← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 166

Sashe 142

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

聽 聽 聽 聽 Da asuba shi ya fara tashi, bai tada Batuul ba dan yasan bacci bai wani isheta ba, kwanciyarta ya gyara mata snn yayi wanka ya zira jallabiya ya fesa turarukanshi masu sanyin k'anshi ya fita zuwa masallaci, a masallaci ya had'u da Abui da Sadiq, Bayan an idar da Sallah snn suka gaisa, Abui yana tambayanshi ya jikin Batuul ya amsa mishi da "Alhamdulillah taji sauk'i", Sadiq ma ya gaisheshi yayi mata ya jiki daga haka suka shigo gida kowa yayi side d'inshi, a hankali ya turo k'ofar d'akin,聽 da mamaki ya kalleta ta kunna bedside lamp tana zaune kan abin Sallah riqe da Qur'an tana karanta Suratul Qasas cikin muryarta mai dad'i, Ido ya lumshe ya bud'e snn ya shigo d'akin tareda mai da k'ofar ya rufe, tunda yake da Ajiddeh bai tab'a ganin ta tashi Sallah batareda ya fad'a mata ba, ko ya fad'a sai lokacin da ta ga dama take tashi tayi, da sauri ya kawar da tunanin Ajiddeh yayi da sauri, daga gefenta yazo ya zauna, godiya ya dinga yiwa Allah cikin ranshi da ya bashi Batuul, a zuci yana bin duk ayoyin da take karantawa, kamar yau ya fara jin Qissoshin Annabawa dake cikin surar jin yadda take karanto shi, har saida tayi kusan rabi snn ta rufe ta shafa addu'o'inta ta maida Qur'anin kan bedside drawer, a hankali ta juyo ta kalleshi tace "Ina kwana", wani farin ciki yakeji a ranshi da ganinta, ji yakeyi kamar ya d'auketa ya kaita wajen da babu kowa, inda babu abinda zai sameta sai farin ciki, ido ta d'an wara ganin yana kallonta bai amsa mata gaisuwarta ba tace "Yaa Abu ina kwana", sai lokacin ya lumshe ido ya bud'e yace "Waye malamin da ya koya miki Qur'an?", cike da farincikin tuna mata malamin da baza ta tab'a mantawa dashi ba tace "Malan Ahmad shine malami na, mey yayi?", ta fad'a tana d'an yatsina fuska yace "Har Tajweed duk shi ya koya miki?", ta kad'a kai tace "Har komai ma shi ya koya mana dukkanmu dasu Ahmad da Sa'eed", yace "Ya complete sunanshi yake and yana ina yanzu?", tunanin mesa yake son sani a hankali tace "Sunanshi Ahmad Abu Hamira Daiba, su Ahmad sun san聽 inda yake, nasan har yanzu yana koyar dasu", a hankali ya janyota jikinshi yayi wrapping duka hannayenshi jikinta yace "In na bashi kujerar Hajj da Umara this year yayi?", da sauri ta shiga k'ok'arin juyowa taga dagaske yake nufin abinda yake fad'i amma bai saketa ba saima k'ara gyara mata zama da yayi ya d'aura fuskanshi kan wuyanta, duk da hijab a jikinta bai hanata jin d'umin numfashinshi dake sata jin wani a iri a jikinta ba, da k'yar ta iya bud'e baki tace "Dagaske?", yace "Kuma a bud'e mishi Tahfeez, inaso in princess ta girma ya koya mata", ya fad'a tareda sauk'e聽 hannunshi kan cikinta, "Inaso in ta girma itama tana min irin k'ira'arki", wani irin juyawa tayi ta rungumeshi sosai, yana jin yanayin bugun zuciyarta, shima d'in sake rik'ota yayi, kamar mai jin tsoron abinda zata fad'a tace "I love you", ido ya lumshe ya bud'e yana jin kamar kullum ta zama magana da zata fito daga bakinshi, ta d'ago da sauri tana kallon fuskarshi tace "Yaaa Abu tun yanzu ka fara sani farinciki, am scared yayi min yawa and mayb you might change nan gaba", kallonta kawai yakeyi for seconds ya kasa ce mata komai, da k'yar ya iya samu yace "Baki yadda da son da nake miki ba ko?, baki yadda I can forsake duk wani farin ciki nawa for you to be happy ba ko?", kunya ce taji ta kamata, lafewa tayi jikinshi hannunta kan k'irjinshi tana jin yadda yake heaving a hankali tace "Na yadda, bana so ne yayi min yawa", bakinshi ya d'aura kan nata ya rufe mata baki, saida ya d'ago yace "You deserve all happiness, ki kwantar da hankalinki kinji, you have got me for yourself", shiru tayi lafe a jikinshi, d'agata yai cak ya kwantar kan gado yace "You need sleep, kwanta kiyi bacci", ya shiga k'ok'arin cire mata Hijab d'in dake jikinta zai gyara mata kwanciya, kai ta girgiza mishi tace "Yaaa Abu da sanyi, I don't want to remove the hijab", bai ce mata komai ba har saida ya cireshi sannan ya rungumota jikinshi ya ja musu duvet yace "I will keep you warm", murmushi kawai tayi tana tuna ranan da sukaje gidanshi a London yanda yayi keeping d'inta warm har ta gama duk abinda zatayi, a hankali ta matsa jikinshi ta gyara kwanciyarta, cikin kunnenta ya rad'a mata "are you still cold?", juyowa tayi tana fuskantarshi da kyau tace "Will you always keep me warm all the time?", ya saka hannayenshi duka biyun yana zagayeta yace "Always and forever", daidai lokacin ta tuna da Ajiddeh, tana son ta tambayeshi ina take tana tsoron kada ya sake mata fad'a kamar na ranan, a hankali taji yace "Yaushe zamu koma gida?", idonta a lumshe batareda ta bud'esu ba tace "Nanfa?", yace "This is Ammah's house", ta zumb'uro baki tace "Ni I want to stay here", yace "No gidanki kuma fa, wa zai zauna ciki?", tace "Inada gida ne ni?, d'ayan ai gidanta ne, d'ayan Kumar kace na love of your life ne", dariya yayi yace "So baki manta ba?", tureshi tayi daga jikinta tace "Ni kam ka dena min dariya, a nan zan zauna", yace "Toh bud'e idonki in fad'a miki wacece love of my life d'in?", kamar yana ganinta ta murgud'a mishi baki, juyo da ita yayi yace "Plsss mana, ki bud'e idonki in fad'a mki gidan waye?", a hankali ta bud'e idonta suna had'a ido tayi maza ta rintse su, dariya yayi ya d'agota yace "Fatima get up and listen, gidan nanfa nakine, I built it for the woman I will love, I designed everything for her, banida ra'ayin k'ara aure, I want to live with just a single wife and then Allah yayi Hauwa baza ta zauna gidan ba, then it was you, tun lokacin da akace zan aureki a raina nasa gidan zai zama naki, I then programmed everything ya koma naki, censor and all but God so kind you turned out to be the love I wanted, the love I wanted to give and take and there the house is yours, kinga sai mu koma ko tunda kinada gida, only I and you have access to wannan gidan", jin shirun yayi yawa a hankali ya k'ira sunanta bata amsa ba, da wayarshi ya haska yaga bacci take, murmushi yayi tareda pecking goshinta ya gyara mata kwanciya suka kwanta bacci
Chapter 142 · 0% Book details