← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 166

Sashe 46

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

kai tace "Ammah Ya Abuu fa ba shiri suke da Batuul ba, ga kuma matarsa masifaffiya muguwa, Batuul baxa ta iya masu ba cutar ta kawae xa su yi tayi gashi ba kowa gare ta can ba, don Allah ku canxa shawara ko cikin family can Maiduguri ki samu dai dai Ajiddehn a aura masa" tsaki Ammah tayi tare da maka mata harara tace "Toh naki yin hkan, da Batuul kadae xuciyata ta Aminta a hada Aliyu, uwar me Jiddahn xata yi mata wanda Allah bae mata ba, shi kuma Abuturrab din idan aka aura masa ita yyi gunduwa gunduwa da ita ya maido mana," mikewa farida tayi har lkcn tana hawaye ta fita daga dakin. Xaune ta ga Abuturrab dakinta ya rike kai da dukkan alama ita yake jira, yana ganinta kuwa ya mike da sauri ya karasa ya kamo hannunta suka xauna gefen gado yace "In tambaye ki farida, wae wnn kawar taki or wat ever ita tace tana son aurena?" Shi kansa jin tambayar yyi wani banbarakwae a baki don yasan Batuul baxa ta taba cewa tana sonsa ba, he is just confuse, farida ta girgixa kai tace "I don't think Batuul tasan da xancen ma, don daxu ta kirani tana ban hkurin xuwan da bata yi yau ba," ya fuzar da iska yace "Do me a favour little sis, don Allah ki xiga ta a kan kar ta amince nasan dae in har tace bata so baxa a mata dole ba" farida tace "Shknn I will try my best, but ni baxan mata magana kai tsaye ba sae in ita ta kawo xancen don ga dukkan alama bata san abinda ke faruwa ba ma" mikewa yyi rai ba ddi ya fice daga dakin. Batuul na xaune dakin Anty duk hankalinta ya tashi ganin ynda uwar tata ke hawaye gashi ta ki gaya mata abinda ya faru, ae bata san lkcn da ita ma ta saka kukan ba tana durkushe kusa da Anty, da kyar Anty tayi controlling kanta ta shiga lallashinta sae dae ta k'asa gaya mata dalilin kukan nata don bata san ynda 'yar tata xata dauki xancen aurenta da Abuturrab ba, bude kofar dakin aka yi Ahmad ya shigo da sallama sae dae ganin ynda Batuul ke kuka hankalinsa ya tashi ssae don xuwa lkcn Anty ta daina nata kukan, hankali tashe ya shiga tambayar Anty abinda ya faru, Anty tace "kanta ke ciwo wae shine take kuka, ya aka yi Ahmad?" Ahmad ya durkusa kusa da Batuul yana mata sannu, sae da Anty ta kuma tambayarsa ya aka yi snn yace "Yayya ce tace in kira ta, kuma gashi kanta na ciwo bari kawae inje ince she's not okay" har ya mike Anty ta dakatar da shi tace "A'a bari xata je, ae ta sha magani" tayi hkn ne gudun wani maganan don har ynzu xuciyarta bae yi sanyin abinda yayya tayi mata daxu ba daga tace ita Batuul baxa ta auri mai mata ba in ma aurar da ita ake son yi gwara ta fito da saurayinta kawae, nn fa Yayya ta dinga xaxxaga mata ta inda take shiga ba nn take fita ba, mikewa Anty tayi daga karshe ta bar mata falon, shine tun lkcn take kuka a daki har Batuul ta shigo ta sameta. Kallon Batuul tayi tace "Tashi ki je Batuul" ba musu Batuul ta mike tana share hawayenta ta fita. Yayya na kishingide tana cin Apple, Baba na xaune daga gefenta ya tankwashe kafa suna magana da kanuri, k'arasowa cikin dakin Batuul tayi sae dae bata da walwala don tasan Yayya ce ta bata ma Anty rae ko bata fada mata ba, Xama tayi dan nesa da su tace "Ga ni Yayya" Yayya ta tabe baki ta mike xaune da kanuri tace "Wato har uwar taki ta xuge ki shine xaki wani shigo ma mutane ko sallama bbu, kin wani hade rae koh" Baba dae bae ce komai ba kansa na kasa, Yayya ta ci gaba da cewa "Toh auren Aliyu dae bbu fashi wllh, yaro d'an arxiki mai asali gaba da baya, waye bae san kakansa ba a Maiduguri?" Xumbur Batuul ta mike xuciyarta na wani mugun bugun da bae taba yi ba har wani rawa jikinta ya shiga yi tana kallon Kakar tata tace "Ban gane ba Yayya" da kanuri Yayya tace "Ohh ke da duk baki san abin da ake ciki ba, toh ae shirye shiryen bikin ki ake da Aliyu jikan Kyari, wato d'an wajen Ahmad" Batuul ta xaro ido cikin kidemewa tace "Ni Yayya?" Ae bata jira cewar Yayya ba ta fice da gudu daga dakin ta nufi dakin Anty, Har lkcn Anty na xaune ta xuba tagumi, ta xube jikin uwar tata cikin rawan Murya tace "Anty ban gane abinda Yayya take gaya min ba ynxu," K'asa cewa komae Anty tayi tana kallonta, hkn yasa Batuul ta fashe da wani matsanancin kuka tace "Wayyo Na shiga uku Anty, wae Ya Abuu ake cewa xan aura, ni ban gane ba" Rungume ta Anty tayi sae dae she's lost of words. Bayan Magrib Abuturrab na xaune daki abun duniya ya ishesa duk ya rasa tunanin da xae yi farida ta shigo tace "Ya Abuu Ammah na kiranka" mikewa yyi yace "kin yi abinda nace maki farida?" Farida tace "Ya Abuu bata fa ce min komai ba har ynxu, meaning she is still unaware, ni kuma baxa ta soma jin komai a bakina ba ka bari..." ficewa yyi daga dakin ba tare da ya tsaya jin sauran xancen nata ba, dakin Ammah ya shiga ya sameta tana waya, ya xauna har ta gama snn yace "Gani Ammah" Ammah tace "Dama cewa xanyi ka shirya kaje can gidansu Batuul ka gaida Yayya, ta shigo tun da rana" rasa me xae ce da ita yyi don bae son bacin ranta, da kyar yace "Toh Ammah" daga hka ya mike ya fita hankali tashe yasan shknn wani ikon Allah kawae xae hana a manna masa Batuul, wae for God's sake me suke son yyi da 'yar yarinyar nn?? Ya ma xae fara tunkarar Ajiddeh da wnn xancen, da kyar ya iya shiryawa ya dauki makullin motarsa ya fita daga gidan. [8/22, 2:05 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐
Chapter 46 · 0% Book details