← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 166

Sashe 112

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abuturrab Bai direta a ko ina ba sai kan gado bayan sun shigo ya haura sama da ita, ita kam sai kallonshi takeyi idanunta na lumshewa dan bacci takeji, fita yayi ya dawo da ledan abincin dake mota, da mamaki ya tsaya kallonta ganin har ta fara bacci, k'arasowa yayi ciki ya ajiye ledan abincin daga k'asa ya hau kan gadon ya d'agota, a hankali ta bud'e lumsassun idanunta ta kalleshi, sulalewa tayi da muryar bacci tace "bacci zanyi" ta koma zata kwanta yayi saurin rik'ota yace "Eat before you sleep", ta zumb'uro mishi baki tace "Na k'oshi ni, bana jin yunwa", tanayi tana lumshe ido, had'e rai yayi yace "cmon kin tashi kinci anbinci kokuwa?, da kikaci mene d'inne kika k'oshi?", bata bud'e ido ba ta bashi amsa tace "ba nasha ice cream ba", d'an tsaki yaja ya d'agota ya d'aurata kan cinyarshi ya janyo ledan ya shiga d'ebo abincin yana bata a baki, da k'yar ya samu taci kad'an tace mishi ta koshi, badan ya so ba ya bar bata abincin hakanan, kayan jikinta ya shiga k'ok'arin cire mata, da sauri ta tashi zaune ta wara ido tana kallon abinda yake son yi, kallonta shima d'in yakeyi yace "Meye, har kin gama baccin?" ta gyara zamanta tace "bafa bacci nakeji ba dama", bai kulata ba yaci gaba da cire mata kayan snn yace "wanka zanyi miki, yau duk bakiyi wanka ba, I want my baby to stay clean", ta tsuke baki jin yace babynshi tace "ni banyin wankan kuma sai anjima" baibi ta kanta ba ya cire duka kayan dake jikinta sai nonnokewa takeyi wai ita kunya ya rage daga ita sai inner wears ya janyo towel ya d'aura mata, cak ya d'auketa yayi hanyan toilet da ita, sai da yaje bakin toilet ganin dagaske yake tayi maza ta sauk'o daga jikinshi, har cikin ranshi yaji wannan wuntsilawar da tayi yayi saurin rik'ota ya had'e rai yace "kinada hankali kuwa, bakisan da Babyna a jikinki ba, I will slap you next time you try this shit", zumb'uro mishi baki tayi tace "Toh zanyi wankan da kaina nace", tsaki yaja ya kamo hannunta suka shiga toilet d'in, tana nan tsaye har lokacin yana rik'e da hannunta d'aya ya had'a mata ruwan wanka a bathtub, ya juyo zai cire mata towel d'in tayi maza ta riqe da k'arfi tayi raurau da ido tace "Dan Allah mana Yaa Abu, zanyi da kaina nace", kallonta kawai yakeyi ganin yadda tayi maganan har idonta ya cicciko ya janye hannunshi a hankali yana kallonta yace "be careful", ajiyar zuciya ta sauk'e ya janye mata curtain d'in yaje ya zauna daga gefe yana jiran ta gama bata fi 8mins ta fito daga cikin abin wankan d'aure da towel d'inta, da sauri ya mik'e ya d'auketa cak yayi waje da ita, kan vanity chair ya ajiyeta, itakam sai mamakinshi takeyi gaba d'aya ganin ya janyo wani d'an box ya fidda hand dryer a ciki, wai Yaa Abu ke yin duka wad'annan abubuwan, wani part d'in zuciyarta kam dad'in abinda ya ke mata ta dinga ji, a hankali ya shiga drying gashin kamar mai tsoron tab'awa, itakam Batuul har wani lumshe ido takeyi dan jin dad'i, sai da ya gama drying ya d'auko man gashinshi ya shiga shafa mata su yayi parking mata gashinta, dariya yadda yayi parking gashin ya bata, murmushin shima yayi, yana gamawa ya shafa mata nashi man jikin ya fesa mata cool turarukanshi, tana zaune ya bud'e wardrobe d'inshi ya fiddo wata shirt d'insa blue mai dogon hannu da boxer d'inshi shima blue and black sabbi duka ya mik'a mata, shi da kanshi mamakin kanshi yakeyi kan abinda yake aikatawa, he never tot he will b doing abubuwan nan for a lady, wara mishi ido tayi tace "Na meye?" Yace "Wear them, ko kinada kayan da zaki sa ne a nan?", da sauri ta kad'a mishi kai tace "Yeah akwai su a wancan d'akin", shi sam yama manta dasu baki d'aya, yace "Yeah I know, I want you to wear these", ta marairaice mishi zatayi magana ya rik'ota zai janye mata towel d'in ta fasa ihu ta riqe tace "Ai zan saka", mik'a mata yayi ta karb'a a sanyaye tace "toh nikam ka rufe idonka", dariya ta bashi yace "in karb'a in saka miki kenan?", da sauri ta girgiza mishi kai, da murmushi a fuskanshi yace "Then wear them", kamar zatayi kuka ta shiga b'are boxer daga cikin leda, shi ya karb'a ya bud'e mata su ya mik'o, da sauri ta juya zatayi toilet a guje yayi maza ya fizgota, had'e rai yayi yace "ban hanaki tsalle ba", ta marairaice tace "toh bazan sake ba", ganin ya tsareta da ido ta fara saka kayan shiko sai mugun smirking yakeyi, baisan lokacin da ya furta "Wow" ba bayan ta gama saka kayan, itakam kasa d'ago kanta tayi ganin y'ar rigar iya cinya, takowa yayi yazo gabanta ya d'ago hab'arta yana kallonta, daidai fuskarta ya sunkuyo yace "You look cute", itakam kasa d'agowa tayi ta kalleshi sai ji tayi ya d'agata yayi gado da ita, a jikinshi ya kwantar da ita ya warware gashin da ya tufke da kanshi ya shiga kwantar mata da gashinta, a hankali ya rad'a mata a kunne "kiyi baccinki", kamar ya sani kuwa bacci ne ke fizgarta, kamin yace komai har tayi bacci a jikinshi, ido ya tsura mata yana kallon tiny figure d'inta dake kwance, ita komai nata k'arami ne, a hankali ya sako hannunshi ta cikin rigarta yana shafa cikinta da yake a shafe tareda lumshe ido yana jin wani exceptional feeling na daban da bai tab'a experiencing ba, da sauri ya d'an d'age rigar yana kallon flat tummy d'inta, wai wannan cikin ne yanzu mutum xai fito a ciki, murmushine yayi escaping lips d'inshi, a hankali ya d'aura lips d'inshi kan cikin nata yayi kissing yace "Fatima can't wait to see our baby, I will love her till my last breath", da sauri ya d'ago kanshi jin yace her, wa yace mishi mace zata haifa, kai ya kad'a yana murmushi yace "I want a baby girl Fatima, just like you", ya kalli Face d'in Batuul dake kwance tana baccinta peacefully ya d'aura yatsunshi kan face d'in nata yace "Including your cute lips Baby", Batuul dai baccinta takeyi bata ma san mey yakeyi ba, a hankali ya gyara zamanshi ya gyara mata kwanciyarta dan taji dad'in Baccin nata, wayanshi ne yaji ya fara ringing amma sabida baccin da ta fara yanzu baya son ya katse mata shi, k'iran na katsewa wani na shigowa, haka aka dingayi mishi har wajen missed calls 8, ganin anqi dena k'iran yasashi jan d'an tsaki ya kwantar da Batuul a hankali ya mik'e ya isa gaban vanity table d'in ya d'auki wayan

