitti, kin tashi Lafiya?", ta tambaya tana gyara tray d'in fruits, a kunyace Batuul ta ajiye pan d'in dake hannunta tace "Alhamdulillah", ta dubi Abu tace "Ya jikin nata?", Saida ya gaisheta snn ya amsa da Alhamdulillah, ya dubi Sadiq da duk ya shagwab'e fuska yana tauna Apple d'inshi yace "Shi kuma wannan mey ke damunshi?", ya fad'a yana tambayan Ammah, Ammah ta zauna ba tareda ta dubi Sadiq ba tace "Ka tambayeshi gaka gashi, kunfi kusa inajin", kallon Sadiq yayi yace "Whats wrong?", a hankali Sadiq yayi wata magana da babu wanda yaji, Abu da ya had'e fuska yace "In ka shirya fad'an matsalarka ka biyoni ka fad'amin", Ammah tace "Shima da kanshi yasan hauka yake shirin yi shiyasa bazai iya fad'a makan ba, ni bara in fad'a mishi yaji yasan rashin hankalin da yake min", Ammah taci gaba tace "Wai aure yakeson a mishi", daidai lokacin Abui ya k'araso dinning d'in yana cewa "wakeson ayi mishi auren?", Sadiq da sam baiso Abui ya Karaso at this time ba yayi maza ya sadda kai k'asa, Abutturab tsabar mamaki kasa cewa komai yayi sai baki da ya bud'e yana kallon Sadiq d'in, Ammah tace "Wai Sadiq keson a mishi aure", murmushi Abui yayi yace "Har ka shirya kenan, ka shirya kula da y'ar mutane", d'agowa yayi suka had'a ido da Abutturab, Abutturab yayi mishi kallon you are not okay yace "wace yarinyar ce zata aureka bakada aikin yi?, Serving d'inma ba gamashi kayi ba bare ka fara maganan settling ", D'an kafad'a ya d'aga alamun am due fa snn yace "But ai inada gida, what else?" Sosai Sadiq ya bawa Abui dariya, Ammah da Abutturab kam ko kad'an abun wasn't funny to them, Farida ce ta sauk'o sanye da kayan bacci da hula kanta tana danna waya, jin maganan da akeyi ya sata k'arasowa da sauri tana maida wayar cikin aljihu tace "Laaah Ammah ku baku San ma yarinyar bafa, wai fa Layla k'anwar Uncle d'in Aunty Amna yakeso, ina jinshi yana waya da ita kullum, ko wallpaper d'inshi picture d'inta ne, bara ma ku gani" taja kujerar gefen Abui ta zauna tana mik'a hannu zata d'auki wayarsa dake ajiye gefe, Hannu Sadiq yasa y make nata hannun, b'ata rai tayi ta zumb'uro baki ta kalli Abui tace "Abui kana ganinshi ko", tunda Abu ya harareta tayi shiru ta d'auki plate ta d'ebi pomegranate tana sha, Sadiq ma harara ya sakar mata, Abui yace "Sadiq ba gida bane aure, it takes a lot fiyeda wannan, you are just 22, kana buk'atar time da kuma nutsuwa kamin kace zakayi settling, ka bari in ka gama Service ka samu aiki then you talk of settling amma banda yanzu, parents d'in yarinyar da kanta ma ba yadda zasuyi da zancen ba in ba aiki ka fara ba", Ammah da tayi serving Abui soup tana mik'o mishi tace "Sadiq in baka rabani da shirman nan ba ranka zai b'aci, itama Laylan da ta biye maka", Wani kallo ya jefi Farida dashi da ta tona mishi asiri, d'auke kanta tayi tana jin haushin make mata hannu da yayi, Sai da kowa ya nutsu yana cikin cin abinci Abu ya kamo hannun Batuul ta k'asa yana kashe mata ido, kallonshi tayi na ya sakar mata hannu, bai sake ba saima sunan Abui da Ammah da ya k'ira, a tare kowa ya kalleshi suna jiran suji mey zaice musu, Batuul dai gabanta sai fad'uwa yakeyi tana tunanin abinda zaice musu tana k'ok'arin kwace hannunta amma ya dad'a k'arfin rik'on, jin yayi shiru Abui ya maida hankalinshi kan abincin da yakeci, Ammah ce tace "Muna jinka", a nutse yace "Ammah inaso mu koma ne, inada aikin dayawa that are pending", tace "Dama can kai ne kayi zamanka, tunda taji sauk'i ka tafi abinka ka rik'a dawowa kana dubata, ido ya lumshe ya bud'e jin abinda Ammah tace snn yace "Ammah tare fa nakeson tafiya da ita, ba nan zan barta ba", Wani kallo Ammah tayi mishi a taqaice tace "baza ta koma gidan nan ba, ka barta nan in ya so ka riqa dawowa kana dubata", marairaice fuska yayi ya kalli Abui da puppy eyes d'inshi, yace "Ammah ba gidan nan zata zauna ba, tun kamin ta fara ciwo take d'aya gidana, Plss Ammah", Abui yace "Anytime you are ready ka d'auki matarka ku tafi", Kallonshi Ammah tayi zatayi magana yace "Meye amfanin barin nata da zaiyi a nan, ko ya tafi hankalinshi ba kwanciya zaiyi ba, su koma kawai zai ci gaba da kula da ita In sha Allah babu abinda zai sameta", Badan ta yadda ba ta hak'ura, Abu kam dariya yayi yace "Nagode Abui, Allah ya k'ara girma da d'auka, Allah ya k'ara Nisan kwana, Allah ya gafartawa magabata yasa a gama da duniya lafiya", "Amin" dukkansu suka amsa, dariya ma ya bawa Abui Dan kawai yace zai iya tafiya da matarsa shine duka wannan addu'a haka, yace "Kaje ka dubo Hauwa?", gaban Batuul sai da ya fad'i jin sunan Ajiddeh, take expression d'in fuskan Abu ya canja jin sunan Ajiddeh, har idonshi ya fara canja launi yace "Abui am not ready, bana so inyi taking decision out of anger, kar inyi abinda we聽 all will regret", kai kawai Abui ya gyad'a mishi alamar he understands him, Batuul dai gaba d'aya kanta ya gama d'aurewa, mey zaiyiwa Ajiddeh da har zaisa suyi regretting, kuma meye sa tunda ta farka bata gidan, tana sak'e sak'enta har suka gama cin abincinsu,