Sashe 139
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lukman get the key to my house, right away", daga d'aya b'angaren Lukman ya amsa da "Hokay Sir but which of the Ouses?", "Mississippi Street, you should get there right now, I will soon be there", yace "Hokay Sir Hi will do that", ya katse wayar ya ajiye, kallonta yyi har lokacin hawaye ne idonta ya bud'e baki zaiyi magana kenan suka iso bakin gate,聽 ya mik'owa masu gadin card d'insu ya fita daga harabar Blue cabana, kallo d'aya yayi mata ya maida hankalinshi kan tuk'in da yakeyi, hijabin jikinta taja taci gaba da goge hawayen dake zubo mata, ita da kanta ta rasa hawayen mey takeyi, attention d'in da bai bata bane ya zauna yana danna waya聽 ko kuma matan da ta gani suna magana dashi harda dariya ya sata b'acin rai, wani iri taji da ta tuna da matan har saida gabanta ya fad'i, batayi yunk'urin goge hawayen ba dan ba daina zubowa zasuyi ba, hannunshi taji a fuskarta yasa ya shafo hawayen yana murzasu yana kallonta, a hankali ta sauk'e idonta k'asa, zaiyi magana wayarsa ta fara ringing ya duba ganin mai k'iran yasa ya d'aga tareda cewa "Sorry badai har kun fito ba", daga d'aya b'angaren Massa ya amsa da "Yanzu haka ita na d'auko, baku dawo bane?", d'an siririn tsaki yaja yace "God man am sorry wlhy ba yanzu zamu dawo ba, I had to but am sorry", Massa dake d'aya b'angaren yace "For real?, I told you gobe zata koma Sokoto kuma dan Batuul zata, ita ta tsaya dubawa", Abu yace "I know, I understand, am having issues over here so nake inyi clarifying before getting back home, bawa Rahamar waya muyi magana da ita", Tsaki Massa yaja yace "You are a jerk kaima ka sani ko", dariya Abu yayi yace "Not better than you, d'an bata wayar nikam, da ita zanyi magana ba kai ba", cikin siririyar muryarta tace "Hello", Abu yace "Hey, am so sorry, wlhy abune ya tsaida mu nan kiyi hak'uri, next time har gida zan kawo miki ita ku gaisa kinji", ya juya ya kalli Batuul yaga har lokacin kanta a k'asa yake, a hankali Rahama tace "No fa, ba komai, there will surely be next time, Allah ya bata lafiya ya k'ara mata lafiya", wani irin sanyi yaji har cikin ranshi jin addu'ar da Rahaman tayiwa Batuul da murmushi a fuskarshi yace "Amin ya Allah, sorry once again and Thank you", murmushin tayi itama tace "Ba komai fa", yace "Yawwwa mun gode Allah ya kiyaye hanya", ta amsa da Amin snn ta mik'awa Massa wayan, Abu yace "Ita mai zuwa dubiyan da kanta ta hak'ura, ka dawo goben ka dubata", Tsaki Massa yaja yace "Kaga ni kai ta sani, zan kaita ta gaida Ammah in kuma ka dawo daga gantalin naka ka samemu, fine", Abu yayi dariya yace "kaima zaka fito聽 gantalin ne anytime soon, just get married", Massa yace "My regards to her, kayi mata ya jiki pls", Abu yace "Sure zataji", ajiye wayan yayi ya d'ago kanshi suka had'a ido, da sauri ta d'auke nata idon tana twitching d'an k'aramin bakinta, murmushi yayi ya kamo hannunta yana murzawa a ranshi yace "She will b the death of me", bata yi yunk'urin k'wace hannunta ba kuma batace mishi komai ba, yace "Rahama tace inyi miki ya jiki?, they wanted coming now kuma nace musu bama gida", d'ago kanta tayi tana kallonshi tanaso ya fad'a mata wacece Rahama dan batasanta ba, yayi murmushi ya sak'e damtse hannunta yace "Mustapha's fiance", batace komai ba ido ta lumshe kawai hawayen da ta kasa riqewa na dad'a taruwa,聽 shima bai sake cewa komai ba amma yana riqe da hannunta d'aya yaci gaba da driving d'inshi, bakin wani baqin gate taga sun tsaya, horn yayi aka wangale musu gate d'in suka shiga聽 tunda suka shiga gidan take k'arewa gidan kallo , ba wani babba bane sosai, duplex ne amma yayi kyau sosai, fitowa yayi daga mota, Lukman dake tsaye jingine jikin tashi motar ya k'araso wajenshi, saida ya gaisheshi snn ya mik'a mishi key d'in, Batuul ya hango zaune cikin mota yace bari su gaisa da Madam, Abu ya girgiza kai yace "No Lukman not now okay, next time", Lukman da murmushi fuskar shi yace "Hokay Sir, Hi will leave now", daga haka ya koma motarshi ya shiga ya tafi, Abu ya zagaya ta wajenta ya kamo hannunta sukayi gidan, parlour ne mai girma sosai, sosai tsarin gidan yayi mata kyau, bai sake mata hannu ba har saida ya zauna bakin gadon bedroom d'in gidan dake sama, Wani fridge ya bud'e ya fiddo ruwa roba d'aya kamin ya dawo ya zauna daga gefenta snn yasa hannu ya juyo da ita tana fuskantarshi ya bud'e ruwan ya mik'a mata, a hankali tasa hannu ta karb'i ruwan tasha kad'an, sai kallonta yakeyi yana lumshe ido ya bud'e, Miko mishi tayi yace "Ya isheki?, ta d'aga mishi kai alamar ehhh, shima shan ruwan yayi ya ajiye gefe snn ya rik'o hannayenta duka biyun, wani irin bugawa kawai zuciyarta keyi, a hankali ta lumshe ido, kamar daga sama taji muryanshi yace "Do you need to see a