A bangaren Ajiddeh kuwa kuka ta dinga risga kamar an aiko mata lbrn mutuwa, ganin kukan ba taimakonta zaiyi ba ta d'auko waya ta shiga neman layin Aliyu, har ya gama ringing bai d'auka ba, bata dena k'iran ba har saida taji an d'auka snn ta fashe mishi da wani matsanancin kuka tareda sakin wani razananne k'ara da ya sashi rintse ido, kuka takeyi sosai ta shiga koro mishi jawabin k'arya da gaskiyan abinda ya had'ata da Farida kuma yazo ya fita da Farida inba haka ba zata bar mishi gidanshi, shi yasan Farida bataji amma bai tab'a kawowa har zata iya yiwa Ajiddeh duka ba, ce mata yayi gashi nan zuwa, kan gadon ya koma yana tunanin barin Batuul ita kad'ai a gidan, gaban desk top d'inshi yaje yayi activating CCTV snn yayi securing gidan, pecking d"inta yayi snn ya fita ya bar gidan, cikin minti kad'an ya isa gida, kai tsaye d'akin Ajiddeh ya isa ya tarar da ita xaune kan gado sai kuka takeyi duk bakinta ya kumbura, nan taci gaba da shirgo mishi k'arya da gaskiya, ba karamin baci ransa yayi ba ya shiga rarrashinta, ganin yadda ranshi ke b'ace ta fara murnan zai yiwa Farida koran kare a gidan, da murna ta biyo bayanshi, k'ofan d'akin Batuul ya tura, Farida na kwance kan gado tana playing Word Crush a wayar Batuul, mik'ewa tayi xaune tana kallonsu duk da yanda gabanta ke faduwa ganin yanayin fuskanshi hakan bai hanata daure fuska ba, ta mike tsaye tace "Yaa Abu tun d'azu fa na dawo ina ta nemanku, ina Besty na take itama bata nan", ta shiga lek'a bayanshi ko zata hango Batuul, sai lokacin ma Ajiddeh tasan Batuul bata gidan ashe, fizgota yayi yace "in the next 5 mins ki tabbatar kin gama tattara kayanki you are going back home", ganin murmushi shimfid'e fuskan Ajiddeh ta had'a rai tayi kamar bataji mey yace ba tace "Yaa Abu kace ta bamu waje zanyi maka magana, bana son gayyar sa ido", wani tsawa yayi mata yace "Ba magana na miki ba?", had'e rai tayi tace "Toh Yaaa Abu mana, nifa hutuna bai k'are ba kuma ni ba wajenku nazo....", wani tsawan da ya daka mata yasa ta razana ta kasa k'arasa maganan, tace "Yaa Abu ni gun Batuul Ammah ta siyamin ticket nazo fa", gnin yana yiwowa kanta yasa ta fasa ihu ta isa wardrobe ta shiga had'a y'an kayanta, Ajiddeh duk da tana murna amma ba haka taso ba, taso ya rama mata dukan da Farida tayi mata yayi mata korar kare, suna tsaye Farida ta shiga had'a kayanta tana hawaye har ta gama tazo ta tsaya gabanshi tace "Toh ina Batuul d'in, mu jira ta dawo sai in tafi", bai kulata ba ya kamo hannunta ya shiga janta har suka sauk'o k'asa, Ajiddeh kam hakan ba k'aramin dad'i yayi mata ba dan dama so take a barta daga ita sai Batuul a gidan, har k'asa ta biyosu tana yiwa Farida habaici, itakam ko kallo bata isheta ba, suna shiga mota ya tada suka tafi.
[10/1, 06:12] 80k: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

76

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Chapter 112 · 0% Book details