therapist?", bata san lokacin da ta bud'e ido ta kalleshi ba jin abinda yace", wara ido tayi a sanyaye ta fara k'ok'arin janye hannunta ya riqe da k'arfi, rungumeta yyi yana d'an rocking d'insu yace "sorry its okay baza ki ga wani therapist in baki so,", a hankali ta d'ago kanta da wani irin smile fuskarta tace "I look mental huh?, ta goge d'an hawayen dake fuskarta, kai ya girgiza mata ya sake rungumeta yace "ko kad'an Fatima,聽 I just want you to be happy, banason ganinki kina wannan kukan, you barely spend 5hrs batareda kin zubda Hawaye ba, and聽 yana damuna, gani nakeyi kamar ban kyauta miki ba, its hurting me nima", kallonshi takeyi har yayi shiru batace komai ba, yace "Say something, bana son kallon nan, I just want you to be happy, I love you sosai Fatima", kamar yanzu ta fara jin kalmar I love you d'in bakinshi, abin nan da takeji kullum shi taji yauma, a hankali tace "Then why where you ignoring me if so d'azun?", wara mata manyan idonshi yayi yace "Dagaske?, I did that?", kau da questions d'in tayi ta sake cewa "those ladies da suka zauna suna maka magana suna dariya fa?, who were they?", sai yanzu ya lura da kishi ya sata kukan nan, shi sam ya ma manta da dasu wlhy, dariya ya fasheda da ya sake kufular da ita, rai b'ace ta tashi daga kan gadon zata bar wajen yayi sauri ya fixgota ta fad'a kanshi, idonshi yasa cikin nata da yasa tayi saurin rintse su zata mik'e, hannu yasa ya zagayeta ya matseta jikinshi har yana jiyo heartbeat d'inta,聽 cikin wata iriyar murya tace "Nikam let go of me, ba dariya kayi min ba", dariyan ya sakeyi yace "ashe kina kishina tinda har kikayi kuka dan kin ganni da wasu", tsuke baki tayi tana son barin jikinshi yaqi saketa, ya tsagaita dariyan yana k'arewa fuskanta kallo yace "You have changed me Fatima, you have changed me a lot cikin k'ank'anin lokaci, ban tab'a kawo zama ina rarrashin mace ba sai gashi kin sani na fara, I get emotional anytime nayi tunanki", "your eyes", ya d'an hura mata iska a fuska, "your lips", ya fad'a yana zagaye lips d'inta da k'aramin yatsanshi, "your cute chiseled nose", ya fad'i tareda聽 had'e hancinsu, "I like everything about you, duk wani uneasiness da nakeji a da yanzu nasan mesa nake jinshi, inasonki but I couldn't realize", hawaye yaga ya ziraro mata a ido, d'an murmushi yayi yace "Bana son zama sanadin zubar precious hawayen nan pls kinji, anytime nayi miki abu just yell, shout, tell me na b'ata miki rai amma banda kuka kinji?, kuka sosai tasa tana son ta tashi daga jikinshi ya sake matseta yace "fad'amin kukan mey kikeyi?", kasa motsi tayi zuciyanta na tsananta bugu, tsorata yayi jin yadda zuciyanta ke bugu ya mik'e tareda zama yana kallonta yace "Fatima are you okay wai, meke damunki ya Allah?", a hankali kamar mai koyon tace "I... love.... you", kamar wani shigewar iska haka yaji maganan ta daki dodon kunnenshi, kallonta yakeyi yanason tabbatar da abinda yaji ya fito daga bakinta, idonta yake nema ya gani dan ko zai tabbatar mishi da abinda ta fad'an, hab'arta ya d'ago yana kallon fuskarta, sauk'e ido tayi tanajin nauyin abinda ya fito daga bakinta, ta d'auka iya zuciya kad'ai ta fad'eshi saida ta gama furtwa tasan a fili ta fad'eshi, yace "Look at me Fatima, pls", da k'yar a hankali ta iya d'ago kai ta kalleshi, suna had'a ido tayi maza ta kauda nata, wani irin runguma taji yayi mata, tare suka sauk'e ajiyar zuciya, a kunnenta yace "son nawa ne ya saki kukan da kikeyi?", a hankali ta girgiza mishi kai, ya d'agota kamar da damuwa a ranshi yace "Toh mey ke saki kuka?" Cikin sanyin magana tace "The very first day i met you, i know something in me has changed da har uanzu bai koma daidai ba, You came into my life lokacin da banyi zato ba, na d'auka you are just here to snatch my happiness, na d'auka duk wani farin ciki da zanyi ragagge ne tunda ka shigo rayuwata, I never thought I could fall for anyone so easily but then I realised kullum anytime nayi tunaninka, I get emotional, anytime I see you, I feel happy, anytime you come in contact I feel shivers down my spine, that feeling that I can't express, tsoro nakeji Yaa Abu, am scared", ta rik'o hannayenshi duka biyu ta rik'esu da k'arfi, kallonta kawai yakeyi, Batuul ce zaune gabanshi tana expressing mishi son da take Mishi, jiya ya gama expressing mata but bai tab'a kawowa kanshi anytime soon Batuul will fall for him, ta fad'a mishi itama heartbeat d'inta is聽 never stable when ever they are close amma ya d'auka tsoronshi ne duka ya janyo hakan, ya sake damtse hannunta ya sunkuyo yana kallon fuskarta yace "Kalleni, mey ke tsorataki, tsoron mey kikeyi when you have me?", ido ta lumshe ta bud'e tayi d'an murmushin jin dad'in abinda yace, mey zai bata tsoro bayan tana dashi, ajiyar zuciya ta sauk'e da